Kenza eBookz

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 28

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 28

Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com Chapter 28: Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by…

4,487 words

Sama-sam TAIMIYYAH ke sauraren Iyah dake ta bata labarin kirkin Hajiyar da suka kaɗe ta,tare da sanar ita cewa Hajiyar tace zata dawo gobe ta sake duba jikinta.

TAIMIYYAH jin Iyah kawai take yi amma sam bata yi magana ba,sai ma wani baccin da taji yana fisgar idanunta ba a jima ba kuwa ta ɓingire ta bar Iyah na ta surutunta ita kaɗai.........✍🏻

#Ɗansabo ce# [12/14, 10:11 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*

*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.

*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*

Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.

_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_

*49*

Washegari ƙarfe takwas da rabi na safe Baba Sani ya taso su Zuhura da Basmah ɗauke da kayan breakfast suka iso asibitin.Sun kuma tadda TAIMIYYAH ta taahi daga bacci,kuma ikon Allah garas ta tashi babu inda tace yana mata ciwo. Zuhurah suka gaida Iyah tare da tambayarta me jiki ta basu amsa da cewa, "Alhamdullillah! Ta samu sauƙi zuwa anjima kaɗan ma sai gida Insha Allah."

Baba Sani da ya isa gaban gadon da TAIMIYYAH ke kwance idanunta a buɗe tana jin duk abinda ake faɗi,isowan Baba Sani wajenta yana mata sannu yasa ta yinƙurawa ta tashi zaune,Baba Sani ya kama hannunta ɗaya yana ɗagota sosai ta zauna yana tambayarta ya jikin nata? Ta ɗaga manyan idanunta ta dubesa da ɗan guntun murmushi saman face ɗinta take gaida shi tare da bashi tabbacin ta samu sauƙi, ya shafa kanta yana faɗin, "Masha Allah Zaynab Allah tsare sai a dinga kulawa da kyau kinji ko?"

TAIMIYYAH ta gyaɗa kai a hankali tana faɗin, "Insha Allah Baba." Ƙarisowan su Zuhura suna mata sannu yasa ta dubansu tana amsawa,idanunta akan Basmah wacce rabon da TAIMIYYAH ta sanya ta a ido tun randa suka haɗu ta ganta tare da Nass. TAIMIYYAH tayi saurin ɗauke kai daga duban face ɗin Basmah tana jin can ƙasan zuciyarta wani abu na motsawa. Iyah ce tace wa TAIMIYYAH ta tashi ta je tayo brush don ta samu ta karya ta sha magunguna.Babu musu TAIMIYYAN ta sakko daga kan gadon ta nufi toilet,tana jiyo su Baba Sani na ma Iyah sallama zasu wuce,Iyah ta raka su bakin ƙofa tana sanar da Zuhurah cewa da sun isa gidan, ta shiga Sasanta ta sanar da Babah Ladi kar tayi wahalan yin abin karyawa tunda ga shi sun kawo.

TAIMIYYAH bata wani jima sosai ba cikin toilet ɗin ta fito,idanunta akan Iyah da ke zuba abinda zata ci cikin plate.Ta ƙariso bakin gadon tana gaida Iyah,Iyah ta amsa tana cewa, "Sannu ya jikin naki kan dai ya daina ciwon ko?"

TAIMIYYAH ta gyaɗa kai tana cewa, "Eh babu inda ke min ciwo sai wajen da akai ɗinki a gefen wuyarnan ne kawai ke ɗan damuna."

Iyah ta dubeta da kulawa tana cewa, "Ayyah! shi ma ɗin zai bari kin san abu a maƙarfafa dole kiji ya dameki,da zaran zaren ɗinkin ya fita shikenan zaki samu sauƙi, sannu bari in zuba miki abincin ki ci, zaki sha tea ɗin ne in haɗa miki babu madara ko kunun zaki sha gashi nan sun haɗo da kunu?"

TAIMIYYAH ta ɗan ɓata face kaɗan cike da ƴar shagwaɓa take cewa, "A'a Iyah ni ba zan sha kununsu ba haɗa min tea ɗin kawai,amma zallah milo zaki samin ko sugar kar kisa inba haka ba zan ji ina jin amai ne da xaran na sha."

