Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 115

Tarko complete novel - Chapter 115

Tarko complete novel Chapter 115: Tarko complete novel Chapter 115. ****** ********** ****** A hankali jiki ba kwari (karfi )yake saukowa daga steps a…

3,092 words

****** ********** ****** A hankali jiki ba kwari (karfi )yake saukowa daga steps a hankali yana saye a cikin wani jallabiya baka ta karbi jikin shi don shi farine fatan shi mai laushi yabi jikin shi tsab jallabiyan ta karbe shi, Dakina ne last din shigan shi ina zaune a bakin mirro ina daura dan kwali fuska wanda yake nuna alaman rashin jin dadi don da gani na a lokacin ba dadin rayuwa a tare dani, Muryan Anty Nani wace ke falo ina jiyo muryan ta da yara suna surutu naji tana cewa ina kwana Yana daga labulen dakina mu kayi arba da shi through mirror din da nake zaune a gaban shi amma saina dan dukar da idanuwa da suka nuna alaman nai kuka , Baya na a juye batare da na juyoba na fuskance shi ba nake cewa Ina kwana,? Sai naji yai guntun murmushi tare da kura min idanuwan shi masu sa mutum a cikin wani yanayi ta mirro din da nake zaune gaban shi, Takowa zuwa gurin da nake zaune naga ya karaso yi hannayen shi suna harde da junan su, Sau biyu mu na hada ido dashi ina dukar da kai na kasa ganin ya nufoni yasani mikewa da sauri, Sai naji ya rikeni ta bayan shi, acikin wani irin karfi da muryan kuka nake cewa sake ni please ? Kamar bada shi nakeyi ba don ko gezau baiyi ba,saima idanuwan shi da yakura,min , Idanuwana a runtse sannan na cije lebena hawaye suka fara gangarowa daga idanuwa na, Ya Sallam na ji ya furta a hankali yana cewa Wai Meenatu bazaki daina kukan nan ba haka ki tsaya mu fahinci juna , Maganar ta bani takaici sosai don haka na dago jajayen idanuwa na kafa a cikin nashi ina cewa , Ina ruwanka da i kabarni yadda kabar mu kafita batun mu Allah yai muna gata, Sautin murmushinsa najiyo a cikin takaici yana cewa kin san aida nabar kune yadda kike nufi da ba haka ba, Don ko banza kin fi kowa sanin halina idan nabawa abu baya nabadhi ke nan har abada , Bake kadai wanan matsalar ta shafa ba amma kin fi kowa daukan zafi, Banza nayi dashi amma a raina sai cewa nake, ashe kasan kamuna abu ke nan kaima, Fuskana nakawar a dayan bangaren ina kuma tunane halin yaudara irin na maza su dake ka si hanaka kika kuma, Kafin wanin mu yai wani magana a daidai lokavin da nakejin rikon da yai min yana batun canza sallo ne Amir ya,shigo dakin da kukan shi, Dalilin da yasa shi saurin sakeni ke nan don kada yaton yagan mu a haka duk da dai yaro karami ne amma yaran ynzu wayo gare su, sosai,

****** ********** ****** Ina zaune ga abinci a gabana amma na kasa cin komai daga cikin abincin sai faman tunane tunane nake ta zaggawa, kawai, Muryan Ramatu ne naji gab dani acikin tausa muryan ta, take cewa uwar dakina don Allah kiyi hakkuri ki daina wanan fushin haka kada ki shiga hakkin Allah, A cikin wasu irin idanuwa da,suka kade min na dago ina kallonta a cikin mamaki , Tace al,amarun ne watau sai hakkuri wallahi don shi har da da kishiya,mai shige shige sai ka kai rayuwanka ni sa, Idan bahaka ba wallahi sai ta halaka kanta ta kuma halaka na tare da ita, Mirmushi kawai nayi mata tare dacewa nagode Ramatu inzha Allahu zan daina ai, Tace shi al,amari na hakkin aure wuya gare shi domin mu mata kasa muke sosai maza sun fimu dara akai, Don haka tun xa har Allah yasa ya sauko sai kiyi hakkuri don dama saukowan shi muke nema ai gashi kuma Allah ya taro muna shi, Ajiyan zuciya na sauke a hankali ina cewa watau idan na tuna abin sai na dinga jin wani zafi araina, Ramatu tace wallahi naki da sauki uwar dakina tace cikin rage murya ita maman Aina ranan bakiga irin yadda yai mata ba a gaban jama,a fa, Tace don haka don Allah koyi hakkuri zancen ya wuce kawai ki rungumi auren ki, Nai mata godiya nace insha Allahu Ramatu zan gyara,ai, a haja muka rabu da ita tana tayi min godiya,

