Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 119

Tarko complete novel - Chapter 119

Tarko complete novel Chapter 119: Tarko complete novel Chapter 119. ****** ********** ****** Da,safe na,shiga,gaida mahaifana,nasamu Baba yana gida bai…

3,268 words

****** ********** ****** Da,safe na,shiga,gaida mahaifana,nasamu Baba yana gida bai fita ba, Yana karya kumallo koko da kosai a,gaban shi mai zafi yana sha nashigo part din da Amir a hannu na, Mama ta fito daga daki tana,ganina take cewa shi kuma ina yan kannen shi da ya karbe masu cinyar, Nai dariya a,daidai lokacin da nake durkusawa a,gaban mahaifina ina cewa ina kwana Baba ya hade kokon da ya zuba a bakin shi yana cewa Aminatu, kun tashi lafiya, Yaya zirga zirga da dawainiyar jama,a, yana kokarin mika hannu ya jawo Amir zuwa gurin shi, Amir don yaki yana,shigewa a jikina nace bazaka je gurin Baba babana, Baba yace kin san bai san mu ba dole yace bazaizo ba ai yadauko kosai yana mika wa yaron amma,sai yaki karba, Na karbi kosan ina,mika,mai ya karba Baba yace dan nema ashe kana so,, Babana yace Uwata ina,son kiyi ta hakkuri da jama,a zomu zauna zo mu saba kuma kowa da halinsa ake zama dashi, Don haka ki kara hakkurin da kikeyi akan duk wanda kike zaune da su, don ko a tsakanin harshe da hakori ana samun matsala, A lokacin ne na kara kaiwa zaune ina sauraren Baba na, inda yake cewa yace jiya,an fada min duk irin yadda kukayi da ita,abokiyar zaman ki din Mahaifiya dake tsaye daga gefe tana kallona a cikin tausayawa irin rayuqn zama acikin wa yan nan gwabza gwabzan kiyoshin nawa, yar karama dani, Babana yace mukan gaskiya Alhamdullahi Aminatu don ko jiya Baban ki Shaibu har nan yake ya,ta sa maki albarka malam kuma yau da safe shima yana kara,sa maki albarka, Don yace duk wani alherin da mijin ku keyi kece sila don kece mai kara sakashi a hanya yayi ,, Nai murmushi tare da,dukar da kaina don jin irin yabon da mahaifina yaimin, Yace da ace baki kwantar da hankalinki ba a gidan aida duk wanan abubuwan sai dai ya kaisu a gurin iyayyen matan shi, Wanan ne hikimar malam ashe da ya,hada auren ku don yana,ce min duk fadin gidan nan kece ya,yarda da halinki na gari yasan cewa,zaki iya irin wanan halin , Yadan kora koko da sauri ya hade yace kin san may ma Aminatu nace a,a Baba na yace wanan zancen agaban duk iyayyen ki maza na gidan nan ya fade shi yau din nan, da,safe, Sosai naji dadin haka Aminatu na kuma godewa Allah da har mahaifina yai alfahari dake, Yace ina mai kara maki addua Allah ya kara,tsare muna ke Allah yasawa zurian ki albarka duniya da lahira Allah ya kara shirya munaku, Daga ni har Mamana muka karba mai adduan shi da,fadan Ameen Baba, Na juya gurin mama ina cewa mama kibani dubu hamsi a,cikin jakata, Tace har dubu hamsi yar Baba may kukeyi ne da kudi haka,wai ? Nai murmushi zanyi magana Baba na yace bata abinta wanan abin alfahari ne agaremu yar mu ta cikin mu tana yiwa zumunci hidima haka, Mama tace ai dama ba hanata zanyi ba don nima ai farin cikina ne hakan , Ta mike ta dauko min lokacin da nake karba ne nake cewa mamakin san yaune wankin Ango muna son zuwane shine zan ba yar mu hada namu gudunmawar, Gobe za,ayi wankin amare muma kinga ai ida n bamuyi masu abin kwarai ba,suma bazasuyi muna ba aiko,? Tace Allah ya tsare Allah ya bada sa,a nace Ameen mamana, tadan harare ni, Part din mama Ladi na,shiga inda na,samu su Anty Safiya suna shawaran yadda za,ayi zuwa kai kayan gara gidajen amare wai gidan angwannai basu kawo mota ba, Nace baga motoci a gida ba Anty aloda kawai akai masi kayan su musan cewa mun rabu da zancen kayan muci gaba sa sha,anin mu, Wasu suke cewa wai ai hakkin sune kawo motan kwasan kayan , Haba dai Anty