Tarko complete novel - Chapter 114
Tarko complete novel Chapter 114: Tarko complete novel Chapter 114. ****** ********** ****** Satin mu biyu cif da dawowa Abuja duk mun sake abin mu muna…
3,058 words
****** ********** ****** Satin mu biyu cif da dawowa Abuja duk mun sake abin mu muna harkokin mu na yau da kullun, Abinda na lura yanzu bani kadai ba ko wani part sun samu sassauci daga gurin maigidan, Ita ko salawatu ba wani power a tare da ita yanzu a gurin maigidan wanda hakan ya dan sata yar rama irin yanayin da ta,saka mu a baya can, Yau anwayi gari da ruwa a garin bayan ruwan ta,dauke sai aka,fara wani iska, mai dan sakar da kamshin kasa don sabuwar damana ce, hakan yadan saka kowa jin dadin yanayin, Ganin duk yaran suna,can dakin su Anty Nani ya,sani bin wanan yanayin don nai barci hakan kuwa barci mai nauyi ya dauke ni nadan huta wa raina,, A cikin barcin wanda ina ga yakai awa daya ina yin sa naji, kamshi kamar na turaren maigidan, Gyara kwanciya,nayi da niyar inci gaba da barcina don a zatona ko mafarki nakeyi a lokacin Gaf da hancina naji saukan numfashin shi yana cewa ina yaran suka shiga kike barci ke kadai, A hankali na bude idanuwa na da,sukai min nauyi don barci ina kallon shi, Fuskan shi dauke da makalalen murmushi yace ina yaran suka shiga ? Wata ajiyar zuciya na sauke yayin da nake dan kokarin mikewa daga zaune nace a raina La,illahaillah mohammadun rasullilah, sai na kai zaune, A sake nake cewa sannu da zuwa yaya ya karba min a sake fuskan shi ba yabo ba fallasa Sai yana cewa aida kinyi barcin ki don dama zan juyane kada na tashe ki, A ladabce na kara cewa ya hanya Yaya,? Sai ya,shareni yana cewa ina tambayan yaran akawo su na gansu don fita nake son yi yanzu, A hankali nace suna gurin Anty Nani a dakin su, nace bari a dauko su yace OK is alright ina daga falo, Hausawa sunce mai sonka shine mai son danka, Ko indan kana son shiri da mutum karasa hanya to kaso dan shi zaku shirya tundai uwa, Don haka ina ganin yadda ya matsu yaga yaran shi sai duk naji na manta da duk wani cin fuskan da yai min a,baya don haka na mike nabi bayan shi, A falo muka,samay shi zaune saman kujera yana karba waya acikin nishadi, Tun fitowana ina saye da doguwar rigar mutanen kasar, Malaysia Tun bayan afkuwan rikicin mu, ban kara ganin kwarjin shi a,fuskana ba irin na yau, Ya kara zama babban mutum don da ganin sa lafiya ta samu gare shi, Mune dai kawai ke fama da dakon son shi a zukatan mu kamar zamu mutu, a kan shi waimq cikin ni ban damu sosai da zancen shi ba, Kamar koda yaushe ya,watso min yaudararin idanuwan shi wanda duk yake rikita mai kallon shi, Ina tafe dauke da Alhassan a hannuwana muka tunkaro shi yayin da Asmau take dauke da Amira, sai Aisha ta riko Alhussaini, Ina jaye da hannuwan Amir muna tafiya a hankali, zuwa gare shi inda yake zaune tare da sauran iyalin shi, a cikin farin ciki gwanin ban sha,awa, Idanuwan shi kyam a kan mu yayin da,naji kafauwa na,suna harde min sai kirjina ya,shiga,dan bugawa saboda ban san da may yau ya shigo muna gidan ba, Tun kan mu karaso naji yana cewa masha Allah yaran nan sun girma sosai, haka a cikin muryan shi msi tankar da ana tillasta shi yin zancen, May kike basu hakane wai sukai wanan girman haka ? Ya tambaya cikin