Iyah ta jinjina kai tana yin duk yadda TAIMIYYAH ta buƙata.Bayan duk ta kammala zuba mata soyayyen dankali da egg ɗin ne, ta haɗa mata tea ɗin tana ɗaukan plate da kofin tea ɗin ta kai mata kan gadon ta aje.

TAIMIYYAH ta fara cin abincin a hankali tana ji gaba ɗaya bakinta babu ɗanɗano sabida muran da ke son kamata.Dama ta san tunda ruwa ya doke ta sai tayi wannan muran, zazzaɓin ma don ta amsa allura da magungunan da take sha ne da yanzu ta san tana kwance sosai.

Suna tsaka da karyawa daga ita har Iyah dake zaune daga ƙasa saman babbar dadduma, suka jiyo sallama daga bakin ƙofan shigowa ɗakin. Iyah ce ta amsa tana bada izinin shigowa don taso ta gane muryan kamar na Hajiyar jiya ce wacce suka kaɗe TAIMIYYAH.

Hajiya Aysha da Dattijiyar me aikinta Babah Rabi suka turo ƙofar suka shigo bayan Iyah ta amsa sallamr tasu da basu izinin shigowa,Babah Rabi hannunta riƙe da ƙaton kwandon ɗaukan abinci. Cikin fara'a Iyah ke musu barka da zuwa tana me nunawa Hajiya kujera ta zauna,ita kuma Babah Rabi ta samu saman daddumar da Iyah ke kai ta zauna.

Hajiya Aysha memakon ta zauna sai ta nufi bakin gado kai tsaye wajen TAIMIYYAH,wacce tun shigowansu ta tsaida cin abincin da take yi.

"Sannu Zainab ya jikin naki,ina fata dai babu wata matsala ko?"

Hajiya Aysha tayi tambayar idanunta akan TAIMIYYAH data ɗan sadda kanta ƙasa,kafin ta ɗago manyan idanunta ta sauke akan fuskar Hajiya Aysha da ke jifanta da murmushi. TAIMIYYAH tayi ƙasa da muryarta tana gaida Hajiya Aysha tare da bata tabbacin taji sauƙi babu wani matsala. Hajiya Aysha ta jinjina kai tana cewa, "Masha Allah,Allah ya ƙara lafiya ya tsare gaba kyakykyawar ɗiyata."

Yadda tayi maganan cike da kulawa yasa TAIMIYYAH dubanta da murmushi tana amsawa da cewa, "Ameen Hajiya na gode."

Daga haka Hajiya Aysha ta koma wajen Iyah suna sake gaisawa, ita kuma Babah Rabi ta isa wajen TAIMIYYAH tana mata sannu.Iyah ta dubi uban kayan da suka kawo tana cewa, "Haba Hajiya ya da wannan ɗawainiya haka mu da za a sallama nan bada jimawa ba,wallahi da baku yi wahalan kawo komi ba, an gode ƙwarai Allah ya fi mu yabawa ya saka da alkhairy sannu da ƙoƙari."

Hajiya Aysha ta jinjina kai tana duban Iyah da murmushi take cewa, "Haba Hajiya babu komi ai abinda duk ya dace ne ayi ake yin,Allah dai ya ƙara mata lafia ai na ga jikin nata Alhamdulillah."

Iyah da fara'a take baiwa Hajiyar tabbacin jiki fa Alhamdulillah! Kafin ta miƙe ɗauke da flask ɗin ruwan xafi ta nufi toilet don haɗawa TAIMIYYAH ruwan wanka.

"TAIMIYYAH ta shi ki je ki watsa ruwan ɗumi a jikinki ko kya sake jin daɗin jikin,kafin mu koma gida kiyi wankan me sosai."

Iyah ce tayi maganar lokacin da ta fito daga banɗakin idanunta akan TAIMIYYAH, wacce zuwa lokacin ta zame ta kwanta lamo kamar ta koma bacci.

