Tarko complete novel - Chapter 113
Tarko complete novel Chapter 113: Tarko complete novel Chapter 113. ****** ********** ***** Saurare take don jin maigida yai wa Meenatu cin mutunci kamar…
3,179 words
****** ********** ***** Saurare take don jin maigida yai wa Meenatu cin mutunci kamar yadda malamin ta yace mata za,ayi, Ranan duk abubuwan da tasan Abubakar yana bukata tai mashi shi batare da,yace tai mai su ba, Yana mamaki ya dai daure yaci abincin shi ya,suce zuwa office kai tsaye, Har yadan yi nisa,da,gida,sai ya tuna da,wasu takardu daya shigo gida,dasu jiya,don haka yajuyo don ya,dauka, Yana shiga,falon yaji muryan ta tanacewa ni wallahi duk da ita da,shegu diyatan ta uku bana kaunar na,bude ido na,gan su agida nan, Tana cewa, wallahi duk yadda zanyi zanyi don naga cewa bai ko son jin ankira,sunan su a,gaban shi,again,, Wani irin runtse idanuwan shi yayi lokaci guda yake ji tankar kafafuwan shi bazasu dauke shi ba, A hankali ya dan fara takawa zuwa bedroom don dauko takardun da yadawo dauka, Gab da zai shiga dakin ne Salawatu ta farga da shigowan shi daki take taji gaban ta ya fadi a cikin dan rudewane take cewa, Honey ,Oga kayi mantuwa ne kadawo kai ya iya,daga mata abinda ya saka zuciyar ta a cikin rudani ke nan, Tana shiga daki sai wata dabara ta fado mai kida zai fito sai ya fito ranshi a washe yana cewa kinata waya ina cewa ki dauko min takarda a daki bakiji ba, Sai a lokacin hankalinta yadan kwanta don tasan bai ji may take cewa ba, Tuki yake amma zuciyar shi sai jiya maganan yake inda yaji tana cewa duk yadda zanyi zanyi tayadda baiko son yaji ankira,sunan su a gaban shi, Yadan goge zufan da ya karyo mai a fuska sai dai still yarasa gane may wanan maganan nata yake nufine wai, don sai yake zaton watakila bashi take nufi ba wani zance ne can na daban takeyi, Da kyat ya samu zance ya fita a ran shi don sai faman tunane yake kala kala yarasa gane inda zancen nata ya dosa, kinsan halin maza da i dont care, Tun wanan lokacin Salawatu salawatu a cikin guilty take don sai taga kamar zai bulo mata da zancen har akai kwana biyu tana darrr dashi A wani fannin kuma ta saka kunuwan ta taji irin halin da,zan shiga tsakani na da maigida, Yau kwana biyu ke nan da dawowan mu daga gida sai ya kasance muna ta faman samun baki makwabtan arziki dana aika masu da dan tsaraba irin na kasan hausa, Wanda tsaraban ba wani abin a,za agani bane amma yai masu dadi sosai don wanda ban ba har da cina tara sukeyi, bzn aika masu ba, Kamar su dangin kuka daddawa wanda gwago habbi tai muna,mai yawa cike da,farin buket, sai ayya da gyada da aka soya, da sugar wani kuma,babu sugar acikin sa, Sai diyan kurna da diyan magarya diyan aduwa,sai karo, duk tsaraban yan uwane da suka bamu abin yaba ni mamaki ganin duk wanda naba yana farin cikki dasu don ni da na raina abubuwan don duk abin kauye ne, Ashe mutane suna da bukatan su ban sani ba sai so su ke tundai Fara soyayya da mu kazo da ita yara suna tacin ta don taji yaji da,maggi, Duk wani abinda malam yace nayi na fannin adduoi a gidan duk munyi shi a,asirce ni da Baba Wadda, kamar yadda yace, Ina zaune a falon gidan muna hira da,wasu bakin danayi makwabtan mune mutanen bauchi sunzo yimin sannu da zuwa duk da ba wani hurda nake dasu ba amma dan tsaraban da na aika masu saboda saurayin gidan yana zama da su Baba Wadda a majalissan su, Shine na diban mai tsaraba nace yakai gidan