Tarko complete novel - Chapter 107
Tarko complete novel Chapter 107: Tarko complete novel Chapter 107. ****** ********** ****** Da tsaban balai Salawatu ta samu Yaya Abubakar a daki tana…
3,040 words
****** ********** ****** Da tsaban balai Salawatu ta samu Yaya Abubakar a daki tana mashi fitina akan Asmau, Wai wallahi yai wa yarinyar nan Asamau fada idan ba hakaba zata ci mata mutunci sosai wallahi, A zuciye ya juyo inda take a tsaye cikin fitina yana cewa, ban son hauka ki fice min daga daki tunda ke bakya girma ko yaushe, Ke kadaice mace a gidan nan, da zata sakaki a gaba to kin yi kadan ki hana yan uwana zuwa gidan nan, Kallon shi take rai a bace tace ni bada ita nake kishi ba da yar ta nake kishi wallahi, Tunda yarta bata kulaki ba yadda kike so yanzu kin samu mai kula dake sai kuyi tayi, Zan kuwa bata maku rai keda ita gabadayan ku wallahi, don bazan laminci fitina ba agidan nan, Bayan kwana biyu ina kwance a dakina ina barci naji kamar ana taba min kafana, Karfin halin bude idanuwa na nayi inda nagan shi a tsaye a kaina, Fuskan shi ba walwala yake cewa kiban list din abinda za,a saya maku don zan shiga gari kafin na koma, Cikin karfin hali na mike zaune ina cewa ya zancen komawan Gwago kaga Dijema ta tafi baka a kasan, lokacin, Maimaita maganata yayi cikin kwaikwayona a shagwabe, yace ke gwagotace fa bataki ba, ko kin mantane wai, Abinda ya sakani yin murmushi kenan tare da kokarin mikewa da kyau nace a,a ai ina zaton ko ka manta da zancen tafiyan nata ne, ai, Yace Ranan laraba su Baba Wadda zasu kai Gwago sai suzo da wace zata dinga kulawa da yaran ko ? Da sauri nace to amma Yaya ai da sai abar Ramatu da Asamau da yaran kawai ko, ? Yace ba maganarki bane mun riga mun gama zancen da malam ko har an samo wace zata zauna dasu, A sake nace Allah ya kawota lafiya Allah yasa ta kwaraice zan samu irin Ramatu, Har juya zai fita daga dakin bayan nagama yi mai list din abin da muke bukata, Sai kuma naga ya juyo wanan karon fuskan shi babu wasa ko kadan a cikin sa, Ya ja ya tsaya yana cewa kiwa Asamau magana ta daina shiga harkan Salawatu please ? Dan rage murya nayi ina cewa, anyi wani abine kuma, again, Bai bani amsaba sai jan kofan yayi yafita daga dakin A yadda na lura shine karar Asamau Salawatu takai gurin shi Shiru nayi iya tunane na ban san may Asamau taiwa Salawatu ba kuma again, Amma dai zan mata magana kamar yadda ya ce nai mata din tun da shi bazai mata ba, Da Gwago zata tafi shirina musan man ne Yaya yai mata don duk abinda tace tana so ansaya mata su, Tafiyan shi da kwana biyu Gwagona tai muna ta baki takoma gidan Birnin Kebbi acikin murna da jin dadi, da tarin abin arzikin da aka siya mata, Matar da akazo min da ita, mai suna Luba bata da matsala gata da zafin nama da tsabta, Don haka na godewa Allah da kuma neman hadin kansu ita da Ramatu, Dole don kwana da yara suka dawo part dina da kwana inda nida Ramatu muke kwana adaki guda, Asamau da Amir da Aisha da Luba a dayan dakin suke,,.
****** ********** ****** Yarana basu da fitina sosai don haka nake samun sauki sosai gurin shayar dasu, Anytime ina dakina bamu fita wanan hiran na gulma da ake duk dare a falon gidan, Sai dai mu dinga tsinkayo hira da dariya da hayaniyar yara daga falon, Sadiyace bata faye damuwa da fitowa ba duk da dai takan dan fito ayi harka da ita, Amma ba fada ba gaba a tsakani na dasu muna gaisuwa idan an hadu wani lokaci, Sun so su ja Luba yar aikina ajiki amma da yake wayayace sai taki yarda don dama tana da dan labarin irin zaman da ake agidan daga gurin Anty Safiya don yar uwar mijinta ce, Yanzu lami yar aiki itace tare da Sadiya da salawatu inda tabasu shawaran cewa ya kamata su tafi gurin wani mutumi wanda yake bada magani na gargajiya akan haihuwa, Allah da ikon shi a lokacin da zasu fita ina a dakina kamar ance infita sai nace zan shiga gidan su Fattu don na mike kafana, Nai mamaki kwarai naganin su a tare Salawa ce ke jan motar Sadiya ta zaune daga gefen ta Lami tana a baya, Nai mamaki kwarai don bantaba ganin su a tare zasu uguwa ba ko wani guri Har shedan zai min huduban zargi amna sai nakawar da zancen da cewa Fattu wace ta rakoni kila Soloon zasu tafi, Fattu bata yarda da zance na ba sai cewa tayi Saloon har da Lami,
Zaune su ke su uku agaban malamin da suka tafi gurin shi, inda yake sauraren bayanin su, Salawatu ce ke cewa malam wata bukatace muka zo da ita akan neman haihuwa, Mu hudune a gurin maigidan mu inda sauran biyun su sun samu ko, dayan ma har yan uku ta haifa bada dewanan ba, Yace ikon Allah,cikin jinjina kai yace ina sauraren ku, tace Wanan ita ce uwargidan mu nikuma nice ta uku, agidan Ita tabiyun mu mai diya ukun yar uwar maigidan mu ce, dayan kuma bawai wani zumunta bane amma a gari guda duk suke da maigidan na mu, Murmushi mutumin yayi yana cewa to zamu fara gwadawa mugani ko akwai rabon samun haihuwa a gidan, Wasu sake saki ya basu yace su dafa su dinga sha suna kuma dama kunu dashi da jar kanwa ake amfani dashi, Sadiya wace duk ta matsu da sufita subar gurin saboda gaban ta sai faduwa yake don tsoro saboda ita irin wa yan nan abubuwan ba damuwar ta yayi ba, Sai Salawtu ta gyara zaman tace malam sai kuma zancen , Sadiya takatse da cewa sai may kuma don Allah tashi mu tafi kawai don ban son mu bata lokaci, A,a Hajiya Sadiya kinga ki tafi kawai a mota gani tafe don wanan zancen na kowane agidan nan, Ba musu Sadiya ta mike tana cewa malamin sai anjima itama Lami bayan ta tabiyo su kabar Salawtu aciki, Tana fita Salawatu tace yeye kawai malam kana jina, wallahi matar shi ta biyu ne nake bukatan akawar muna da ita a gidan idan kuma hakan bazai yi ba a danbalata ta yadda akoda yaushe sai fitina a tsakanin ta da maigidan, Murmushi yayi karo na biyu yana cewa idan don wanan ne kadai ba matsala don komai zai dawo a hannun ki, Nan ya shiga yan zane zanen sa a kasa yana kada kai yana gogewa har dan lokaci, Can yadago kai ya na duban ta yace wanan yarinyar da kike zance akanta gaskiya akwai matsala, Don zamu iya yin nasara da farko a kanta amma kuma asiri baya wani tasiri sosai a kan ta, Tace cikin kaguwa malam badai abin zaiyi tadiri ba ba akanta ko na kwana gudane,? Sai dai kuma fa ba wai lalaine aikin yai wani tasiri mai tsawo akanta ba, Saboda kamar yadda na fada maki yarinyar tana da