Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 106

Tarko complete novel - Chapter 106

Tarko complete novel Chapter 106: Tarko complete novel Chapter 106. ****** ********** ****** Sai gab da Azumin watan Ramadam zai kama maigidan ya dawo…

3,067 words

****** ********** ****** Sai gab da Azumin watan Ramadam zai kama maigidan ya dawo kasan tare daga kasan waje, Abuja yayo direct gurin iyalin shi, tun kafin ya iso kowace mun sai shirye, shirye take don taron maigida kowa tana kokarin ganin cewa ta burge shi, Nidai ba lafiya gareni ba don haka babu wani shiri mai yawa da mukayi mundai gyara part din mu duk da dama akoda yaushe a gyare part din yake, Sadiyace ta karbi girki kamar yadda yaba da umurni kafin isowar shi garin badon komai ba sai don kawar da fitina a tsakanin su, Baba Ramatu duk da nasan cewa bazata haifeni ba amma don girmamawa nake kiranta da wanan synan tun tana hanawa har yakai ta kyaleni ina kiran ta hakana, Itace ta gyara falon gidan tsab yadda yadace tasaka mai kamshi a kowani kusurwa na falon, Hakan kuma taima nawa part din komai sai kyali yake yana daukan ido, Yana saye a cikin kananan kaya mai baiyyana mai suran kurciyan shi, Duk suna falo suna kokarin rugumar shi inda Sadiyace kawai ta nuna halin girma ta dan dakata daga baya kadan, A lokacin muka shigo falon nida Asamau, da Ramatu sai Maman Biu da Gwagona Habib, Yana rugumay da Salawa sai fatima adayan gefen rugumay da yarta a showel, Ganin fitowan mu ya dan sake su ya riko hannun Sadiya yana cewa Uwargida rangida ya gidan yake, Sai a lokacin tai yar murmushi tana cewa Alhamdullahi, Cikin dan fadada murmushin ta ke cewa andawo lafiya ? Yadan matse hannayen ta yana cewa Alhamdullahi mun shawo turai sosai, Idanuwan su Salawa akan yadda ya matse hannuwan Sadiya yana cewa yagida, Take wani irin kishi da bacin rai ya ziyarci zukatan su, a lokacin guda, sai murmushin su yajuye bacin rai, Daga inda muke a tsaye muna iya hango fuskokin su ya sake zuwa bacin rai, Hankalin shi yana gare mu yayin da muke mai sannu da zuwa acikin fara,a daga gefe guda, Daga can kafin ya karaso garemu yake cewa, Gwago Mama sannunku da gida, Gwago tace cikin daga murya maisunan malam barka da hanya, Yakaraso zuwa gare mu acikin irin girmamawan da mukewa iyayyen mu yake cewa tare da durkusawa kasa gwago nasamay ku lafiya ? Irin gaisuwan da yai wa maman biu ke nan itama kamar yadda ya gaida gwago Habbi,, Sai kuma ya dago idanuwan shi zuwa gare ni ya na mai dan langabar da kan shi tare da cewa, Kaunata how far ? Ya kike ya yan three's da big man ban bashi amsa ba sai dan murmusawa danayi tare da mai signal da ido inda yaran suke a tsaye hannun Ramatu da Asma,u na, Batare da jin kunya ko nauyin su Gwago dake gurin tsaye ba ya miko min hannuwan shi babu bata lokaci namika mai nawa tare da shigewa jikin shi, Rugumoni yayi yana mai sauke ajiyan zuciya a hankali tare da dan shakan kamshin jikina, Gani nayi kamar ya matanta da cewa akwai mutane agurin don haka nake kokarin jaye jikina daga jikin shi, Amma sai naji yai min rikon da bazan zare jikina daga nashi ba, Ji nayi ya soma kokarin dan jana zuwa saman kujera, mafi kusa da mu. , Zaman mu yai daidai da kiran wayan shi da akayi wanda yake kokarin fidowa daga aljihun shi Dago fuskan shi yayi yana ma su Ramatu da Asamau inkiya da su kawo mai yaran kusa ya kuma juya inda Fatima take, itama yace ta kawo yarta, Ganin hankalin shi, ya dauke ga yaran shi ya sakani dan sauke numfashi, a hankali na mike na bar gurin batare daya ankaraba, Abinda yakeyi yadaka yana dubana tare da yin murmushi. Nan na barsu a falo tare da iyalen shi na, shige gurin su Gwago na na zauna, Sai bayan shigewa na ya dan sauke ajiyan zuciya tare dacewa Salawatu Madam work kamar yadda yake kiranta in yana nishadi, Murmushi ta dan sauke da ajiyan zuciya, tana cewa Oga naga kana duban lafiyan iyalen kane ai, bai bata amsa ba sai yar murmushi don yasan nufin ta, Dukkan su, sauran suka dubeta don sun san maganan ta da manufa aciki , Fatima tace aikowa domin shi yake a gurin nan don haka dole ko ya duba kowan mu, Dariya abin ya bashi, tare da dan dan girgiza kai yace har yanzu baku daina halin ba ga yara kun fara tarawa a gaban ku, Sadiya tace ai barsu kawai sai yaran sun fara rabasu fadan nan nasu dabaya karewa ko yaushe aka hadu, Ta juya tana cewa idan ka rarage ruwan wanka yana jiran ka a ciki, Daga haka itama tai shigewan ta part din ta inda ta fara sintiri daga part din ta zuwa nashi part din, Bai dauki lokaci ba yadan duba agogon hannun shi tare da mikewa ya shige part din shi inda yabar su nan suna hira sai dai duk rabin hiran gulma ne duk da Fatima bata yarda ta zure da yawa ba,

