Tarko complete novel - Chapter 116
Tarko complete novel Chapter 116: Tarko complete novel Chapter 116. ****** ********** ****** Kwanan shi biyu da tafiya ina zaune a falon part dina muna…
3,419 words
****** ********** ****** Kwanan shi biyu da tafiya ina zaune a falon part dina muna kallo kawai wata zuciya tace min nakira shi mu gaisa, Inda ba bata lokaci nabi shawaran zuciyata na daga waya na kirashi, Duk da yake a lokacin nasa cewa lokacin aikine amma hakan bai hanani kiran wayan shi ba, Zaune yake yana tsakiyan aiki da,wasu dirctorcin su, wayar shi tai kara kamae kada ya dauka,don ba dabiar shi bane daukan waya lokacin da yake aiki, Daukan wayan yai daidai da sakin ajiyan zuciyar da yayi a cikin wani irin murya maikama da rada yake cewa, My Sister , Nace a yar murya Yaya ka koma lafiya,? Ya dan ja numfashi,tare da furzar da iska yana cewa Alhamdullahi Ya na barku ya yaran, duk kowa lafiya ko naji dadin wanan, tambayan da yai min don ni a rayuwana ina son mai son diyana, Shiru muka,dan yi na lokaci guda, can naji muryan shi a,cikin dan wani yanayi yana cewa, Meenat kin huce ke nan da hushi da yayan naki, Yar gajerar murmushi nai mashi batare da na furta uffan ba, Please Meenat ki sassauta min nasanna cancanci duk wani hukunci daga,gare, ku duk da ban san takamaimain laifin da nai maku ba har kuke min wanan hukuncin haka, Amma duk da hakan ina son ganin kin sake ranki kamar yadda,yan uwanki suka, hakkure min, Shiru nayi ina sauraren shi batare da na tanka mai ba, Yace yanzu please muyi magana kafin na dawo, don mu fahinci juna dake, yana,magana tamkar zaiyi min kuka, Hmmm namiji nace a raina wani yar karamar nan Yaya Abubakar kewa wanan marairaicewan haka, Amma a irin yanayin da yake magana sai na soma jin ya fara kara min zuciya da dadadan kalaman shi masu ratsa jiki, da tausayi, Allahu Akbar ance tsakanin mata da miji sai Allah, a take naji ya bani tausayi, Nace a sanyaye Yaya komai ya,wuce insha Allahu Masha Allahu, ina dai kara baki hakkuri, don Allah Meenatu ki saki ranki a cikin gidan ki kamar kowa, Inda,na kashe wayan nan nai zaune ina tunanen irin abubuwan da,ya,wakana a baya, a lokacin sherin Salawatu na akan shi duk dama ko yanzu da alaman sauran shi, Ba komai yasa na fadi hakan ba,sai ganin duk irin fitinan da,suka kwaso a ca wanan zuwan da yayi ya fuce don da ta,samay shi da zancen cewa wai bata san dalilin rashin bata girki da,bamuyi ba sai yake tambayan mu, Amma sai kowa yai shiru ba,wanda yai magana daka cikin Sadiya da,Fatima, Mamaki suka bani sosai don dafa garesu zancen yafito, amma yanzu gasu sunyi shiru, Sai ni ce a cikin karfin hali nace munyi hakane don ganin cewa ita can take zaune tare da kai zuwa tayi, Cikin bacin rai Salawatu tafara fada tana cewa kwana nawa nayi a garin nan da za,ace wai ina can tare dashi ba zanyi duty ba, Sai a lojacin Fatima ke cewa koda wata daya kikayi baza mu yarda ba don muma matan shi ba farkokin shi ba Yadda kike takaman auren shi kikeyi muma haka zaman auren shi mukeyi, Cikin wani murya ta juya gare shi tana cewa bazaka sa baki a zancen ba don kaji abinda sukace, Yace cikin wata murya kamar wanda ake juyawa da romote, kubata girkin ta don Allah a bar zancen hakana please, Sadiya tace a cikin karfin hali baza,abata girkni ba Fatima ce zatayi don ba fin mu tayi ba anan cacan baki ya fara inda mukafi karfin su dole a ka kyale Fatima tayi girki a ranan, Abinda yakara sani bata raina dashi kenan har zuwa yanzu abin yaki fita a zuciyana Amma dole babu yadda zanyi da raina dole na hakkuri da abinda yafi karfina, Yanzu muna waya dashi a akai akai kuma ban daina,adduan da nakeyi ba na samun galaba akan sherin Salawatu , Sosai Salawatu ranan ta je baci da ganin yadda kowatakeyadda taga dama agidan musan man part dina dake da yan aiki da yawa suna harkokin su kaman yan gida, baza kace yan aikin gida bane, su, A cikin wanan yanayin ne har Allah yadawo muna dashi lafiya abinda nasanine da zaran naga Fatima a part dina nasan cewa tana da bukatan wani abune a rayuwa, Hakan nema yau yafaru don fitowa na daga bedroom ke nan ina kokarin hadawa Amira magani don tana,fama da mura mai zafi duk ya toshe mata hanci, Man albasa ne nasa a sayo min a islamic chemis, don na bata tasha in kuma na shafa mata adukkan sassan jikin ta, Kallon kwalban maganin take don a zaton ta ko wani maganin sihirine nake son bawa yarinyar ina kallon irin yadda ta kurawa kwalin maganin ido, Nace a lokacin da nake girgiza kwalban maganin nace batai barci ba a,daren jiya tana fama da mura, Wanan mayye za,a bata ne wai, sai da nai dan murmushi yayin da na bude kwalban ina kokarin zubawa a spoon, Nace man albasa ne na kwalba aka,sayo don a bata saboda muran ya katse mata, Tace o,wo acikin kokarin daukan kwalin maganin don ta duba nan ta,fara karanta amfanin shi, Tace ashe sai na sayawa babyn mama kenan itama nace si ance yana da kyau maigoyon ta,ajeshi a tare da ita, don tana amfani a yara sosai, Can naji ta nisa tace dama nazo ne don mu san abin yi saboda ance karshen satin nan maigidan zai shigo, Na matse bakin yarinyar ina dura mata maganin nace to wani abin ya,farune kuma ? Ta dan gyara tsayuwan ta tana cewa wanan yar iskan mana yadda zamuyi mu bake ta mu hanata shakat a gidan, Da sauri na,dago kaina ina kallon ta don jin abinda tace, Cikin mamaki nake cewa akan may zamuyi mata haka kuma ? Tace har kin manta da zancen daukan fansan mu a kanta, Nace nifa ban fahintaba har yanzu wai may zamuyi matane wai halan,? Tace so nake mu bake ta tayadda duk wani sheri nata bazamu bari ta sakata ta wala ba sai dai ta rasa gane kan komai, Murmushi nayi ina kokarin bude nono naba yarinya nake cewa yanzu kina ganin cewa zamu iya kara hanata daukan girki a gidan nan, Tace kwarai dagaske ko har kin manta tadda muka kwasa dasu wancan zuwan da yayi, Nace cikin girgiza kai nidai gaskiya badani ba acikin wanan gaskiya don abin ai yazama shiga hakki kuma, Fon ita macuciya ce shine muma zamuyi mata cuta ai kawai mubarta da halinta kawai,Allah ya shige muna gama, Mu dai muyi ta kan mu mu san yadda zamu samu zaman lafiya a gidan Shiru tayi abinda yasani fahintar cewa zancen bai mata dadi ba gaskiya amma,sai nace idan kuma kunga zaku iya daukan mataki sai ku dauka kawai, Shiru tayi ranta a bace tana dan jujuya kwalin maganin dake hannun ta can tace tau shike nan amma ni gaskiya bazan yarda tace wai saitayi girki nayi ba, Nidai ban kara tanka mata ba sai bawa yarinya nono kawai nakeyi abina, A haka tafita daga part dina inda na rakata da harara a raina ina cewa muguwa dama fadan kanta takeyi shine take son cewa muma mushiga mu taya ta don muna mahaukata ko ? Fitan ta shigowan Asmau na tabi ta da kallon mamaki tana cewa, wanan kuma may ta shigo yin nan part din wai,? Nace cikin murmushi ki tambaye ta mana idon ta akan yarinyar dake a jikina tace ambata maganin nace mata eh sai naga takai zaune tace halan Yaya, zai zo garin nan ne, Nace may kikagani halan a lokacin da nake mika mata yarinyar tace, tana karban yarinyar naga wacan tsohuwar tana wani rawan kafa wai har da bada sakon a sayo mata kan "Sa, sabon yan ka an fada mata cewa akwai shi a cikin freezer tace wai sabo take so yafi dadi, Nace wani mugun abin take son yi dashi ke nan indai wanan da,bata da tauhidini ita komai nata na,sihirine, Zai kare a kanta ai inji anty nani dake tsaye daga kofa tun fara maganar mu, Tace ina Maimu na,fada mata kada ta fara,ta amshe shi, don ita ce yar kwadai tana ita karbanshi taci, Nace ai ki barta kawai taci don ba zai mata komai ba tunda ba donta akayi ba, Cikin tausa harshe tace a,a kedai ai ni ban ma,son ko kiga,wanan mugun hadin balle ki shaki kamshin sa don kinsan mugu yasan yadda zai samay ka, Haka muka ci gaba,da hira a tsakanin mu ba tare da mun fita ba, Ita Ramatu tana can main kitchen tana muna miya don idan ta,dora bata dagawa gurin sai tagana ta dauko tukunyan zuwa part din mu Kin san gidan yawa sai da taka tsantsan duk dabaran Salawatu don tai muna,sheri ga abinci mu amma Ramatu bata yarda ta daga a,gurin, Sai fa idan ta hada takwaso komai ta,dawo part din mu dashi,
****** ********** ****** Muna zaune bayan sallah magariba wayata tai kara abinda yasa Maimu miko min wayan dake makale a caji da sauri,, Yaya Abubakar ne don naji ringing turned din da nasaka mai mai taken Madina, akwai dadi danaje ni banso indawo ba, Na dauki wayan acikin yar murya mai jan ra,ayin mai sauraren ta nace, Hello Yayana, Sai naji yace cikin murmushi Meenatu yaya kuke ne,? Naso na shigo yau din nan amma, aiki yai min yawa bazan samu zuwa ba kuma, Sai nace a cikin sanyin murya, sai yaushe kuma Yaya ? Naji ya saki ajiyan zuciya yana cewa Meena aikine mai girma ya taso min anan din don haka banda time din zuwa yanzu, Na amsa mai da cewa tau, Can na nisa nace Allah ya taimaka Allah ya tsare yasa a dace, Ameen Amin nagode kwarai Sai naji yace ko zaku shigone ku samay ni nan din ? Nasan zolayata yake yi don ina zan tafi da yara kanana haka buuuu, damu, Ban san zancen zucin da nakeyi ba yafita fili sai dariyan shi naji yana cewa ba gidan uban su za,a zo dasu ba, Na dan lumshe idanuwana a cikin wani irin yanayi nake cewa Allah dai ya dawo dakai lafiya Allah ya tsare, Yace Wadda ya fada min cewa yau Mamana bata da lafiya,wai tana fama da mura, Nace eh amma na bata magani ta samu sauki sosai don gatanan tana barci tun da,zun, Sai da ya tambayi lafiyan duk yaran acikin so da kauna irin yadda ko wace uwa ke son uba ya kula da dan shi sannan mukayi sallama dashi na kashe wayan, Ina mai sauke zuciya na dubi su Antyn Nani nace yau sai yaya ina mai dafa kan shanu ga maigidan yace ya fasa shigowa yau, Ramatu tace ashe yau akwata don dai har tashirya dinning table tundazun ko, Nan muka,aha dariya inda Anty nani takara han kunnen Maimu a kan kwadai, Baba Wadda ne yashigo yake fada masu cewa Yaya ya,fasa,shigowa garin yau, Salawatu da tasha kwalliya ta,sa wani bubu na lace ta daura,zani ta baya, Sai bugun zani take takalma na kus kus a gidan wai tayi hakane don ta tayar muna da hankali a dole ita zata karbi girki idan yazo Sai akai sa,a kowa ya saka mata idanuwa sai gashi Allah ya kamata ya,fasa zuwa bayan tagama hada komai, Baba Wadda yana fitowa take ce masa wai yaxo su diba,su sha, Bata san su Anty Nani da Asmau sun tsorata baba Wadda yace bazai sha ba yafita don kada ta takura mai, Mukan muka rufe part din mu don gudun kada ta zo muna tayi miyan ta mai agumo yaji hade hade sihiri, Sai faman tsuki take ta,shige kitchen da kayan tana masifa ciki ciki,
****** ********** ****** Bai shigo ba,sai da yakara kwana tara a,kai kuma kafin ya,shigo sai da ya bugo ya,sanar dani cewa na shirya taron sa, Don wai nice mai masaukin shi idan yazo sai dai cikin dan marairaicewa nake cewa amma ai banice ya kamata na karbi girkin ba yau, Yace ni kuma kece nace zakiyi don haka ban son jin wani zance kawai kishirya tarona, A tsanake muke aiwatar da,duk wani shirye shiryen da ya kamata muyi gurin taron nashi Kafin ya iso dagani har yara duk mun tsala kwalliya irin yadda yadace nayi, Mun fito taron shi a cikin tsari wanda sauran abokan zamana tankar zasu fada a wuta don haushi Anty Sadiyace kawai bata ji zafin hakan ba don tasan yana,da dalilin yin hakan da yayi, Amma tun isowar shi Salawatu tafara tsegumin cewa don may Meenatu zatai girki yau tunda ba itace yadace ace tayi ba, Dakatar da wasan da yake da Amir yayi yadago kai yana cewa wanan kuma ra,ayinane don ni nace mata tayi, saboda a gurinta zan sauka yau din ,, Sai cewa tayi amma wanan ai rashin adalci ne ko da zakace wai ita kake son tayi girkin, A daidai lokacin ne na karaso gurin naji zancen da sukeyi, Gaba daya muna sauraren su yace cikin daure fuska ai rashi adalci sai ke yarinyar nan yaushe rabonta da girki a gidan nan wai, ? Don haka ita nake bukatan tayi girki a yau din nan, Daga haka yace Amir yahe gun little mummy Anty Asmau yake nufi kaunata, Yana shigewa don na dada bata haushi nabi bayan shi nima, A kusan tare muka shiga,dakin nashi dashi sai kamshi ke tashi dakin yasha gyara ta ko ina ga sanyi A c ya gauraye ko ina na dakin, Juyo yayi yai tsaye ya kare min wani irin kallo kamar ranan ya fara gani na karo na farko, Fisgoni yayi zuwa jikin shi ya rugumay ni tsab yana wani sauke numfashi, Tausayi sosai yabani inda nakewa Salawatu Allah ya isa azuciyata na raba tsakanin mu datayi na wani lokaci, Daga tsaye muka kai kwance saman gado da kyat na,samu yasakeni inda naje ce mai yai wanka ya ci abinci ko zai ji dadin jikin sa, Zama yayi a bakin gado yana cewa Meenat kamani na mike duk a gajiye nake wallahi, Na zuba mai ido inda na fahinci da gaske yake na kamadhi hakan akayi na kamadhi zuwa bathroom sai da naga yana shirin cire tufafin shi nai mai dabara nagudu, ****** ********* ****** Babban magana a gareni shine yadda zan tafi da,yara har uku kwana dakin maigida , Amma ina zaune gaban mirro ina gyara jikina Anty Nani ta shigo tana cewa hajiya sai kibar yaran tunda muna,da yawa anan wanda ya farka,sai mu bashi madara, ko, Cikin dan murmushi nace amma baza su hanaku barci ba tace ai kin san basu faye farkawa ba dare badu da fitina, Yana tsaye yana waya a jikin window dakin shi nashigo dakin da sallama acimkin shirina na kwanciya don yau na,shirya taron shi sosai, Ido ya kuramin inda,shigana ya burge shi duk na canza mai na zama kamar wata diyar larabawan tsakiya, A hankali na taka har zuwa inda yake a tsayen nadan rungumoshi ta baya ina sauke numfashi a hankali, Acikin hikima yadan zagayo dani zuwa jikin shi yana cewa ina yaran suke ne Nace kamar mai rada suna gurin su Ramatu da Antyn Nani sun ce na barsu a,gurin su, Yace cikin lumshe idanuwan shi Allah ya,saka masu da alheri ai sun taimaka minsosai,
ZEEE MAKAWA YELWA SEENABU
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣1⃣3⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SUBBAHANALLAHI WABI HAMDIHI SUBBAHANALLAHI AZEEMU,,,,,
Bayan komai yakammala a tsakanin mu,ne ya dan rugumoni zuwa jikin shi yana mai sauke numfashi a hankali, Yace wai amarya ce yau na,samu ko kuwa dai idonane yakw min gizo ? Murmushi zancen shi ya sakani kawai don nasan cewa zolayata tace yake yi kawai,. Gaba dayan mu munyi shiru babu mai magana kowa da irin abinda yake tunawa a zuciyar shi Can naji ya dan sauke numfashi da karfi sai naji ya nisa yana,cewa a cikin wani irin murya mai taushi, Meenatu duk abinda zaki min daga yau bana son ki kaurace min Ki dauki duk matakin da zaki iya,dauka a kaina amma banda wanda zaki hana min rabuwar ni,imar ki gareni, Shiru nayi na gaza cewa komai tun lokacin da yafara magana,saboda nima kaina,nasan cewa nayi missing din mijina fiye da tsan manin maikaratu, Banda abinda zance sai dai nace Allah ya,isa a tsakanin mu da Salawatu kawai, Har safe nakai a dakin hankalina a kwance kamar ba goyo gareni ba, Inda Allah ya,tai makeni tun haihuwa da yake nasan cewa ni mai zuwa turakar maigada kwanane don haka sai ban yarda na sabawa yarana kwana manne da jikina don kada,su saba da,tsotson dare, Hakan a hankali har suka saba da kwana batare dani don Asmau da Anty ko Ramatu suke yawan kwanci a,kusa dasu da zaran yaro ya farka sai adan bubuga mai baya ya,koma barci, Sai a,suban farko nabar dakin zuwa part dina don na duba yaran, Tura kofan naji shi a bude don haka nashige zuwa cikon bedroom dina, kai tsaye inda na kara tsarkake jikina tare da,dauro alwala, Ina zaune a,saman salaya gurin da na idar da,Salllah ne Anty Nani tashigo dakina,daukan feeder Amira,dake dakin na Ta samay ni zaine ina zabga adduoi, hannaye sama,a,dake taji mamaki kwarai da ta,samay ni a,daki lokacin don cikin dafirgita take cewa a, ashe kina cikine , Amira ce ta,farka kuma feeder ta yana nan akace da hannu nai mata nuni da gurin da shike Tafita tana mamaki aranta tana ganin kamar a dakina na kwana ban tafi turaka,ba, Idan da,a bayane bayan na idar da,sallah asuba zan koma na hada,mai ruwan wanka idn kuma yana da bukatan na sai na tsaya Sai gashi yau sabanin hakan don dai ban koma ba part din nashi, Agurin da, na idar da,sallah barci yadan kara kwasa na inda na,dunkule gurin ina barci, Shigowan shi dakin ya,samay ni a yadda nake kwance, yadan dade a tsaye yana,kallon yanayin da nake kwace a,saman sallayan, Lokacin da na,farka yakai kusan awa daya da,fita,daga,dakin nawa amma dakin har zuwa lokacin yana kamshi Yaya Abubakar, Yaran aka kawo min daya bayan daya suna dan tsoha nono, duk d da,alama sun sha madara amma sun dan taba sha, nonon, Wanka na koma yi na kimtsa, a cikin wani atamfa mai zubin yar ibo wanda akai min dinkin doguwar riga mai hannuwa shara,shara, na dauro dankwali mai lailaiya, Simple makeup nayi wa fuskana tare da,dan ziza man baki sai kamshi da na,sakawa jikina, Ina zaune a,gaban mirro yashigo dakin yana,saye da kananan kaya, da suka karbi jikin shi tsab, Saboda zaman shi a can kasan iyamurai ya,sa shi yanzu ya fi da,son ya,saka kanan kaya, a jikin sa, Ya,shigo dauke da Amir a kafadan shi yana cewa kyale Ramatu itace taki goya,ka,ko ? A hankali na,dago idanuwana ina kallon su yayin da Yaya ya nufi bakin gadona ya,zauna a hankali still yaron yana makale a kafadan shi,, Ya na zama yana,duban fuskana wanda ba yabo ba fallasa a cikin sa sai dai na,dan dukar da kaina Meenatu naji ya kira,sunana a bazata, batare da na daga kai na kalle shi ba na amsa da naam, Yace yaya akayi baki dawo hada min ruwan wanka ba da safe, Shiru yayi sai naji ya nisa yana cewa what happen ne wai ko har yanzu fushin ne ? Nace cikin yar siririyar murya tare da girgiza kai nace Babu abinda ya faru kawai dai na kwanta ne bayan na idar da Azakar sai barci yakwashe ni, Murmushin ciki naji yayi inda yace hmmm, Kincanza min Meenatu ba kamar yadda kika sabamin ba da farko, Jin abinda ya,fada, yasani dago daradaran idanuwa na,na,sauke su a kan shi, Ya,sakar min wani lalausar murmushi da kafeni da firgittatun idanuwan shi, Nace bani ce na canza ba Yaya yanayi ne ya canza min yanzuba kamar farkoba, Don yanzu kaga akwai yara a tare dani dole ne hankalina ya kasu gida biyu kuma ai bani na canza ba kai ne kafara canzawa Sai kuma na kasa karasawa nai shiru kawai ina dan kallon kasan dakin batare da nai magana ba, Kenan zancen bai kare ba ashe ko ? Nace a hankali ya kare magana ne kawai ai akeyi ba,wai zancen bane, Amir ne ya,saka hannuwan shi a fuskan uban nashi yana dan wasa dashi, Dagagurin da nake nakewa yaron da yabari a cikin tsawa, Hannu ya daga min yana cewa ki barshi kwana biyu da baiganni ba,ai baiyi ba yanzu nima kewan diyana ne yake,yawan damu na don nasan cewa matsalata ce babba hakan ban sa su ajikina ba,, Nace ai baka garine shiyasa basu saba da,kai ba amma ai zasu yarda,da,kai idan suna ganin ka, time to time, Murmushin ciki kawai naji yayi tare da,kara,sauke ajiyar zuciya shiru gaba daya mukayi babu wanda ya,kara,furta wani kalami again,