babban al,amari mai girma kanta ,, Cikin wani irin murya Salawatu tace wallahi malam shegiyar yarinyace ni wallahi idan ma son samu ne duk ayi ,,,, Sai ta dan dakata ta duba kofan gudun kada Sadiya taji ta idan tana kusa, Sai ta sauta muryan taje malam so nake duk ayi waje da su gaba dayan su har shegun diyan su, Yace to zamu gwada mugani indan hakan zai yiyu sai muyi, Ta balle jakarta ta zube mai kudi bayan na farko da suka bashi tai mai sallama, Sadiya wace ke tsaye duk haushi da takaici ya cikata alokacin tana hango ta tafe taja wani tsuki, ta ce , Haba malama don Allah may kika tsaya jira kuma bayan munyi abinda ya kawo mu,, Murmushi tayi a cikin tace uwargida ke nan aikin san abubuwa ba karewa sukeyi ba akan zancen ciwon kafanane na dan koka mai, Ai kawi kibari da alama kila aikin wanan mutumin akwai sa,a acikin sa, Sadiya tace cikin dan tsaki ni kin san ban faye son irin wanan abubuwan malam ba wallahi, Tuki take a cikin nishadi sai dai tana tuna nen irin halin mace kamar Sadiya dake zaune dirin bawani gyara ko kwas kkwarima Wai kuma a haka take son miji yaso ta kamar ko wace mace, kai amma dai tir wallahi Namiji madai mugune wallahi wai a haka Oga ke kwana da wanan mace dirin haka ba wani show, Ita ko Sadiya sai Allah Allah take su isa gida lafiya kada wani abu ya samay su a hanya ace agun malami suka , fito,,, A cikin ikon Allah suna dawowa dani suka fara arba ina zaune a falo ina waya da Anty Amarya acikin jin dadi da farin ciki, Inaganin su kawai naji gabana ya fadi hakan ya tabbatar min cewa fitan su ba alheri bane,, A fili na furta Innalillahi wa,ina alaihim raj,un Allahuma ajirni fimasibati wa,akalifli hairum min ha,,,
****** ********** ****** Lokacin dawowan maigidan yayi don haka sai shirye shiryen taron maigida matan gidan keyi, Wanan ranan ne kuma Salawatu ke kokarin ganin ta aiwatar da duk wani shiri akan kudirin ta, ga maigidan, Tayi hade hade wanda yasha tsumi acikin sa kasancewa itace da maigidan yau, Allah ya kawo shi lafiya sai zuwa sannu da zuwa ake mai, Nima nafito nasamay shi zaune atsakiyan matan shi ana ta yan darara ku Naimai sannu da zuwa tare da tambayan shi aiki da kuma hanyanya ban eani dade ba na shige abina nabarsu, Saida yai wanka ta gabatar maida abinci da abin sha wanda ya sha jiko da tsimi acikin sa, Nan yaci yasha yai kat dashi kafin su shige daki ya karasa sauran ajikinta,,
ZEEE MAKAWA YELWA SEENABU
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣0⃣6⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH AN NUR
Kamar kullum idan ya shigo haka muka samu kulawa daga maigidan kamar yadda ya saba idan yana a gari, Har yai muna kwanakin da ya Saba yi muna idan yazo garin, Da zai tafi yai muna irin sallaman da ya saba muna idan zai koma gurin aikin shi, Ya koma muna cike da kewan shi damu da yara dama duk wani wanda ke gidan a lokacin, Munci gaba da harkokin mu, kamar yadda muka,sabayi yau da kullun, Abinda na fara lura dashi shine irin yadda aka kwana banji kira daga Yayana ba, Har a,na batun kara kwana banji ya kirani ba kamar yadda ya,saba kiran mu da safe da rana idan ya fito sallah azahar da kuma dare kafin mu kwanta, Nice na kawar da halin mu na matan hausawa naga ya kamata na kira shi don muji lafiyan shi, Amma sai na samu layin shi a busy yake don haka,sai nafan dakance shi har ya kare wanacan called din, Don nasan idan yaga nice zai yi calling back don muyi magana, Amma sai naji sabanin hakan don har nafara jin barci na dan daure na kira layin nashi, Irin yanayin da ya karba min ya sa jikina yin sanyi inda niko kamar yadda na saba nake cewa Yayyana acikin wani irin murya da nasan yana bukatan nakira shi, Ina cewa a cikin shagwaba bakaga kirana bane da kagama waya, Ya amsa a wani irin murya yana cewa nagani mana yaya akayine, ? A rin yanayin da yai magana sai naji banji dadi ba amma sai na daure nace Yaya,love munyi missing dinka ne tun jiya aiki ya rike muna kai, Tsuki naji yayi a cikin fada yake cewa idan babu wani dalili kwakwara bana son kira hakana please, Don banda enough time din yin shirmay yanzu please take note, A sanyaye a cikin kunya na amsa mai da cewa tau Yayyana insha Allahu,,,, Wani irin dummm ne ya ziyarci zuciyana don ban taba jin yanayinshi a haka ba koda fada yake min kuwa, Amna sai na anyana a zuciya wata kila akwai abinda ya bata mai rai ne a lokacin shine na hadu da fushin,
****** ********** ****** Na shiga cikin tashin hankali don yau kusan sati babu kiran Yaya Abubakar gashi kuma yai warning dina na daina kiran shi any how idan har ba reason, Ina gani kamar ni kadai ce a cikin matsala sai daga baya na fahinci har da Sadiya da Fatima, A gurin Salawatu ne kawai muke dan jin labarin shi koshi ba wai ta fada muna ba sai dai muji tana waya ko zance tace ai yai tafiya ko kuna tace ai anyi kaza a can garin da yake aiki,,,,, Wanan abin yai matukar tayar muna da hankali a gidan amma ni saboda ina tare da Ramatu da kuma mai rainon yarana sai damuwan ya dan rage min, ba kamar Sadiya da Fatima ba, Yau dai nace barin sauke girman kai na kira layin nashi, Ai har kiran ya katse bai daga ba nasake kiran shi again gab da wayan zai tsinke ne yadaga yana cewa, For Allah sake Aminatu baki barina wai na hutane da wanan bakin kiran da kike min ne wai, ? Idan ba so kike ki tarwatsa min zuciya ba don Allah ki barni na huta please, A take naji zuciyana tankar zai fashe don tsoro da fargaban abinda kunnuwana suka jiyo min daga bakin Yaya Abubakar yau, A cikin kuka nace Innalillahi wa,ina alaihin raji,un, Nace a cikin kidimay wa Yaya Abubakar may ne maka ne wai don darajan Allah ka fada min, ? Yace shout,up my friend na fada maki ban son yawan damuwa wallahi, A hankali na maimai ta ina cewa acikin wata yar siriyan murya, Yaya nice kuma mai sakar ma da damuwa yau, ? Don Allah idan wani abin nai maka kayafe min don ban san may nayi ma har yai zafi haka ba, Idan baki da na fadi zan kashe wayana don aiki nake, daga hakan ya ko kàshe wayan dip, A tsaye ya barni cike da mamaki zuciyana a lokacin jinta nake kamar zata fashe, kirjina tafito don tsabar bugawan da takeyi, Dafani naji anyi daga bayana ashe Baba Ramatuce tace cikin dan fuska mai nuna yanayi samu guri ki zauna sai muyi magana, Daya daga cikin kujerun falona na zauna a kai, yayin da ta miko min Amira wace ke bukatan shan nono, Na karbi yarinyar duk a lokacin ban a cikin yanati duk a rikice nake hankalina a tashe, Saida taga na gyara na fara bawa yarinya nono duk tana tsaye a kaina take cewa, Uwar dakina duk mace mai aure idan tana da keep shiya takan fuskanci itin wanan yanayin , Yau dadi gobe hakkuri don haka idan ma har shiga tsakani ne akayi to ki daure ki nuna a fili komai ba komai bane, Saboda na fahinci ba ke kadai ke cikin irin wanan halin dashi ba harda Fatima da uwargidan ku, Saboda naji ita Fatima tana waya a gidan su tana fadan cewa tana cikin wani hali don gaba daya mai gidan ya fita zancen ta Asmau na ce ta shigo ganin irin halin da nake a ciki ya sata tambaya a cikin rudewa May yafaru ANTYNA ? May yasamay ta Baba Ramatu, ? Ko yarinyar ce bata da lafiya duk a rude take jefo wanan tambayan a lokaci guda, Ganin yar uwata ta rude kuma nasan halin irin na Asmau kamar fetur take wuri ci na dan kirkiro yar murmushi a fuskana, Amma duk da haka bata yarda ba sai ma kara matsowa gab dani da tayi don ta ji ko may ke faruwa, Nace a cikin yanayin bacin rai, Asmau ba komai bane kawai dai al,amarin Yaya Abubakar ne wallahi, Nan na kwashe yadda mukayi nake fada masu inda kafin na karasa mai reno, Anty reno tashigo, dakin, A tare suke cewa wanan shiga tsakani ne wallahi mutumin da yazo aka rabu lafiya dashi, Tace naji uwargidan ku tana cewa har yanzu ace bai zoba bayan har lokacin zuwan shi garin ya wuce tun sati biyu da ya,shige, Amma sai dayan kishiyan naku ke cewa wai ai baya kasan yai tafiya ya tafi kasan China aiki, Da sauri nadago kai ina mata kallon mamaki nace a cikin mamaki baya ma kasan ke nan tace eh amma, wai a jiya da naji suna magana zai shigo Nigeria din, Innalillahi na fara maimaitawa don samu sauku a zuciyata saboda wani irin zafi duk jikina ya dauka, Anty Wallahi kada ki sa zancen shi a ranki ya halakaki ga banza don ke ga ko kin mutu shi baida hasara tunda ba ke kadai bace gare shi, Iyayyen ki da dinyanki damu yan uwanki mukai hasara, Gaba dayan su sukace wa Asamau wanan gaskiya ne to amma akwai damuwa a irin haka, Don babu dadi ba fada kayi da mutum ba amma ya canza maka yanayi a lokaci guda, haba dai hakan baiyi ba wallahi, Ramatu tace cikin gyara zaman ta a kusa dani ni abinda nake so Uwar dakina shine ki kwantar da hankalin ki kada sauran su fahinci cewa kina cikin rudani don Allah, Ki dake ki daure kibar wa Allah al,amari sai kiyi takai kukanki ga Allah ai Allah ba azzalumin kowa bane, Insha Allahu in har shiga tsakani ne abin ba zaiyi wani tasiri ba in har kina kai kukanki ga Allah, Abinda duk mai kishiya dole sai taga hakan sai dai ta wata tafi ta watane, Kawai dai kema yanzu dolene ki tashi tsaye a gurin neman tsari da kuma bawa yaran ki su ma don har da yaran ana iya fitar mai dasu a rai, Asamau tace wallahi da yaji kunya kuwa yaranshi yayi banza da su? Antyn raino tace kai Asmau ina ruwan asiri da yaran shi ko uwar shi ba sai arabata da shi ba, Asamau tace don Allah Anty share shi kawai, ki kama harkokin ki indon wanan tsohuwar matar tashice ai jin su za,ayi, A wanan ranan nasan advantage din zama da mutane kirki a duniya dakuma zama a kusa da mutane da mu,amula acikin mutane, Ashe yana ragewa mutum tension sosai don daga zancen da kowan su keyi nake ta picking din solution akaina, Ashe shiyasa ma,aikata maya kamar malaman asibiti da malaman makaranta masu cudanya a cikin mutane basu yawan shiga matsala saboda suna sharing din a ideas a tsakanin su , Don haka sai nayi kamar yadda sukace min na gyagije tankar babu wani abin dake damun rayuwata a lokacin,