Rukaiyya manene amfani samu agida tunda har Allah ya hore muna don Allah dai yanzu anzama daya tunda an hada zuria dasu, Kawai mu kwashi kayan ga motoci nan agida a kai masu nan wasu yan uwa,suka bani goyon bayan hakan, Mun kai kayan a gidajen ko wace amarya a cikin mutunci da karramawa, Mun dawo zuwa karfe hudu muka,shirya zuwa inda akafara,kwasan mutane zuwa government logged gurin wankin angwanne,, Munyi shiga ta azo a gani ranan matan Abubakar ko wace ta yi shigan fito na fito don kowa ta sa nuna halin ki, Tun daga tufafi sarka takalma jakka a,warwaro sai muka koma kamar yan zuwa gwajin gasa, Kowacen mu da nata mukarraban ta a cikin nata motan, Duk kan su suna,son ganin nawa shigan don haka ban shirya,ba,sune suka fara tafiya don mun fita zuwa sayen wasu abubuwa koda,na,dawo na,samu su Fattu suna jirana , Nan suke zaiyyana min irin shigar da,kowa wacen su tayi, Nidai bance komai ba Ramatu tace taji Salawatu tana,waya tana fadin cewa ai tasan cewa babu wace zata gwada mata wani abu tunda ba, wace ke samun abinda take samu a gurin maigidan, Sai gashi taga shigan Sadiya ma ya girgizata yau don bata zaci hakan ba , Dama ita Fatima yar gaye ce don haka ba mamaki don ita Fatima sai hura hanci takewa mutane tana basarwa Nashirya a cikin wani dogon riga da aka,dinka da,wani material din kasan Indian rigar dinki kasar Dubai ce, kalar baki da silver, sai gyale shara shara mai ruwan silver, Na sanya,white gold a wuyana gashina da tasha gyara tun Abuja yana nade a cikin dan kwalin kayan, Takalmi hill shoes silver na,saka mai kyau da,daukan ido, na shafe ko ina,da kamshi mai taushi saboda mutane zan shiga, Sosai ni kaina nasa nayi kyau da,wanan shiga wanda Anty Barister ce ta hado min shi saboda wanan bukin da ta,tagi Dubai, ita da maigidanta, Gurin ya cika ya batse da jama,a inda kishiyoyina duk suna daga gaban kujeru zazzaune suna kallon abubuwan da akeyi a gurin, Ina a tsakiyan ayarinda muka,shigo inda na haska gurin kamar nice amaryan, Muna tako daya daya ga,yan uku na da Amir dauke a hannun mutane na, muka keto taro aisai kallo yadawo gare mu, Har na iso gurin kujerun da aka,ware muna mu da su Anty ,, Habba kallo ya dawo gare mu idanuwan kishiyoyina sai satan kallo na,sukeyi, Duk da,su ma,shigar su ba laifi su yi fitan yan birni matan manya, Wani irin sauke ajitan zuciya Fatima tayi inda a,daidai lokacin Salawatu ma take cewa cikin tsaki sallon banza kawai, Anfito da angwanne mukafito mukashiga watsa naira guri duk ya,rude, nan aka,shiga zancen cewa, Aikin may mijin su keyine haka masu fadan gaskiya,suna fadi masu karya na karawa, nsn naga wasu class mate dina nice da kaina na nufi gurin su na,rungumo su, Sai cewa,sukayi wallahi basuyi zaton zan zo mu gaisaba nace saboda may wai don yanzu nafi karfin su, Munyi hotuna,dasu nace don Allah mu hadu kafin na,wuce dasu, munyi photuna da mutane da,dama a gurin gwanin bansha,awa, Sai gab da kiran sallah magariba,aka,dakatar da kidan dake tashi ana ta kwasan rawa, Mun dawo gida,agajiye mun samu maigidan ya iso yana,dakin mahaifiyar shi, Nasamu su Salawatu da Anty Sadiya a dakin gaba dayan mu muka shiga tare da yan uwan shi, , Duk taron jamaan dake dakin idon Yayana kyam a kaina don ya kasa boye feeling din shi gareni, Cikin murmushi nake cewa,sannu da zuwa Yayana yaya hanya da jama,a, Yace cikin dan lumshe idanuwan shi see you ina kika shige ne wai tundazun, Nace muna can muna sallaman mutanen da,sukazo ne yace anji dadin gida ke nan ko,? Nai murmushi ina cewa yaya gida,dadi gare shi fa yace zonan naga,wanan adon da kyau don naga na kowa, Inaga ya manta da cewa mama tana dakin ne ko yayane wani irin kunyane ya,rufeni nake cewa cikin make kafada