kura min ido yana son jin amsa daga gare ni, A takaice nace mai kwanciyan hankali suka,samu daga uwar su, Ni kaina amsar da,na,bashi batai ma,ana a gareni ba amma dai shine kawai irin amsan da zan iya bashi a lokacin don ban san da wace yazo muna ba, Badon komai ba,sai tunawa da irin wullakancin da yai min wani zuwa da yayi inda ya dinga daka,min tsawa daga kawai, nazo magana da shi, Tun wanan lokacin duk da nasan cewa ba,yin kan sa bane hakan amma, rayuwa na ya,baci sosai da hakan, da yai min, Ina mika,mishi yaron dake a,hannuna a,lokacin hannuwan shi mai taushi, yagogi nawa wanda hakan ya sakar muna da,wani irin shock, wanda yasaka,zuciyoyin mu a,wani yanayi, Cikin murna ya,karbi yaron dake hannu na, inda,yake cewa a miko mai Alhassan, da Amira, Mun samu yar wurin Fatima already a hannun, shi yana dauke, da ita, daukan yarana da yayi yasa shi aje yar nata yana cewa, Kai,kai mamana kinyi nauyi ne haka may, kike shane wai haka kukq yaran keyi basu yarda ya,dauke su wai, Lokacin ne Baba Wadda ya shigo falon shi da hamza take yaran su ka nufi gurin su, su kai shiru, don sun saba dasu sun san su sosai, Bakaramin bacin rai hakan ya,saka shi ba don sai da yaji wani iri a cikin ran shi, Wata kakkarafan ajiyan zuciya ya saki fuskan shi ta nuna damuwa yace acikin yar murya Ok baku san Daddy ba ko,? Maganar da yayi ta a cikin wani irin yanayi ta saka kowa dake gurin jikin shi yai sanyi a lokacin, Can ya sake numfashi yana,duban su a hannun Wadda da hamza yana cewa ai kwanq biyu duk zaku wayeni ku daina wanan kiwar, Fita su kayi shi da Lawal zuwa wani guri wanda bazan iya cewa gashi ba ni, Bayan gitan shi har na juya zan wuce naji muryan Fatima tana cewa ki dakata Meenatu muyi magana ko ? Na juyo acikin mamaki don ban san maganar da take nufi zamuyi ba a lokacin, Amna,sai na umurci su Asmau da su shige da yaran ina tafe idan na hada, Na zauna a saman daya daga cikin kujerun falon ina mai son jin may zasu fada, Fatima ce ta fara magana da cewa dama akan zancen girki ne nace ki tsaya don muji ya za,ayi ne wai Azuciyata nace ai kin fi da nan uwar yan son kwana da miji, Amma a fili murmushi nayi ina mai cewa ai duk yadda kuka tsara ni banda matsala fa, Sai cewa tayi amma dai kin san bada madam zamu raba wanan duty din ba tunda can tafito ita, Wai tana nufin cewa Salawatu ba zatayi duty ba har maigidan ya tafi,, Nace cafdi jam amma fa kun san zaku nemi rigima tunda kunsan cewa duk suka zo da ita ake raba duty tun farko, Fatima tace shi yasa nake son mu sasanta kan mu yadda bakin mu zai zo daya akan zancen, Nace Ok duk yadda kuka tsara ba matsala ai duk dayane, Uhum inji Sadiya wace shiru tayi tun farko tana,sauraren mu sai yanzu da ta,motsa, Ta dan dube inda Fatima take tana cewa wai ke may kike son cewwa ne wai, Fatima tace ba wani abu bane idan yau kin duty gobe sai maman Amir tayi zuwa jibi kuma ni nayi, Azuciyana nace waddari Fatima tafara ladab din shegu ke nan don taga go no go, A cikin murmushi nace hakan yayi idan har babu wani matsala a kai ai, nafada tare da mikewa, Daga,nan ban sake cewa uffan ba,sai kokarin mikewa da nake don zuwa part dina gurin yara,
****** ********** ****** Yaya Abubakar kan yana can duk, zumudi da doki ya cika shi, Don ya matsu ya,samu ya