su daga ciki har da kuka da,daddawa da kulikuli, Matar fara kyakkyawa yar gajera maidan giba tana min godiya a cikin hausan mutanen bauchi wanda mu a gurin mu kamar kananci muke daukan suke yi, Sai zuwan mu Abuja ne na fahince cewa kowani state da kalar hausan su ashe har namu na sokoto din don yan zamfara hausan su daban da ta sokoto haka ma mu yan Kebbi state kalar tamu hausa, daban da na mutanen sokoto, Sosai hankalin matar mai suna Maryam ya raja,a ga yan uku dake ta wasa a gefena inda take cewa au dama yaran nan uan uku ne ashe hankalinta yana a kan su take cewa amma kuwa kina kokari yarinya karama dake da goyon tagwaye haka har yan uku, Murmushi nayi ina cewa ai Allah ya rufa min asiri don ina da masu kama min da wa yan nan masu tsotson ban san ya zanyi da suba ai, a gidan nan, Takece min ita tana sha,awan tagwaye amma diya biyu gashi ance wai sai an gaji haihuwan su ake samun su, Nace haka akace to amma ni ai wanda ya haifi mahaifiyata ce tagwaye, sai kuma Gurin kakan mu shima tagwaye su ka haife shi amma kin ga ni da na tashi dauko hannun sai ma duk na,fisu na dauko har uku, Muka,saka dariya a lokaci guda kafin nai magana,wayata ce tai kara, Anty Amarya kan layin, Da murna na dauki wayan ina mata yaya gidan, ya hakkurin da jama,a ? Sai naji tana cewa, hmmm Meenatu shina kin ka gudu kikabar Antyn ki,da jamma,a Nace nasan cewa zaki iya dasu ai Anty wallahi Yaya Abubakar ya kwabsa min so sai don kiri, kiri, ya hanani zuwa attending, din bukin, Tace ai gara da kika wuce abinki don na ma hana ai wani didima saboda kwantawa nayi ina nishi dole asibiti anka kwana dani ranan, Washegari babu zancen yin wani didiman shagalin buki dole haka aka,dunkulo Amanya zuwa dakin ta,saboda duk maigidan ya rude, Anty kibari don Allah tace af ke ce nan ni yanzu haka ina asibiti saman gado ina shan peppersoup abina, Innalillahi nace tace Meenatu da na tsaya azo a sakani a gaba ana min ihu da guda akai ai gara na kwanta a nan na huta don dama ina bukatan hutu sosai saboda tayar min da hankalin da yayi, Kinga yanzu gani tsakiyan yan uwa da abokan arziki ana ta min sannu don babu mai cewa kishine saboda ansan cewa ina da tsohon ciki mutane ma yanxu sai zagin Uncle din ki sukeyi, Saboda rashin imani,ne ace namiji yai wa matar shi kishiya da tsohon ciki, ko a lokacin alolayin shigar cikki Ajiyan zuciya nayi lokacin da naji Anty tai shiru duk da tana kokari dani amma sai ban ji dadin zahin uncle dina datayi ba na cewa anata zagin shi, Amma dai method din da tayi ya burgeni don ba fada ba zagi bataga wani abin tayarda hankali ba don gashi taja hankalin uncle a gareta acikin ruwan sayi, Bayan mun kashe wayan ne nakewa bakuwar tawa labarin irin hikimar da Anty Amarya tayi na hana ganin tashin hakali Mun dauki lokaci da matar muna dan hiran rayuwan mu da ita, Bayan fitar matan wace muke cewa maman Amal na mike zuwa dakina don yi sallah la,asar don lokaci ya gabato, Ina aza wayan saman gado na juya don nashiga bathroom sai naji wani call ya shigo min duk da ban dauka ba nasan cewa maigidan ne don ringing turned din da nasaka a gurin sunan shi, Na juya zuwa gurin da na aje wayan don na dauka kafin ta katse, min, A irin yanayin muryan da na dauki waya sai naji muryan shi a vikin dan damuwa yana cewa may ya samay ki may ya,faru ne wai Na kara amsa mashi a,sanyaye saboda ban san da wace ya kirani ba ina cewa ba komai, Naji yace