Tarko complete novel - Chapter 112
Tarko complete novel Chapter 112: Tarko complete novel Chapter 112. ****** ********** ****** Sai harkokin gabana nakeyi irin shirin zuwa Sokoto gurin…
3,356 words
****** ********** ****** Sai harkokin gabana nakeyi irin shirin zuwa Sokoto gurin zancen auren Uncle dina don na kara bawa Anty Amarya hakkuri, Tsab na shirya nayi kitsona da kunshi da sauran yan shirye shiryen zuwa buki, Muna zaune ina jiran dawowan Asmau wace ta tafi gidan wata makwabciyar mu anso min sakon da zankaiwa Anty Amarya, na kilishi wanda wata mace ke yi, acikin shiya mai dadi, Shigowan Asmau da leda bakake manya manya a hannuwanta, ina kallo a cikin mamaki, don naga abin yai yawa sosai very chief, Take ce min in bari tazo zata dauko abu a wajene, yanzu tadawo, Na cewa Ramatu wanan abu da araha yake Baba Ramatu duk wanan abin akan dubu biyar kawai, Ban idar da zancen da nakeyi ba naga Asmau tajuyo da sauri da alaman a dan tsorace take,a lokacin, A tsorace, nake kallon ta ina son sanin ko may kefaruwa tashigo haka agigice, Aikuwa kafin tai magana sai ganin Baba na, nayi tare da jin sallaman shi, Da sauri namike tare da dan gyarawa ina cewa sannu da shigowa Baba muke cewa a tare, Ya amsa kamar mai rada yana cewa kuna dai lafiya ko mamana na amsa dacewa acikin dan girmamawa lafiya kalau muke Baba , Ya amsa da cewa yauwa damanazo in sheda maku cewa gobene zaku koma ko ? Cikin mamaki na dan dago kaina ina dan girgizawa nace Baba ba gobe bane sai zuwa jibi, Gobe Sokot,,,, zan ke rufe min baki mara hankali Babana yace a cikin dan sakar min harara ranshi a bace, yake cewa sam ban taba zaton haka ba daga gareki, Mijinki duk ya damu da ya ga kun dawo amma ke don rashin sanin ciwon kai har kitsaya ko jiran may, o,hoo, Gobe kishirya ki koma dakin ki don ban son inkarajin kince wai malam yace, sai kin kwana biyu, Ina daga gefe na rakube acikin tsoro don ganin irin yadda hankalin shi ya daga,, akan zancen tafiyan don da alama Yaya Abubakar ya fada mai maganganu akan zancen,, tafiyan irin yadda naga hankalin shi ya daga, Ya juyo yana cewa inda Baba Ramatu take zaune yana cewa gobe ku kama hanya ku koma kinji boyar Allah, Kanta ta gyada acikin da nuna tsoracewa take cewa insha Allahu zamu kama hanya goben, Muna hada ido da Baba naga ya sakar min harara yana cewa rashin sanin ciwon kai zaki tsaya kina gaddamar komawa da mijin ki, Kaina na kawar gefe cike da jin haushin Yaya Abubakar wanda ya kawo min cikas ga al,amurana da dama, Ranan harda kuka nayi saboda bacin rai, da bakin ciki ga zancen zuwa gurin uwar dakina Anty Amarya babu shi ,
Washegari shiri sosai na keyi don ko zuwa gurin malam tsoho banyi ba saboda bacin rai gashi nasan cewa tafiyan dare kenan zamuyi yau don rana yai muna, Ban san ya akayi malam tsoho ya samu labarin tafiyan mu ba sai gashi a fusace yana cewa ,, Aminatu dama tafiya zakuyi banda labari ashe ? To nace baza kuba tafi din ba sai kwanakin ku ya cika zaku koma, Kuka kawai na saka mashi hankali a tashe ina cewa malam ya hadani da su babane sunce sai na koma yau din nan,, Bazaki koma ba nace nace babu inda zaki tafi sai kun cika sati uku, Baba shaibu da baba musa suka biyo malam suna cewa haba malam kabari su tafi tunda shiyace su dawo hakana ai sai su shirya su koma, Dakyat akasamu malam ya yarda gobe da safe zamu kama hanya mu koma Abuja, Saida dare muka samu kebewa da malam a part din shi inda ya aiko a kirani, Sai dana zauna na natsu sosai sannan yake cewa Aminatu ai dazun ko da ki kaga ina fadan baku komawa da biyu naken hakan,, Saboda ina son nn samu n 8gudanar