****** ********** ****** Kowa yau agidan namu sai murnan dawowan maigidan akeyi yayin dashi sai kokarin yin adalci a tsakani yakeyi gurin ganin yabawa kowa hakkin ta, Da yake shigan safe yai muna nikan danaga cewa ban da wani abinda zan gudanar sai kawai na shiga barci abina saboda yanzu wani irin barci ne yake zo min Nasan cewa rashin barcin da ban samun yi a can baya asibiti,ne nake maimaitawa a yanzu, Shigowan shi sau biyu daki na amma yana samuna ina barci sai ya tsaya yana dan min kallon tausayi saboda yadda duk na ramay na kara yin wani fari na koma wata fayau dani, Koda na farka daga barcin sai naji kamshi oud din da yake amfani shi ya kauraye sakin nawa hakan ya sani fahintar cewa ya shigo dakin nawa, a lokacin da nake barci, Bankai ga mikewa Asmau tashigo dauke da Alhasan a hannun ta duk da ba gane yaran nake sosai ba take ce min kin dai sha barci, yau kan, Nadan dago ina murmushi nace karfe nawa yanzu, ? Take ce min shigowan Yayan sau biyu dakin nan amna dai naji fitan shi dazun nan bada dadewa ba, Tamiko min yaron tana cewa karbar shi yadan tsotsa don tun safe bai sha nono ba shi, Badon naso ba na gyara nabawa yaron nono don ya sha, kafin na fita zuwa ban daki, Yana cikin shan nonon tashigo tana ce min wai,ni Antyn mu wayan nan kishiyoyin naki kuwa suna da kunya kuwa ? Wai yau ita Salawtu din nan har da daukan Amira hassina, a gaban Yayan mu, Ai nake ce mata tabada ita don zata iya kuka tunda bata taba daukan ta ba, Sai na dago da sauri nake cewa haba Asma,u kika ce mata hakan, Tace kwarai kuwa don ita wai zatai muna kilibibi saboda tafa uban su a kusa don yace ai tana kula yar, Nace bakya tsoron Yaya yai maki fada ko ya kunyataki agaban su, Tace cabdi wallahi da sai na fadamai gaskiya cewa bata taba daukan yar ba dabaya gari sai yau da tagan shi a kusa, Murmushi nayi nace kai Asmau baki da dama wallahi tace ai ina fadan haka naga sun wani kalleni gaba dayan su niko nayi mirsisu dasu na karbi diyata na bar su nan a zaune, can ta matse masu, Dariya taba ni inda namike ina mika mata dan ina kokari tashi tsaye don zuwa gabatar da awala saboda na makara, Bayan na idar da Sallah ina zaune ina dan jan tasbaha, naji shigowan mutum dakina inda na juto don ganin ko waye a lokacin ya shigo, Daidai lokscin da yake karasowa nake cewa Sannu da zuwa Yaya ban samu zuwa na gaishe ka ba harnai barci sai yanzu na farka Baiyi magana ba sai karasowa zuwa bakin gadona da yayi ya zauna, Yana cewa, may ke damin ki yanzu a jikin ki Meenat sai naga kamar har yanzu kina jin jikin naki dai, Batare da nace mai komai ba nadan kai zaune gefe guda daga inda yake ina cewa,, Yaya ni fushi na keyi don tunda katafi, nake cewa kacewa likita ya sallamay ni amma yaki sai da na kara sati biyu a gurin su, Murmushi yayi yana cewa to Allah ya huci zuciyar