later on yayana, Fam su Salawatu akacika take cewa cikin rashin kannewa tace ai zaka bari ku fita dakin mamadai ko ? Kedai yar sa ido ne Anty Safiya ke cewa Salawatu din keda,aka ga naki fa, Tace a,cikin tabe baki ni awa za,a kalli nawa gadai amarenan su za,a kallah ai, Dariya kowa,yasa Anty Samira tace ke tashi kije don Allah ya,shaki wanan kamshi kada yabi iska a banza, Dariya aka kara,sawa gurin ana ta barkwanci da raha gwanin ban sha,awa kowa yana zolaya yan uwa, har Salawatu din da,Sadiya, Mama ladi tana,daga gefe a cikin jin dadin ganin mu gaba daya a gaban ta, Ya mike yana,dauke da dan lelenshi Amir a kafada yake cewa bari naje na,samu ruwa na watsa hakana, sai naci abinci, Mamatace kutashi ku bashi abinci mana ya,samu ya huta hakana don Allah kun cika,shi da,surutu, Yace cikin dan rausaya kai kyalesu dai mama ai zan rama nima idan sunzo min bakunta, Ya fita,dauke da,yaton ajikin shi yanacewa inda yake fiskanta na hada min ruwa zan tafi gurin malam na dawo, Bayan ya,fita daga dakin kunya ya hanani motsawa daga inda nake saida Anty Sadiya tace Meenatu je mana ki hada mai ruwan kinsan halin shi kada yadawo ya,samu baki hadaba naki ya samay ki, Wani kunya naji yadan kara lulubeni inda nadan mike a,sanyaye zuwa part din mu, Salawtu tabini da hara a witsiyar ido tare da,surfamin zagi a zuciyar ta, A part din mu na samu su Fatima,da yan uwanta anata zuba yare a cikin daga muryq wai suna hira a tsakanin su ,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA SEENABU

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣1⃣5⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

HASBUNALLAHU WA,NI,IMAL WAKEEL,,,,,,

Tsab na,gyara,mai ko ina mun shirya,mai abincin shi wanda nabawa maman tai min aikin shi a,tsanake, na gyara dakin guda,daga,cikin bedroom din falon, A lokacin yana,gurin malam tsoho babu abin da ake tayi mai sai adduoi da,fatan samun gamawa,da,duniya lafiya, Duk iyayyen mu maza wanda duk yazo sai godiya zai mai tare da kara yaba irin yadda yake masu kokari, Sosai yaji dadin wanan abin a,rashin don yasan ko ba,komai yafita bakin yan uwa masu cewa can baya baida tai makon yan uwa, Ya ji dadi har ga,Allah don yasan cewa Meenatu ce silar wanan godiyan da ake mai yau haka,a gurin mahaifan shi, A,gajiye ya dawo part din mu yana dauke da yaro kafadannun shi, tsayawa yayi a tsakar part din yana tambayan inda nake na karbi Amir, daga hannun shi, Uwar iyayi salawatu har ta fito tana cewa kawo shi na mika mata,shi yace mata No ki bar shi don kada ya,tashi , Itace taje fada mai ina a cikin room din falo nan ya nufa bakin shi dauke da sallama , A lokacin na,sa wata yar bakar rigar barci don zafi ake sosai a garin don muna da zafi idan lokacin shine idan kuma sanyi ne sai ince munfi kowa sanyi muda sokoto da zamfara har ma da katsina, A gurin karban yaron hannuwan mu suka hade guri guda inda kowan mu ya,saukewa dan uwa kasala, Wani irin sanyi Yaya Abubakar yaji a zuciyan shi har sai da fuskan shi ya baiyyanar da farin cikin shi afili, Gurin dana tanadar wa yaran na kwanciyar sune na kai yaron, Ban san cewa yana bayana ba sai muryan shi naji yana cewa ina su Ramatu suke nake ce mai sun shiga cikin gida gurin da ake aikin abinci amma zasu shigo, Ya sake murmushi yana cewa wanan gidan yai muna karami da sauka ina son na samu fili ai muna wadatacen gina yadda kowa zai wallah a cikin sa, Naji dadin wanan maganan nima,cikin farin ciki nake cewa, gaskiya aiko da mun gode yaya, Nagabatar mai da,abincin shi inda yake cewa ruwan wanka zan fara bashi ya,watsa, Bayan ya fito wanka,sai kuma ga,wayan Aliyu yana son yafito suga juna amma sai naji yana ce mai yanzu zai ci abinci idan ya gama kuma yana