Jin maganar da Iyah tayi yasa ta tashi tana ɗan zumbure baki alamun bata son yin wankan,uwa uba su Hajiya da ke zaune a ɗakin wanda haka kawai take jin nauyin matar.Amma babu yadda ta iya haka ta sakko daga kan gadon idanunta a ƙasa,sam bata yadda ta dubi inda suke zaune ba amma tana jin idanunsu ya yawo akanta.

A hankali ta kai hannu ta dafa guiwar ƙafarta tana tafiya zuwa hanyar banɗakin ta shige,Hajiya Aysha da me aikinta Babah Rabi suka bi TAIMIYYAH da kallo Hajiya Aysha na jin wani abu na ratsa zuciyarta akan Yarinyar.

Ta maida dubanta kan Iyah lokacin da TAIMIYYAH ta ɓacewa ganinta tana cewa, "Hajiya wannan Auta taki ba dai kyau ba,gata komi nata cikin sanyi da nutsuwa take yinsa,amma wannan laluran ƙafar a haka kika haifeta da shi ne?"

Iyah ta saki murmushi me faɗi tana duban Hajiya Aysha take faɗin, "Ko ɗaya Hajiya wallahi bada shi aka haifeta ba daga baya ne Ubangiji ya aiko da lalurar,ta fara tafiyarta tana yawo ko'ina sai zazzaɓi dare ɗaya, washegari daga yin allura ƙafa ya saki shikenan mafarin sanadin ƙaddaran shanyewan ƙafar da akai ma allurar,mun sha fama sosai kafin ma asamu ta fara takawa da taimakon dafa guiwar ƙafar...."

Iyah ta cigaba da bayyanawa Hajiya Aysha yadda suka ci wuya akan laluran ƙafar TAIMIYYAH,kafin a samu ta fara takawa da ƙafar a haka yadda take tafiya.Ta cigaba da faɗin,

"Amma kin ga cikin ikon Allah da taimakon dafa guiwar nan da take tana takawa babu abinda bata iya yiwa kanta,tana harkokinta komi babu abinda ke gagararta sai kaɗan daga manyan abubuwan da dole sai an taimaka mata,amma tana da ƙoƙarin ayyuka da son yin komi da kanta bata ma so ace za a yi mata abu inba gagararta yayi ba."

Hajiya Aysha ta jinjina kai tana cewa, "Allah sarki haka Ubangiji ke ikonsa nata ma da sauƙi ai tunda tana yawonta ko'ina da ƙafar a haka,wasu a keken guragu ake turasu,wasu basa ma jirgawa ko'ina sai da taimakon jan gindi,sai a godewa Allah bakomi nakasa so da yawa wani baiwar ne,mutane ne kawai ke nasu shirmen ki ga ana nuna musu bambamci da kyaran su a wasu lokutan,ita dai Zainab gashi an mata baiwar kyau da nutsuwa ,lokaci ɗaya na ji ta shiga zuciyata Hajiya,ina fata dai tayi karatu ba a tauyeta ba an ƙi sakata a makaranta?"

Hajiya Aysha tayi magana idanunta akan Iyah da ke faman murmushi,kafin ta fara faɗin, "Aiko dai Hajiya tayi karatunta sosai don ma wannan yajin aikin da malaman makarantun jami'a suka tafi ne yasa bata cigaba daga NCE da ta kammala ba,amma yanzu haka ma wani makarantar Computer take zuwa,a islamiya ma tayi sauka ta sauke har da manyan littafai,sai makarantar haddah da ake daf da yayesu sun kusa kammala haddar Qur'ani baki ɗaya,ina ga bazai ma wuce nan da sati uku ba za a yaye su."

Iyah ta kai ƙarshen maganar dai-dai lokacin da TAIMIYYAH ta fito daga banɗakin,tana ɗaure da zani a jikinta ta yafo rigar data cire akan kafaɗunta. Hajiya Aysha ta bita da ido tana cewa, "Kai Masha Allah,Allah yayi wa rayuwarta albarka ya bata mijin aure na gari wanda zai riƙe ta da amana."

Iyah ta amsa da cewa, "Ameen." Ita dai TAIMIYYAH tuni ta isa bakin gado ta zauna duk kunya ya isheta tunda ta fahimci hiranta suke yi,cikin sanyin murya ta dubi Iyah tana cewa, "Iyah kayan fa baki ciro min ba."

Iyah sai ta tashi ta isa wajen jakan da ta sanyo musu kaya ta cirowa TAIMIYYAH doguwar rigar atamfa,ta haɗa da man shafawarta da ta zo mata dashi ta kai mata bakin gadon ta aje.

TAIMIYYAH sai ta ɗauka kayan da man ta koma banɗakin don shiryawa,sabida ba za ta iya shiryawa akan idanun su Hajiya Aysha wacce bata iya ɗauke ido daga duban TAIMIYYAN.

Komawar TAIMIYYAH xuwa banɗakin ya saka Hajiya Aysha cigaba da hiran su da Iyah akan masu lalura iri-iri,cikin hiran ne Hajiya Aysha ke tambayar Iyah bayan TAIMIYYAH tana da wasu yaran ne? Iyah tayi murmushi tana cewa, "Hajiya kenan wannan ɗin ma ba ni ce na haifa ba jikata ce ƴar wajen ɗana,mahaifiyarta ta rasu tun tana cimman goyo ni na raineta har kawo yanzu,kuma cikin hukuncin Ubangiji wata ɗaya da wasu kwanaki kenan da rasuwan mahaifinta da ƙanninta su biyu duka rana ɗaya ajalinsu ya sauka...

Iyah ta baiwa Hajiya Aysha labarin yadda mutuwarsu Abie ɗin ya kasance,ta ƙare maganan da cewa, "Yanzu bata da uwa bata da uba sai ni da ƙanin mahaifinta kawai mu ne gatanta, ko fuskar uwarta bata sani ba sai a hoto, yadda kika ganta haka uwar take har kyawun duk na uwarce ta ɗakko,da sanyin halin da komi babu inda tabar marigayiya Zainab TAIMIYYAH.Dama kuma sunan uwar aka saka mata shiyasa muka cigaba da kiranta da TAIMIYYAH yadda ake kiran marigayiyan."

Hajiya Aysha ta jinjina kai wasu hawaye na taruwa a idanunta,na tsananin tausayin TAIMIYYAH da taji ya cika zuciyarta.Shiyasa lokacin da TAIMIYYAH ta fito daga banɗakin Hajiya Aysha ta zuba mata ido,tana sake gano kyawun TAIMIYYAN tare da jin wani ƙaunarta me tsanani na ratsa zuciyarta,tana cigaba da jinjina ƙudiran Ubangiji me yin yadda ya so a kuma lokacin daya ga dama.

TAIMIYYAH ta wuce su a kunyace zuwa kan gado ta zauna,bayan ta aje kayan data fito da su a ninke daga bakin gadon.Ta warware ɗankwalin kayan tana rufe kanta zuwa ƙirjinta da shi,tana me zamewa ta kwanta ta juya musu baya sabida yadda take jinta a takure musamman kallon da Hajiya Aysha ke bin ta da shi.

Shigowar Likitan ɗakin yasa TAIMIYYAH sauke ajiyar zuciya tana fata ya kasance sallamace,aiko cikin sa'a yana sake duba jikinta yayi mata ƴan tambayoyi ta bashi tabbacin babu wani damuwa,sai ya juya yana wa Hajiya Aysha da Iyah magana akan cewa shikenan yanzu zasu iya tafiya gida.

Dama already an riga anyi clearing bill tun jiya,sai kawai Iyah ta ɗaga waya ta kira Sani akan ya zo su wuce zuwa gida an sallame su.

Bayan ta kira Sani driver sai ta kira Baba Sani shi ma ta sanar da shi,ita dai TAIMIYYAH na daga kwance har lokacin tana sauraran Iyah.

Hajiya Aysha ta dubi Iyah tana cewa, "To Hajiya bari mu amsa lambar wayan juna ko a dinga zumunci,kuma Insha Allah zan zo har gida idan an kwana biyu in sake duba jikinta,don gaskiya wannan ɗiya ta shiga raina matuƙa da gaske."

Iyah ta saki murmushi cike da jin daɗin kalaman Hajiyan tace, "Aiko ya kamata kam mu amsa lambar juna Insha Allah za a riƙa gaisawa akai-akai,idan bikin walimar gama haddarsu ya tashi ma, kin ga saina sanar miki ki zo mana bikin walimar,ga wayata sai ki sanya taki lambar idan kika kira sai duk mu yi saving."

Hajiya Aysha ta amsa wayar Iyah ta sanya lambar ta kira, kiran na shigowa ta kashe tayi saving number ɗin tayi ma Iyah itama saving nata numbar.

Ta miƙawa Iyah wayarta tana takawa zuwa bakin gadon da TAIMIYYAH ke kwance,ta tsaya kusa da ita sosai tana cewa, "Ɗiyata tashi zaune muyi magana kinji, ki bar jin kunya ta ni yanzu zumunci nake so mu ƙulla nima ki ɗaukeni kamar Iyar taki kinji ko?"

TAIMIYYAH ta tashi a kunyace tana murmushi kafin ta buɗe baki cikin sanyin murya take cewa, "To Hajiya nagode da kulawa Allah saka da alkhairy."

Hajiya Aysha ta amsa da, "Ameen Zainab Allah ƙara miki lafiya,yanzu ga wayata nan saka min number ɗinki zan dinga kiran ki,ke ma kuma sai ki dinga nemana a waya muna gaisawa."

Tayi maganar tana miƙawa TAIMIYYAH wayarta me nauyin kuɗi tamkar ba Dattijiya ba,inji TAIMIYYAH cikin zuciyarta lokacin da wayar ya je hannunta. Ta loda lambobinta tana miƙawa Hajiyar wayar don tayi saving da sunan da take so. Hajiya Aysha ta amsa wayar ta yi saving sukai sallama da TAIMIYYAH akan cewa sai ta ji kira,daga haka ta juya zuwa wajen Iyah suna magana. Babah Rabi kuma ta miƙe don ɗaukar kwandon abincin da suka zo da shi wanda ba a taɓa komi ciki ba,sai Hajiya Aysha ta hanata tana cewa, "Babah Rabi aje kawai su tafi da shi gida,tunda har mun zo da shi ba za mu koma da abinci gida alhali wacce aka shirya domin ta bata ci ba,gwara su je dashi duk randa Allah ya nufa na samu lokaci na je gida sake duba ta sai na amsa kulolina."

Iyah dake saurarensu tana jinjina karamci da mutuncin wannan Hajiya sai ta riƙe haɓa tana cewa, "Ayi haka Hajiya ai ɗawainiyar tayi yawa,da kun koma da shi bakomi wallahi mun gode matuƙa."

Hajiya Aysha ta girgiza kai tana cewa, "Gaskiya Hajiya ba za a koma da abinci TAIMIYYAH da aka yi dominta bata ci ba."

Hakanan Iyah ta haƙura suka bar kwandon abincin,ta tafi yi musu rakiya zuwa bakin mota. Ita dai TAIMIYYAH iyakarta bakin ƙofa Hajiya Aysha tace ta koma ta gode da rakiyan ta yafe,Iyah dai sai da ta ga tafiyarsu sannan ta juya zuciyarta na jinjina kirki da karamcin wannan Hajiyar, wacce basu san hakiƙanin wacece ita ba. Amma dai daga yanayin shigar da ke jikinta zuwa ƙatuwar motar da ake janta aciki ya tabbatarwa Iyah cewa akwai masu gidan rana a tattare da Hajiyar wato (Kuɗi).

Tafiyar su Hajiyar bada jimawa ba Sani ya iso shi ma,suka tattara yanasu-yanasu Sani ya kwashi kaya da basket ɗin abinci zuwa mota. TAIMIYYAH ta sakko tana zura hijab ɗin da Iyah ta aje mata suka fito tana takawa a hankali har zuwa wajen mota. Iyah sai da ta tabbatar basu manta komi ba sannan ta fito daga ɗakin ta nufo wajen motar,tana shiga Sani ya tada motar suka baro asibitin zuwa gida..........✍🏻

#Ɗansabo ce# [12/14, 10:11 PM] +234 703 769 7050: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.

Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*

*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*

Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.

_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._

*50*

Motar Sani na shigowa cikin gidan ita kuma Umma na fitowa daga Sasan su, hakan yasa ta nufi wajen motar Sanin kai tsaye don gaida Iyah da yiwa TAIMIYYAH sannu da jiki kada tayi laifi wajen Iyah.

Bayan sun gaisa da Iyan ne ta dubi TAIMIYYAH wacce ta fito daga cikin motar ta furta, "Sannu Zainab Allah ƙara lafiya,sai ki dinga kula tunda kinsan kina da matsala ki daina abu irin na masu lafiyan ƙafafu."

TAIMIYYAH ta jinjina kai kawai ba tare da tace komi ba tayi gaba abinta,Umma ta bi bayan TAIMIYYAH da harara tana taɓe baki.Iyah ita gaba ɗaya hankalinta ma na kan Sani da ke sauke kayan da suka dawo da shi ne,sai daga baya ta dubi Umma lokacin da Sani ya aje kwandon abincin da su Zuhurah suka kai asibiti tana cewa, "Yauwa Zuwaira sai ki wuce da ragowar abincin aba masu ci,kin ga wani nan ma ko taɓawa ba a yi ba Hajiyar da suka kaɗe TAIMIYYAH ce ta kawo asibitin."

Umma ta dubi tsadaddun kulolin da ke cikin basket ɗin zuwa shi kansa basket ɗin da ke ɗauke da kulolin abincin,wanda kana kallo kasan ba ƙananun kuɗi ne suka saye shi ba, ta wani taɓe baki tana cewa, "Allah sarki ashe dai mutanen kirki ne da wasu ne fa guduwa za su yi Iyah."

Iyah ta tamke face tana faɗin, "To su Allah bai sa haka suke ba,mata ce me mutunci da sanin darajan ɗan adam,duk arziƙinsu bai sa ta kasance me wulaƙanta halittan Ubangiji ba."

Umma da tuni ta fara jiyo ƙamshin jirwaye cikin maganar Iyah sai tayi saurin ɗaukar basket ɗinta tayi gaba tana cewa, "To Iyah Allah ƙara sauƙi bari in miƙa kwandon ciki nima fita zanyi na ga dawowar ku nace bari in tsaya mu gaisa."

Iyah ta taɓe baki tana cewa, "To madallah." Daga haka tayi gaba abinta Sani na biyo bayanta da kayan zuwa ciki.

Tuni TAIMIYYAH ta isa ɗaki bayan sun gaisa da Babah Ladi da tai mata ya jiki,tana isa kan gado ta nufa ta zauna tana sauke numfashi. Bacci-bacci take ji a idanunta shiyasa ta miƙe ta jona wayarta a caji ganin a kwai wuta,ta baro wajen tana nufan wajen kayanta ta ciro wata doguwar riga me taushin jiki,ta cire na atamfar jikinta ta sanya wanda ta ciro ɗin. Direct sai ta nufi gado ta kwanta ba a ɗauki lokaci ba kuwa bacci ya sace ta.

Iyah da ta kammala kintsa kayan da suka dawo dasu sai ta nufi ɗakin TAIMIYYAH, tana son sanar da ita abubuwan arziƙin da ta gani cikin kulas ɗin da Hajiya suka kawo,sai ta tadda TAIMIYYAH tayi bacci hakan yasa ta fitowa ta nufi ɗakinta itama don ta huta.

Koda Ummi suka shigo gaida TAIMIYYAH sun samu daga ita har Iyah suna bacci,sai Babah Ladi kawai suka tadda da ke ta hidiman ɗaura girkin lunch. Ummie sai ta koma sasanta ta bar Inna Larai za ta taya Babah Ladi aiki,don wataran idan ta shigo ta kan shiga kitchen suyi aikin tare, tunda Iyah ce take zuba musu abinci ana kuma sanya musu daga sasan Baba Sani ma,duk da cewa babu abinda ba a aje musu na kayan abinci a sasan su ba ,sabida idan sunyi ra'ayin dafa abinda ran su ke so su girka abinsu.