yar kaunata, amma babu yadda za,ayi nabari a sallamay ki acikin irin halin da kike a lokacin, Nace amma ni a lokacin nafi son na dawo gida naci gaba da jiya a daki na don zaman kadaici ya damay ni a can din, Yace Meenatu da ki ka yi hakkuri yanzu baga shi kin dawo gida lafiya ba, Barinki a gida acikin wanan yanayin hankali na bazai kwanta ba musan man, ma irin fitinar da ake kai,akai agidan nan, Don haka bazan barki agidan nan ba cikin wayan nan fitinan nun daba zaki samu wani kulawa ba ma agare su, A cikin fahitar manufar shi yasani cewa a kasale hakanane kuma don zama acan din yai min rana sosai wallahi don nasamu kulawa sosai daga ma,aikatan asibitin, Kusan minti goma muna zaune tare dashi a dakin ganin yadan dauki lokaci a dakin nawa gudun fitinan matan shi ya sani cewa Bari na dan kimtsa na samay ka a falo ko,? na fadi hakan cikin dan kura mai ido, don inji may zaifada min, Murmushi naga yayi sai naji yana cewa au yau kuma korata kikeyi ne kaunata, A hankali na girgiza kaina ina cewa cikin dan girmamawa a,a Yaya ba hakana bane inadai gudun zargine daga matan ka, Kafin ya kai ga cewa wani bu sai kawai naji anshigo dakin kamar a hasale babu sallama sai cewa tayi, Asheko kana dakin ke nan don cwa nayi baka ciki abari nazo na duba don muna a falo zaune, gaba dayan mu, Atake raina ya baci don shigo min daki da tayi babu sallama, Nace a kufule haba malama zaki shigowa mutane daki babu sallama idan an miki haka baza kiji dadi ba ai, Ta,ce dakata malama ba gurin ki nazoba sai ki bari wanda nazo gunshi yai magana, A lokacin har Yaya Abubakar ya kai tsaye daga zaunen dayake rai a bace yana cewa, Nace wanan ai rainin hankaline abinda mutum baiso aimai to kada yai wa wani shi, Na,fahinci kawai wani hanya ne na son magana, Wani kallon mamaki naga tana min don tai mamaki da taji yadda nake mata magana a hasale, A hasale naji muryan shi cikin kufula yana cewa kifita kawai Salawa ban son yawan surtu haka please, Idan na gama abinda nakeyi zan fito tunda ba,a nan zan kwana ba, Tace to haka ma kace yace a hasale hakadin nace and so what, Daidai zata fita daga falona sukai kayi kicibis da Asamau tana dauke da flask din ruwan zafi dauke a hannun ta Tun daga nesa Asamau ta watsamata wani irin harara na tsana , Suna isowa gaba da junan su ta sake mata tsuki mai karfi, Tare da kwasanta tawatsar gefe guda ta wuce direct gurin da muke aje flask din ruwan zafin shan madaran yaran a falona, Tana ce muna funci dodo ta Allah dai bata mutum ba, wallahi, Salawatu ta so ta tsaya taiwa Asamau cin mutunci amma sai ta tuna cewa maigidan yana part din kuma da alaman ranshi a bace yake da shigowan datayi masu babu sallama ,, A zuciye naga yafita batare da yakara furta min komai ba wanan yasani sanin cewa yau Salawatu zata sha masifa a gurin shi ke nan,

