Tarko complete novel - Chapter 108
Tarko complete novel Chapter 108: Tarko complete novel Chapter 108. ****** ********** ****** Kwana biyu a tsakani ina nan a cikin damuwa amma a boye, babu…
3,062 words
****** ********** ****** Kwana biyu a tsakani ina nan a cikin damuwa amma a boye, babu irin tunanen da banyi ba a lokacin ba Amma sai na ke kai kukana agurin Allah don samun mafita akai, Baba Wadda ya shigo rai a bace ina zaune da Fattu muna duban wasu turaren wuta da Mama biu tazo dashi daga Maiduguri, ta sayo muna tace mu bata dan kudi kalilan akai, Na gaida shi cikin girmamawa kamar kullun a matsayin shina kanin mahaifina Yana daga tsaye batan Fattu ta gaida shi yake cewa Meenatu shin may ke faruwane gidan nan wai, ? Naga yanzu ko keys din mota sai mai sunan malam yace wai muba wanan doguwar mai kama da waya ko wani abu muke so yanzu gurin ta muke zuwa, Murmushi na dan kakaro a fuskana nace hai Baba ai kasan tun can itace mai yawan kula da kayan yace cikin sauri ba gaskiya bane, Don ai shi da kan shi yake cewa muyi hakali da ita don kada ta sayar mai da kaya ko ta bata, Nai murmushi nace Baba da ne can baya yanzu ya fahince ta ai komai ya wuce, Sai naga ya kai zaune a cikin takaici yace wai ko kin san cewa gobe zata tafi can inda yake aikin, Kafin in magana Fattu tace cikin wani irin waigowa tana fuskantar Baba Wadda tace Pothercourt din zata tafi ko may wai, ? Sai da ya hade yawu bakin ciki yake cewa can din mana wai shi bai ko jin kunya ace matar shi ce Salawa, Nace wani irin kunya kuma Baba mutum da matar shi ta dace taje ne shi yasa ya tafi da ita, Sai dai abinda basu sani ba a lokacin wani irin naji numfashina ya kusa daukewa wani azababben kishi ke, taso min ina jin kamar numfashina zai tsaya, Da kyat na iya matse hawayen dake, shirin kwaranyo min a zuciya ta, a lokacin,, Ga gabana dake bada wani sauti dam a lokaci lokaci na shiga cewa cewa a raina lalai tabas Salawtuce umul,aba,isin jefa rayuwan mu a haka , Sai kuma nai saurin yin istigifar don zato zunubi ne koda ya zama gaskiya, Wata kilama ba ita bace, wani dan akasine aka samu can daban, Haka na daure har dare wanan daren haka nagan shi idona tangaran babu irin tunanen da banyi ba akai, Da naga abin zai iya yi min illa sai na mike na fada bathroom na dauro alwala nafara salloli ina kai kukana ga ubangiji hawaye yana shatata daga idanuwana , Ina zaune a haka ina tsabhi har akafara kiran sallah Allah ya taimakeni babu yaron daya farka daga barci a ranan, Daga nan namike nagara dauro alwala nazo na tayar da sallah ina ma kara mika kukana ga Allah ubangiji subbahanahu wata ala, Ranan don kada naga takaice kwanciyana nayi daki ban fito ba don kar naga tafiyan ta, Yadda tafiyan nata ya gudana shine, Bayan an fita mata da kayan tafiyan ta ne tafito tana saye acikin wani dogon riga marun colour ta saka wani dan karamin gyale a wuyan ta acikin sauri tafito don gudun makara, Ganin Fatima a falo take cewa to ni zan tafi ina sauran mutanen gidan, ne ? Ina zaki tafi Fatima take tambayan ta acikin son sanin ida zata tafi, Tace gurin Oga a takaice , Bata tsaya jin may zatace ba ta nufi gurin Sadiya daga can ta fito zuwa dakina, Ina zaune ina waya da Anty Amarya tashana wani rawan kai, Ina ganin ta naji