bukatar hutawa yabari idan Allah ya kaimu gobe, Daga inda muke muna jin hayaniyan mutane a,sauran dakunan alaman cewa basu yi barci ba ke nan,musan man a,dakin Fatima, Sai naji yace min shin wasu irin abubuwane kikazo dasu daga Abuja wanda baki fada,min ba, Don ana ta bugamin waya cewa nabaki kaya ki shigo dasu BK bada sanin kowa ba, Ban boye mai ba nafada,mai gaskiyan zancen irin abinda na kashe, kafin nazo, Shiru naji yayi sai yake tambayana a ina kika,samu kudin yin wanan abubuwan haka,? A cikin sanyin murya na dan langabe kaina, nace mai, sarkan da ka sa min na haihuwan Amir na sayar, A take naga ranshi ya baci a hasale yana cewa, waya baki wanan mugun hawaran kuma, Nace ba wanda ya bani nice dai naga ya kamata ace nayi wani abin shine nai wanan shawaran don dai kada nazo naji kunya , Inda yake shiga,banan yake fita,ba yana ta,min masifa akai shiru nayi don nasan cewa idn yzna fada kana bashi hakkuri zancen bai karewa, A,dakina ya kwana don dama,koda yazo nice mai girki a lokacin sai washe gari yasamu ganawa da,sauran matan shi, Sai da safe ne ya kiramu gaba,dayan mu kafin jama,a su taru, mai a gida, Dubu dari, dari yabawa kowan mu yace na,sha,anin buki, Anty sadiya ce tafara,dauka,sai ni sai salawa fatima ce ta,dauka a karshe, Yace bai son yaji wani fitina yafito daga kowacen mu kuma,yazo damu gidane don akara fahintar juna a,tsakanin mu da yan uwanshi don wanan ne kawai opportunity din da,yaje dashi wanda zai kawo iyalin shi a mahaifan shi a,cakudu tare da,kowa don kowa yasan kowa, Don haka baya son jin wani rigima,daga kowacen mu har a watse daga wanan taron kowacen ta karba da,fadin insha Allah, Can kuma yace ke Fatima da,salawatu zancen kayan da kukace nabawa Meenatu shin wasu kayane wai na bata gata zaune, Gaba,dayan su basu so ya,fadi hakan ba,don wani sirine nasu ai wanan magana Shiko hikimar yin haka gareshi shine don ya,wanke kanshi daga zargin da sukeyi mai dakuma nuna masu cewa nayi abubuwanane don fita kunyana, Shiru gurin yayi ya kalli waccan ya dubi wancan can dai yanisa yana cewa ban san damay tazo garin nan ba, Kada kuma ku manta da cewa itama agidan su ne ake wanan bukin dole tayi nata lakuran wanda ba,sai na,sani ba Ga sadiya,nan ku tambaye ta da muke zuwa buki a,baya nakan zo da wani abune kawai ni nasan matsalata ne da iyayyena maza na taimaka masu da abinda nafi karfi, Kowan ku ai tana zuwa buki kuma nakan bata abinda zata tafi dashi amma ke na baki wani abu tsakani da Allah, Kafin in ce wani abu sadiya tace wanan ai sai dai indan mutum yaso fada amma ai kowa yasan halaiyar ka, ta fadi hakan a cikin yanayin zolaya, Nan dai ya kara jawakowa kunne cewa bai bukatan yaji wani baraka a tsakanin mu don shi wallahi zai dauki mataki akan duk wace taso ta tozartashi a gidan su, Fatima taji haushin wanan abinda ya fadi don haka anan yabar mu zaune yafita zuwa gurin bakin shi a waje, Sadiya tace a cikin nisawa bari na tafi nadan shiga gidan yayana kafin a fara zancen wankin Amare, Salawatu tace cikin tsuki ni shiyasa ma ban so na,zo ba amma Ogana ya matsa cewa dole sai nazo din, A cikin yatsine fatima tace dama ai mutum bazai taba gane gaskiya ba kawai dai ayi sha,ani ankawo mutum guri anata mashi wulakanci, kawai, Da hanzari na juyo don jin may ta fada ina cewa wanan kuma dai fada ne kawai amma ai mutum bazaice ga abinda akai mai ba, Murmushi nayi tare da cewa to ai dai mutum yazo kwata idan da hakkin shi a,ciki,, Duk wani harkan da zanyi na sha,anin buki sai na fadawa wakowan su cewa zamu tafi guri kaza yin abu kaza, Abincin da za,ayi wa bakin Yaya Abubakar don ashe akwai maza da,zasu biyo shi daga Abuja, daurin aure, Fatimace na mikawa wanan harkan zancen abincin ita da yan uwanta suke ta iyayin su, Ita kuma Salawatu tare suka tafi gidajen amare ita da sauran sisters din mu, ****** ********* ****** A gajiye nadawo inda na,wuce gurin malam tsoho don tunda na,fita ban samu ganin shi ba, Har gaban shi gab dashi na isa na durkusa gwiwa biyu nace dan tsoho mai ran karfe, Yana,daga kishingide yana jijiga kai yace matan takwara tunda kikazo an hana mu zauna dake ko , Nace wallahi malam amma insha Allahu yau idan mun dawo wankin Amare zan zo mu zauna, Yace kin dawo a gajiye ina zaki samu gani na ku dai Allah ya bada sa,a Allah ubangiji yasa kufinan Meenatu ko bayan raina kici gaba da irin wanan halin naki na alheri, Badon komai dama na dana wanan Tarkon a kan kiba Meenatu don sanin cewa irin tarbiyan da Uwar ku tai maku a gidan nan, daban yake da sauran diyan wani shiyan, Yanzun ba gashi ba yau kowa yana alfahari da,wanan hadin nawa don ko ba komai Meenatu kin dawo mu a da,dan uwanki a cikin zurian mu Wanda tashin farko so ma akayi a rabashi da kowa nashi gabadaya yabar mu, Ita kuma mahaukaciyar uwar shi bata,da,tunanen abinda,ya,kamata tayi a kan shi sai haukan da,takewa mutane ita,a dole danta mai haline, Wanan ne yasani hango cewa ya kamata nayi wani abu tun ina a raye don gudun barin baya da kura, Su iyayyen ku nasan cewa iyayyen zamani ne bazasu damu da cewa su kafa shi acikin yan uwa da abokzn arziki ba, Sai dai yatafi can a haifawa 'ya'yan duniya suyi tamore mai mu muna nan a cikin wahala, Yace amma yanzu ga,abin yaiwa kowa dadi lokacin da yake wa,sauran matan shi dawainiya dolene kema ya tuna damu nan uai muna, Haka kuma kema zakiga wani daga cikin mu yana da bukata kiyi masa hanya a,gurin shi ya,samu, Sabanin ace watace can daban a gidan wace bazamu iya zuwa gurinta,ba kai tsaye ta taimaka muna, Amma kin ga yanzu Alhamdullahi don na tabbatar kowa ma yai farin ciki da,wanan hadin nawa, Gashi har tufafin da kika dinkowa ladi ance shine ta,saka a jikin ta,, Murmushinayi nace hmmmm malam ho, hikimar ku ta mutanen dauri ka,sauke a kaina ke nan, ko? Yace to aikoke Aminatu yanzu abin yai maki dadi har iyayyen ki da yan uwa don yanzu kinga komai a gida yake, Mazan yanzu fa,inwan giginyane su na nesa ka,rabe su, Wa yan yaran da,Allah ya,baku wallahi ko su kawai sun ishemu alfahari, Yace ai shi mijin naki na fada mashi dazun da,safe da yake fada min itin kokarin da kikayi ke da kanki, Nakuma kara bashi shawara da ya yi ta hakkuri don shi dama can mutum ne mai sa,a a rayuwan shi, Mundauki lokaci malam na min nasiha mai kama da,bankwana amma,sai na ke ganin ai girmane kawai kuma ai hakan halinshi ne sai dai idan baka zauna dashi ba, Anty Rukaiyyace tazo kirana nazo mu shirya lokaci yana kurewa, inda naimai sallama yana cewa tafi gurin yan uwanki kada,suce na tsare ki, Nasihan da maigidan yai muna yasa yau a tare muke komai namu, bamu ware kawunan mu ba, Sai dai a gurin kwalliyan dai still akwai, banbanci sosai, don kowa da irin nata kalar wankan, Anko mukayi yan gidan mu nawani swiss lace cotton mai kyau, shi na,saka sai dai a,gurin dinki zaka gane cewa daban nake da,kuma irin sarka da takalmi da gyaken da na,yafawa kayan , Anyi duk wani didima buki irin na mutanen kasar Kebbi da aka saba yi idan ansaka buduruwa ko yanmata a lalle, Washe gari aka,daura aure da yamma akakai amare dakunan su lafiyq sai dai muyi fatan Allah uban gi ya hada kowacen su da,alherin ta a dakin ta, Buki yai kyau kuma yai suna a cikin gari don dan uwan su yafitar dasu duk wani kunyan buki na,al,ada,dakeyi, Sai godiya da nuna,farin cikin su suna kara,sona,da kaunar mijina a,cikin ran su inda har iyayyen su mata,suma godiya,suke ta famayi,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull