Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 120

Tarko complete novel - Chapter 120

Tarko complete novel Chapter 120: Tarko complete novel Chapter 120. ****** ********* ******* Dakin Fatima yaya Abubakar yake don haka munkai wani lokaci…

2,792 words

****** ********* ******* Dakin Fatima yaya Abubakar yake don haka munkai wani lokaci tab a,dakina muna hiran irin abubuwan da akayi agurin bukin a cikin raha tare da yan uwana da buki yasa yau zasu kwana a gida, Muryan Dije ne acikin tashin hankali yasamu yin shiru, can mukaji muryqn Baba hamza a rikice yana cewa ina mai sunan malam din yakene yafito mana , Gaba dayan mu muka fito zuwa waje don ganin may ke faruwa ne wai,? Ina fitowa acikin tashin hankali Baba ke cewa ina mijin ki ne,kirashi da,sauri malam ba lafiya, Tako biyu zuwa uku nayi sai gani a kofan Fatima nafara bugawa da karfi muryan shi a cikin yanayi yake cewa wai waye nace Yaya fito malam ba lafiya ga Baba a,waje yana jiran ka, Yana,saye da jallabiyar shi fara yafito yana cewa may yasamu malam din cikin son jin amsa, Bayan,shi nabi muka nufi part din tsohon dake can ta dan kofan shigowa daga gidan, Gaba daya yaran malam suna a kanshi cikin tashin hankali, wasu har kuka,suke daga cikin su, Kutsawa Yaya yayi yana fadin may ya,samay shi ne wai, ? Ganin irin yanayin da tsohon yake ciki yasa shicewa Mustapha kamamin shi mukaishi a mota, Ke dauko min keys din mota da,sauri acikin sauri nakoma nace wa Fatima tabani keys din shi tana wani jan aji ita a dole an katse mata barci da miji, na karba na juya a,guje nakai masu, Alokacin na,samu malam ya,shiga cikin wani hali, sosai Sun tafi su dasu baba ga sauran mutane nason zuwa don haka na ce a kira min layin Baba Wadda suzo da mota na dake gurin su, Bamu samu motan gida ba nakoma tare da su anty muka,shiga yar vespe zuwa F M C a cikin daren nan, Muna isa su baba suka haumu da,fada cewa mu koma,gida ana ciki dashi likita yana,dubashi, Amma dole suka,bar mu harzuwa lokacin da aka fito dashi zuwa male ward aka kwantar dashi ma,ana anbashi gado ke nan,, Sai a,lokacin na tuna cewa nabar yara a,gida ashe ita Ramatu tun fitowar mu takoma ta zauna da yaran , Sauda muka,dawo na,samu ta,rufe kofan dakin nabuga tabude acikin dan damuwa take cewa uwar dakina ya maijikin dai ? Nace a cikin fuska mai nuna yanayin damuwa Ramatu Allah dai yaba malam.lafiya, Saida muka,zauna nake dan labarta mata yadda abin yake ita da,Fattu , Nan Fattu ke ce min ashe bayan mun kwasa mun fita ita Ramatu dawowa tayi don duba yaran anan na,samay su da wanan sarkin tsegun din da cewa danta ya tashi yana son shan tea wai, Naji tausayin Ramatu tare da kara,son matar a,raina don tasan yakamata sosai wallahi, Hakana,muka yi barcin fargaba duk ka,gidan kowa hankalin shi a,tashe jigon gida ba lafiya, Washe gari tun safe aka kwasa zuwa duba jikin nashi ba laifi yadan samu sauki don sai barci yake a lokacin, Amma kana kallon shi zaka fahinci yana jin jiki sosai a gaskiya ba karamin jin jiki yake ba, Shigowan Yaya Abubakar da likitane yasa mutanen dakin watsewa zuwa waje, har zan fita sai naji Yaya Abubakar yana cewa motan da kukazo da ita tana da lafiya,dai ko, Tsayawa nayi ina,fada mashi cewa lafiya take don sai da,akai mata service kafin muzo da ita, Naji yace ku shirya ina ga zamu tafi yau din nan, da sauri na dube shi na kuma,juya inda malam yake kwance sheme saman gado nace a,sanyaye da malam din zamu tafi ke nan yace eh a takaice, Hakan dai ake ta shige da fice a asibitin har zuwa lokacin da aka gama shirya komai akan zancen tafiyan nashi, Bashiri muka kama hanya a,rana ga dumbin gajiya ga kuma,fargaba a tare da mu, Dole saida aka hada da motar haya,muka kwasa kuma,sai Abuja, Mun iso a,cikin dare gashi gabadayan mu ne tafiyan don haka mun samu yar tsohuwar kirki Maman Biu tai muna girki shi muka,samu muka ba,wasu Baba da mukazo dasu, daga gida, Asibiti akawuce dashi direct don a motar F M C akazo dashi nan a cikin daren akaba,su gado, Ban samu zama,ba,saboda duk wani