ko jikin ne wai har yanzu mamaki ya kamani don yanzu watana biyar da haihuwa zai ce min wai wani ko jikin ne? Sai nake cewa lafiya ta kalau nake kawai dai gajiyace don nayi wankin yara ne yau, Yace a hasale kece kuma mai wanki da kanki ina Ramatu nace Ramatu tana fama da rigiman yara da girki, ita kuma Asmau yau bata jin dadi, Anty Nani kuma bata dawo ba sai next week in Allah ya kai mu, Wata karfafan ajiyar zuciya naji yayi sai naji yana cewa a,dauki wata mana mai aikin idan har aikin zai maki yawa ne, Don banson ace kina irin aikin mai wahala haka hidimata, da dawainiyata kawai nake bukatan matata yi, Maganar tashi ta dan sakani yin yar dariya mai dan sautin, nace amma yaya ai lalurar yara nice ya kamata nayi, da kaina, Yace na fada maki ki nemi wata yar aiki su taimaka maki don ban son takura ko kadan a gare ki, Hmmm nace a cikin yar kunya ina cewa zanyi alwala a na kiran sallah, a cikin kunyan nake fadar haka, Naji yace zan kira naji ko an samu wata yar aikin naji ko ya kuka shirya,
****** ********** ****** Salawatu wace take a tsaye tun fara wayan shi ta sauke numfashi tana cewa cikin hausan ta yanzu kuma wata yar aikin ce za,a kara dauka a part din Meenat, Wani irin kallo ya watso mata yana cewa aciki yar harara ina ruwanki ne wai ko kin fi so nabarta tana aikin wahala da aiki a jikin ta, Tace gaskita har mutum nawa ga Ramati ta koma gurin ta da zama kirikiri ga kuma wanan matar mai kula dayara, Sai wanan yar rashin kunyar yarinyar da tazo ta kakace guri wai ita yar gida, Duk da yaji takaicin zancen ta amma sai ya kyale ta inda ita kuma taci gaba da fada mai bakaken maganganu bata san cewa zancen ta kamar zuban ruwan zafi yake jinsu ba a zuciyar shi, Sai cewa tayi ni wallahi ban san may yasa ba ita wanan Meenan kaman tafi kowa a gidan nan komai sai ace wai meenat, Tau wanan karon gaskiya bazan yarda ba ace wai za a kara mata yar aiki a part din ta again, A cikin mamaki irin yadda ta hakikance tana zuba mai zance son ran ta irin yadda taso, Acikin wani murya ya daka mata tsawa yanace ke Salawa, mind you don ban son shashan ci, A take taga yanayin sa ya juye ya koma kamar wani namijin zaki a gaban ta, Hakan ya sata yin shiru batare da ta bashi amsa ba saboda ganin yadda ya harzako mata lokaci guda, Sai cewa taje a cikin kunkuni ni wallahi wanan shegiyar yarinyar bazata zauna tana muna yadda ranta yaso ba, A ciki ciki take magana batare da tasan cewa yana iya jin taba daga gurin da yake abinda ya kara harzuka mai zuciya ke nan rai a bace yake cewa, Ki shirya ki koma gida wanan satin, insha Allahu, don wata tazo daga cikin ku, Ai kuwa baka isa ba don babu wace zata in mahar wata kake kwadayin zuwan ta bayan ni, Kina ko da hankali Salawa kece ma zaki bani umurni ke nan ashe,, Ta wani juyo tana cewa eh na fada babu inda zani don kaji ka sani,,,, Kafin ta rufe baki taji saukan mari wanda yasata ganin wani haske sai da ta duka, Sai kusan minti biyarta dawo saitin ta aiko sai ta,fara ihu tana cewa ni zaka daka don nace haka, Ai ko sai zagi da cin mutunci nan ya samay fa yai mata nak ta bugu liss ya kuma ce ta hada kayanta a cikin daren nan tun da safe zata wuce zuwa Abuja, Bata da na fada don tsoron irin dukan da yai mata dole tai shiru sai bin umurnin shi, xa tayi tafara hada kayanta,
****** ********** ****** Ina zaune ina shan rake wanda mijin Fattu ya,sayo muna mai yawa aka raba akabawa kowa, Ina son rake bawai don zaki ba kawai don sanin amfanin shi a,jikkin mace musan man wace ta dan fara haihuwa , Wanan ne dalilin da idan na samu rake bani masa shan wasa zama nake nai mai shan tsakani da Allah, Zaune nake kamar ikon Allah sai ga Fatima ta fito inda nake zaune ta zauna tana cewa, Wanan rake da,akwai shi da zaki kuwa don ban sha tawa ba saboda na ganshi kamar baya zaki, Nace tau ni dai gaskiya wanda muka,samu yana da zaki sosai, Har ta shige part fin ta,sai ga babban yar ta dauke da yar baby ta wai ta fadi a kasa don haka sai ta karbe ta tana dan lalashin yarinyar har ta kai zaune, Abinda ya jawo hankali Anty Sadiya wace ke waje tana magana da Hamza, a lokacin, don basu sako, Muna a falon gaba dayan mu sai yar fira ake sama sama a tsakanin mu, a lokacin don kowa tana jin kanta wata tsiyace ita duk da mijin ma bata kan mu yake ba, Sai ganin Hamza mukayi yana jaye da troler a hannun shi yana ja, Hankalin mu gaba daya yakoma gare shi a cikin mamaki muke kallon shi niko sai rakena nake sha inda nake zuba tukar raken a wani katon roba, Waye kuma yazo uwar rashin son baki ke tambayar shi ko wani bako mukayi sai cewa yayi ai hajiyar office ce ta,dawo, Fuskan shi a,washe yake magana daalamar akwai abin kallo a tafiyan, Hakan yasani dakatar da shan raken da nakeyi ina mai fuskantar kofan shigowa gidan, Kallo guda,nai mata naga irin yadda fuskanta ya canza kama kamar tayi accident, Da sauri nakawar da kaina don kada ace naga mugun abu, Subbahanallahi may hakan kuma sai kuma tai shiru Anty sadiya,da,sauri ta,dago tana kallon yadda fuskan Salawatu da jikin ta ya koma, Dasauri take cewa lafiya dai ko sai take cewa lafiya dai ko ta,watso muna harara batare da ta,tsaya ba, tashige part din ta tasaka key tana bude dakin, nata, Tana shiga dakin tafada saman gado rub da ciki sai hawaye ke fita daga idanuwanta, A falo Fatima tace cikin yar dariyan nuku nuku anyi tsita da gani a gurin nan con wanan fuskan bugu ya sha, Sadiya tace bari na shiga naji tana shiga ta samay ta ta kwanata rub da ciki take cewa ashe kina tafe ne hanya, Eh kawai tace ba tare da ta kara furta wani zance ba akai, sai dai taki yarda ta,dago fuskanta, Ba a adauki wani lojaci ba itama Fatima ta shiga don ganin kwam aikuwa har zama tayi agefen gado tana cewa sai naga kamar fuskanki ya dan hau, Tace eh bugewa nayi jita da,safe ina shirin tafiya kuma a lokacin na shirya don gaka na,wuto kawai dashi Ta fahinci cewa matsalace aka samu da ita da maigidan don haka ta mike tana cewa Allah ya sauwaka, Tanafita ta hau dariya duk da Salawatu tana jin abinda take cewa a kunnu wanta amma bata tanka mata ba, An kusan awa daya bayan na dan kimtsa ne, nashiga na,samay ta a can bedroom din ta tana tsaye a gaban mirro tana kallon fuskan ta, Nashiga da,Sallama tana jin sallamata na sai wani irin haushi na da takaicina ya turnuke ta take ji kamar ta hauni da duka ta rama dukan da tasha agurin maigida, Nai mata sannu da zuwa da cewa ya gajiyar hanya ta amsa da cewa kalau, Nadan dubeta nace tau ko nasa Ramatu ta kawo maki abinci ne, don naga kamar baki ci komai ba, Kin san dan sheri gani yake ai shima za,a iya mashi sheri irin yadda yayyi wa mutane, Don haka,sai cewa tayi cikin dan kawar da kai gefe No ki barshi kawai na koshi na gode, Murmushi nayi din na fahince ta abinda take nufi da cewa a,a bazata ciba, Nikan nafita abina zuwa yin abin dake gabana nafita zancen ta, Sai waya take tana fadawa Lubbuna abinda ke faruwa da ita,
ZEEE MAKAWA YELWA SEENABU
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣1⃣1⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH AR RASHEED
NA SADAUKAR DA WANAN SHAFIN GA MAHAIFAN MASOYIYATA ABIN ALFAHARI NA ANTY MAMI, MARIGAYI ALHAJI NURU JIBRIN BAUCHI SARKIN FADAN BAUCHI DA MATAR SHI MARIGAYIYA HAJIYA UMMAI DIMIS UBANGIJI ALLAH YAKAI RAHAMA A KABARIN SU ALLAH YA SA ALJANNAN FIDDAUSI TA ZAMA MASAUKIN SU ALLAH YA GAFARTA WA DUK KAN AL,UMMAN MUSULMAI DA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA NA ANNABI YA TAYANI JA MASU KULHUWALLAHU KAFA GOMA SHADAYA ALLAH YA KAI HASKE A KABARIN SU,,, 👏👏👏
Tun dawon mu sai yau muka,fita don naje gaida mutane wanda fitan nawa yanzu ba koda yaushe nake yin sa ba kamar farko Sai idan lalura mai karfice nake fita yanzu ma ankawo mahaifitar Anty barister ne Abuja bata da lafiya,shine nake son zuwa na gaida tsohuwan, Mun jewa,tsohuwan da abin dubaiyya inda take ta murna da zuwan mu tana ta cewa sannun ku sannuku fa nagode nagode kwarai, Da sauri nace mama kibar muna,godiya Allah dai ya baki lafiya, Kin san hausawa sunce idan kaje gaida mara lafiya yana cewa yagode tau da,wuya ya tashi wannan jiyar da yakeyi, Abinda yasani sauri cewa tsohuwar ta daina gode muna hakana, Anty rana tambaya na cewa mutanen kasar ibo suna can lafiya dai ko,? Kafin nai magana Fattu tai farat tana cewa ai ke dai Anty mutumiyar tana nan ta dawo yau kwana hudu ke nan da fuska a kumbure, Salati Anty ta saka tana cewa Allah kenan kaikayi koma kan mashekiya, idan taje badon Allah ba gashi ta dawo bandon Allah ba ai, Duk abinda mutum zaiyi yayi don Allah ya bari don Allah, a zaton ta a haka zasu nare dama da sheri kizo ki samu mutum da iyalin sa kice duk ya basu baya sai ke kadai zai saka a gaba kamar yar gwal, Yanzu dai ai taji kunya idan har ta san shi don dai wallahi babu abinda yafi wanan katafi gurin miji kana wa saura feleke sai aga kadawo da fuska a kumbure kasha nashi,, sai aka,sa dariya gaba daya gurin nice kawai ban dara ba,saboda banga abin dariya,ba a nan, Idan na tuna irin yadda muka dan sha wahala cikin da takin da,Salawatu ta jefa,mu a cikin sa, gaba dayan mu gidan babu mai fatin cikin rayuwa sai ita kawai da na tare da ita, Nace wanan ai abintane ya koma mata duk wani mai mugun hali, irinta ai a haka zai kare, Ita bata ko tausayawa yaran da ta raba da mahaifin su bata damu da halin da zasu shiga ba na nisanta su dashi da tayi, A nutse na kara cewa dama ita rayuwanta ke nan a tauye wani a gyara mata ita, Mun dauki lokaci ana zance guda a gidan Anty mukayi masu sallama muka tafi, Gurin Anty saloon muka biya don mu gaida ita mun samu tana da mutane, da yawa a,shagon ta don haka bamu wani dade ba, Sai muka biya wani katon store muka danyi sayayya a gurin , agajiye muka dawo gida Mun samu Anty Nani, ta dawo a ranan da ihun mu, mukai mata sannu da zuwa tana ta jin dadi, Sadiya tafito don taron Antyn Nani don matar babu ruwan ta itama don har da sako ta karbo daga gurin sister din sadiya ta kawo mata, Ta zo min da wata yarinya yar kimanin shekara sha, uku wace ita aikin ta kula da kayan yara kawai, ban san cewa ma har ya buga gida yace a samo min mai aiki ba,sai da suka zo, din, Duk kwanakin nan Salawatu tana daki bata fitowa muma agidan ina ganin babu wanda ya damu da harkan ta, kowa tashi ta fissheshi,