raina ya wani dan baci amma a fili sai nake murmushi na gaisa da ita acikin fara,a Ta dan kureni da ido tana cewa zata tafi nace ina fa sai take cewa gurin yayanki yau zan tafi,,, Tana mai kureni da Idanuwan ta don taga irin reaction din da zan nuna don jin inda zata tafi, Cikin fara da yar dariya nace kice yau Yayana yana da babban bakuwa ashe ? Muna gaisheshi da aiki aiki ya rike muna shi kwana biyu Allah dai ya tsare Allah yakai lafiya adawo lafiya, Nace cikin fara,a har ina cewa bari muzo rakiya mu ga tashin ku, Tace cikin wani yanayi aida kun bari kawai don airport zamu tafi da jirgi zan tafi, Nace ai yafi sauki don tafiyan mota akwai nisa sosai wallahi, Ta amsa a dan getsire azuciyan ta tana zagina wanan shegiyar yarinyar ita bata damu ba da tafiyana take nufi komay wai ? Muna tsatsaye muna daga mata hannu Lawal mijin Fattu yaja mota da ita suka wuce zuwa airport, Suna bacewa na sauke wani irin ajiywn zuciya duk da dai nasan cewa ni a lokacin ai ba girki na karba ba, To amma ai ya kamata na samu kulawa daga maigidan na mu, bawai sai ina duty ba kamar kowa, Muna shiga daga ciki, na samu Fatima a haukace tana ta fitina, duk da nima ina jin zafin kishi a lokacin amma sai da tabani tausayi abinda naji tana fada tana cewa, Wanan wani irin rashin adalci ne ace mutum mai mata hudu ya mayar da hankalin shi a gurin guda gaba daya duk ya canza a gidan nan, Wallahi ita bazata yarda ba tunda mace ba finta kama tayi ba ba,a fita da komai ba har za a dinga mata wulakanci, akan mace yar uwar ta, Murmushi nayi ina cewa Maman Aina maynene duniya wai,? Idan ki kayi hakkuri watarana kema dake za,a tafi, insha Allahu, Sai a lokacin ta dan sasauta murya tana cewa, haba Meenatu wanan abin da mutumin nan ke yi gaskiyane, Kwanaki fa can idan kin tuna tare suka tafi kasan waje da ita yanzu kuma ace wai itace zata samay shi a garin da yake, Mu ana nufin ba mata bane ko may ko itace tafimu waye ne wai,? Nai yar dariya nace ba hakana bane kawai dai kila akwai dalilin da yasa yace tazo din, Sadiya da take daga bayana tsaye tace, wanan ba gaskiya bane kawai dai akwai wani abune wallahi, Don wanan munafukan matar da kike gani muguwace har ta karshe wallahi ni ina zargin da akwai wani mugun abin da take kullawa agidan nan , Wanda ba kowane, yasan tanayi ba amma ni kinga ina zargin koma may ye wallahi da Lami ake kulla shi, Mukace Lami kuma ? Tace eh Lami fa don itace ta kai mu gurin wani mai magani wai na samun haihuwa shine ita muguwar naga ta mayar da gurin wurin zuwan ta akoda yaushe, Nace Allah ya fita duk wani Sherri da zata kulla akan ta zai koma in har bamu da alhakinta a kan mu, , Nan hira ya kaure a tsakanin mu kowa tana fadin irin mugun abinda ya sani akan salawatu, Sam ban yarda na fadi komai ba akai don nasan cewa sunfi kusa kada nace tak nawa ya fita nasu ya boye, Don haka nace Uhmmm, kawai ku kyale ta idan badon Allah bane tafiyan ai Allah na ganin ta, Daga haka na juya nabar falon zuwa part dina kamar babu abinda ya damay ni a zuciyana, Zuciyata jinta nake kamar zata fashe min don dunkule min da naji tana cushe min, guri guda, Rana gidan namu zakace ba kowa acikin sa sabda tsit din da gidan yayi, Kowacen mu tana dakin ta zuciya babu dadi ko kadan sai kishi dake cin mu, daga karshe nabarwa Allah komai na ci gaba da harkoki na kamar kullun ina hira da yan dararakuna kamar yaddana saba bisa umurnin Anty Amarya, Hakan yasa aka zaci cewa ban damu da tafiyan Salawatu gurin maigida ba, ****** ********** ****** Isan Salawatu gurin shi komai ya canza, don rayuwan shi gaba daya duk ya canza Ya manta da wasu matan shi can a gida sai yake ji kamar salawatu ce kawai matar shi a duniya, Baya ganin kowa a idon shi sai Salawatu wanda hakan ne ma yasaka shi matsa mata da cewa sai ta biyo shi nan garin Porthercort, da yake, Duk da zuwan ta ya dan saukan mai da nauyin da yake ji a kan ta, hakan yasa a fannin Salawatu, Take shan jiki a gurin shi domin Abubakar ba karamin jarumi bane, Amma duk da haka Salawatu, ta daure tana daukan dawainiyar shi, tana yawan jure bukatan shi, koda ace bata da bukatan shi a lokacin, Duk yadda Salawatu tasan cewa zata dauke mai hankali ba tare da ya tuna da zancen matan shi na gida ba shi take yi, Don tafe take da jakar kayan sihirin ta, don ance tsafi gaskiyan mai shi, Tana jin irin yadda sukan ta masifa da Fatima ko Sadiya a waya idan sun kirashi, sai dai tace mai wai kishine ba komai ba ya fita batun su kawai, Baida yadda zaiyi tunda magani yana aiki a kan shi a lokacin don haka sai kawai ya share su, Ganin cewa na kirashi har sau biyu amma ya shareni tun a lokacin nafita batun shi bankara kiran shi a waya ba, Gashi zuwa lokacin na mayar da jikina nai kyau duk da ina da damuwa a tare dani, amna bai hanani nuna cewa nayi lafiya, Bakin cikin Salawatu shine bata taba jin na kira layin shi ba in yi korafi akai, kwatakwata ma batajin na kirashi,, Yau suna zaune a falo yana aiki a vikin system din shi ita kuma tana kwance tayi filo da cinyan shi, Tace mai wai Oga ita Meenatu bata Abujane naga bata kiran ka sam, Duk da odan yaji zance na alokacin wani irin yanayi faduwan gaba yake ji, Amma sai ya daure yana cewa ina zata tafi kawai dai bata da ra,ayin kirane kawai, Wani haushi taji a ranta don ba haka taso ya fada ba a kaina taso taja zancen ta samu ta zuga shi, Hakan yasa ta anyanawa a ranta cewa lalai sai takara tashi tsaye a kan wanan yar iskan yarinyar jikan malamai, Nan ta soma tunane irin matakin da zata dauka akaina tunda ga dama ta samu yanzu, To amma wai may ye matsalane tunda duk umurnin da aka bata ta aiwatar kamar yadda malam yace tayi, Amma sam bataga wani canzawa ba daga Meenatun har ma shi Abubakar din don bataga yana ma Meenatu cin mutunci da yake da sauran matan nashi ba, Shiru tayi tana ci gaba da tunanen irin matakin da zata dauka akai, Yana magana da ita amma sam bataji may yake fada ba har sai da yadan tabota yana cewa ta hado mai ruwan zafi yasha magani, Ta mike zuciyan ta fam da tunanen sheri tana nasa cewa, du yadda zatayi ko ta wace haline sai ta raba shi da kowace a duniya don ita kadai take son ta mallake shi a duniyan nan,
****** ********** ****** Hakuri kawai nake da daure a zuciyata amma wanan sharinyan da Yaya yai muna yai muni da yawa gaskiya don yanzu kusan wata biyu kenan rabon shi da ya ziyarci iyalin shi yana can tare da Salawatu wace ke ta cusa mai mugun agumo yana shanyewa, A zuwa wanan lokacin hakurina ya kai bango don haka nake shirin zuwa gida birnin kebbi nida yarana da sister dina sai Anty raino, Amma sai Ramatu ta tafi tafadawa mijin Fattu inda yai min nasiha kancewa nayi hakkuri don Allah kada na yarda na bari a gane halin da muke aciki, Saboda shi kan shi Lawal din yana dan yawan yi mashi nasiha amma sai yace shi kawai bai ra,ayin zuwa ne a lokacin amma ba komai bane hakan, Fitan shi daga part dina ina jin muryan shi a falo suna magana da Sadiya, A daidai lokacin da na mike don zuba ruwa a cup in sha tea saboda yarana su samu ruwan nono wadattace su sha, A lokacin ne wayana ya fara ruri alamar kira ya shigo min, Ina dubawa naga malam tsoho ne ke kirana a lokacin wani irin dadine ya ziyarci zuciya na ya baibaye min duk jikina, Na dauki wayan da sallama a bakina sai naji shi yana cewa ai nazaci kema bazaki dauki wayan ba irin na mijin ki, Nace acikin dariya haba malam banda kazafi fa Yayana ba zai taba kin daga wayan kowaba balle kai Aminin shi, Sai naji yana cewa cikin dariya ho "yan nema bata bari mijin ta yai laifi, ai, Zaune na kai a bakin gadona ina cewa malam ina kwana ya amsa cikin murya mai dadi da cewa lafiya Aminatu yaya yaran yaya kuma karfin jikin ki, Na amsa dacewa malam duk muna nan kalau wallahi, Murmushi naji yayi yana cewa masha Allahu Aminatu na kira layin mijiki jiya da dare amna bai daga wayan ba shine nace barin kiraki in fada maki cewa ina son yin magana dashi, Nace a sanyaye da tau malam zan bugawaya in fada mashi sakon ka insha Allahu, Nan naji yana cewa Wadda ya fada min cewa ya kwana biyu bai samu shigowa gurin nakuba, Nace aikine yai mashi yawa acan din shi yasa bai zo ba, Naji yace tau Aminatu na sanki da hakkuri ki kara hakkuri akan wanda kike dashi don zaman duniya sai da hakkuri, Balle irin rayuwan ku na birni da kuke mu,a mullada mutane da yawa, Ga mijin ku mai son tara iyali, ne shi a rayuwan shi, don haka ki kara hakkuri ki rubonya hakkurin ki akan wanda kike da shi,, Na amsa a cikin sanyin murya da cewa tau malam nagode insha Allahu zan tsare, amar yadda kace, Ya amsa da cewa madallah Meenatu Allah ya albarkaci auren ku yai wa zurian ku albarka ya tsone idon makiya akan ku kiyi ta addua kinji meenatu, Na amsa murya a raunane dacewa insha Allahu malam nagode zanyi duk abinda kace, Yace yauwa Meenat kada ki manta sako na dan Allah ki fada wa mijiki yakirani akwai maganar da nak3 son muyi dashi, Nakara amsawa dacewa insha Allahu malam zan fada mashi, a haka mukayi sallama dashi acikin dadin rai, Kalaman malam tsoho sun tsaya min a rai matuka inda azuciya nake cewa da malam yasan irin halin rayuwan da nake ciki a yanzu da yasan cewa ina hakkuri sosai, Inda ga rashin lafiya ga yara har hudu amma mahaifin su sam bai damu da yaji lafiyan mu ba , Yana can ya samu tsohuwar mace ya lake mata suna ta masha,an su,, Ban san lokacin da idanuwana suka kawo hawaye ba a hankali tausayina dana yarana yafara ziyaran zuciyata , Gamu a garin mutane wanda ya kawo mu garin yai banza damu ya tafi ya barmu, Cikin rashin kulawa da sanin irin halin da muke ciki a nan din, Amma yanzu mutanen gida suna can suna zaton muna nan mna jindadin rayuwa mn fita batun su, Sakon malam tsoho ne ya tsaya min a rai na rasa yadda zanyi na fadawa yaya Abubakar gashi nasan cewa tunda malam din ya bugo min wayan yana da bukatan magana da shine din kamar yadda yace, Don haka na daure na daga waya da niyar nakirashi na fada mashi sakon tsohon dake bukatan magana dashi, Kafin nakirashi sai da nadan dauki lokaci ina rike da waya a hannuwana sai faman tunane nake a raina yadda zai karbi wayan nawa, Don kada ya tuhumi ko nayi karanshine a gurin dan tsohon mai albarka, Cikin daurewa na dauki wayan na latsa kiran nomban shi inda naji tafara ringing, Kalman sha hadda na sauke sau uku kafin ya dauki wayan yadaga daga bangaren shi don dama nasan bawai lalai ya daga wayan ba,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA YAURI SEENABU,,,,,,
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣0⃣7⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH AL HAADI
JUMMA,AT MUBARAK TO OUR BROTHER'S AND SISTERS IN ISLAM ALL OVER THE WORLD,,,, WISH YOU BEST OF LUCK FOR THESE SPECIAL DAY ALLAHUMA AMEEN YA ALLAH👏👏👏
Sometimes yakan yi tunanen iyalinshi amma da zaran ya ji muryan su sai yaji gaba daya hankalin shi a tashe yake da su bai bukatan jin muryoyin su a kunuwan shi ,,, Sai yayi niyar kiran watan Meenatu amma sai yaji wata zuciya ta hane shi da kiranta a lokacin , Shi yanzu baida abin so da sha,awa daya wuce mai matar shi Salawatu don a ganin shi a gareta ne kawai yake samun piece din rayuwan shi, Haka itama bangaren Salawatu duniya ta dawo mata sabuwa yanzu sai wanda kanta yake tana cin karen ta ba babbaka,, Sai kokarin mantar da shi kowa take a rayuwa tana kara blackmailing din sauran a gurin shi musan man Meenatu, Amir yai zazzabi kwana biyu, ban fada mai ba nice da Lawal mijin Fattu mukai ta kaishi asibiti har Allah yaba yaron lafiya, Inda na godewa Allah shine yarana ba masu fitina bane don haka nake kara kula dasu una kuma basu abinci yadda ya kamata, Abinda ban sani ba ashe mijin Fattu ya fada mashi zancen ciwon Amir din sai ya kama fada wai don may ni ba zan kirashi in fada mashi ba, sai dai yaji a gurin mijin Fattu din har yake cewa shi gaskiya yagaji da irin halaiyan da nake nuna mashi hakana, Salawatu tashiga aikin zuga shi ya cika fan yana jiran na kirashi yai min cin mutunci,,, Daga karshe yaga har anyi kwanaki bankira ba ga kuma zancen ya tsaya mai arai shi ne ya yanke shawaran yau ya kirani yai min tas, Sai gashi yaga ina kiran shi a waya don na fada mai sakon malam tsoho din wanda ke bukatan yin magana dashi, Ban sa cewa zai daga watan ba amma dai duk da hakan ina ta yin kalman shahada da Ya Fattahu a bakina, Gaba da wayan zata katse naji ya daga wayan yana cewa he'llo Sai ni kuma na dauka da cewa Assalamu Alaikum, Azaton shi zancen Amir ne zanyi mai don haka babu ko gaisuwa saicewa yayi knga yaron ya kai ga galabaita yasa kika bugo wayan ko, Sai kije kiyi yadda kike so tunda bukatar ki ta biya yanzu, A hankali na maimai da cewa yaro wani yaro kuma ganin zai hauni da fada nace dakata malam , Ni ba wani abu yasa na kirakaba sai don na fada ma cewa malam yana son magana da kai don ya kiraka baka daga waya ba, Daga haka na kashe wayan a cikin bacin rai ba tare da na tsaya jiran jin amsan da zai bani ba, Raina a bace duk da jin muryan nashi ta haifar min da wani irin yanayi a zuciya ta amma sai na dake da irin abinda nake ji na basar dashi, kawai,