TAIMIYYAH da Iyah sai azuhur suka tashi daga bacci,kai tsaye TAIMIYYAH wanka ta shiga ta fito ɗaure da alwala tana jin daɗin jikinta sosai. Kanta sayau take jinsa duk ciwan kannan ya tafi sai dai mura dake son damunta kaɗan,shima ta san tana shan maganinsa da aka haɗo mata daga asibiti za ta samu sauƙi.

Bayan ta idar da sallah ne ta fito falo don cin abinci ta kuma sake shan magani, lokacin ne kuma ita ma Iyah ta fito daga ɗaki.Hakan yasa Kusan a tare suka isa wajen cin abincin, wanda Babah Ladi ta aje har kulolin abincin da suka dawo da shi daga asibitin.

TAIMIYYAH ta fara da bubbuɗe kulolin don ganin abinda ke ciki, sai ta ga su chips ne da akai wa haɗin sauce na musamman da liver,sai farfesun naman kaza da gasasshen naman rago da akai raping ɗinsa cikin foil paper,wani irin gashi da yayi romo-romo sai azaban ƙamshin spices ke tashi. Nan take TAIMIYYAH ta ji gashin naman ya shiga ranta,ta ɗauki plate ta zuba kaɗan tana ɗaura jallop ɗin shinkafan da Babah Ladi tayi akai.

Iyah ganin naman ragon da ɗan yawa yasa ta zuba itama, suna ci suna santin daɗinsa,TAIMIYYAH na yabawa duk wanda yayi wannan gashin naman da cewa ƙwararrene.

Tana kammala cin abincin ɗakinta ta koma ta kunna wayarta,don tasan tabbas an nannemeta anji wayarta a kashe. Aiko tana kunna wayar bada jimawa ba kiran Yasmeen vid call ya fara shigowa,TAIMIYYAH ta ɗauka tana zama daga gefen gado ta fara da cewa, "Besty sai yanzu zaki nemeni kiji lafiya ta gaskiya nayi fishi."

Yasmeen da ke kallon fuskar TAIMIYYAH tar a wayarta ta saki murmushi tana faɗin, "Sorry Tawan kece ai kika kashe wayarki ni kuma ban kira ta line ɗin Iyah ba.Ya jikin naki ina fata dai babu wani matsala? Kawai sai muka ji wannan tsautsayi Allah ya tsare gaba TAIMIYYAH."

TAIMIYYAH ta amsa da cewa, "Ameen Yasmeen,ai abun ya zo da sauƙi ma tunda ban ji wani rauni me yawa ba,kuma nayi dace wallahi matar da driver ɗin nata ya kaɗeni me kirki ce,su suka kaini asibiti yauma kuma ta sake dawowa duba ni, baki ga abincin data zo da safe ta kawo ba,kuma har sai da aka bani sallama sannan ta tafi, gaskiya Hajiyar tana da mutunci sosai."

TAIMIYYAH ta cigaba da baiwa Yasmeen labarin yadda abin ya faru,Yasmeen ta jinjina kai tana cewa, "Allah sarki haka ne dama sai ki ga Allah ya haɗaka dana gari wani lokacin,amma ta kyauta sosai tayi abinda ya dace." Yasmeen ta cigaba da cewa, "TAIMIYYAH dama abinda ya faru tsakaninki da Yah Emran kenan shi ne baki sanar min ba,sai jiya Mamie ke bani labari kin kyauta kenan ?"

TAIMIYYAH ta ɓata fuska don ita sunansa kawai da Yasmeen ta kira sai da ranta ya ɓaci,ta shagwaɓe murya tana faɗin, "Yasmeen to ni banga anfanin sanar miki bane tunda ba abin arziƙi ne ya faru ba,wallahi ni am sorry to say na tsani jin ko sunansa ba don yana jinina ba.Ai Iyah ta sanar min wai Guggo Bilki tai masa cin mutunci sosai har da Abbah ta haɗa shi ma."

Yasmeen ta saki tsaki tana cewa, "Hmm! Wallahi abin ya matuƙar bani mamaki da ɗaure min kai,kinsan bamu taɓa sanin bad side ɗinsa ba sai da hakan ya faru, ashe shi Yah Anas dama ya san Yah Em ɗin na neman matansa,amma shi kansa cewa yayi bai san abun nasa yayi riƙan da har ke zai iya cewa zai ketawa mutunc ba,kiyi haƙury TAIMIYYAH ki yafe masa don gaskiya yayi nadama daga baya,har ni jiya ya sama da daddare yace in sake baki haƙuri wai duk kinyi blocking line ɗinsa,kiyi haƙuri ki yafe masa maganar soyayyace dai koni ban goyi baya ba,don Abbah cewa yayi ma kar ya sake jin maganar."

TAIMIYYAH ta sauke numfashi tana cewa, "Shikenan ya wuce Yasmeen,ni bama abinda ya sake ɓata min rai irin yadda ya lallaɓo yazo ya tsara Iyah wai sona yake da gaske."

Yasmeen ta saki murmushi tana cewa, "Ina ruwan shegen kaya ai ya iya tsari da kike ganinsa a miskilinnan,to ai Mamie tai masa tas tace in ma son ne na gaske ya kama zuciyarsa sai dai ya kashesa, kada ma ya sake nufo ta da maganarki tunda shi baida mutunci."

TAIMIYYAH ta ɗan saki murmushi tana faɗin, "Wayyo Guggo Bilki kice dai an masa taron dangi ne, don Iyah itama tace ta kira shi ta zazzagesa tas!"

Suka saki dariya a lokaci guda Yasmeen na cewa, "Wai ni kam ina mutanenki ne ashe Zuhurah kuma an sanya lokaci to Allah ya kaimu da rai da lafiya,ita ma Basmah ance ta samu wani za a zo a sanya lokaci ayi bikin duk gaba ɗaya ko?"

TAIMIYYAH da idanunta ke kan fuskar Yasmeen ta cikin wayarta,tayi saurin ware ido tana jin wani abu na sukar zuciyarta.Cike da dauriya tai magana tana cewa, "Haka kika ji Yasmeen? Ai ni bamma sani ba nasan dai ta samu wanin ,amma bansan maganan cewa za a sanya lokacin ba,Allah ya sanya alkhairy toh."

Yasmeen ta amsa da Ameen tana noticing yadda mood ɗin TAIMIYYAH ya canza,hakan yasa ta cewa, "TAIMIYYAH lafiya ya dai mood ɗinki na ga kaman ya canza?"

TAIMIYYAH dake ƙoƙarin danne abinda take ji na taso mata daga zuciya, sai tayi saurin duban Yasmeen ɗin tana cewa, "Yasmeen tsakaninmu babu wani maganan ɓoyo kinsan waye Basmah ke tare da shi har ake maganar za a sanya musu rana kuwa?"

Yasmeen ta girgiza kai cikin sauri, kafin ta furta, "No bansani ba waye shi ɗin ni naji abun yazo da gaggawa ne ai, ita dake complain kullum akan rashin masu kulata,waye guy ɗin da yazo cikin gaggawa haka?"

TAIMIYYAH da ke ji har hawaye ya fara taruwa a idanunta, sabida tsananin ɗacin da take a cikin zuciyarta tayi ƙarfin halin fara faɗin, "Yasmeen Nass ne fa,Nass nawa da muka rabu shine ya dawo yana son Basmah,na kasa gaya miki ne tun ranan da mu kai ido biyu da shi yazo wajenta.....

TAIMIYYAH ta kwashe yadda aka yi tana kuka ta sanarwa Yasmeen,har ta kai ƙarshe hawaye na zuba a idanunta tana jin ciwan wannan cin amana da Basmah za ta yi mata na ƙona ranta.Yasmeen da gaba ɗaya ta shiga shock! Sai ta yanko wani irin zagi tana cewa, "Kutumar ubancan kayyasa! TAIMIYYAH ko dai idon ki ne ya gane miki me kama da Nass ,amma ba dai shi Nass ɗinki dana sani ba?"

Readers Also Read