kasance da matar shi, a tsakanin su don su fahinci juna saboda ya fahinci akwao canjin fuska a,tsakanin shi da ita sosai, Sai da ya,dawo gurin cin abinci ne ya fahinci wace ke da duty a ranan sam ba haka yaso ba aran shi amma,sai ya,share ya,dake tankar ba abinda ke damun shi,a rai, Ina kwance a saman gadona dakina tun bayan fitowa na wanka da na gyara jikina tsab don hakan al,adatace na gyara jikina ko banice da girki ba, Ina daga kwance yayin da,fuskana yake fuskantar TV dake manne a bangon dakina, Sam banji shigowan shi dakin ba don fuskana yana akan TV mutum zai dauka cewa hankalina yana ga tv ne, Tsaye yake daga kofa ya zubo min ido ina saye da wani rigar barci sky colour a jikina, Kayan ya bala,in karban jikina idan kagani bazakace nice mai kananan yara irin haka,ba a gabana, Don zaka zaci ko yar sabon aure ce ni saboda irin yadda nake tsab dani, Idanuwan shi kyam a kaina, don nai mai balain kyau tankar wata diyar larabawa, ga hular da na ya dan fitar da gashina dake tufke a baya, Alamar akwa mutum a kaina naji abinda yasani kai idanuwana a kofan shigowa dakin nawa ke nan, Ganin shi yasani saurin dagowa don na mike amma kamar abin walkiya, sai gashi a gabana Idanuwan shi kyam a kaina inda yake min wani shu,umin kallo, Nagane nufin shi inda shima ya gane nufina don haka kafin na mike zaune yakai zaune daga gefen bakin gadon ta yadda bazan iya dagawa ba daga kwancen, Kawar da kaina nai niyar yi amma acikin zafin nama yai saurin juyo dani gare shi, Cikin wani irin murya da ban san ina da irin shi ba nake cewa, don Allah ka barni na zauna ban da lafiya ne, Ido ya kura min na dan wani lokaci sai ya dan sakeni yana cewa wai may ke faruwane Meena, Na lura kamar kina fushi danibda alamar akwai matsala please ki fada min abinda ke faruwa, mana, Haushi da takaici ne suka,rufe min zuciya watau bai masan cewa akwai abinda ya yi min ba koda yake ba laifin shi bane don yaga ban dauki fansa bane tun farko, Sai kawai na girgiza kaina a cikin takaici yauin da wasu hawayen bakin ciki suka dan fara silalo min daga idanuwana, Take ya dan firgice duk da yana kokarin boye damuwan shi gare ni, amma sai yake cewa acikin murmushi mai nuna damuwa, Yace kin canza Meenatu ba kamar yadda na san ki ba a baya, Yana kokarin rugumana yana cewa ki fada min Meenatu mai nai maki ne wai haka ? Zo mana ki fada min don nasan akwai dalilun hakan , Zubur na mike a cikin zagin nama ina mai ture shi tare da girgiza kaina hawaye da kukwna yana yawaita, Ina cewa Yaya Abubakar don kaga banda wanda zai daukan min fansa a kanka akan cuta min dakakeyi, shi yasa zaka ce wai may kai min, Don girman Allah ka tashi ka fita min daga daki ka koma gurin matar ka, abin kaunar ka kabarni inci hakkurina ni da yarana, Kasa karasa zancen nayi inda na,fada kife saman gado ina mai rusa kuka irin mai shiga zuciyan mutum, Nace a cikin kuka ka duba Yaya yadda yaran nan ma basu san kabw ma imaging, ace wai yara kanana ma basu san uban su ba fa, Ba karamin taba,mashi zuciya maganganun da nake fadi sukayi mai ba, Mikewa naji yayi yafita daga dakin yabar ni nan na,darji kukana,son raina, Wanda wanan kukan danayi shine yadan sako min dan sasauncin abinda nake ji gamay da shi a,raina, Zuciyar shi cunkushe da bakin ciki yake tafiya a daidai tsakiyan falo suka hadu da Salawatu wace tun shigowan shi garin sai a lokacin ya ganta, Wani shock tayi daganin shi inda ya zabga mata wani harara yake ji a ranshi kamar ya make ta ya huta, Ya,shiga daki a nan ya,samu Sadiya,wace itama,dai din korafi ne tafara yi mashi na irin nakasata da wullakanta ta da yakeyi , Kan sa,duk ya,daure ya shiga tunanen irin maganganun da kowan mu ke fada mashi akan rashin kula hakkin mu da baiyi, Yasan cewa shi mutum ne mai kokarin ganin ya ba wa ko wace mace hakkin ta ba ma tan shi ba har, duk wani wanda yake a,karkashin shi, Abubuwan da sukai tayi da,Salawatu yake dan iya tuno wasu yake runtse idanuwan shi, Tabbas matan shi sunyi gaskiya musan man ma,yarinyar nan Meenatu wace, gashi ba lafiya ya ishe ta,ba ga kuma,dawainiyar yara dake a kan ta, A,gaskiya bai kyataba amma kuma,shi ya,rasa ko may yasa yake jin Salawatu irin wani iri daban a cikin matan shi ne yanzu, duk da ta bata mashi rai amma sai yake jin ta daban da sauran,
****** ********** ****** Washegari ranan da su kace wai nice da girki ban ki ta tasu ba don tun da safe muka fara,shirye shiryen girki kamar yadda na saba yi idan ina da,girki, Don bani barin yar aiki tai aiki nice da kaina ke aikin komai na farko don na samu lada nabiyu don na gyara,ran mijina na uku don nice nasan abinda ya dace nayi wanda zai jawo hankalin kowa bawai yar aiki ba, Don haka daga gyaran gida goge goge share share da,sauran su duk nice naketa yin abina, Tun karfe biyun rana zaka fahinci cewa yau nice mai girki a gidan abinda ya sa har Salawatu wace ma ba ai meeting din rabon girkin da ita ba tagane cewa yau zan karbi girki bayan tsawon watan nin da nayi bana tare da miji a gidan a sanadiyar kwanciyan asibiti danayi da haihuwa kuma na watanni masu yawa, Tana kwance tana tufka da warwara daga waya da kuma fili, Taji ta shaki kamshin turaren wuta da room,fresh masu dadin kamshi, da sauri ta mike a saman gado tana jin dip dip a cikin zuciyar ta a fili ta furta Meenatu ce, Yau yar iskan yarinyar nan zata fara girki a gidan na kai ina gaskiya da,sake idan Meenatu ta fara girki duk susuce Abubakar zatayi don makirar yatinya ce har ta karshe, Don haka a rude ta fara zage zage da surfawa Lami ashar tana cewa duk yadda akayi Lami ta cuce ta ne bata aiwatar da abin da ta sata yi ba daidai, Gashi maimakon a saki Meenat ko wullakantawa ita tasha duka da zagi harda rotse a fuska da hannu, Shiko maigidan ya fito yana saye a cikin jallabiya da yar gajeriyar wando budan kofan shi kamshi gidan ya tare shi abinda ya sakashi saurin kai idanuwan shi gare ni ke nan dan ganina Yafito ne dama don ganin su malam Abdullahi da sukazo yi mai sannu da zuwa, ya riskeni ina goge gogen karfen hawa steps din dakin shi, Sai naga ya,sake wani irin lalausar murmushi a fuskan shi tankar ban san yana yi ba na share shi naci gaba da aikina nida yarinyar da aka kawo min daga Kebbi, Sai da,na tabbatar da baya gidan yafita da Amir dasu Aisha da diyan Fatima yasani shiga part din shi, Aikine na,samu a part din tukuru zakace babu macen dake kwana a dakin, Aiki sosai na,darza a,dakin nashi gashi ban shigo da yar aikin tawa ba don dakin mijinane sirinane nan, Ko ina sai kyalli yake da kamshi don na goge komai na dakin, Daga haka na,dawo fanin girki wanda dama already na sa Baba Ramatu ta fara min wasu aiyuka, ko, Abincin gargajiya nai mai don nasan yadade rabon da yaci, tuwon masara da miyar kubewa, gashi abinvin da yake so ne tun yana yaro amma kiuyya bai bari matan shi su yi mai na,saka mai manshanu sai kamshi ya keta shi, komai na tabbatar da cewa na hada mai, Har a lokacin da zaici abinci zuwa dare duk ina gurin tsaye tare dashi sai dai banci ba don na e mai munci da Asmau shi da Amir sukaci da Baba Wadda suna hiran gida A ranan komai da zanyi duk nayi shi a cikin ikon Allah ba abinda ya rage min har ruwan shan shayin shi na hada nakai na aje, mai a daki Daga haka natattara yarana da sauran yan part dina muka shige part din mu, Hira suke a falon amma hankalin shi yana ga kofan part dina ko zaiga giccina na fito yin wani abin, Amma,shiru azaton shi ina jiran ya shige ne nabiyo shi dakin abinda bai sani ba ina can na shige abina uwar daka har mun kwanta ko don dama jikina da gajiya, Ranan baiyi wani dogon hira ba,ya,shige part din shi a cewan shi zaiyi aiki a system din shi ne, Shiru, shiru baiji na shigo ba, yasa shi daukan waya don kiran layi na but is switch,off, Yaja tsuki tare da cewa ga yar raini wayon yarinya kawai bata,san ina jiranta bane wai, Ya dan kara bada time shima din shiru, babuni babu labarina ban shigo ba sai zuwa dare lokacin ya tabbatar kowa a gidan ya shige ya fito a fusace zuwa part dina, Don yana gudun yafito wata ta ganshi daga cikin matan nashi yaji ku ya don yakan yawan cika baki cewa shi bai bin mace wallahi, Ya murda kofan yaji part din mu a rufe gam yakara murdawa a rufe yake gam , Har yadaga hannu zai buga kofan sai ya tuna cewa ai wani zai iyajin shi ko afito a ganshi, Ranan haka ya koma dakin shi yai ta mukurkusa shi kadai har yasamu zuwa dare sosai barci ya kwashe shi, Haka ya kwana ranshi bace dani yana ta kulla irin martanin da zai mayar min, da safe ai zan shigo yin wani abin gurin shi, Niko ina can nima zuciyata a cushe na kasa sukuni don dai nasan ban kyauta ba to amma aikuma dole ne na nunacewa nima din fa mace ce mai daraja da kima ba abin wullakan tawa ba, Yadda yai zaton da safe zan shigo hada mai ruwan wanka irin yadda na saba da kuma zuwa don gabatar mai da breakfast sai yaji shiru don ban fito ba, Haka ya gaji don karan kanshi yafito don duba sauran matan shi kamar yadda al,adan shi take duk safe zai dan zafa dakin ko wace mace su kara gaisawa, Wani kamshin dadi dake tashi ako wani kusurwan falon ya daki hancin shi yace a ranshi kamshi may tunda baki da tausayi, Suko sauran matan sai kishi ya rufe masu ido suke ganin ai rawan kafa yake saboda yau ya kwana dani bayan tsawon watan,ni da mukayi bamu tare, Kowace sai amsa mai take sama sama gashi sunga yai masu kwarjini a fuska wai shi ya angwance, Kishi ke nan ya rufe masu idanuean su har sun kasa gane matsalar dake a tsakanin mu, Badon komai ba ya hana su ganewa sai ganin irin yadda naita rawan kafa da rana adole ni zan karbi girki maigida a ranan nawa ne, Basu san zama acikin manyan mata yasa ni iya makircin mata sosai, Nida natashi a babban gida ina ganin yadda ko wace macen gidan mu ke fama da matsalolin maza tun ina yar karama ko kuma inji ana gulma,wata intai wani makircin,