ZEEE MAKAWA YELWA

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣0⃣5⃣

ZAINAB IDRIS MAKWA

ALLAH AN NAAFI

JUMMA,AT, MUBARAK TO, ALL MUSLIMS UMMAH IN THESES WORLD,,,

Washegari ban fito daga part dina ba sai da dare bayan kowa ya idar da duk abinda ya keyi a lokacin, Ina saye da wata doguwar riga baka maidan zuben jallabiya saidai rigan tanada dan fadi don bata matse ni ba sosai, A hankali nake tafiya don gudun tangarda ga jikina shi yasa nake dagwa dagwa, ina kafa kafa da komai, Tun ban karaso ba jikina yabani yanzu gurin zai sauya inda na isa, A zaune su ke a na dan hiran sama, sama hiran gwale junan su kowan su da abinda yakeyi , Maigidan yana, duke a jikin computer yana aiki ga goran ruwa a gefen shi guda, yayin da naga yar wurin Fatima daga dayan gefen shi kadan, Abu ga dan Adam kuma mace da kishi ina ganin yarinyar sai naji wani irin kishi ya dan turnukeni amma sai na dake na wayance nan nunawa a fuskana,, Sai dai acan cikin raina ina fadin Innalillahi don samun sauki, Ganin nafito falon ya saka su gaba daya sako min idanuwan su don suna bala,in,bakin ciki su ga na fito wanan zaman, falon cikin su, Sannun ku da hutawa nace bayan nai masu sallaman da ban tsanmanin sun karba min ba, Idan har nace zan zauna a kasa yanzu bazan ji dadin hakan ba, don haka sai na dan zagaya daga bayan kujera na dan duka a kai, aa@ Yayin da na tokare hannaye na asaman kujeran na dan kwanto da jikina a sama, Yaya Abubakar dake a duke jin nice na fito kuma har nai masauki a bayan kujeran shi ya saka shi kokarin juyowa, don ya fuskance ni, Yarinyar dake a kwace tana dan wasa a cikin gwalanci tana daga kafan ta nake danyi wa wasa a lokacin , Yayin da idanuwan uwar ta yake kyam a kaina kamar tana zaton zan wa yar nata wani mugun abu nan, Nace cikin sakin fuska kece babu ko sock's a kafan ki bakyajin sanyi ko Uwar wace ta tsureni da idanuwan ta fuska ba yabo ba fallasa aciki ta ce ai yau babu sanyi sosai, Fuska Yaya a kaina acikin murmushi yake cewa, Ya jikin naki yau kuwa nurse din ta shigo gidan nan kuwa, ? Gaba daya naga sun sha mur kowace tadan daure fuskanta Nace cikin wani muryan jan aji wanda ya sake masu jin haushinna Na amsa eh tazo har ta dan sani indan dinga yawata,wa don na kara jin karfin jikin nawa, Fuskan shi dauke da murmushi yace Good , good hakan na da kyau, don zaki dinga yin exercises din jikin ki a hankali don gurin ya hade sosai, Nace dama nazo na fadama cewa mun samu gifts daga kungiyoyi da dama da zamu dawo gida yan asibiti su ka ba mu tare da list din masu kyautan, Kokarin mika mai takardan na keyi don ya duba na kara da cewa doctor yace yaso ya kawo gida tun kana nan amma sai yaga a lokacin ba,a gaba kawowa ba shi yasa su kai parking dinsu a side, List din ya karba a cikin farin ciki tare da jn dadi yana fadin masha Allah inda yafara kiran sunayen wa yanda suka kawo muna gifts din tare da alakarshi da su, Inda yake cewa sai da safe zai shigo ya bude ya gani don ya ga abubuwan dake a cikin parks din, A lokacin da muke magana shiru gurin yayi babu mai motsi daga cikin su tankar babu kowa a gurin, A, a yan uku kan Alhamdullahi gaskiya yanzu duk wanan tarin kayan na gifts ne haka ashe ? Mu muna ma ce ai ko duk na uban su ne wanan sayayan mai yawa haka Sadiya ce mai wanan maganan acikin mamaki take ce lalai zato zunubi don ni wallahi nazaci duk wanan sayayyan uban su ne, ai, Lalai munga haihuwan arziki aike Meenatu kin iya haihuwa wallahi na Amir ma naga haka aka tara maku kayan kaman zaku bude shago, A to ai yanzu bamu gani kayan ba mu don haka babu abinda zai damu mutum wallahi, Kaya ai basai keep n gani ba don mu bamu gaji yin riya ba a gidan mu, Idan kina son ganin su kije rugga fullani kisha kallo ikon Allah wallahi, Asmau ce daga gurin hawa steps din da zai kai mutum kitchen din gida take bama Salawatu amsa, Sai mukaji muryan Fatima tana cewa ai idan fitsari banza ne to kaza tayi mugani don zancen banza wai har ace wata ta ita haihuwa wata vata iya ba, Ai sai agwada mu wanda bai iya ba mugani afili zancen banza zancen wofi, Cikin tsawatawa Maigidan ke cewa kada ku kawo min zancen fitina a gida yanzu rayukan ki ya baci, Yayin da Salawatu ke cewa wallahi Oga kayi wa yarinyar nan kashedi don wallahi ta rainani da yawa a gidan nan, Ni ko yar ki wallahi gatanan ba sa,ar yina bace, balle ke, Ita kuma Sadiya sai cewa tayi ai sai kiyi don ni zancena a gida nake magana da akace kayan da mutanen gida suka tara akawo wa su yan uku wai Mama ta rike tace baza,a kawo ba tunda na Amir ma suna nan ba, ai komai da su ba, Shine ke azaton ki kike gani wai ke nakewa shagube ke ma ina antara maki gwargwadon samun ku, Enough don Allah zancen ya isa haka please don ban son yawan fitina wallahi, Ganin wuri ya rikice ba kuma lafiya gareni ba yasani juyawa zuwa part dina cike da mamakin zancen wai Mama Ladi ta hana akawo min kayan da muka samu, Bance komai ba na shige falona inda na samu su Gwago a zaune nadan hau two seaters na kwanta na dunkule guri guda ina mai sauraren hiran su, Shigowan Asmau nake cewa Asmau don Allah ki fita harkan Salawatu a gidan nan please ban son abin fitina wallahi, Tace wallahi Anty wanan matar muguwace kullun zancen kine a bakin ta idan kuma tagan ki sai tayi kamar tana kaunar ki da gaske Murmushi nayi nadan gyara kwanci ina fuskantar ta da kyau nace Asamau ke nan ke kin taba ganin inda kishiya taso kishaya ko na rana guda, ai saidai na dariyan hakora kawai, Wani kallo tai min na mamaki tana cewa amma dai ba harda ke ba nace cikin dariya ni ba mutum bace Asmau. Suna kishina ina kishin su don haka kinga ai kowa nayi Sai dai kawai na wata yafi na watane kawai amma ai ba macen da zatace bata da kishi a duniyan nan, Tace amma Anty wanan matar wallahi, nata yai yawa don munafukace, Bata kaunar ki sam keep duba fa ranan naji suna gulma wai duk wanan gifts din da kika dawo dasu daga asibiti wai Yayan mu ne ya saya maki su, Zanyi magana Baba Ramatu ce ta hana nai mata magana take ce min wai na kyale ta halinta ke nan,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull