Tarko complete novel - Chapter 110
Tarko complete novel Chapter 110: Tarko complete novel Chapter 110. Yau kimanin sati uku da tafiyan su inda muna nan muna ta rokon Allah akan irin halin…
2,803 words
Yau kimanin sati uku da tafiyan su inda muna nan muna ta rokon Allah akan irin halin rayuwan da muke a ciki, Sannu a hankali nake shirin tafiyan da naiwa yaya Abubakar nason zuwa ganin yan uwan mu a gida Birnin Kebbi, Mun shirya tsab inda zan yi tafiyan ne da duk wani wanda ke tare dani don har da Ramatu da ita zamu tafi saboda diyanta babu kowa a garin duk sun tafi makaran ta a lokacin, Nan muka rufe part dina inda zamuyu tafiyan ne da motoci guda biyu Lawal mijin Fattu wanda ke gudanar da komai na gidan a halin yanzu shine, yai muna shirin tafiyan,, Abin idan ka gan mu gwanin ban sha,awa inda mota guda nice da yarana sai su Asmau na da Ramatu Antyn Nani, da suke cewa Antyn raino, atare dani, Baba Hamza' yana jan mu, Sai dayan motan da ke dauke da kaya Baba Wadda da abokan su yusuf, da Aminu su ka biyo mu , Mun iso da yamma lis, lokacin marance yayi akwai mutane a kofan gidan mu masu daukan karatu, Isowan mu yai daidai da akwai wasu daga cikin iyayyen mu a gurin karatun, Tsayuwar motocin mu a kofa yajawo hankalin mutanen kowa idon shi a kan mu, Kafana dake saye a cikkin takalman kasan indiya na kamfanin Bella, bakake, na fara sakowa daga waje inda ya fara daukan idon jama,an gurin, Nan, muka fara fito gwanin ban sha,awa inda akayo kan mu ana muna sannu da zuwa acikin so da kauna, Sai murna da jin dadin munga yan uwa mu keyi a lokacin inda yarana ake ta karban su a cikin mutunci, ga kuma so da kauna, A part din mahaifana muka yadda zango inda jama,an gidan mu da yara ke tururuwan zuwa muna sannu da zuwa, acikin murna, Ga ruwa da fura mai sanyi yaji nonon shanu a aje muna a gaban mu ga kunun aya sai kamshi ke tashi, Murna da dokin ganin mahaifiyana ya hanani shan komai daga cikin abinda aka gabatar muna, Dije tashigo inda na mayar da hankalina a garesu muna yaushe rabo suna min yaya jiki da sauran jama,a, Dije tace Meenatu wa zai Hank a haka yace kece kikayi irin wanan jiya wata bakwai a renon ciki asibiti har kika kai kusan wata daya acan, Dan gajeren murmushi nayi, nace alamarin Allah ke nan Dije, Tace wallahi baki ga yadda kikayi wani kyau bane kin dan yi kiba ga haske, Naji dadi sosai da,ba,ace na ramay ba sai gashi duk da halin rayuwan da nake ciki ana cewa wai nayi kiba, Hakan ba karamin dadi yai min ba araina so sai don ko ba komai ai zan ji dadin kara boye sirina sosai, Sai kuma Dijen ke cewa ga abin sha annaje maku banga kinci komai ba kin san fa cikin ki har yanzu akwai jego a tare da ke, balle wanda ke shayar da har diya uku, alokaci guda, A cikin yar sakin fuska nake cewa sun min sanyi ne kin san ina shayarwa shiyasa ban son shan abu mai sanyi , Saboda yaran musan Amira wace bata da wuyan kamuwa da sanyi da zaran ta dan sha sanyi yanzu kiji ta fara atishawa, Dije tace, ashe yaran kulawa suke samu sosai shi yasa sukai wani irin kiba tankar inji na hura su, mursmushi kawai nai mata muryan mahaifiyata ce naji tana cewa, Tau a kawo maki abincine inji Mamana Saratu, Nadan girgiza kaina nace wallahi a koshe nake naciyo abinci a mota da mukazo da shi, Sallah zan tashi na dauro alwala kafin aikira don ko la,asar bamuyi ba, Dije ta bude baki za tai magana mukaji muryan daga waje ana fada wai don may za,a kawo kayan da mu kazo da su a part din iyayyena , Dole akaisu part din ta har da mu din mu koma acan tunda aure nake ba wai a karkashin su muke ba, Ikon Allah nace alokacin da na ke aduke daniyar daukan buta don zuwa yin alwala,, Mamaki ya cika min zuciya nace a cikin dakiyar zuciya akawo min kayana nan do bana wanda ake tsan mani bane, Wanan kalamin da yafito min abaki ya farune a sakamakon jin haushi abinda mama takeyi haka, Gashi dan nata da take kuri dashi ba ma wani kulawa muke samu daga gareshi ba da har zata fadi hakan, Don haka kamar yadda na bada umurnihakan yaran gidan mu yan kan,ne na suka dinga jido min kayana zuwa part dina tare da taimakon baba Wadda, Yau na bawa Mama Ladi mamaki kwarai inda ta taso wai da zuman yi min masifa akai, Amma abin mamaki tana shigowa alokacin na idar da alwala ina dan diga ruwa a bakina, ina karanta lailahaillah wa,adahulashari,kallahu har zuwa karshe shi, Ta shigo part din namu babu ko sallama tana cewa ina Meenatun din take ne, Na amsa da cewa gani Mama, sai kuma naga tayi dan dabur dabur duk sai tai tankar ta dan rude tana cewa, Au to kunzo lafiya ? A cikin mamaki nima na karba mata gaisuwan dace wa Lafiya Kalau, Yanzu idan nai sallah zan shigo ai, mu gaisa, Sai take cewa nazo ne akan naga ana son nuna min iko nida jikokina nace azo dasu inda nake akece min wai kin ce komai a nan za, a kawo maku shi,, Nace eh duk wani, kayan danazo cewa nayi akawo min su nan inda nake, ne, nace mata hakan ba a cikin rashin kunya ba, Ido ta dan kura min kamar wace zatai wani magana amma kuma sai naga taja ta juya zuwa inda ta fito, rai a bace, Na rasa dalilin da yasakata kariya da ga masifan da tazo muna dashi, a part din mu, Abinda ban sani ba shine ashe wanan hailalar da tasamu ina yi dana idar da Alwala shine ya sakata yin taushi saboda karfin shi, Tana daidai fita daga part din namu sukayi kicibis da mahaifina wanda dawowan shi ke nan daga gurin sana,ar shi, Kallon kallo suka sakar wa junan su kowa yana tuhumar dan uwa, Saboda shi Baba yana mamaki don ganin ta a part din shi don yasan ba banza ba tazo sashen nashi, Yayin da itama take wa Baba kallon macuci yana son su mallake ma ta danta su kadai,
****** ********** ****** Bayan na idar da sallah nashiga cikin gida don na gaida mutane niyata sashen Mama Ladi ta zama karshen shigan mu, Amma ina shiga sashen malam tsoho sai naga Baba Buhari zaune tare da malam inda naji malam din nacewa yauwa gama yar halas din ta shigo, Na karasa da mamaki ina gaida duk wani wanda ke gurin a lokaci amma kuma sai na fahinci iyayyenmu maza ne zaune su uku sai Mama Ladi daga dauan gefen tare dasu Mama Dije, Malam kecewa na samu guri nazauna na saurara da kyau, Bayan na zauna yai dan gyaran murya sai a lokacin nadan lura da dan tsohon naga yaramay min sosai a idona ga tsufa ya taso mai sosai duk ya yankwamay sosai, Sai naji wani iri a raina mutumin da yake fari a tsaye karfafa dashi wanda zance hasken shi da yawa yan gidan mu suka kwaso, Gyaran muryan da yayi ne yasani dawowa daidai daga dan tunanen da na shiga, Naji yana cewa dama zan aika akira min ke ne sai gaki Allah yakawo muna ke, Yace Amina ko kin san cewa mijin ku yai maku masauki a gidan nan ? Cikin mamaki nadaga kai alaman eh nasani sai naji tau madallah don Allah daga yau idan kin zo garin nan a nan zaki dinga sauka bake ba har sauran yan uwanki matan shi, A cikin sakin fuska batare daxnuna komai ba nace insha Allahu malam haka za,ayi yace madallah Allah yai maku albarka na amsa da amin malam,, Ya juya inda iyayyen mu su ke yana cewa shike nan kunga yanzu anraba garda sai ta koma dakin ta ta zaunq har tayi kwanakin da zasuyi su koma, Har zan daga na basu guri sai naji malam nace yaki mana Aminatu dawo mana mu gaisa, Sai na koma na zauna ina murmushi ina cewa aida zan bari sai da safene mu gaisa, Asmau kaunata na kira a waya ina fada mata cewa su je can part din mu su gyara min dakin da akace yanazamana, Wanda lokacin da su Fattu suka zo sunan Amir aka sauke su a cikin sa, ida nace su katbi makulli a gurin Baba Buhari, kamar yadda malam yace, Ana gama watsewa Dije ke cewa ikon Allah yau Ladi ce wai ke fada a gidan akan zuwan Meenatu, garin nan, Malam yai murmushi kawai mai nuna alaman yasan may yin hakan ke nufi ko kuma inda Mama Ladi din ta dosa , Sai naji kafin Dije taci gaba da magana yace ke Aminatu , Nayi maza na amsa mashi da cewa naam malam , Yace saurareni ni ki ji may zance maki don ki samu kije gurin yaran ki don dare ya soma, Jin haka yasa su Dije mikewa don barin gurin saboda sun san cewa zamuyi serious magana kenan, da shi, A cikin natsuwa ya somayi min magana dacewa kun zo lafiya ko yaya karfin jikin ki, Na amsa mai dacewa Alhamdullahi na samu lafiya sosai, Nace min samay su lafiya ko sai naga yar murmushin yake yana cewa lafiyan dai da sauki Aminatu, Mijinki bai fada maki cewa banda lafiya bane duk yan watannin nan da suka shige, Mamaki naji sosai jin malam yaji jiki haka wai yai rashin lafiya banda labari, Ina daga zaune ina mamaki naji yace, ai shi da kanshi ya dinga turo min da magani nai tasha har na samu lafiya haka acikin ikon Allah Al,amarin yaya Abubakar yai nisa kawai a barshi da halin shi yanzu ace har malam tsoho yai ciwo haka ban da labari daga gurin shi, Mama Ladi tana barin guri ta daga waya ta kira Abubakar tafada mai karya da gaskiya, dama mai neman fitina ne aiko a take ya hau fam, Na samu an gyara muna daki yadda ya kamata Nida Ramatu da Aisha sai Asmau na muka kwana a part din da yarana, Yai kiran layin waya na a cikin daren nan bai samay mu ba take ranshi ya kara bacu sosai, yakira ayin Baba Wadda wai ya kai min waya din, Amma sai ya samu har mun kwanta mun rufe part din ya buga mai waya yaba sheda mai cewa ya samu mun rufe kofa ko, Bayan sun kashe wayan ne yake Nanak n jun Baba Wadda yace a part din shi nake zaune sabanin yadda mama ta fada mai, abinda ya dan sasauta mai rai ke nan, Washegari tun da far safiya Mama Sa,a ta shigo ta kwashi yaran zuwa part din ta tai masu wanka ta shirya su tsab ta dawo min da su, A take aka cika mu da abin karyawa kala kala daga wani part na cikin gidan mu, Abinci sai wanda ranka ya zaba zakaci gashi nan a zube inda yan matan gidan mu duk suna a tare da mu munata hira, Sai da kyat na saci jiki zuwa cikin gida nagaida iyayyena maza kafin su fita sai dai ban samu mahaufina ba don shi mutum ne mai sakko zuwa gurin bida, Nadawo nashiga raba tsara daga cikin gidan mu har makwabtan gidan mu, Tsofin tufafina duk na kwaso su na raba wa yan uwana mata don nayi sabbin din kuna, Iyayyen mu matan na sayo masu turamay zannuwa a Sahad Store danagani very chief sai faman murna suke yi, Waban rabon shi ya kara tayar wa mama ladi da hankali don sai take gabi dukiyan danta ne na debo nake rabawa a gidan mu, sai faman mita da jinini takeyi tana masifa, Kwana biyu da zuwan mu nadan shigo cikin part din mahaifana don in gana da Mama ta, Anan Anty Safiya ta samay mu wace munyi da ita zata shigo mu fita tare don wai Anty Nani ta bata labarin duk irin halin zaman da muke yanzu a ciki gidan mu, Wanda sam ban so hakan ba don wanan ai sirinane ba abin fadawa wasu bane, Saukin abin Anty Safiya ce duk da ciki guda suka fito da Yaya Abubakar tana iya nata kokari a kaina, Zaune muke muna hira da ita da Mama sai wayata tai ringing, ban kula dana dauka ba har ta katse a lokacin kafin na dauko ta acikin jakata ta, Yaya Abubakar ne yakirani wanda sam ban tsan maci kiranshi ba a lokacin, Kara kirana yayi inda na dauka a cikin natsuwa ina mai yin mai sallama, A cikin wata murya mara fara,a naji yakarba sallaman ina kokarin gaishe shine naji muryan shi maikama da fada yana cewa, Ba,a fada maki cewa na bugo waya abaki bane ranan da kukazo, Nima acikin muryan da bata da ma,ana na amsa mai da cewa ba wanda ya fada min ni, Yace OK kuma sai ke baki azanci ki bugo min ba saboda rashin sanin ya kamata ko ? Mamaki zancen ya bani har nace a ,a acikin wani irin yar sauti, Yace a gadarance yaushe ne zaku dawo ne wai ? Da mamaki na ce dawowa kuma Yaya har yaushe mukazo da za a fara zancen dawowa, A hasale yace OK anan zaku zauna kenan ko nace cikin muryan fushi a dadare ni bance a nan zamu zaunaba amma dai naga duka duka fa yau kwanan mu biyu da zuwa ko gurin yan uwa bamu fara zuwa ziyara ba, Ok bazaku dawo yanzu ba kenan kike nufi ko ? Nace a cikin yar murya aa bawai bazan dawo bane , So nake gaskiya mu dan huta agida mukwana biyu muga yan uwa sosai,,, Dip naji ya kashe wayan ba tare da mun kai karshen zancen ba, Na dan dubi wayan ina cewa acikin raina jifa kamar wanda mu kewa wani abu a gidan mutumin da zai yi kwana barkatai baji lafiyan mu ba ma Shiru Mama da Anty safiya su kayi su na sauraren mu, Anty Safiya ke cewa wai so yaje ku dawone kuma na gyda mata kai a hankali alaman eh , Daga haka mukai shiru sai mamace tace kashen wayan yayi ke nan nace eh rai a bace don duk ya na son bata min lissafina, Mama tace to ai kiranshi zakyi don kiji yaushe yake son ku dawo Anty Safiya tace gaskiya ne, Amna ahi kuma yaya tunda ba, agari yake ba ai yabar ku kuyi kwanan k ku mana, Mama tace kirashi dai kuji idan yace ku koma ne ba sai ku koma ba, Ban soba amma dole na daga waya na kirashi don mama ta tsureni da ido Ina kira kamar ba zai dauka ba can naji ya daga wayan yana cewa yaya akayine kuma, Cikin hade wasu miyau masu daci na ce naga kayi fushi ka kashe wayan bamu gama magana ba, Yace, kina ina yanzu nadanyi dummm a daure nace ina tare da Mama Sare da Anty Safiya, Yace OK nasan da hakan idan sati yai maku sai ku shirya ku dawo gida, Zanyi magana naji ya kara kashe wayan batare da yajira yaji may zance ba, Nace a dan hasale ni gaskiya da malam zan hada shi don ya barmu muyi kwanaki mu a nan, Cikin bacin rai mamana take cewa tunda yace ku koma ma may zaku tsaya yi kuma basai ku shirya ku koma ba, Batare da nacewa Mama komai ba naci gaba da harkokina inda muka shirya ni da Anty Safiya muka fita zuwa unguwa a cikin motan maigidan da nazo da ita, Duk inda na wuce zaki ga mutane suna kallona gwanin ban sha,awa, Ba komai ke kara jan hankalin mutane ba sai ganin noban motar da kuma irin kyaun motan da tsadan ta, Gashi nima din duk da karama ce ni amma sai motar tasakani komawa wata babban mace, Anan kwatance ya tashi a cikin gari ana kwatancen da Yaya Abubakar wanda mutane ke cewa iyanzu ya zama wani last Don a Abuja,,, Sai da dare bayan mun dawo daga unguwa da Anty Safiya, Nasamu malam tsoho ina sheda mai abinda Yaya Abubakar yace na mu dawo zuwa kwana uku, Fada ya fara yi yana cewa shida baya gari idan kun koma wani abin zakuyi mai acan din, Dadi naji don nasan cewa zai mai magana sosai, akan yabar mu mu sha gida, Hakan akayi don yai mai magana cewa shi yace na tsaya gida har a kwana biyu don nadan kara samun sauki, Murmushi yayi kawai don yagane cewa plan di na ne hakan nice nasa malam din yai mai magana don haka kawai yace ba matsala, Ashe bada gaske yake ba don waya ya bugawa Babana cewa kada na wuce kwanakin da ya bamu, Malam yana ta ci gaba da abubuwan da ya kamata ya taimaka muna dashi a cikin tsanaki,