Tarko complete novel - Chapter 109
Tarko complete novel Chapter 109: Tarko complete novel Chapter 109. ****** ********** ****** Mamaki ne ya cika mai zuciyar shi fam irin yadda na bashi amsa…
2,908 words
****** ********** ****** Mamaki ne ya cika mai zuciyar shi fam irin yadda na bashi amsa a zafafe abinda ban taba yi mai ba a rayuwa ke nan, Sai kuma tunanen abinda nace malam tsoho yana son ganin shi ke nan ana nufin cewa na kai karan shi a gurin malam din ke nan ko may, Yasan dan tsoho da dadin lafazi zai iya tilasta shi akan mu don haka ya yanke a ranshi cewa ba zai kira tsohon ba ma kwatakwata, Bayan ya koma gida yake fadawa Salawatu wace a yanzu sai yadda tace don komai sai ya fada mata saboda irin maganin da taje ta dinkira mashi yana ci da sha da wanka , Gashi a koda yaushe rana manne dashi bata bari yayi wani isassashen ibada kamar yadda ya kamata ya dinga yi, Don tasan idan ya fara yin ibada to duk wani plans din ta zai rushe ne kuma, Gashi tasha alwashin duk sai ta rabashi da kowa nashi tabarshi daga shi sai ita tayi yadda ranta ke so, Kwana biyu kenan da wanan zancen namu amma bai kira tsohon ba don bai son fitina, Gashi kuma zuciyar shi taki sakat a lokacin don haka ya kasa sukuni da walwala a tare da shi, A cikin yanayi mara dadi yake zaune duk abin dunita ya damay shi ya hana shi sakat a lokacin Kiran tsohon yashigo mai Allah ya taimaka a lokacin Salawatu bata a tare da shi tana gida, Ya dauki wayan a cikin sanyi jiki duk da gaban shi sai mugun faduwa yake ji Muryan dan tsohon a cikin sallama irin ta addinin musulunci ya dauki wayan yana cewa , haba takwarana yau kusan kwana uku ke nan ina son ka dauki waya muyi magana, Azaton Abubakar akan zancen iyalinshine za,a yi magana sai cewa yayi, Malam nasan cewa ba kowa zai kai karana gurin ka ba sai Meenatu don bata da kunya yatake son na raba rainane wai ? Aiki yai min yawa anan shi yasa na zauna amma su duk basu fahince ni ba sun mayar da zancen fitina. Maisuna ka saurareni ni babu wanda ya kawo min karanka gurina, Matsalace ta rashin lafiya nadan samu shine nake kiranka in fada maka ko Allah yasa kun san magani acan gurin ku a taimaka min, Subbahanallahi Abubakar yace tare, da cewa malam may ke damun ka, Cikin dan canza murya yake cewa, wallahi matsalace dai ta gurma nake gani don fitsarine ke min wuyan yi inda naje yin sa, Subbahanallahi malam ai ba karamin matsala bane wanan kaje asibiti yace natafi sun bani kwayoyi kwanakin baya , Sai gashi kuma yanzu naga lalurar ta kara dawo wa kuma, Shiru Abubakar din yayi yana nazari can yace yanzu abinda za,a yi idan na bin cika zan kira ka nai maka bayani, Malam din yace madallah idan har an samu akirani don Allah don matsalan ba dadi wallahi, Shine da nakira layin ka baka dauka ba na bugawa ita Aminatu ina fada mata cewa ina son magana da kai ka kirani din, Naji shiru nake ce ko bata fadama bane yasa na kara bugo maka inji Duk ya daburce yarasa na cewa sai sabari yake yana dan kamay kamay kawai, A haka su kai sallama da junan su batare da sun tsaya wani dogon hira ba, kamar yadda su ka saba yi kullun,,,, Sai dai bayan sun gama wayan ne kowan su ya shiga nazarin sabanin ra,ayin da suka samu da dan uwa, Malam ya ce a ranshi may Abubakar ke nufi, da cewa Meenatu ta kawo mai karanshi wurin ta, Hakan Yana nufin cewa ba lafiya a tsakanin su, ke nan, komay hakan ke nufi ne wai, Amma zai kira Meenatu yaji daga bakin ta ko may ke gudana a tsakanin su, Shi kuma Abubakar din tunane yake cewa watau Meenatu bata, kai karan shi ba ke nan shine dai yake tuhuman hakan, Gashi bai ko samu tambayan lafiyan Amir ba yaji wani hali yake ciki ? Amma zai kira Lawal mijin Fatttu ya fada mashi cewa yaje ya duba mai lafiyan yaron, don hankalin shi gaba daya ya koma ga yaton, Amma kuma dai Meenatu takai yar zurfin ciki, ace wai har da malam da yake zaton takai karan shine gurin shi ashe bata kai shiba wani zancen ne can na daban ya ke neman shi da shi, Sai kuma zancen rashin lafiyan tsohon yafado mashi a rai inda yake cewa ba karamin case bane, wanan ciwon da ke son kama malam din,
****** ********** ****** Ina zaune a kasan ties din falon gida inabawa Alhasan nono tare da dan shafa mai mai a jikin shi don naga kamar jikin shi yadan bushe wayana tai ringing Asmau ta dauko tana miko min, Tana cewa, ga tsoho mai ran karfe yana kiran ki fa Anty, Abinda yazo min a rai shine, Yaya Abubakar bai kira shiba yake ganin cewa, ban fada mai bane, Ina dauka muka gaisa sai nake cewa malam don Allah kayi hakkuri nafada mashi amma bai tsaya ya fahince ni ba zan kara kiran shi in fada mai, Malam yace Aminatu yanayin yadda ya kira sunana yasani fahintar cewa serious magana zai min, a lokacin, Na amsa da cewa naam malam yace tambayan ki nake son yi amma ina son ki bani ansa tsakani da Allah, Na amsa mai da cewa insha Allahu malam zan fada ma koma may nene idan na sani, Ya ce Meenatu may ke tsakanin ki da mai gidan ki ne wai,? Tambayan tazo min a bazata don haka sai nai shiru batare da na iya cewa komai ba, Naji ya kara kiran sunana a karo na biyu don haka maimakon nayi magana sai kawai na saka mashi kuka, Bayi magana ba sai ji nayi ya kashe wayan nashi hakan yasani barin falon zuwa uwar dakin nawa, inda na kwanta saman gado ina mai zubar da hawaye, Kiran layin malam din na kara yi inda ya dauki wayan da murmushi yana ce min Meenatu kwantar da hankalinki kiyi min bayani yadda zan fahinta, Nan na fara zayyana mai irin halin da muke ciki gaba dayan mu a gidan har yaran mu, Sai cewa ummm, ummm malam ke yi da fadin assha assha, Nakwashe komai kaf na fada mai inda naji ya sauke ajiyan zuciya yana cewa akwai sakacin addini ga maisuna na, sosai, Kuma bayan haka shi asiri wani babban al,amari ga maiyin shi idan yasaka gaba a yin shi sai yaga yakai ga samun nasara, akai musanman sanan yake sake wani sabon shiri, Don haka tun farko Meenatu ita wanan shumar abokiyar zaman taku bawai ta bar halinta bane akoda yaushe a cikin kawo maku hari take, Amma Allah yana tsare ku daga sherinta yanzu haka wani sabon shiri ne ta sake wanda yafi wanda take a kan ku can baya, Amma aida kin fada min tun lokacin da kika fahince cewa ga inda suka tafi don kinga tana shanmatan shine ta hanyan cewa maganin haihuwane take nema, Tana tapka barna ta wanan hanyan wanda har halan ya gusar mai da hankalinshi baki daya, Wanan matar ba sai an fada ba tafi ku wayo sosai wallahi duk acikin ku babu sa,an yinta, Na amsa da kai dakuma fadan cewa hakane malam nima na sani duk sunfi wayo da shekaru, Sai naji yai murmushi yana cewa, amma ai Aminatu mijin ku kuma yafi kaunar ki aduk cikin ku, Cikin kuka nace malam haka dai ake gani amma gaskiya yafi kauna ita Salawan da Fatima ai, Malam yace ba gaskiya bane hakan Aminatu Abubakar yana kaunan ki tunfarko don da bai kaunar ki da saboda fitinan mahaifiyar shi da ya sake ki, Amma saboda yana kaunar ki duk fitinar Ladi dole ta saka mashi ido dake, gashi auren ku ba wani dadewa yayi ba Allah ya albarkace ku da zuria masu albarka, Murmushi nayi don jin may yace yace to ko ke fa amma zaki ce wai bai son ki yana sonki fiye da kowace mace a duniyan nan, Na bude baki zanyi magana sai yace Aminatu watarana ko ina da rai ko banda rai zaki fada da bakin ki nace yana son ki yana kaunar ki fiye da tsan manin ki, Nan yaci gaba da kwantar min da hankali tare da kara min karfin gwiwa akan na kara hakkuri kamar yadda nake don Allah yana tare da masu hakkuri akoda yaushe, Daga karshe yake fada min cewa insha Allahu badadewa ba zasu yi kokatin ganin sun karya duk wani asirin da Salawatu taiwa Abubakar din ,
****** ********** ****** Sati guda bayan hiran mu da malam sai gasu sunzo muna bakin weekend shi da salawatu abinda yasa na kirashi da bakin weekend shine, Tunda suka zo gaba dayan mu baida lokacin mu sai uguwa suke fita shida ita wai zuwa gurin tsabgogin ta da yan uwa, Sun iso a cikin dare ne babu wanda yasan cewa zasu shigo a ranan, Ramatu ce tazo take fada muna isowan shi sai da na dauki lokaci sannan nafita zuwa yi mashi sannu da zuwa Na samay shi adakin shi tsaye yana waya ina saye da wani dogon riga wanda ya matse min jiki hip's dina sun fito gwanin ban sha,awa, Daga kofan shiga dakin na tsaya ina cewa sannu da zuwa Ya daga min hannu alaman ya karba min ban tsaya ba na juya nabar dakin abina zuciya ta tana muradin shi alokacin amma sai nadake na basar dashi kawai, A tsakiyan falo na hadu da salawtu tafito ta rufa towel a jikin ta banga wani canji ba a gareta, Fuskana dauke da fara, nake cewa aa mutanen kasan kudu sannu ku da zuwa tafiya babu sanarwa balle a shirya maku, Saicewa tayi wallahi sai da rana muka shirya tafiyan batare da mun wani shirya ba, Aisha ce ta katse mudaga sakon da take sanar damu cewa itace ta sa aitafiyan a hakan, Aisha tana ce min mummy Amir ya fadi bakin shi yana jini, Nace a hanzarce a ina take ce min a falon mu yataka ruwane, Da sauri na wuce batare dana karasa saurarenta ba zuwa gur8n duba Amir din wanda ya fadi, Sai harkokin su suke muna kallon ikon Allah ba wanda ya tanka masu, Allah ya taimakeni da farko har na tayar da hankalina kamar yadda naga Fatima takasa zama ta kasa tsaye, Daga baya bayan na roki Allah akan ya bani hakkuri da dauriya sai ko Allah yacire min duk wata damuwa a tare dani, Nan na mayar da duk wani abinda sukeyi ba komai ba inda nake shigewa part dina nida yarana da duk wasu mutane na don kafin duk su fito da safe duk mungama wani abinda zamuyi mun shige ko, abin mu, Ashe wanan abin yana bata mashi rai don dama tun can farko shi mutum ne mai son gani iyalin gidan sun hadu a falo ko guri guda ana cuwaniya a tare amma sai gashi ba kowa daga part dina duk muna daga cikin sashen nawa,gaba dayan mu, Ina zaune a tsakiya falo ina bawa yarana nono ga plate din abinci daga gefena kaina babu dan kwali, sai gashina da yasha gyara yana dukule yana sheki, Dariya na keyi alokacin saboda yadda yaran ke ta kokarin kama nono a tsakanin su, Bamuyi aune ba sai ganin shi mukayi yadaga labulen falon fuskan shi a daure yana bin mu da kallo daya bayan daya, Tankar ban gashi ba sai kokarin gyara kwancin hassan da na keyi asaman ciyana sai ya dago kafa guda yatokarawa dan uwan shi take abin ya bamu dariya na cire kafan yaron cikin cewa ji babban kawai kana jan dan uwan ka fada, Daga can kusurwan dakin Asmau ke cewa sannu Yaya, Ya amsa a dakile, dacewa yauwa sannun ku dai, Ban kula shi ba naci gaba da wasa da yarana nafita batun shi kamar zaiyi magana sai kuma naga ya juya yafita, Nabi bayan shi da kallo har yakulewa ganina, na sauke ajiyan zuciya tare da dan lumshe idanuwana, Fitan shi yai daidai da fitowan Salawatu daga part din ta sai wani kallon tuhuma take mai na may yakaishi part dina, Nan yadan fara kamay kamay yana cewa tun safe banga kowa a waje ba daga cikin yaran nan shine ashe suna daga ciki, Duk ya rude saboda wani irin abu da yake ji lokacin da ta watso mai harara akan may yasa ya shiga gurin mu,, Allah ya kyauta Sadiya tace daga gurin da take zaune a cikin tagumi, Duk hiran da yake mata fuskanta a murde yake bata saje mai ba duk ya shiga rudani ya susuce saboda rashin gani sakin fuskan ta, Itako sai cika take tana batsewa wai ya kula wata ba ita ba, Fitina irin na Salawatu duk da tana can tare da maigidan bai hanata da tazo ba wai ta karbi girki,, Inda yadan turza shine da yake cewa may zai sa ta karbi girki a ranan bayan mu ukune anan din, Sai take ka manta cewa Meenatu bata girkine ita yace saboda may fa sai take cewa wai aikin da akai min mana, Yace har yanzu bata karbi girki bane may taje jirane wai ? Bata saurare shi ba ta shige bedroom din shi ta kwanta abinta ba yadda ya iya dole ya shige gurin ta, Da safe washe gari ina kwance ban tashi ba daga barcin safen dana koma yi,naji ya shigo dakin nawa a cikin barci naji muryan shi yana magana yana cewa Asmau baya tashi bane, Sai Asmau take ce mai tana ciki ta kara kwantawa ne ya shigo dakin yana saye da rigar barci a jikin shi, Ance jiya Amir bakin shi ya kunbura wai ya fadi ya akayi yafadi yake tambayana, a lokacin da nabude ido mukayi arba dashi, Yana tsaye ya harde hannayen shi a saman kirjin shi yana mai kura muna ido nida Amira kwance a saman gado, Sai da na dan gyara kwanci ya tare da kokarin bude idanuwana da sukai min nauyi nace, Faduwa yayi a saman ties shine bakin yadan hau, Ba,a goge gurin ne da har akabar ruwa ya fadi har baki ya fashe, yana inane yaron ? Nace a cikin daure fuska yana gurin Ramatu ta goya shi don gurin yana mai ciwo baiyi barci ba da dare, Shima fuska a daure ya saki ajiyan zuciya yana dubana a cikin wani irin yanayi maradadi yace ya akayi baki karbi girkiba har yanzu, Mamaki da takaici ne suka rufeni sai kawai na kallr shi na kawar da kai, Tuni haushi ya rufe shi sai naji yace ba ke nake tambaya ne kin kyaleni, Nace saboda lafiyata shi yafi min komai a rayuwa har yaushe na tashi daga jinya dazan je karban wani girki can, Haushi da bakin cikin maganata suka rufe shi sai yake cewa ni kike raina wa wayyo haka meenatu ? Nace a takaice bazan karbi girki ba sai naji karfin jikina sosai saboda idan wani abu ya samay ni hasaran iyayyena ne da yan uwana, kawai, Ido ya kura min acikin takaici don danne zuciyar shi kawai yake don wani irin haushi da takaicina yake ji a zuciyan shi amma dai ya daure yana kokarin ganin yafitar da hakin shi gareni, Banza nayi dashi tankar ban sanda yana gurin ba don nima zuwa lokacin haushin, shi nake ji, Kawai don ya mayar dani ban san ciwon kaina ba zai shigo min da wani zancen wai karban girki, Bai kara cewa uffan ba ya juya yafita daga dakin rai a bace nima jin yafita na kuta tare da kokarin mikewa ina cewa don ina Aminan mahaukata kawai don ka bukaceni sai na samay ka a haka babu wani kulawa ko dubaiyya, Tun wanan lokacin nakara kama kaina ga harkan su har suka karashe abinda ya kawo su suka kwasa suka koma, Koda zasu tafi har sun shirya tafiya ne na samu labari a gurin Baba Wadda yake ce min wai ranan zasu koma da dare, Daya shigo bani kudin amfanina ne yakecewa wai sun fito ke nan su zasu koma Batare dana kalle shi ba fuskana a daure nace Allah ya sauke ku lafiya, yasa kai yafita don kada taga ya dade a gurina, Fadan su biyu da fatima wanan zuwan don ita sam bata da hakkuri ko kadan, da sun mata data maganta kuma ba magani sai makara kiyayyan dake shiga tsakanin su Inda na koma asibiti don likita ya kara duba lafiyata tare dana yara kamar yadda suka umurce ni danayi duk karshen wata saboda jikin danaji da yawa, A gidan bayan tafiyan su a haka muka kasance acikin damuwa saboda wanan zuwan ya tabbatar muna cewa da control din Salawatu yanzu yake komai, saidai yana iya kokarin ganin ya dan boye amma abin bai boyuwa, Saboda sunan sunyi girkine kawai amma yana manne da Salawatu duk yini ba sauki ga al,amarin sai na Allah, Bayan komawan su acan sukai ta fada a tsakanin su wai may zai sa yazo yana kula sauran matan shi, Yazo yana mata wullakanci agaban mutane duk ta saka shi ya shiga cikin wani yanayi gashi ta karbo sabon kulli agurin bokayen ta duk ta rikitashi sosai, Wani irin shaukin ta yakeyi don sam bai kaunan yaga bacin ranta ko kadan, Ga kudin da take karba agurin shi kamar an aiko ta ba tausayawa sam,
ZEEE MAKAWA YELWA SEENABU
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣0⃣8⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH AL BADEE'U Yan uwa musulumi ina muna fatan alheri acikin wanan lokaci da muke a cikin sa na shiga sabuwar shekaran nasara,