ZEEE MAKAWA YELWA SEENANABU

[1/3, 9:30 PM] Makawa: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣1⃣2⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AS SABUR

Ya Allah ka,gafartawa duk kan kullumin musulmin Allah da suka riga mu gidan gaskiya, Allah ubangiji ya kyauta namu bayan nasu Allah kasa mu cika,da kyau da imanin ubangijin mu👏👏👏👏

A haka ya daure ya koma gurin aikin shi inda nima naci gaba da harkokina sai dai na kudurta a raina duk sanda ya dawo insha Allahu zan sassauta mai, Anty Amarya ta bugo min waya tana fada min irin takai din da suke kwasa da amaryan gidan su take cewa wai dama Meenatu irin rikicin da kike gani ke nan akan kishaya, Ai mai kishi da mace daya ba kishi yasani ba sai gasa kawai, Tace nifa hada min kai akayi da mummy ku da Amarya komai yanzu a tare sukeyi wai don kawai a bake ni, Tace da har Uncle dinki zai biye masu a hade min kai dashi dukka amma,sai nai mashi kwal nasa mashi waigi, Yanzu wai har unguwa a tare suke fita haka kuma in a gida suke suna likeda juna dakin daya, Hmmm nace wani sabon sallo ke nan kuma akazo dashi ashe Yanzu ita mummy da shekarunta ta yarda da wanan hadin kan sheri, Nace Anty ki saka masu ido don karshe abin bazai masu kyau ba baran baran za,a kare Tace tun yaushe ma tunda basu bar kansu ba kishin junan su, suke suma, Nace to dama ai babu kishiyar da ke son kishiyar ta tsakani da Allah sai dai kawai mutum ya kwatanta na Allah kawai don tsoron ubangiji, Nace idan har kin yi hakkuri anty zaki gan su a rana sosai wallahi don ranan zakiji fallasa har sai kin toshe kunnuwan ki, Na ce kada ki yarda da zancen hadin kai da kowan su wai don a cutawa wata, kedai kawai gyara kan ki tsakaninki da mijin ki, Nace ni kinga Anty duk irin sherin da Salawatu tai min bai hana,na kulata ba a,fili don ko abu take so yanzu gurin mu take zuwa, karba, Anty tace muguwa yanzu wai ita adole tayi kwanton kasa sheri na cikin ta a boye, Mun dauki lokaci da Anty muna wayan akan matsalolin gidajen mu inda daga karshe mukayi sallama saboda bakin da suka shigo gurin ta,

****** ********** ****** Kwanan shi biyu da tafiya ina zaune a falon part dina muna kallo kawai wata zuciya tace min nakira shi mu gaisa, Inda ba bata lokaci nabi shawaran zuciyata na daga waya na kirashi, Duk da yake a lokacin nasa cewa lokacin aikine amma hakan bai hanani kiran wayan shi ba, Zaune yake yana tsakiyan aiki da,wasu dirctorcin su, wayar shi tai kara kamae kada ya dauka,don ba dabiar shi bane daukan waya lokacin da yake aiki, Daukan wayan yai daidai da sakin ajiyan zuciyar da yayi a cikin wani irin murya maikama da rada yake cewa, My Sister , Nace a yar murya Yaya ka koma lafiya,? Ya dan ja numfashi,tare da furzar da iska yana cewa Alhamdullahi Ya na barku ya yaran, duk kowa lafiya ko naji dadin wanan, tambayan da yai min don ni a rayuwana ina son mai son diyana, Shiru muka,dan yi na lokaci guda, can naji muryan shi a,cikin dan wani yanayi yana cewa, Meenat kin huce ke nan da hushi da yayan naki, Yar gajerar murmushi nai mashi batare da na furta uffan ba, Please Meenat ki sassauta min nasanna cancanci duk wani hukunci daga,gare, ku duk da ban san takamaimain laifin da nai maku ba har kuke min wanan hukuncin haka, Amma duk da hakan ina son ganin kin sake ranki kamar yadda,yan uwanki suka, hakkure min, Shiru nayi ina sauraren shi batare da na tanka mai ba, Yace yanzu please muyi magana kafin na dawo, don mu fahinci juna dake, yana,magana tamkar zaiyi min kuka, Hmmm namiji nace a raina wani yar karamar nan Yaya Abubakar kewa wanan marairaicewan haka, Amma a irin yanayin da yake magana sai na soma jin ya fara kara min zuciya da dadadan kalaman shi masu ratsa jiki, da tausayi, Allahu Akbar ance tsakanin mata da miji sai Allah, a take naji ya bani tausayi, Nace a sanyaye Yaya komai ya,wuce insha Allahu Masha Allahu, ina dai kara baki hakkuri, don Allah Meenatu ki saki ranki a cikin gidan ki kamar kowa, Inda,na kashe wayan nan nai zaune ina tunanen irin abubuwan da,ya,wakana a baya, a lokacin sherin Salawatu na akan shi duk dama ko yanzu da alaman sauran shi, Ba komai yasa na fadi hakan ba,sai ganin duk irin fitinan da,suka kwaso a ca wanan zuwan da yayi ya fuce don da ta,samay shi da zancen cewa wai bata san dalilin rashin bata girki da,bamuyi ba sai yake tambayan mu, Amma sai kowa yai shiru ba,wanda yai magana daka cikin Sadiya da,Fatima, Mamaki suka bani sosai don dafa garesu zancen yafito, amma yanzu gasu sunyi shiru, Sai ni ce a cikin karfin hali nace munyi hakane don ganin cewa ita can take zaune tare da kai zuwa tayi, Cikin bacin rai Salawatu tafara fada tana cewa kwana nawa nayi a garin nan da za,ace wai ina can tare dashi ba zanyi duty ba, Sai a lojacin Fatima ke cewa koda wata daya kikayi baza mu yarda ba don muma matan shi ba farkokin shi ba Yadda kike takaman auren shi kikeyi muma haka zaman auren shi mukeyi, Cikin wani murya ta juya gare shi tana cewa bazaka sa baki a zancen ba don kaji abinda sukace, Yace cikin wata murya kamar wanda ake juyawa da romote, kubata girkin ta don Allah a bar zancen hakana please, Sadiya tace a cikin karfin hali baza,abata girkni ba Fatima ce zatayi don ba fin mu tayi ba anan cacan baki ya fara inda mukafi karfin su dole a ka kyale Fatima tayi girki a ranan, Abinda yakara sani bata raina dashi kenan har zuwa yanzu abin yaki fita a zuciyana Amma dole babu yadda zanyi da raina dole na hakkuri da abinda yafi karfina, Yanzu muna waya dashi a akai akai kuma ban daina,adduan da nakeyi ba na samun galaba akan sherin Salawatu , Sosai Salawatu ranan ta je baci da ganin yadda kowatakeyadda taga dama agidan musan man part dina dake da yan aiki da yawa suna harkokin su kaman yan gida, baza kace yan aikin gida bane, su, A cikin wanan yanayin ne har Allah yadawo muna dashi lafiya abinda nasanine da zaran naga Fatima a part dina nasan cewa tana da bukatan wani abune a rayuwa, Hakan nema yau yafaru don fitowa na daga bedroom ke nan ina kokarin hadawa Amira magani don tana,fama da mura mai zafi duk ya toshe mata hanci, Man albasa ne nasa a sayo min a islamic chemis, don na bata tasha in kuma na shafa mata adukkan sassan jikin ta, Kallon kwalban maganin take don a zaton ta ko wani maganin sihirine nake son bawa yarinyar ina kallon irin yadda ta kurawa kwalin maganin ido, Nace a lokacin da nake girgiza kwalban maganin nace batai barci ba a,daren jiya tana fama da mura, Wanan mayye za,a bata ne wai, sai da nai dan murmushi yayin da na bude kwalban ina kokarin zubawa a spoon, Nace man albasa ne na kwalba aka,sayo don a bata saboda muran ya katse mata, Tace o,wo acikin kokarin daukan kwalin maganin don ta duba nan ta,fara karanta amfanin shi, Tace ashe sai na sayawa babyn mama kenan itama nace si ance yana da kyau maigoyon ta,ajeshi a tare da ita, don tana amfani a yara sosai, Can naji ta nisa tace dama nazo ne don mu san abin yi saboda ance karshen satin nan maigidan zai shigo, Na matse bakin yarinyar ina dura mata maganin nace to wani abin ya,farune kuma ? Ta dan gyara tsayuwan ta tana cewa wanan yar iskan mana yadda zamuyi mu bake ta mu hanata shakat a gidan, Da sauri na,dago kaina ina kallon ta don jin abinda tace, Cikin mamaki nake cewa akan may zamuyi mata haka kuma ? Tace har kin manta da zancen daukan fansan mu a kanta, Nace nifa ban fahintaba har yanzu wai may zamuyi matane wai halan,? Tace so nake mu bake ta tayadda duk wani sheri nata bazamu bari ta sakata ta wala ba sai dai ta rasa gane kan komai, Murmushi nayi ina kokarin bude nono naba yarinya nake cewa yanzu kina ganin cewa zamu iya kara hanata daukan girki a gidan nan, Tace kwarai dagaske ko har kin manta tadda muka kwasa dasu wancan zuwan da yayi, Nace cikin girgiza kai nidai gaskiya badani ba acikin wanan gaskiya don abin ai yazama shiga hakki kuma, Fon ita macuciya ce shine muma zamuyi mata cuta ai kawai mubarta da halinta kawai,Allah ya shige muna gama, Mu dai muyi ta kan mu mu san yadda zamu samu zaman lafiya a gidan Shiru tayi abinda yasani fahintar cewa zancen bai mata dadi ba gaskiya amma,sai nace idan kuma kunga zaku iya daukan mataki sai ku dauka kawai, Shiru tayi ranta a bace tana dan jujuya kwalin maganin dake hannun ta can tace tau shike nan amma ni gaskiya bazan yarda tace wai saitayi girki nayi ba, Nidai ban kara tanka mata ba sai bawa yarinya nono kawai nakeyi abina, A haka tafita daga part dina inda na rakata da harara a raina ina cewa muguwa dama fadan kanta takeyi shine take son cewa muma mushiga mu taya ta don muna mahaukata ko ? Fitan ta shigowan Asmau na tabi ta da kallon mamaki tana cewa, wanan kuma may ta shigo yin nan part din wai,? Nace cikin murmushi ki tambaye ta mana idon ta akan yarinyar dake a jikina tace ambata maganin nace mata eh sai naga takai zaune tace halan Yaya, zai zo garin nan ne, Nace may kikagani halan a lokacin da nake mika mata yarinyar tace, tana karban yarinyar naga wacan tsohuwar tana wani rawan kafa wai har da bada sakon a sayo mata kan "Sa, sabon yan ka an fada mata cewa akwai shi a cikin freezer tace wai sabo take so yafi dadi, Nace wani mugun abin take son yi dashi ke nan indai wanan da,bata da tauhidini ita komai nata na,sihirine, Zai kare a kanta ai inji anty nani dake tsaye daga kofa tun fara maganar mu, Tace ina Maimu na,fada mata kada ta fara,ta amshe shi, don ita ce yar kwadai tana ita karbanshi taci, Nace ai ki barta kawai taci don ba zai mata komai ba tunda ba donta akayi ba, Cikin tausa harshe tace a,a kedai ai ni ban ma,son ko kiga,wanan mugun hadin balle ki shaki kamshin sa don kinsan mugu yasan yadda zai samay ka, Haka muka ci gaba,da hira a tsakanin mu ba tare da mun fita ba, Ita Ramatu tana can main kitchen tana muna miya don idan ta,dora bata dagawa gurin sai tagana ta dauko tukunyan zuwa part din mu Kin san gidan yawa sai da taka tsantsan duk dabaran Salawatu don tai muna,sheri ga abinci mu amma Ramatu bata yarda ta daga a,gurin, Sai fa idan ta hada takwaso komai ta,dawo part din mu dashi,

****** ********** ****** Muna zaune bayan sallah magariba wayata tai kara abinda yasa Maimu miko min wayan dake makale a caji da sauri,, Yaya Abubakar ne don naji ringing turned din da nasaka mai mai taken Madina, akwai dadi danaje ni banso indawo ba, Na dauki wayan acikin yar murya mai jan ra,ayin mai sauraren ta nace, Hello Yayana, Sai naji yace cikin murmushi Meenatu yaya kuke ne,? Naso na shigo yau din nan amma, aiki yai min yawa bazan samu zuwa ba kuma, Sai nace a cikin sanyin murya, sai yaushe kuma Yaya ? Naji ya saki ajiyan zuciya yana cewa Meena aikine mai girma ya taso min anan din don haka banda time din zuwa yanzu, Na amsa mai da cewa tau, Can na nisa nace Allah ya taimaka Allah ya tsare yasa a dace, Ameen Amin nagode kwarai Sai naji yace ko zaku shigone ku samay ni nan din ? Nasan zolayata yake yi don ina zan tafi da yara kanana haka buuuu, Q¹ [1/3, 10:08 PM] Makawa: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣1⃣2⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AS SABUR

Ya Allah ka,gafartawa duk kan kullumin musulmin Allah da suka riga mu gidan gaskiya, Allah ubangiji ya kyauta namu bayan nasu Allah kasa mu cika,da kyau da imanin ubangijin mu👏👏👏👏

A haka ya daure ya koma gurin aikin shi inda nima naci gaba da harkokina sai dai na kudurta a raina duk sanda ya dawo insha Allahu zan sassauta mai, Anty Amarya ta bugo min waya tana fada min irin takai din da suke kwasa da amaryan gidan su take cewa wai dama Meenatu irin rikicin da kike gani ke nan akan kishaya, Ai mai kishi da mace daya ba kishi yasani ba sai gasa kawai, Tace nifa hada min kai akayi da mummy ku da Amarya komai yanzu a tare sukeyi wai don kawai a bake ni, Tace da har Uncle dinki zai biye masu a hade min kai dashi dukka amma,sai nai mashi kwal nasa mashi waigi, Yanzu wai har unguwa a tare suke fita haka kuma in a gida suke suna likeda juna dakin daya, Hmmm nace wani sabon sallo ke nan kuma akazo dashi ashe Yanzu ita mummy da shekarunta ta yarda da wanan hadin kan sheri, Nace Anty ki saka masu ido don karshe abin bazai masu kyau ba baran baran za,a kare Tace tun yaushe ma tunda basu bar kansu ba kishin junan su, suke suma, Nace to dama ai babu kishiyar da ke son kishiyar ta tsakani da Allah sai dai kawai mutum ya kwatanta na Allah kawai don tsoron ubangiji, Nace idan har kin yi hakkuri anty zaki gan su a rana sosai wallahi don ranan zakiji fallasa har sai kin toshe kunnuwan ki, Na ce kada ki yarda da zancen hadin kai da kowan su wai don a cutawa wata, kedai kawai gyara kan ki tsakaninki da mijin ki, Nace ni kinga Anty duk irin sherin da Salawatu tai min bai hana,na kulata ba a,fili don ko abu take so yanzu gurin mu take zuwa, karba, Anty tace muguwa yanzu wai ita adole tayi kwanton kasa sheri na cikin ta a boye, Mun dauki lokaci da Anty muna wayan akan matsalolin gidajen mu inda daga karshe mukayi sallama saboda bakin da suka shigo gurin ta,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull