Tarko complete novel - Chapter 117
Tarko complete novel Chapter 117: Tarko complete novel Chapter 117. ****** ********** ****** Tsafi gaskiyan maishi don ranan da Salawatu ta fahince…
2,655 words
****** ********** ****** Tsafi gaskiyan maishi don ranan da Salawatu ta fahince maigidan ya kwana dani ranan a cikin wani irin shock take wanda kallo daya zakai mata ka fahinci cewa tana a cikin wani irin yanayi na tashi hankali, Wanan ranan haka rayuwan ta yi shi cikin tashin hankali don babu zancen dake mata yawo a,rai kamar zancen malamin ta sa yake cewa kiyi duk yadda zaki kada ya kara kusantar ta nan da wuri don idan har haka ya kasance a gaskiya zaki sha mamaki sosai, Don zaiji a duk cikin matan duniya babu macen da takaira dandano da kyautatawa sai ita kawai, Tace malam kana nufin cewa hankalin shi zsi koma gareta ita kadai ke nan malamin ya kada kai yace kwarai da gaske don kin ga ai sunanta yafi fitowa sa yawa ga aikin, Kaikaiyi zai iya komawa kan mashekeyi don abinda ya kamata yaji a gareki sai aji shi a gurin ta,, Gabanta yaba da dam don dai in ba,zato take ba babu tantama yau wa yan,nan mauratan sun kwana tare don tun shigan meenatu part din bataga fitowan ta ba, Yau ne karo na farko da tai nadamar aikata irin wanan rayuwan na tsaka mai wuya badon komai ba don ansha warning din ta akan wanan yar hasabibiyar yarinyar da tayi a hankali saboda jinin su yana da karfi, Koshi saida akayi da,gaske kafin a samu abinda zaiyi tasiri akan shi, A lokacin baida tsarki a jikin shi tabashi wanan mugun hafin da,akai mata a matsayin drinks ya shanye, Tunane barkatai take wanda ya hana zuciyar ta sukuni, Daga gurin da take zaune taga fitowan shi daga part dina zubur ta mike zaune tana cewa dama ina son ganin ka ne dear, Da,sauri yace batare da ya,tsaya ba ki bari har nadawo zan fita,da yara ne unguwa, Ya haye sam da,dan gudu,gudun shi, inda ta bishi da kallo har ya bace mata, Yayin da ta dan cije leben ta tare da,sake dan kwafa, tana mai jin wani iri a cikin rayuwan ta, Tana tsaye a gurin ya fito a cikin shirin shi bai bi ta kanta ba yake cewa Aisha da yaran Fatima su fito a lokacin ne ttaga,ashe, har da harda Meenat ne zai fita, Yazo ta gabanta ya,wuce ko kallon gurin da take tsaye baiyi ba ko duk daukin zai fita da matar son shine hakan Oho, Daga tsaye takai zaune saman kujera jagwab kai kai wanan al,amarin da ban mamaki yake, sai bin kofan da yafita tayi da kallo tana mai sauke ajiyan zuciya, A daidai lokacin ne na fito saye da,wani dogon riga irin dinkin Afrcabaya, yadin rigar mai shaking nai rolling din kaina acikin wani gyale orange colour, Sai kamshi Arabian Oud wanda ake yayi ke tashi a jikina, wanda ke isar wa kishiya da,sakon nafito, fa, A cikin wani irin kallo muka hada idanuwan mu ni da ita sai nake cewa sai mun dawo ko, Hakika,ban taba zaton zan iya hango tatin sheri a zahiri ga idanuwan Salawatu b sai yau din nan, Don gaba daya babu alheri a kwayan idanuwan ta z lokacin sai sheri, don haka nabita da A,uzu,bikalamatillahi tammat min,sherin ma halak, Bayana tabi da kallo tana mai,jin kamar acs ta bini da dukan tsiya sai na daina nufashi , Don dai yau ta,fahinci cewa duk na,wargaza mata wani mugun kulli da,sherin da tayi wa dan wan nawa, Gashi kuma ta gani a zahiri don a gabanta na dauke shi muka fita dagani sai shi da yaran mu, Damuwa ne ya rufe ta a lokaci guda duk hankalinta ya tashi, har take ganin cewa, bazata iya kara koda minti biyu ba a gurin, Jiki a,sabule ta mike zuwa part din ta, a cikin tashin hankali da,rudani, abinda taje juyawa yadda ranta yaso yau gashi tana gani a hannun wata, kishiya ke nan, A dakin ta taji hayaniyar mu a lokacin zamu shiga mota don haka gulmanta yasata daga labulen window ta dan leka A motar shi ce mu kai fitan kuma nice mai jan motan,mu shi yana daga gefe a zaune yana mai dan sake murmushin nan shi da alamar yaji dadin hakan,, Da sauri ta sake labulen taga a cikin tashin hankali ta fada saman gadon ta hankali a tashe, acikin ranta tana fatan na halakasu motar ta fadi taga karshen so, Su kan sauran ba su wani samuwa ba sosai duk da dai fitan ya dan touching din zuciyan su amma sai suka share, kawai, balle ita Fatima da ma har da yaranta muka fita,
****** ********** ****** Muna barin haraban gidan na juya ina ce mai wani guri zamu tafine, Ya dan yi jim can yace mu fara kai yaran nan park tukun na ko su dan yi wasa, Na ce tau Yallabai, angama don haka na dauki hanyar zuwa park din kamar yadda yace min, Daga gurin da yake zaune yake kallon irin yadda nake tuki a cikin gwanin ta gashi kuma nasan hanyoyin sosai, Nace batare da,na kalli gurin da yake ba hankalina a saman titi, nace ko dai nabaka kajamune ,? Yadan lumshe idanuwan shi kadan yana cewa saboda may gashi naga kin san garin ma sosai, Na dan waiga kadan na kalke shi nace cikin murmusawa ai dole na,san gari ka manta Baba Hamza ne ya koya min mota, Murmushi ya sake tare da,dan rugumaya yarinyar dake hannun shi yana cewa, Ga kuma abokiyar fitan ki Fattu ko don naga ita ai yar gari ce, murmushi nayi don dama nasan cewa sukanyi hiran hakan shi da lawal cewa muna yawa ni da Fattu, Murmushi na,sake tare da dan kada kai nace haba Yayana ai yakamata ace ka shedeni don nakan yi sati biyu ban fita,sai dai idan gyaran kai zan fita yi kawai, Daga bayan mota babban yar gurin Fatima take cewa Maman, Amir kinga Iklas tana cewa,wai sai an bata Alhassan ta dauka ko, Shi ya juya yana magana da yaran yayin da hankalina yake a saman titi ina han su a hankali, Nace wa yarinyar Iklas ki bari idan mun koma gida sai na,baki shi ki dauka kinji, Acikin park din na,samu guri na parker motan muka fifito da yaran, Yaya Abubakar ya,wuce gurin da ake karban receipt yakarbo nan muka fito da carpet daga bayan mota da abubwan da mukazo dashi muka samu guri muka zauna Sai hira yake da yaran gwanin ban shaawa inda idanuwa yana akan su cikin so da kauna, Wayana dake a cikin post dina yai kara na,dauka inda na iske Anty barister ce ke kirana tana,sheda, min cewa wai gata gidan mu ita da maigidan ta yana,son ganawa da Yayana, Idanuwan shi kyam a kaina yayin da na dago idona don na,fada mashi cewa munyi baki a gida suna,son fanin shi, Irin kallon da naga yana min yasani dan juya idanuwana wanda ni ban masan cewa nayi mai su hakana ba, A cikin dan in,in,niya nake gaya mai Antyn Barister ce da maigidan ta suke son ganin ka,wai, Kai naga yagyada tare da,saurin daure fuska yana cewa lafiya dai ko suke son ganina ? Acikin dan sanyin murya nake cewa wallahi ban san ko may ya kawo su ba, Nasan cewa shi ba mutum bane mai son shiga mutane baya hurda da mutane barkatai haka, To may zai kawo Anty Barister gurin shi da mijin ta, yanzu gabana yabada dam nace kar dai, Anty suce sunzo yiwa Yaya nasiha akan zaman mu, Duk da dai ban wani fada mata irin rayuwan da muke ciki dashi ba,sosai muryan shi ne ya katseni inda yake cewa kice suzo su samay may mu nan ko, Don kinga yaran nan sunji dadin wanan fitan da akayi gasu sai wasa sukeyi, A sanyaye na fadawa Anty gurin da muke inda take cewa gasu nan zuwa su samay mu din
****** ********* ****** Sun samay mu gurin nan suka,gausa inda na fahinci basu san juna ba,dashi dama, amma yasan Anty barister sosai, Saboda yawan zuwa gidan guri na ko kuma,ya samay mu a,tare da ita,wani lokaci, Mun basu guri inda ta tayani kwasan yaran zuwa gurin da zasu hau dawakai da lillo, Naso natambaye ta abinda ya kawo su amma sai na kama bakina don nayi yarinta da,shiga harkan manya, Itace cikin nuna jin dadin ta take cewa kaunata nayi farin ciki kwarai da,ganin ki a haka don ko baki fada,min ba nasan abu yayi sauki ke nan, Murmushi kawai nai mata tare da cewa insha Allahu hakane Anty Allah ya kawo saukin al,amarin yanzu don dai tun wancan zuwan al,amuran sunyi sauki sosai wallahi, Tace haka ake so dama ai shi irin abin sihirin nan bai kaiwa ko ina,ba,dadewa yake ajikin mutum ba,sai dai idan mai sihirin na,yawan yi a koda yaushe, Tace Allah dai ya kare mu daga,duk wani sherin shedan, mutum, ko aljan ko wani dabba ko kwaro, Na amsa da cewa Ameen ya Allah Anty, nagode da kokarin ku gareni, Tai murmushi tare da,cewa haba Ameenatu ke fa tankae kainata Ameenatu ce da ta rasu nake daukan ki don gani yar uwa nake maki sosai nakara cewa nagode Ta canza zancen da cewa,sai kika gan mu kuma da yamman nan ko ? Nace hakane tace nima ya damay ni da zancen don Allah na kawo shi gurin maigidan ki tun lokacin da, na fada mai aikin maigidan naku, Sai a lokacin hankalina yadan kwanta don na dan fahinci abu daban ne ya kawo su gurin shi, Nan mukai ta,harkokin mu da yaran mu sunata dan ihuce ihucen su inda su mazan sunkai kusan awa daya a tare sukayi sallama suka tafi mu kuma muka cigaba da sha,anin mu a park, Muna barin gurin ya nufi wani katon shago damu indai yaiwa yaran sayyaya masu tsadan gaske, Wanan karon shine mai jan mu a motan don ina,bawa Alhussaini nono saboda yai barci a,jikina, Muna cikin tafiya yake cewa ba tare da,ya dubi inda nake ba yace, Mijin Antyn ki hanya yaje so nai mashi na business din qurl oil wanda ba kowane ke samun wanan hanyan ba, Amma dai nai mashi alkawarin zan bincika naga idan za,a,samu, din, Nace cikin nuna jin dadi mun gode kwarai yaya Allah ya kara rufa,asiri, Maimakon yace Ameen sai naji yace Hmmmm, kawai bai kara cewa,komi ba again, Sai marance lis muka,dawo gida,da kayan mu niki, niki mun samu matan gidan a falo suna zaman falo, A gajiye naje don yaron dake a jikiba yai barci yai min nauyi don haka sannu kawai nai masu nashige part dina, Yayin da,duk suka,bini da idanuwa kowa da,abinda zuciyarta ke fada a gamay dani lokacin, Yashigo tare da yaran gaba dayan su kowa da abinda,ya,dauko a hannun shi sai yake cewa yaran Ota kukaiwa Mummy a dakinta ta,raba maku ko, Hakan baiwa Fatima,daidi ba,aranta amma,saboda kada ta bayar da dama gurin Salawatu wace take jin tankar zata shake ta tace wa mai gidan sannun ku da,dawowa,acikin wani murya mai nuna rashin dadin yanayi,take mai sannu din, Sadiya ma,ashigen muryan ta gaida,shi amma a,dan washe da,baki tana cewa yau kan yara sun ga gari, Salawatu wace a lokaci rayuwanta kamar zata kuwata don bacin da yayi don haka ta kasa ce mashi komai, Na fito falo na,sanu sun jibga min kayan a,nan sai da,nai sallah na zauna na,rabawa kowani yaro nashi inda na bawa Maimu, nace takaiwa su Aina nasi part din su, Kayan lashe lashe ne irin na yara,sai kayan wasa da ya,saya masu kowa ya zabi abinda yake so acikin su aka,saya mai, A haka rayuwan ta kasance muna wann zuwa kowa yai kokarin gyara,tsakanin ta,dashi don washe gari Anty Sadiyace ta karbi girki inda ya dauke ta,suka fita unguwa tare, Next daya sai Salawatu wace tun bayan rabuwan su acan gatin aikin nashi da suka rabu tsiyatsiya ya turo ta gida sai yaune zata karbi girki din, Saidai abin ya,wuce tsan manin ta,don har yanzu ba,wani sakewa a tare dashi, kawai dai, sun kasance a tare ba irin yadda ya saba mata ba, Hankalin ta a tashe, yake saboda irin yadda,maigidan ya karbe ta, Wanan daren haka ta gan shi idon ta,biyu, tamgararan babu irin tu nanen da batayi ba, Shiko yana,daga gefe sai barcin shi yake hankalin shi a kwance, sai zuwa sallah asuba,ne ta,samu barci, , Washe gari ina,daki abina ban fito ba,don gudun fitina saboda haka muna,daga ciki a bin mu shiko ya shigo gurin mu yafi a,girka a,ranan don rshin ganin mu a,waje da,baiyi ba, Samun da,yayi muna kallo ne yashi zaton cewa ai kallon ne ya,dauke muna hankali bamu fito ba, Fitowan da zaiyi ne ya iske Salawatu ta hau tayi fam wai don may yake shiga part dina,duk ya,shigo gidan, A,daki ta,samay shi zai shiga bandakj take gaya mai wanan maganan haka, Ya,juye da sauri a,cikin daga mata hannu yake cewa Salawatu kin san dai na fada maki sharadin zaman ki a gidan nan cewa ban son fitina ko ? Na,fada,maki cewa ki zauna da kowa lafiya a,gidan nan don bazan lamunci wani tashin hankali ko rigima,ba,daga daya,daga,cikin ku, Don haka idan har ki ga kamar cewa ana tauye maki hakkin ki ne zaki iya daukan ma kanki mataki ki akai, Tunda ke duk abinda,mutum ke yi a kanki bakya gani ku.a bakya godewa Allah akai, Tajuya tana ginaguni ita,wallahi bazata tsaya ana mata bakin ciki ba irin haka tana,gani Ko don bata haihu bane yasa yake mata wanan wullakancin hakane wai ? Ya bita da kallon cikin girgiza kai da jin takaici yana cewa, wanan sai nayi maganin ta, a gidan nan, Daga haka ya shige zuwa cikin bathroom din don yin abinda zai yi a lokacin,
****** ********** ****** A haka rayuwan gidan mu ya ci gaba da gudana a kowa,yana kokarin tausasa zuciyar shi, Don dama shi kishi a zuciya yake wa mata duk, yadda mace ta, yayi dole, sai taji wanan kishi din, Amma idan kana dan bawa kanka hakkuri sai kaga abubuwa suna zuwa,su na wucewa kamar ba a yi ba, A haka yake yiwa iyayyen mu alheri irin yadda ya kamata ya taimaka masu,, Yanzun haka, shirin zuwa gida birnin kebbi mu keyi gurin buki, yan uwan da za,ayi, Bukin Anty murja da Anty Aisha duk sungirmay ni amma,saboda ni malam ya badani tun ina karama yasa na riga,su yin aure din, Yan mata hudu za,a, saka lalai a gidan namu kuma,duk kan su nabawa Yaya shawara akan yai masu duk wani kaya da uba kewa diyan shi idan zatayi aure ,, Don haka,shi ya,dauke wanan nauyin bukin yan matan gidan namu da za,a yi a karshen wata, Gashi part dina muna da yawa kuma ina,son zuwa dasu gaba,daya don su je suga gida, Amma,sai naji yadda ake shirya tafiyan tankar sune tafiyan yake a hannun su, Wanan zancen ne yadan kawo sainsa a tsakanin mutanen gidan ni jin su kawai nakeyi don tafiyana,ba,daya,ba,da tasu ma, Yanzu a tsakani su Fatima da,Salawatu an dan fara smun fahinta,don dama halin ratuwan su gudane,
Karfe tara na dare yana zaune a,falon shi hankalin shi yana akan system din shi, Wayan shi dake a gefen shi yai kara inda ya,dauka,don yaga mai kiran shi, Sunan My lovely sister ne yagani a,rubuce, wanda wanan sunan da ya,saka agurin contact dina sai da ya,sa su fada,da,Salawatu a,lokacin amma dole ta,saka mai ido ta barshi a,hakana yadda ya,rubuta Ya dauki wayan a nutse yana cewa lovely sister ya,akayine kuma, Nace Yaya zancen tafiyan mu gidane ai don ina,son na,isa don na,samu ko wani event da za,ayi, Yaso ya dan tsaurara cewa banzan tafi ba,sai an tashi a tafi gaba daya amma,sai na dan fara yi mai dan dadin baki da yan kwaskwarima Sai naji ya,sauke ajiyan zuciya yana cewa,yaushe ne kike son tafiyan, Nace saura kwana uku a soma,bukin nake son mu isa garin , Yace cikin jan aji irin tasu na maxa maza,wa yanda suka karba sunan su na maza da cewa, Kibari sai nayi shawara zan kira ki na,snar dake yadda za,ayi,,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA SEENABU
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣1⃣4⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
WALLAHU GALIBUN AL,AM,RIHI,,,,,