Tarko complete novel - Chapter 118
Tarko complete novel Chapter 118: Tarko complete novel Chapter 118. Sosai na,shirya wa wanan tafiyan da zamuyi don dai ina, iya kokari na gurin ganin cewa…
2,240 words
Sosai na,shirya wa wanan tafiyan da zamuyi don dai ina, iya kokari na gurin ganin cewa duk wani abin da zamu bukata acan gida na saya don kada bu bukata a bata, Shirin da nakeyi a boye na shirya komai yadda,abokan zamana baza su gane cewa ina wanan shirin ba don gujewa maganan anyi ance, Hatta,da ranan tafiyana,ban yarda sun sani ba,sai ana i gobe zamu wuce nake fada masu da, dare cewa gobe zan fara hanya,don na je mu samu program din da za,ayi, Fatima ce a cikin tabe baki take cewa au tafiyan ma daban daban ne za,ayi shi kuma, Na bata amsa da cewa eh don kin idan nace zan jira mu tafi tare bazan samu wasu abubuwan ba kuma a karshe mu kin san yawa gare mu, Au duk da,kowa ke nan zaki tafi nace eh don na, kaisu suma su ga yan uwan su a gida, Tace a hasale amna dai gaskiya hakan baiyi ba don dai, gaskiya ban so zuwa da harira ba cewa yar aikintw da ta dauko daga gida don ta san cewa matar da,wuya ta dawo, Dama nasan cewa tana da dalilin son rashin zuwa da yan aikin mu da basu kaunar yi, Sadiya ce naji tana cewa amma Meenatu may yasa,baki fada min cewa gobe zaki tafi ba aida sai na,shirya mu fara hanyar tare don nima kinga muna,da buki a wanan jumma,an, Salawatu wace tun shigowa falon take wani fuskewa kala bata ce min ba, Nace to ko zamu tafi tare din ne a,goben a cikin yar wasa itama dai din cewa tayi cikin dan murmusawa , A,a,a ki tafi kawai Allah ya kai lafiya mima ai zamu shigo zuwa weekend, nasani indai ba ya canza shawara bane, Nikan daga haka ban tsaya ba na sa kai zuwa part dina don mu karasa shiri, Washe gari tun safe Ramatu tai muna abincin da zamuyi tafiya dashi, tare da aminiya,ta,Fattu, da yaranta biyu, sai dan karamin cikin dake jikin ta, Mu ka kwasa sai Kebbi jahar dake da karamci da mutunci ga son baki, ga noma ga kasuwanci da kamun kifi, uwa uba kuma addini da zaman lafiya da lumana, A cikin moan Yaya Abubakar da ya sayo sabuwa, fil, daga,wani tafiyan da yayi, sau guda ya shige ta tare da Sadiya, Sai gashi yau sunga da ita zamuyi, tafiya abinda ya kara ruda,masu zukatan su ke,nan kishi ya turnuke masu zuciya, Ganin irin kayan da helux din mu ya kwasa,yasa zukatan su wani zargi can, na daban, Bayan tafiyan mune kowan su tashiga part din ta rai a bace Mace ta,farko da tafara kiran Yaya Abubakar a cikin masifa tana cewa may zai sa ya fara turani gida tare da,damka min komai a hannu na, A Cikin mamaki yake sauraren ta,don bai san kayan da take nufin cewa ya hadani da,su ba, Zata kara magana yace a cikin fada, Ke Fatima bukin gidan kune ko na,gidan mu ? Idan kin ga zaki iya zuwa kije idan bazaki ba ba matsala, ki zauna don ban son yawan tsegumi, Ke da kika tafi buki gidan ku kwanaki wayace maki wani abu, daga cikin su,, Don haka ban son abinda, zai tayar da fitina for god sake, Shiru tayi tana sauraren shi kamar wace ruwa ci har ya gama fadan shi don tasan cewa bata da gaskiya, Bayan sun gama wayan yake tunanen cewa wasu kayane Fatima ke zancen yabani in tafi dasu ne wai,, Don shi yaga cewa baiko samu sallamana ba na matsa mashi cewa zan fara hanya, Sai zuwa karfe daya ya idar da Sallah wayan Salawatu ya shigo mai sun gaisa sun dayi magana akan zancen zata fita zuwa gurin gyaran jiki sai kuma take cewa sai kuma,ga meenat ta wuce da kaya mu damay zamu tafi ke nan idan zamu shiga garin, ? Sai abin da Fatima ta fada mai ya dawo mai a rai yake tunanen wai may suke nufi ne hakan, ? Yace mata a,gadaran ce eh kin san ai bukin gidan su ne akeyi dole ta tafi da kayan ai ko? Ke ai ko ba buki ba kina loda kaya zuwa gidan ku kuma kisa na sai masu abu a aika masu dashi, Kenan mu ba,yan gida,bane da za abari mu tafi hannu empty ko ? Bai bata amsa ba,sai cewa, yayi idan kin gama zan kashe wayan, Tagane nufin shi bai son aci gaba da zancen ke nan don haka taja bakin ta tai shiru, kawai,
Sai dare mu ka isa garin saboda tsayawan da mu kayi a,Minna gidan wasu mutanen Birnin Kebbi dake zama anan don akwai abinda zan karba a,gurin matar hakan yasa muka dan dade ba mu isa ba, Kamar yadda mu kayi da Anty Safiya na agyara muna part din mu a nan zamu sauka don gudun fitina, daga gurin mama ladi, A part din namu muka sauka inda duk wasu kayan gift da sauran abubuwan da na sayo na sa a kai min su gidan, matan Yaya mustapha mu, a boye min amna,su kayan girki a part din mu na,sa a,sauke min, Murna isowar mu amare keyi don duk abinda suka sa na,sayo masu dama wanda basu ce ba amma naga dacewan a,saya din nazo dashi, Na koma kamar wata babba a gidan komai sai ace ai ina Meenatu tun ciki n daren da muka isa part din mu yake cike da yan uwana mata muna ta shirye shiryen mu don washegari ne za,ai sa lallai, Yarana suna koyon tafiya yanzu don haka banda matsala a kan su don suna gurin mamana da mama Sa,a ko Dije sai kuma,Ramatu wace idonta yana akan komai nawa, Ba laifi wanan tafiyan muna dan dasawa da Mama Ladi, don ina a,part din tare da,su Anty Samira muna harkokin mu, Nasa an gyarawa sauran abokan zamana dakunan su tsab duk da nasan cewa ba godiya amma ni don Allah nayi, Fatima wace bata da,daki tun farko sai na,bar mata,dakina ni na sauka a,falo tunda muna da yawa ,
****** ********** ****** Ankon kamu ne muka,saka a jikin mu gaba dayan mu har yaran an masu wanan anko din, da kaga zurian gidan mu a ranan zaka gane don wanan anko din na yan gida da muka saka a,yasu yasun mu, Sosai gurin ya cika daga dangin mu da kuma yan uwan iyayyen amaren mata, Yan gidan ango da abokan arziki, gidan kanin kakan mu wanda ke a Tudun Wada akai kamun, Mun raba gifts gwargwado da yan a bubuwa daga dangin tsintyan shara masu laushi, da penti, tsinken kitso, lallai, da mafaifaici masu kyau da penti, Ina tsakiyan yan uwana ina kuma bin wanda na dade bangani ba muna gaisawa, Kamar yadda ki kasan cewa zansha nunawa da kuma dawo da tarihin auren mu da Yaya Abubakar a,gurin haka ne ya ke ta faruwa ga mutane, Masu alaka da kishiyoyina kuma,sai gulmana ake kowa da abinda yake fadi, Duk da,nasan cewa idanuwana, sun dan bude yanzu, amma, hakan bai sani daukan kai, a cikin yan uwa ba kamar yadda wasu mutane keyi idan Allah, ya daukaka su a cikin mutane,, Mota guda na shiga tare da,su Anty samira da sauran yan uwa muna tafe ana hiran irin yadda bukin ya wakana, Duk da a gajiye muka dawo gida bai sa mu huta ba sai shirin yin walima mukeyi wanda za,a yi a gidan wata gwagon mu da ke Gesse,phase 1,,,, Sosai muka,shirya ma waliman inda sai dare mukai barci a lokacin gidan mu duk ya cika da,baki, Washegari tun safe bani gida mun fita ko wanka banyi mun tafi gurin masu hada muna masan walima da kayan snacks, Waya ake ta buga min cewa nazo na bawa yara nono duk inda zan tafi da Fattu muke tafiya sai idan tagaji tace zata huta, Mun dawo don shirin zuwa walima ake tamin fada cewa wai na tafi nabar yara Mama Ladi tankar zata dakeni a rana sai ranan nasan cewa tana,son jinin ta, Don ance har goya Alhassan tayi a bayanta a part dinta na zauna ina ba yaran da suka kewayeni nono, Nace Ramatu ta shigo min da abinci nan muci a part din mama, nan muke sai da na dan sullace jikina zuwa part din parents dina nai wanka a can na,shirya, Anty Rukaiyya ta shigo take cewa wai Baba MUSA yana nemana a part din shi, Da sauri na,saka hijab dina nanufi gurin da yake kiran nawa, nan na,samay shi tare da Baba Shaibu , Na rusunna a gaban su tare da cewa Baba ina wuni , Yace Meenatu am yaya gajiyan jama,a da kokari Allah yai maku albarka keji, Nace cikin dan jin kunya Ameen Baba ance kana kirana, Yace Meenatu zancen garana don sunce wai gobe da safe zasu kai kayan gashi bamu hada su ba, dukka, Nadan dago kai gurin da Yaya mustapha da Yaya Abdul suke zaune nace, a hankali Yaya baku yi zancen kayan garan dashi bane ?, don har da zancen kayan gara na lissafa mai,, Yace gaskiya bamuyi wanan zancen bs nace to barin kira shi in tuna mashi, muji, Ban bata lokaci ba nadan kauce wa idon manya na nufi dayan dakin matan Baba musa din na kira layin Yayana, Ya dauki wayan yana cewa, ai ina zaton buki bazai bari ki kirani ba yau, Nace cikin da tausa murya waneni in manta da rabin raina , Yace ina kika, shiga naji mama tana fada cewa min fita kunbar yara da yunwa wai za,a kashe su, Nai yar dariya nace ai basu damuwa tunda Anty nani tana tare dasu ai, yace nima na fada mata amma tace wai shi yasa Amira bata kiba don bata samun kulawa Murmushi nayi ina cewa kai mama ho, Nace Yaya dama zancen garane wanda za,a kaiwa Amare, Yace garan may, kuma Meenatu wai har yanzu baku fama hada kayan bane,? Nace Yaya ana aure ba garane ai dole sai dasu, shiru naji yayi nasan yana tunane ne, Nace yaya tunda gaka kuma Allah ya hore ma ni ban son ace su Baba sunyi wani wahala acikin wanan harkan nafida,son ka,samu wanan albarkan kai ma, Yaya kako ji yadda ake ta,saka ma,albarka tare da fatan gamawa lafiya, Ke ni dai fada min damay damay za,a,sayane wai kuma,nawane za,a kashe inga kozan iya, Nace barin inba Yaya mustapha don gamu tare dasu harda,baba MUSA na,fadi hakan nedon yayi masu abin kwarai, Nan suka,tattauna da Yaya mustapha da su Baba yace zai turo kudi a account din Yaya Mustapha, Ranan mun sha albarka a gurin su Baba MUSA da,sauran yan uwa ganin yadda akaita shigo da,buhuhunan abinci,
****** ********** ****** Alhamdullahi, don munyi waliman mu gwanin ban sha,awa taro ya,watse lafiya kowa ya,wadata da dan abinda muka tanada don bawa yan uwa da,abokan arziki, Mun dawo gida bamu jima ba bakin Abuja suka iso inda dama na tanadar masu abinci ko angyara masu gurin kwana shi maigidan jirgi zai biyo zuwa sokoto, Guri ya kara rudewa inda yan uwan Fatima da Anty Sadiya,suke ta shiga da fice, Sosai nake harkan bukina ban tsaya wani tsegumi ba akan su, Inda na lura da cewa tun zuwan su Fatima ke son fitina damu duk da wanan ne karon ta na farko da zata kwana a gidan mu tun auren su da Yayana, Ga yan uwanta sai yare suke tayi don gulma saboda kada muji may suke fada,, Ashe Anty Nani tana dan jin zabarmanci taji suna cewa wai don may zan sauka a falo yafi girma in bar mata dakina, Tace ita bazata yarda ba sai dai na koma dakina nabar mata falon ita da maigida, Anty Safiya tace wallahi in har wanan matar tai magana sai na,watse ta nikuwa,don bazata zo ta,dinga yiwa mutane fitina ba ko yaushe, Anty Safiya tace Meenatu bata ko son sauka nan din nice na matsa mata,cewa ita tana da mutane ta,sauka nan tabar mata,wancan dakin , Ai,kuwa, baifi minti ashirin ba,sai gata,tashigo tana,saye a,cikin wani dogon riga baki take cewa, Maman Amir yaya akayi naji ance dakin kine wancan da kika barmin ke kikadawo nan part dinaigidan, Zanyi magana naji Anty Safiya tace Saboda nan din mukaga ya dace da ita da kowa nata don mu wallah Tace don Allah Safiya,badake nake ba kada ki shiga zancen daba naki ba, Tace nice nace tabar maki can din ta,dawo nan ita da mutanen ta,don kuwa can din ba zai masu ba, Sai tace to ban yardaba a bani falon don nan dama akace ni zan sauka, ai, Nan suka fara cecekuce a tsakanin su kafin wani lokaci har an fadawa sisters din mu sai gasu buuu sun shigo, ganin yawan su yasa Fatima yin shiru ta,wuce fuuuu zuwa dakinta, Aiko sai ga Mama Ladi tashigo tana cewa ina takene dangin tsiya dangi Allah tsine, May ake da irin ki ana taron arziki ki kawo muna gaiyyan tsiya a gida saida Baba Shaibu yashigo ya tsawata sannan kowa ya,watse, Nai mamaki kwarai wai yau nice mama ladi take shigarwa Fada a gidan mu, lalai hakkuri bai bar komai ba, Sanin halin mama yasa Fatima,shigewa daki kamar bata gidan, Wayan maigidan ta kira tana kuka take cewa ita gidan su zata,koma ta,sauka,gashi daga zance daki ita da,Meenatu yan gidan su sunyi gaiyya wai zasu bata kashi, Ranshi ya baci sosai acikin fada yake cewa kada kije ko ina ki bari har na shigo gobe sai inji dalili, Sam ita ba haka taso ba taso ace tatafi gidan su ta,sauka acan don ta samu yadda take son ta,wala,