Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com - Chapter 29
Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by hausanovels com Chapter 29: Taimiyah book complete document by ayshat dansabo lemu txt by…
4,474 words
TAIMIYYAH sai tayi murmushin yaƙe cikin raunin murya take faɗin, "Wallahi Yasmeen shi na gani ganin idona ba labari aka bani ba,ni yanzu duk abinda aka ce min mutum zai yi ya daina bani mamaki,sabida na gama gane halayyar mutane yadda ta lalace kawunansu kawai suka sani,ba a maida cin amana abakin komi ba, kullum na tuna yadda dama ba sona suke ba sai inji mamakina ya ragu,amma abinda ke ɗaure min kai shine ta ina har suka haɗu da Basmah suka jone har soyayyah ya shiga tsakaninsu? Koda dai ta gaya min dama tun randa ta fara ganinsa ta ji ta kamu da sonsa,sai na tuna irin kallon da take binsa da shi tun a wancan lokacin,amma maganar gaskiya Yasmeen abin na tsananin min ciwo a zuciyata."
Yasmeen da gaba ɗaya ranta ya gama ɓaci tana ji kamar tayi tsuntsu ta zo Zaria,ta saki wani ashar ta dannawa Basmah tana cigaba da faɗin, "Kar ki damu kiyi haƙury Besty Allah zai miki kyakykyawan sakayya ne soon Insha Allah,ita kuma ƴar banzar mara kunyan ki zuba musu ido kamar yadda Iyah ta faɗi ne,aure indai na cin amana ne wallahi babu inda yake zuwa,ko yayi ƙarƙo to zaki ga ana fuskantar tarin matsaloli a cikinsa.Kuma tabbas ina ji ajikina ba haka kawai suka barsa ba, da asiri suka nemesa ko rantsuwa nayi bana ji zan yi kaffara akan hakan,haba abin da ɗaure kai amma koma miye zai fito fili komin daren da daɗewa,za mu zuba ido mu sha kallo don Allah ki cire damuwa ki barwa Allah komi, in sunyi ne don su ci amanarki su tazartaki to kansu zasu ci amana da yardar Ubangiji, ai Allah baya bacci ya kuma san manufan da ke zukatan dukkan bayinsa."
TAIMIYYAH ta sauke zazzafar numfashi tana kai hannu ta share hawayen da suka zubo mata tana me cewa, "Hakane Yasmeen wallahi ina iya bakin ƙoƙarina wajen ganin na manta cewa mun taɓa soyayya da shi,amma na kasa daina jin ciwo a cikin zuciyata duk sanda na tuno wai Basmah ce xata min haka,amma bakomi koma miye ina musu fatan alkhairy, Allah yasa rakiya tayi nisa,ni kuma Allah ya bani ƙarfin zuciyar fuskantar kowace irin jarabawa,amma soyayya ya gama fita daga kaina Yasmeen bana sha'awar in sake ɗanɗanarta."
Daga haka suka cigaba da tattaunawa akan irin yadda ƴan matan wannan zamanin suka kware wajen iya cin amana.
Lokacin da suka kammala yin vid call ɗin da Yasmeen,TAIMIYYAH sai ta aje wayarta tana sauke zazzafar numfashi,cikin zuciyarta take al'ajabin yadda rayuwa ke juya mata daki-daki,tare da fatan Allah ya bata ikon cin jarabawa,amma sam soyayya ya fita ranta baki ɗaya.
Tana cikin duba messages da ke shigowa ta online kiran Zee ya shigo wayarta. Sai ta kashe data tana receiving call ɗin suka gaisa da Zee,TAIMIYYAH na sake tambayar Zee ɗin jikinta.
Zee ta sanar da ita cewa ta samu sauƙi,ta ɗaura da yiwa TAIMIYYAH complain akan kashe wayarta da tayi,don ta kira ta bata sameta ba.
TAIMIYYAH ta sanar da Zee ɗin tsautsayin da ya sameta bayan barowanta gidansu,Zee ta saki salati tana godewa Allah da TAIMIYYAN bata ji rauni me girma ba.Su kai sallama da juna Zee na sanar da TAIMIYYAH cewa da zaran ta sake samun sauƙi za ta zo ta duba ta.
TAIMIYYAH ta aje wayarta saman gado tana tashi ta ɗakko system ɗinta ta jona a wuta don yin chargy.Tunawa da tayi cewa Ummie ta shigo gaidata tana bacci yasa ta yanke shawaran zuwa Sasan Ummie ɗin,ta fito bayan ta zura hijab akan shigar jikinta, tama sanar da Iyah cewa za ta Sasan Ummie ta dawo. Iyah tai mata a dawo lafiya ,TAIMIYYAH ta fito tana tafiya cikin takunta a hankali cike da tarin nutsuwa har ta isa sasan Ummien.
Bata baro sasan ba sai bayan ta idar da sallar la'asar,cikin tafiyar a hankali take takowa don komawa zuwa sasan Iyah.Kamar an ce ta ɗaga kai ta dubi sashin gate ,sai ta hango shigowar Nass cikin compound ɗin gidan daga wajen gate . Yana sanye cikin ƙananun kaya da sukai masa mugun kyau.TAIMIYYAH sai ta tsaya cak! Kamar wacce aka saka remote control aka tsaida ta,kirjinta ya shiga bugawa da ƙarfin gaske lokacin da Nass ɗin ke cigaba da takowa zuwa cikin compound ɗin.
Akan idanunta suka gaisa da Tukur mai gadi Nass ɗin na ɗaga waya ya kai kunni alamun kiran waya zai yi. Sam hankalinsa bai kai kan inda TAIMIYYYAH ke tsaye dafe da ƙafarta ta zuba masa manyan idanunta tamkar wacce aka dasa a wajen,gaba ɗaya ta kasa koda ƙwaƙwƙwaran motsi sabida yadda take ganin komi tamkar a mafarki,so take yi ta sake tabbatarwa kanta wajen Basmah yazo a wannan karon ma ko kuwa?
Sai dai ko mintuna biyar ba a yi ba ta hango fitowar Basmah daga Sasan su, tana nufan wajen da Nass ɗin ke tsaye cikin taku na ɗaukar hankali.Nan da nan TAIMIYYAH ta ji kanta ya fara juya mata, ta shiga nanata kalmar Innalillahi wa'inna'ilaihirraju'un! Ta dinga nanata kalmar, tana ji a hankali ƙafafunta na yin sanyi lokacin da Basmah da Nass ke neman ɓacewa ganinta,suna takawa jere da juna suka nufi cikin Sasan Baba Sani.
TAIMIYYAH sai tsinci kanta da silalewa daga tsaye zuwa tsugunne ,tana jin saukar wasu irin zafafan hawaye daga idanunta zuwa kuncinta. Ta jima haka a tsugunne bata san ma wani irin tunani zata yi ba, zuciyarta na tsananin zafi da ciwon wannan lamari da take fata Ubangiji yasa mata ƙarfin zuciyar iya haɗiye abinda take ji a cikin zuciyarta.
Da ƙyar ta iya tashi tsaye tana ji kanta na mata wani irin ciwo,ta kai hannu ta dafa guiwar ƙafarta ta fara takawa don isa sasan Iyah,bayan ta tabbatar babu ɗigon hawaye ko kaɗan akan fuskarta. Sabida bata so Iyah ta sake ganin raunin zuciyarta akan wannan issue ɗin na Nass da Basmah.
Har ta isa sasan Iyah bata daina jin nauyin da ƙirjinta yayi na damunta ba.Shiyasa tana shiga ciki bata tsaya a falo ba ta shige zuwa ɗakinta ta kwanta,tafi mintuna sha biyar tana jinyar zuciyarta kafin ta kai hannu ta janyo wayarta,ta shiga wajen da ta adana karatun Qur'ani ta kunna suratul Rahman,tana fata Ubanjigin rahama da tausayi ya sanyaya zuciyarta cikin gaggawa,idanunta a lumshe suke lokacin da daddaɗan kira'ar Abdullahil Maɗrooth ke ratsa kunnuwanta. Hawaye suka fara sauka a hankali daga idanunta suna jiƙe pillow ɗin da kanta ke kai,a haka ta fara jin nauyin da zuciyarta yayi na raguwa a ƙirjinta ta fara taji tarin nutsuwa na shigarta, bakinta ya buɗe ta fara bin karatun a hankali cikin muryarta da yai ƙasa sosai sabida yadda zuciyarta babu daɗi ko kaɗan ........✍🏻
_Allah sarki TAIMIYYAH Insha Allah alkhairy me girma na tafe cikin rayuwarki da gaggawa.....Irin wannan cin amanar bashi da daɗi ko daga bare ne bare ɗan uwanka na jini.Allah ya baki juriya da haƙuri Zainab TAIMIYYAH inji Ɗansabo_ 😰
*Hello! Readers what about dis chapter? kun ji tausayin TAIMIYYAH ko bayan Basmah ku ke bi? Sai na ji tarin comments daga gareku son so domin Allah.* ❤️
#Ɗansabo ce# [12/14, 10:11 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*51*
"Basmah yanzu duk wannan uban kayayyakin Nass ɗin ne ya kawo miki?"
Zuhurah ke wannan maganar tana faman zaro wasu haɗaɗɗun riguna ready made daga cikin wani bag, me tambarin sunan wajen da aka sayi kayan.
Basmah ta jinjina kai cike da tsananin murna take faɗin, "Ke dai bari wallahi duk nawa ne guda 2 na zaɓa na tura masa, kawai sai da ya zo naga ashe har guda 4 ya saya min,ai gaskiya za a je da Cweety ɗinnan nawa Yah Zuhurah,don na ga alamu har ya fi Ameeru hannun kyauta."
Zuhurah da take taji zuciyarta ya sosu sai tayi saurin tamke fuska tana faɗin, "Abin kuma har da cin fuska Basmah,ke fa baki faye kunya ba wallahi."
Basmah ta saki dariya tana cewa, "Sorry Sis ai gaskiya na faɗi amma, bayan kayannan da zai wuce 10k ya aje min,ni ganin abin nake kaman a mafarki wai ni ce namiji kewa rawar ƙafa haka?Gaskiya ko nawa Maharaxu Boka yace a biya shi bamu faɗi ba don aiki fa yaci ba kaɗan ba,wallahi ba kiga yadda duk yake susucewa idan ina kusa da shi ba,cewa yayi duk ya ƙosa ayi aurennan ko xai hutawa zuciyarsa,ranar Saturday dai magabatansa zasu zo Insha Allah."
Basmah ta kai ƙarshen maganan tana wani blushing cike da tarin farin ciki.Umma da ta fito daga ɗaki ne ta iso inda su Basmah ke zaune a falon, idanunta akan bag ɗin da Zuhurah ta zazzage kayan ciki take cewa, "Basmah har Naseer ɗin ya wuce ne,wannan kayan kuma fa?"
Basmah ta dubi Umma tana faman washe baki tace "Umma waɗannan rigunan dana ga ana tallah a IG ne nace miki na turawa Nass nace ya siya min,to shine ya zo min dasu wannan zuwa weekend da yayi,kinsan a Abuja me sai da kayan take shine ya je wajenta ya amsa bayan ya tura mata kuɗin,guda biyu fa na zaɓa amma kin ga guda 4 ya siyo."
Basmah tana maganan ne tana ɗagawa Umma rigunan tana ganin kyawunsu.Umman ta dubi Basmah bayan ta kammala gani tace, "Masha Allah,gaskiya wannan za a je da shi da alamu hannunsa a sake yake ba a dunƙule kamar na ƴan dambe ba,to ya maganan turo manyan nasa? Don ni fa na fiso ai komi gaba ɗaya tare dana Zuhurah ko na huta,sai inji dana Sadeeq da zai biyo baya tunda shi namiji ne."
Basmah sai ta saki murmushi tana sanar da Umman ai Nass ɗin yace zuwa next week Saturday za a zo,yana jin ma gaba ɗaya da zuwa da sanya ranar za a yi a lokaci guda,sabida daga shi har Uwarsa a matse suke ya yi aure,musamman Uwar da take son ganin ya rabu da gurguwarcan,shiyasa yana zuwa mata da maganata ta amince babu wani dogon bincike,ita dai burinta ace ya rabu da gurguwar da bata so bata san tuni muka ɗauke tunaninsa daga kan wata gurguwa ba,ni kaɗai yake ji da gani."
Basmah tayi maganar bil hakki tana sakin dariyar mugunta Umma kuma na taya ta.Zuhura ta ɗan ja ƙaramin tsaki tana faɗin, "Wallahi Basmah ni har kin fini so kiyi aurennan ma,irin wannan rawar kan da kike yi haka kamar zaki kai kanki."
Basmah tayi fari da ido tana sakin dariya tace, "To miye a ciki aure ai abin so ne musamman idan kayi dace da wanda kake so,kinsan yadda nake jin Nass a raina kuwa? Hmm! Ba a magana ke dai kawai Allah ya ara mana lokaci mu more."
Zuhurah ta amsa da, "Ameen." Suna cigaba da tattauna yadda za su tsara bikinsu idan an sanya ranar auren Basmah nan da sati me zuwa.....
TAIMIYYAH bayan idar da sallan la'asar da tayi,cigaba da zama tayi a ɗaki tana ta tilawar Qur'ani sabida so take yi zuciyarta ta sake sanyaya, daga ƙunci da ɗacin da take ji a cikin ranta tun ganin da ta sake yiwa Nass da Basmah a tare. Sai ana dafda kiran magriba sannan ta tashi ta fito falo wajen Iyah da ke zaune. Ta isa kusa da Iyah ta zauna tana faɗin, "Iyah sannu kina ta kallo ne,ni tun ɗaxu ina tilawa ne kinsan an kusa yayenmu sai da tilawa sabida haddar ya zauna da kyau."
Iyah ta dubi TAIMIYYAH tana cewa, "Hakan yana da kyau,ai ina jiyo karatun naki daga nan nace to gaki can ana ta ƙoƙari,Allah yasa albarka yasa anyi na tsoran Allah ne."
TAIMIYYAH ta amsa da, "Ameen." Iyah na cigaba da jan ta hira har aka kira sallah suka nufi ɗakunansu don ɗaura alwala.
____________
*Abuja, 9:05pm.*
Suhailah ce ke tsaye a cikin kitchen ɗinta da ke upstairs,tana ƙarisa haɗawa A.Maleek haɗin Beef Salad da yace shi zai ci a daren.
Bayan ta kammala haɗawan ne kuma ta nufi Coffee maker, ta haɗa masa ruwan Coffee ta juye cikin ƙaramin Mug flask me kyau,ta haɗa komi bisa madaidaicin tray ta fito zuwa falo ta aje daga ƙasan carfet,don ta san ba zai taɓa hawa dining ba.
Tana ƙoƙarin tashi ta nufi ɗakinta don yin wanka,ya fito daga ɗakinsa sanye cikin Pajamas Ash colour da suka haske fatarsa.Suhailah tayi saurin dubansa tana cewa, "My Maleek na kammala zan je nayi wanka yanzu, ko in tsaya ka kammala ne?"
Da hannu kawai yayi mata alama ta tafi sabida yau da alamu ƴan miskilancin nasa na kusa ne,sabida haka suka yini da shi tun rana yana faman shan ƙamshi. Suhailah ta saki smile tana yin gaba abinta,cikin zuciyarta take jinjina halayyar Maleek ɗin masu wuyar sabawa.
Lokacin da ta fito yayi nisa wajen cin Salad ɗinsa wanda yayi masa yadda yake so.Ya ɗago manyan idanunsa ya sauke akan Suhailah lokacin da take takowa zuwa garesa.Tana sanye ne cikin fararen Nighties riga da wando wanda suka lafe a jikinta tareda bayyana surarta a fili.Sabida kayan basu da kauri ko kaɗan,hatta ƙirjinta da bata sanya komi ba a na hangosa muraran ta cikin rigar. Maleek yayi saurin ɗauke idanunsa akanta har ta ƙariso wajen da yake zaune, ta zauna kamar zata shige jikinsa ƙamshin turarenta dana Humrah da tayi amfani da shi na cika kafofin hancinsa.Ta miƙa hannu ta amsa fork ɗin da ke hannunsa tana cigaba da ciyar da shi ba tare da tayi magana ba,kamar yadda shima bai ce uffan ba ya dai sakar mata fork ɗin tana ciyar da shi yana buɗe baki a ƙasaice yana amsa har ta kammala bashi.
Ta haɗe kayan da suka ɓata ta nufi kitchen ta wanke su ta kife,don bata son kwana da plates da akai anfani dasu ba a wanke ba.
Lokacin da ta dawo cikin falon samunsa tayi ya miƙe ƙafafunsa sosai yana kallon labarai a tashar NTA Abuja. Ta zauna kusa da shi jikinsu na gugar juna kafin tayi ƙasa da murya tace, "Yah Maleek next week ɗin za ka shiga Zarian ne?"
Bai yi magana ba ya dai ɗago manyan idanunsa ne daga kan TV ya sauke akanta,kafin ya kai hannunsa duka biyu ya kwanto da ita zuwa jikinsa, yana gyara mata zama bisa laps ɗinsa yake cewa, "No ina ga sai zuwa upper week zanyi tafiya xuwa Anambra bazan samu shiga Zaria ba, kina son wani abu ne daga can?"
Yadda yake maganar cike da ƙasaita hannunsa na lalube jikinta yasa Suhailah lumshe idanunta,dukkanin jikinta na amsan saƙon da yake isarwa a sassan jikinta.Ta buɗe baki murya can ƙasa tace, "So nake mu je tare dai my Maleek coz nayi missing Hajjah sosai."
Tayi maganar cike da marairaice masa murya,hakan yasa Maleek ɗago face ɗinta da hannu ɗaya,ɗaya hannun na cikin rigarta ya manna mata harara yana cewa, "Aiko ba za ki Zaria nan kusa ba sai kin samu kaman 3 month ina ga zaki fi ɗokin ganin Hajjan da kyau,zuwa lokacin kin daɗe da shaye magungunanki kila ma har kinyi ciki,kinga sai ki je kina mata ɗan amannan da kuke yi kina tara miyau a baki,sai ta gane cewa ɗan Abuja ya samu."
Suhailah ta waro ido tana duban Maleek sosai,wanda ya haɗe face ba za ka taɓa cewa shine ya zayyano dukkanin kalaman ba.Ya kai bakinsa yayi kissing idanun nata yana cewa, "Hey! Babe karki cinyeni da wannan kallon mana."
Yayi maganan har lokacin fuskarsa ɗaure yana jefa mata harara, Suhailah ta saki dariya tana sake shigewa jikinsa.Ta ɗaga kai tana kai bakinta bisa wuyarsa tayi kissing kafin tayi masa raɗa cikin kunni wanda sam banji me tace ba.Sai gani kawai nayi Maleek ya dungure mata kai da hannu yana magana can ƙasa-ƙasa yake cewa, "Zaki yi bayani ne yarinya amma ba a nan ba sai a Bed."
Suhailah dake faman dariya ta ɗan shagwaɓe murya tana faɗin, "Ni kam babu ruwana Yah Maleek,amma kana ganin zuwa lokacin da zan kammala da magungunan komi zai iya zama normal har in iya ɗaukar ciki?"
Tayi maganar da wani expression wanda yasa Maleek ɗagota baki ɗaya ya mannata da ƙirjinsa yana cewa, "If Allah yayi nufin hakan sai ya kasance wife,addu'a zamu cigaba da yi dai sai kuma in sake zama rigimammen da kike cewa idan rakinki ya tashi,watakila a duba ƙwazona a bamu rabo kurkusa ko Babe?"
Yayi maganan yana sanya idanunsa cikin nata,da yasan tasirin irin yadda yake dilmiyar da zuciyar Suhailah idan yayi hakan, daya sassauta mata don wani irin gubar ƙaunarsa yake zuba mata me asalin ƙarfi dake illata zuciyarta nantake.
Ta lumshe idanunta da sauri tana buɗesu akan kyakykyawar fuskarsa,ba tareda da ta bashi amsa ba ta kai bakinta saman nasa tana fara manna masa wani irin french kiss,wanda shi ya koyar da ita amma sai gashi ta fishi ƙwarewa a harkar. Cikin lokaci kaɗan ta gama kunna zuciyar Maleek,sai da abubuwa sukai nisa ne ta fara danasani. Don da ƙyar ta kwaci kanta a hannunsa lokacin da ya nuna bai san komi ba, illah ta bashi abinda ta san shi kaɗai ne zai kashe wutar rikicin da take hangowa cikin idanunsa.
A daddafe suka kai 10:30pm anan falon suka nufi ɗakinsa bayan ya gama shan coffee ɗinsa,yana fitowa daga toilet yayi musu light up ya nufi kan Bed inda Suhailah ke kwance cikin duvet.
Ya miƙa hannu ya lalubota tare da janyota zuwa jikinsa,jin ta yayi a yadda yafi so don har ta cire kayan jikinta babu komi a tare da ita,hakan yasa shi manna mata sumba a biki cikin murya can ƙasa ya furta, "Luv u my sweet wifey."
Daga haka labarin ya fara canzawa zuwa wani salo na daban abinda ya kore ni daga ɗakin kenan na fito kamar zanyi tuntuɓe......Lol
__________
*3 Weeks Later*
TAIMIYYAH ce zaune tare da Iyah suna tattaunawa akan saka ranan auren Basmah da Nass da akayi sati biyu da suka wuce.
TAIMIYYAH ta dubi Iyah tana tana faɗin, "Ni Iyah kinsan me ke bani mamaki?" Iyah ta girgiza kai tana cewa, "Sai kin faɗa TAIMIYYAH." TAIMIYYAH ta ɗan tsuke face alamun koma me zata faɗi yana hurting ɗinta a zuciya kafin ta furta, "Wallahi Iyah randa na shiga yi musu Allah sanya alkhairy Umma cewa tayi wai ai dama ban je ba, tunda ta san daga ni har ke baƙin ciki muke yi sabida uwarsa tace bata sona don ni gurguwace,yanzu kuma mun ga ya dawowa Basmah har gashi an sanya musu rana ai ta san baƙin ciki muke yi,Allah sanya alkhairin ma na gulma ne na je yi,wallahi Iyah na ji zafin kalaman sosai a raina."
Iyah dake sauraren TAIMIYYAH ta jinjina kai tana cewa, "Kiyi haƙury Zainab akan koma me zasu ce miki,ke dai kawai ki musu fatan alkhairi,ki kuma sanya musu ido wanda hausawa kan ce maganin lalatacce,kuma maganar baƙin ciki da take faɗi da baƙin cikin muke yi,da ni da kaina na soke batun auren na tona musu asiri,don kuwa idan na sanar da Sani yadda abin ya faro har kawo dawowarsa wajen Basmah,suna ji suna gani zai yi kora da maganar sai dai kuyi biyu babu,sakarya wacce bata da lissafi ko kaɗan a cikin kanta,har abada bazan fasa yiwa Sani takaicin kasancewa da mace jahila me son zuciya irin Zuwairah ba,domin na jima da tsanar halayyarta don ba za ka ce ka ƙi mutum ba sai dai ka ƙi mugun halinsa,amma ina mata fatan shiriya idan tana da rabo."
Iyah ta kai ƙarshen maganan cike da tsananin ɓacin rai,don har cikin zuciyarta take jin ciwan irin abubuwan da sukewa TAIMIYYAH ,wacce bata taka musu ba bare ta zubar musu.
Daga wannan hiran suka koma kan shirye-shiryen walimar yayensu TAIMIYYAH da za a gudanar asabar me zuwa. TAIMIYYAH na sanar da Iyah cewa tana son sayan sabuwar Abaya da za ta sanya a ranar. Iyah ta murmusa tana cewa, "To ai sai ki saya ɗin Zainab,nawa ne kuɗin Abayar sai in baki ai,munyi magana da Babanku Sani ma nace ina so a kayar da ko raguna biyu ne, a gasa kowa yaci naman,don taro sosai zan yi aci a sha a taya mu farin ciki."
TAIMIYYAH ta saki kyakykyawar murmushin farin ciki tana cewa, "Iyah Allah ya ƙara girma ya baki tsawon rai me anfani,bani da bakin da zan iya kwatanta adadin ƙaunar da nake miki a duniyar nan sai dai ince Ubangiji ya baki Jannatul firdaus ,ke da su Abie da Mamata dasu Nahar da mu baki ɗaya."
Sai kuma hawaye suka fara zubowa TAIMIYYAH sharr...!! Iyah tayi saurin kamo hannunta tana faɗin, "Ameen Zainabu don Allah bar kukan haka, kiyi haƙury Allah ya gafarta musu ya ƙara mana dangana,nawa ne kuɗin Abayar maza ki faɗi min kin ji Zainabu na."
TAIMIYYAH ta share hawayen da suka zubo mata tana jin kewar Abie ɗinta me tsanani yana cika zuciyarta. Ta yi ƙarfin halin murmusawa tana sanar da Iyah adadin kuɗin Abayar.Iyah ta jinjina kai tana faɗin, "Karki damu gobe zan baki kuɗin Insha Allah."
TAIMIYYAH tayi godia tana cigaba da cewa, "Iyah ai online na siya Abayar nama tura da kuɗin ta account ɗina,kawai dai na san zaki yi faɗa ne kice meyasa ban bari kin saya min ba,wajen wata chuchu na siya na tura mata kuɗin gobe za ta sako min a mota sai Sani ya je tasha ya amso."
Iyah ta aikawa TAIMIYYAH harara tana faɗin, "To ai kin kyauta da baki sanar min ba sai da kika siya,sai ki amshi kuɗin ai ki mayar cikin asusun naki."
Kafin TAIMIYYAH tayi magana taji kira ya shigo wayarta,ganin sunan Hajiya Aysha yasa ta yi receiving call ɗin ta kai wayar kunni tana amsa sallamar da Hajiyar tayi.
TAIMIYYAH ta gaida ta cike da ladabi tamkar tana gabanta,kafin tayi jim tana sauraren abinda Hajiyar ke faɗi daga nata ɓangaren,zuwa can tai ƙasa da murya tace, "Eh Mama ranan Saturday ne idan Allah ya kaimu,ashe Iyah bata manta ba ta sanar miki."
Ta sake yin jim! Kafin ta furta, "Bakomi Mama duk abinda ake buƙata anyi nagode sosai na kulawa sai kun zo ɗin."
TAIMIYYAH ta cigaba da blushing tana sauraren abinda Hajiyan ke sake faɗi mata,kafin ta sake cewa, "To shikenan Mama nagode gama Iyan a kusa dani bari in bata wayar."
Daga haka TAIMIYYAH ta miƙawa Iyah wayar tana mata raɗa da cewa Hajiyar Gonar Ganye ce,kamar yadda suka raɗawa Hajiyar tun randa sukai waya ta sanar da Iyah cewa a Gonar Ganye suke zaune.Iyah ta amsa wayar suka gaisa ita dai TAIMIYYAH bata ji me Hajiyar ta sanar da Iyah ba,ta dai ji Iyah na godia kafin ta miƙo mata wayar sukai sallama da TAIMIYYAH.
Lokacin da TAIMIYYAH ta aje wayar a jikinta ne ta dubi Iyah tana cewa, "Iyah gaskiya Hajiyar nan akwaita da kirki cewa fa tayi lallai in faɗi me nake son ta kawo min gift ranan walima."
Iyah tayi murmushi tare da jinjina kai tana faɗin, "Wallahi Zainab nima na yaba da kirkin matarnan Allah kaɗai yasan alkhairyn da yake nufi ya haɗamu ta hanyar gitta tsautsauyi a tsakaninku,sosai kika shiga zuciyarta na ga alama,ai nina kirata ɗazu kina bacci na cika alƙawarin dana ɗauka na cewa zan sanar mata idan lokacin walimar ya kusa,shiyasa kika ji ta kira ki yanzu."
TAIMIYYAH ta jinjina kai itama tana jin ƙaunar Hajiyar har cikin ranta,sabida yadda take nuna mata ƙauna da kulawa.Suka cigaba da tattauna yadda hidiman walimar zai kasance,sai da kiran Yah Deeku ya shigo wayar TAIMIYYAH ne sannan ta tashi ta nufi ɗaki,don ta san shima dai zancen walimar yayen nasu zai mata,don tun jiya yake fama akan ta turo masa details ɗinta taƙi don bata son ɗaura masa ɗawainiyar sai ya bata wani abu.
Sun daɗe suna magana tana faman bashi haƙury da cewa yanzu zata tura masa details ɗin, sabida yadda ta ji ransa ya ɓaci.Suna ko gama wayar ta tura masa ko minti biyar ba a yi ba k sai ga alert na 50k.
TAIMIYYAH tayi ta kiransa don tai masa complain akan kuɗin yayi yawa,amma sai yaƙi ɗauka sai dai ta tura masa text message ɗauke da kalamai masu daɗi na godia.Ta fita da sauri don zuwa ta sanarwa Iyah don ta taya ta godia wajen Yah Deekun........✍🏻
#Ɗansabo ce# [12/14, 10:11 PM] +234 703 769 7050: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin*👇🏻 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*52*
Kwanakin da suka biyo baya gaba ɗaya TAIMIYYAH da Iyah sun maida hankali ne wajen shirye-shiryen walimar kammala Haddar Qur'anin su TAIMIYYAH,ana gobe za a yi walimar Yasmeen da Guggo Bilki suka iso daga Kano.
TAIMIYYAH suka rungume juna ita da Yasmeen,suna murnan ganin juna tamkar ba kusan kullum sai sunyi vid call ba.
Da daddare bayan sun kammala cin abinci ne suka ƙule a ɗakin TAIMIYYAH don zantawa da juna,sabida tunda suka iso ana ta kammala shiri ne sai yanxu ne suka samu time ɗin kaɗaicewa.
Yasmeen ta dubi TAIMIYYAH tace, "Sis kinsan ni duk na ƙosa muyi ido biyu da mara kunyar Yarinyar can Basmah,ɗazu da naje sasan gaida Baba Sani ban ga kowa cikin su bane,dana tambayi Umma sai cewa tayi basa nan wai sai gobe da safe za su dawo ma,ni kuma na sha alwashin kafin in bar garinnan sai naji yadda akayi ta Ƙulla alaƙar soyayya da Nass har ga shi an sanya musu ranar aure,wannan ai cin amanace kuma ni a yadda tunanina ya bani koda ace baku rabu don mahaifiyarsa ta nuna ƙinki ba,dama can suna da wani manufa na son cin amanarki ne kawai."
TAIMIYYAH wacce take ta faman kauda kayayyakin gift data fara samu, ta dubi Yasmeen tana cewa, "Yasmeen wallahi bana son jin zancen Basmah da Nass a yanzu,sabida na sanyasu cikin wani littafi na daban na kulle dukkanin shafukansu,idan har zan iya baki shawara kema ki ɗauka to don Allah kada kiyi mata maganar koda wasa,matuƙar ba fatan alkhairy kawai zaki yi ki kulle bakinki ba,kinsan meyasa nace haka?"