da sauran shirin da nakeyi akan shi din kiga kuwa ai ba damar na fada masu afili don haka na jajirce masu kawai, Sai a lokacin nai yar murmushi don na fahinci plan din tsohon, Anan ya bani duk abinda zai bani tare da bayanin duk yadda zanyi, Anan yake kara jamin kune da nasiha acikin taushin murya nan nake godiya tare da kara mai bayanin abindake wakana a gidan, yanzu, Cikin dan yi murmushi tare da gyara zaman shi yana cewa in har kinyi duk yadda nace tau insha Allahu zaki ceto dan uwan ki daga halakan shuumar mace, Nace insha Allahu malam zanyi kamar yadda kace ayi komaida mun koma, Munyi sallama dashi yana ta sa min albarka tare da fatan gamawa da duniya lafiya, inda yake ta jadda da min cewa inyi ta hakkuri da jama,a Nai godiya tare da fatan Allah ya kara hadamu lafiya namike zuwa gurin mamana wace take shirin tafiya itama gobe don zuwa halartan bukin dan uwan ta a Sokoto,
****** ********** ****** Kusan sau uku Fatima na kiran wayan shi amma sai Salawatu ta kashe wayan, A take fatima tafanci cewa sherin Salawatune hakan don bata son suyi magana dashi, Don haka sai ta ari wayan mijin Fattu takirashi acikin kukan kissa take magana dashi tana cewa na bugoma waya, sau uku kana rejecting din wayan nawa,, Cikin kuka take cewa dama zan fadama cewa yau kwana kusan biyu kenan amma jikin baby yaki lafiya munje asibiti har ance wai gado za a bamu, Subbahanallahi yace tare da fadin yaushe ne kika kira layina na ki daukan kiran ki sai ta fada ma shi nandai ya fada ma ta cewa ta je taga likita zaiyi magana da su, Tsaye yake yana shirin fita inda yake mamakin wanan irin makircin na salawatu, Tun shigowan ta dakin yake sauraren zuwan ta don ya jidaga bakin ta, Tambaya ya jefo mata da cewa waya bugo min waya ne da ina waje ? Ta girgiza kai tace ba wanda ya kira layin ka ai, kuma ina a dakin banjiba, Yace har da Fatima yau bata bugo min ba kikace sai tambayan yazo mata a bazata, Tace a daburce Fatima wace Fatima wai, Yace tambayan ki nayi acikin daka mata tsawa har sai da ta dan razana don tsoro, Amma sai ta daure tana cewa eh takira amma baka kusa shine kawai, wai ita yar duniya sai tana kokarin shige mai ajiki Tureta yayi tai dan tangal tangal kamar zata fadi kasa tajuyo acikin mamaki tana kallon shi, Suna cikin haka wani abokin shi mutumin Arewa ya sallama mashi suka fita, tare yabarta nan da mamaki shi, Itace bata kara ganin shi ba sai washegari tashigo mai wa tazo gashe shi, Yace kije zan fito yanzu in samay ki sai tai wani irin tabe baki tare da mai wani irin kallon wullakancin da ta saba mai lokacin da take murda kanbunta, Sai tajuya zuwa falo zuciyanta tamkar zai buga take jin sa ga wani irin kishin Fatina yana ci mata rai, Takai wani lokaci zaune a falon tana zaman jiran shi yafito daga dakin, Takon kafan shi taji yana itowa daga dakin, yana saye acikin kananin kaya, Ido ta kura mashi farq Kamar a ranan ta fara ganin shi har ya karaso zuwa inda take zaune yana cewa ina breakfast din shi, Ta dubeshi a cikin mamaki acikin hausan ta na yare take cewa, ni ban yi komai ba jira nake idan kafita katuro min da take away dina please, Yayi sauri dakatar da ita yana cewa ke may kike daba zaki hada muna ba sai an sayo a waje, Acan saye mukeyi ko ku keyi ,? May ye amfanin zuwa dake nan dani don ki taimaka min da wasu abubuwan amfani na da bukatocina, Amna sai kizo ki zama min wata liability a rayuwa idan zaki canza ki canza, Ta zuba mai ido yayin da zuciyar ta ke harbawa tana girgiza don ganin alamun duk kwanakin nan Abubakar ya canza mata sosai, A cikin dakewa take cewa, yanzu ni kakecewa na zama maka liability a rayuwa Oga, Yace karya nafadi to ? Ta mike tsaye a kufule tana cewa akan Fatima kake kokarin yi min rashin mutunci irin haka , Tace na fada maka ka aiko min da breakfast dina don yunwa nakeji, Yace baza,a aiko ba yafada ranshi a bace sai ta shiga fada mai bakaken maganganu a cikin bacin rai, A take rayuwan shi ya baci yanufeta gadan gadan inda ita kuma tadake taki kaucewa Yace idan ta isa ta kara tankawa taga may zai mata, Shiru tayi don ganin irin yadda a lokaci guda ya juye mata ya koma wani mahaukacin zaki Shirun da yaga tayi yasa shi wurga mata harara tare da jan tsaki bai kara tanka mata ba ya juya ya dauke yar case din shi zuwa waje rayuwan shi duk abace, Yana mai tir da halin irin na salawatu wace bata da tausayi ace yarinya bata da lafiya amma don bakin kishi ta ki bari abugo mai waya a fada mai, Yana fitane daga gidan ya kira wayan Fatima yana tambayan ta zancen yarinyan idan sun ga likita ? Take ce mai ai sun tagi yabasu magani yace bayan kwana biyu su koma, Tana kashe wayan mamaki sosai yadda yau shida kanshi yakira layin ta har yake tambayan ta lafiyan yarta, Can ya tuna zancen dawowan su Meenatu da yake ji a ranshi ceea idan basu dawo ba kamar kan shi zai tsage a gidan, Yana daukan waya yakira Baba wadda yana tambayan shi ko mun dawo sai yake shefa mai cewa bamu dawo ba malam ya hana sai gobe kila, Nan ya bugowa malam din waya yana cewa malam may hujjanka na rike min matata ne wai Cikin dariya malam din yace don in nuna maka cewa na isa, Abubakar yace kabar min matata su dawo gida haka kaji min tsoho da rigima, Malam yai murmushi yana cewa yanzu kasan cewa tana da amfani agidan ashe, Yace haba malam mutum da abinshi har za,a fada mai hakana kawai dai dama dan wani matsalace kuma yanzu duk bashi, Murmushi malam yakarayi yana cewa mai suna kadaina sakaci da ibada domin sakaci da ibada yasa shedan da shedanu su samu kafar yiwa mutum sheri, Don haka ka kula da ibadan ku ko yaushe kadai na wasa da harka mata da ma iyali baki daya, Yaya Abubakar yace insha Allahu malam nagode nan yake tambayan labarin jikin malam din, Da haka sukayi sallama a tsakanin su suna godewa junan su, Yakashe wayan yana murmushi yana cewa Allah yabar min malam, Matsalan shi guda yanzu shine irin yadda yake jin sauran zafi a kan iyalen shi, Yarasa may ke sa bai son kasancewa dasu ne yanzu duk zafin su yake yawan ji duk abinda yakeyi kawai a cikin daurewa yakeyin shi,
ZEEE MAKAWA YELWA SEENABU
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣1⃣0⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH WARRIS
Alhamdullahi mun iso lafiya,sai dai duk a,gajiye nake saboda nisan tafiyan da mukayi ga kuma dawainiyar yara danake yi saboda munbar Anty Nani a birnin kebbi, don suna da buki sati mai zuwa, a lokacin, Mun samu part din mu yayi kura saboda kwana biyu da yayi a rufe, Mun dauki lokaci muna gyara yayin da Baba Ramatu take muna girkin abinda zamu ci, Duk da dai Lami ta kawo abincin da,suka girka da rana a gidan, Ba laifi don matan gidan sun fito sun muna sannu da zuwa, a tsatsaye, Inda nake sheda masu cewan mutanen gidajen su suna gaishe su, a take naga fuskan Fatima ya sauya, don a zaton ta ko na tafi gidan su ne, Amma sai nake cewa da zamu shiga motane Aliyu ya samay mu ya kawo muna sako, Tana fita daga dakin Asmau na take cewa ji mata fa a zaton ta wai kin tafi gidan sune fa, Murmushi nayi ina cewa kai Asmau anya kuwa kishiyoyin ki sun shiga uku, Abincin da Lami ta kawo muna kawai naji hankali bai kwanta da shi ba Har Asmau tazo da zumar ta bude taci wai yunwa takeji ita da Aisha nai mata magana acikin tsawa da cewa kada ki bude abincin nan please Irin yanayin da bai magana yabata tsoro don haka na umurci Ramatu da tafi dashi daga dakin takai kitchen, kawai,, Dan wani lokaci sai ga Lami ta shigo kitchen din ta bude kulolin a hankali taga cewa bamu ci abincin ba, Tace kai wanan yariyar da shegen wayyo take watau basu ci abin nan ba ke nan, Tace shiru zanyi ince wa wanan masifaffiyar matar sunci, kawai don idan har na fada mata cewa basu ci ba zata hauni da masifa ne Ai kuwa dan jimawa kadan ta,bugo tana tambayar ta cewa to yaya ina sunci abincin dai ko tace sosai ma uwar dakina har ma sun kusa cinyewa gabadaya, Tace da kyau halama kin saka abubuwan dadi a cikin sa, ? Lami tace sosai ma ai in fada maki sai kamshi kawai ke tashi inda na gauraye shi da maganin ta yadda baza,a gane ba, Tace da kyau tawa idan zan zo tsaraban ki ta daban ce don ki sani, Ta na kashe wayan tace bakaji ba inda da na yarda na fada mata aida ban samu wanan kyautar ba, Da dare muna zaune a falo sai hiran mutanen gida muke a lokacin ne wayata tai kara, Na dauka daga gefe na don ganin mai kirana a lokacin, Mahaifina ne ya kirani, a lokacin inda ya ke muna yaya gajiyan hanya na amsa mai a cikin ladabi da cewa lafiya kalau Baba Mun barku lafiya baba nace a cikin sakin rai yace Alhamdullahi Aminatu, Yana Aminatu Allah yai maku albarka dake da zurian ki kinji ki ta hakkuri da abokan zaman ki kin ji Aminatu, Na amsa da cewa cikin girmamawa da insha Allahu baba nagode, Aminatu ki ta hakkuri da mijinki don duk halin da yashiga ciki yana neman taimakon ku, Duk da bami fada min ba na,samu labarin duk irin halin da kuke a wurin baban ku Wadsa ya fada min komai, Bi izzinillahi Allah na kawo karshen al,amarin da yardan Allah, don muna taya ku da addu,a a,kai, Ai yadda kikazo gida kika rufawa dan uwan ki asiri yai min daidai Aminatu Allah ya,kara rufa maku asiri duniya da lahira, Zancen zuwa sokoto kuma daga baya kyazo kiga amarya idan mijiki ya yarda, Kiyi tq hakkuri da kowa ki rugumi yaranki da da mijiki ki fita zancen duniya Allah ya,tsare muna ku, A sanyaye na karbawa baba da cewa Amin baba na gode nagode kwarai baba, A take duk naji jikina yai sanyi a lokacin ke nan mahaifina yasan da halin da nake ciki amma bai nuna min ba, Naji dadi sosai a,raina da irin adduan da na,samu a,gurin mahaifina, Malam tsoho ma ya kirani a waya yana kara yi min nasiha akan rayuwan duniya, inda na bashi Asmau sukai waya da ita, Saboda gajiyan da mukayi yasaka mu saurin kwanciya,a,ranan muna a dakina ina sakawa, Amira permpers naji kiran waya lokacin kusan karfe tara da,rabi na dare, Na dauki wayan ina mamaki wanda ke kirana a wanan lokacin, haka a maigidan ne ashe, daukan wayan nayi cikin wani irin kasalaliyar murya yake cewa, Ya, kun dawo lafiya ko ? Ya kuke ya yara kowa lafiya dai ko,? Cikin natsuwa tare da,dan jin nauyi na amsa mai da cewa lafiya kalau duk muke, Yace ina yaran ko duk sunyi barci ko ? Shiru nayi don ban san irin amsan da zan bashi ba saboda sai naji yau abin ya zama min wani irin banbarakwai, Don haka sai nai shiru kamar ban ji shi ba shima din ya fahinci ban sake jiki ba don haka sai naji ya dan ce a takaice,sunyi barci nasan yanzu a,shafa min kan su Na amsa cikin wata irin murya mai nuna rashin sake jiki da cewa tau, Yac OK ance da Asmau kuka dawo ai ko ? Nace eh da ita ne muka dawo yace ace ina gaida ita abinda yadan sakani daga idanuwa na, na dubi gurin da take tsaye, Sai naji yana cewa zuwa weekend insha Allahu zan shigo don naso nazo kafin ku dawo don na,samay ku acan amma hakan bai yiyo ba, Anan ma shiru nai masa ina batare da na bashi wani amsa ba Wata karfafa ajiyan zuciya na ji ya sake yana ce tau ku huta gajiya Allah ya,bamu alheri, na amsa a sanyaye da Amesn kawai, Ina kashe wayan muka hada ido da Asmau tace sweet mouth kawai wani dadin bakin yake fada maki ne wai, Nai murmushi nace mata cikin dan harara waya,fada maki dadin baki yake min, Ta dan tabe bakin ta tana cewa ya je dai yai yai ta kayan tsohuwar matar shi ai, Harara na kara zabga mata ina cewa gulma dai ajaline dan adam mai wuyan gane hali, Cikin wata yar dariya tace au to goyon bayan mijikin ki ma kike ke nan ashe, Nayi dariya nace ai kin san ba yin kan sa bane kawai dai sherin shedaniya ce kawai, Uhm, uhum tafada tare da cewa ko ra,ayi ba , Nace to bari in yazo saiki fada mai ta kwallo idanuwanta tana cewa rufa min asiri kada na tafi Birnin Kebbi da kafa, Ta mike tana cewa wai wankq nake son shiga amma kinga wanan mai dafin ya lake min sai dana goya shi, Ramatu ta,shigo dakin tana cewa yau naga abin mamaki a gidan nan wallahi, Sai hankalin mu gaba daya ya koma a gareta, inda taci gaba da cewa, wallahi uwar dakina abincin da kikace nafita dashi dazun , Na koma in dauko cups kawai sai na hango Lami kamar mai sanda ta bude kulolin abinci a hankali, yayin da hancin ta yake a like kamar bata son shakan kamshin abincin Allahu akbar na iya furtawa tare da cewa Allah mun gode ma wallahi ina ganin wanan abincin sai naji gabana ya,fadi kawai ra, ras har sau uku, Tun a lokacin na fahinci cewa akwai wani mugun abu a cikin abincin nan, Don wallahi hankalina bai kwanta ba sam daganin wai don mun dawo Lami takawo mu a abinci, abinda da can baya bata yi muna hakan ya fara sani tuhumar ta tu da nasan suna tare da,shu,umar nan Salawatu, Ramatu don Allah duk wani abin amafani,na da yaran nan agidan nan ki taimaka ki kula min da,su Ku saka idanuwan ku sosai a kan duk wata shige da fice da Lami zatayi a gidan nan, Da sauri Ramatu tace yo hajiya ai ba Lami ba ma,da kowa a gidan nan ma, Asmau tace ai ni wallahi duk matan gidan nan tsoro suke bani dama don wallahi ban yarda,da su ba sam,tun farko, Ramatu tace dama aikishiya wallahi ba,abin yarda bane, ko kadan kawai dai ana,so saboda musulunci mutum ya dan dinga,kamanta kishin sa, Tace ni dai ina rokon Allah kada,ya,kaini gidan mai mata, Dariya, Ramatu ta,saka mata inda nadan watsa mata harara ina cewa ai bakisan sirin dake ciki bane shi yasa kika fadi hakan, Ramatu tace ai mutumiyar in fada maki daki auri mara,mata a zamanin nan gwara ma mai matar don ki san kishiya ce gare ki, Nace ai Asmau wanan duk rashin sanin ke sa mace ta fadi hakan, Don kinga maza wallahi sai sun auro mace da tafara haihuwa daya biyu zuwa uku sai suga,wai ta tsufa wata,kuma zasu fara hange a waje, Sai suga aike duk kin tsufa a idanuwan su wace zasu dauko koda bata kai ki kiraba da halitta a gareta zasu koma,, Ke kin zama chus ke nan har angama yayin ki ko an koma a wata, kuma, Sai naga, fuskan Asmau ya dan matse tana cewa nidai Allah ya sa ba mai hange hange wasu a,waje Allah zai hadani dashi ba, Dariya muka,saka mata ina cewa ni dai Ramatu don Allah ki tabbatar da cewa kin rufe kofan shigowa part din mu da Bissimillah, Ta amsa dacewa ai har kullun tun da malam ya fada min irin addu,oin da zandingayi wayaran nan tun acan nake yawan yi masu shi, sosai, Nace adan cikin murya mai dadi nagode kwarai Ramatu Allah ya kara rufa muna asiri, Tace Amin uwar dakina nagode kwarai zata fara jero godiyan ta nace Ramatu sai da safe ta juya tana dariya tabar ni na fara yiwa yara adduan shiga barci