shige da fice nice ke ta faman kokarin yin shi don ganin komai ya tafi daidai, Yarana basu da time dina tun zuwan mu sai dai nadan zauna na basu nono sama sama na tashi, Kwana biyu da zuwan mu malam yadan fara,samun sauki abinda yasa hankakin mu fara kwantawa ke nan ganin yafara,magana,yanzu, Ko da yaushe ina asibiti ga kuma aikin abincin baki da yai muna yawa , Abincin da ake masu bai min ba,don haka ni da kaina nake ma iyyyena girki, Babana,Baba musa da Baba shaibu akazo dasu Abujan sai uwargidan malam din Na lura,dacewa duk matan yaya sun sa min ido suga yadda zanyi da bakina, Acikin ikon Allah haka nake ta gudanar da,al,amarina batare da nadamu da rashin sa hannun su ba, Sai al,amarina nake hankali na,akwance nidai bukatana naga malam ya samu sauki, Likita yafitar da,sakamakon ciwon malam da irin abincin da,za,a dinga,bashi yaci, tare da,maganunuwan shi, Tun da,safe nashirya bayan na,dafa mai faten wake da Alaiho, nai mashi jeloup dashi, Amma malam din baya,son cin abinci don haka yau da kaina na zauna a,bakin gado gab dashi nace ya,tashi nabashi yaci, Yaso yaci da kan shi amma nace ya,bari na,bashi, A hankali nake dan diban faten wanda yai ruwa ruwa,da,spoon da kyat na samu yadan ci spoon uku na bashi maganin shi ya,sha, na mayar dashi saman gadon a hankali ya kwanta tare da cewa nagode Aminatu kinji, Nace haba,malam ai yiwa kainane hakan yanzu dai kadan samu kayi barci kaji, A hankali naga yadan runtse idanuwan shi tare da,dan kara lumshe su yadan hade miyau a hankali, Idanuwa na kyam a kan shi ina mai dan kura mai ido naga yadda duk ya,ramay a,cikin dan lokaci guda, Sai naji yace a hankali Aminatu Allah yai maku albarka kin ji yafada,yana mai dan lumshe idanuwan shi, Ba bata lokaci barci ya,dauke shi, shigowan su Yaya Abubakar a dakin yasa shi dan bude lumsasarsun idanuwan shi, ya,sauke a,gare su, Gaba,daya hankalin su yana,a kaina suna kallon irin yanayin damuwar da,na shiga, Yaya Abubakar yana tambayan ko yaci abincin da likita yace abashi yau da safe, Su baba sukace yanzu mutumiyar shi ta,dan bashi yaci kadan yace ya koshi, Yaya Abubakar yace tunda Meena ce ta bashi ai zai ci ko bai so yadan bude ido a hankali yace haka zakace ko ,? Yace bagashi ka,kawoni gurin likita yana ta,sokamin allura ba, yace ko yanzu ma gasu nan zuwa su kara maka wani alluran , Hakan yai daidai dashigowan likita da nurse a bayan shi dauke da,dan farantin maganin allura aciki Malam ya bude idanuwan shi ya,sauke su a gaban litan da ke kokatin nufo gurin da yake, kwance, An mai aluran inda ya koma ya kwanta ya fara barci, mai nauyi yaya yace a fita abarshi dakin ya huta,,, Hakan yasani komawa gida don nima nadan samu hutuwa, a gida kafin zuwa yamma na dawo, Na,samu barcin zuwa la,asar na fara nai wanka tare da dauro alwala , Alkurani mai girma nake karantawa murya kasa kasa,a cikin sauti mai dadi , Kaina a,duke don haka ban san shigowan shi ba adakin nawa, Na,dago kai a hankali ina,duban gurin da yake tsaye, yana mai kallona acikin burgewa da,sha,awata, irin yadda nake karatu a cikin natsuwa da dadin murya, Muna hado ido ya,aiko min da,sakon murmushi dake dauke a fuskan shi, Ina kai ayya na, dakatar da karatun ina cewa sannu da,shigowa yaya, Ya zauna a kasalance a bakin gado yana,cewa na shigo dazun ake cewa wai kina barci dama nazo ne nace may malam zaici ne idan ya farka, Nace ai matsalar malam baya cin abinci shi wanan abin yana daure mun kai, nadan karashe a cikin sake hawaye, May ye na kuka kuma bayan yana,samun sauki sannu a hankali, shiru nayi yayin da hawaye ke ci gaba da silalomin daga idanuwana, Naji yasa hannun shi a cikin nawa yadan murza a hankali yana cewa wanan abin addua ne kawai zamu tayi wa malam din don Allah ya,bashi lafiya, Don haka kada ki daga hankalin ki don ko ni daurewa nakeyi amma nasan cewa malam,yana jin jiki, Amma idan yana ganin mu a sake hakan zai kara mai karfi gwiwa ya,samu yadinga dan sake jiki, Magan ganun da yake fadi yasani dan dakatar da hawayena ina,sauraren zancen shi,

ZEEE MAKAWA YELWA SAEENABU

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣1⃣6⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

WAL,SAU,FA YUTTIKA RABBUKA FATTAR,DE,,,,,,

Fatima ta tashi bata,da lafiya, saboda gajiyan dake tare da ita ya,sakar mata da zazzabi wanda hakan yasa ake, zaton ko shigan ciki ne hakan,, Dalilin da,ya saka Salawatu shiga wata sabuwar tashin hankali ke nan, Ni kan ina,asibiti a koda yaushe gurin jinyar kakana wanda zuwa yanzu Alhamdullahi yasamu sauki sosai, Acikin wanan yanayin dole Yaya Abubakar ya dan koma,bakin aikin shi don tsaro, Saidai hankalin shi yana,gurin mara lafiyan akoda yaushe yana,waya da likita ko wani daga cikin mú, Ya gama,waya,da likita yana,mashi bayani akan cewa ciwon ya,dan dade yana cin tsohon a,jiki kuma ba,a kawo shi asibiti, ba , Inda likita ke cewa abin ya,riga yai mai illi yanzu sai a,hankali sauki zai ta,shigan shi, A,daidai lokacin da yake kokarin aje wayan ne kiran Fatima yashigo a,wayan shi, din, Yana,dubuwa,yaga itace mamaki yake a zuciyar shi yace may kuma wanan take bukatane wai da,safe nan, Ya,dauki kmwayan yana,cewa fatima yaya jikin naki ne kuma ? Ajiyan ziciya yaji ta sauke tana cewa ai babu wani sauki don har yanzu jikin yaki ya,warware mata, Ya ce Ya Allah, Fatima kina ko shan maganin ki kuwa, ? Ta amsa a wani irin murya tana cewa magani kawai zan ta,sha batare da na tafi an min gwaji ba, asan may ke damuwana, Kawai kafita zance na,sai zancen kakan ka kawai ke gaban ka,baka damu da irin halin da nake ciki ba Ya ce cikin sauke numfashi ikon Allah, Fatima may kike son nayi maki nace ki tafi kiga likita,ai maki duk abinda ya,dace, For god sake wai yaya kike son nayi ne damay zan ji a rai nane wai dan Allah, Tace ai dole acd haka,da,watace da yanzu kana nan kana rawan kafa akai ai, Yayi saurin katse ta,da cewa kke yanzu dai ki tafi gurin doctor mansur yai maki duk irin abindaya dace, kafin nazo, Bai karasa zancen shi ba yaji ta kashe wayan nata abinda yasa shi sakin dan guntun murmushi ke nan yana cewa Fatima,badai son fitina,ba, Doctor Mansur din ya kira yana,fada,mashi cewa Fatima zata shigo ai mata duk abinda yadace kafin ya shigo weekend,

****** ********* ****** Karfe tara na safe ina,asibiti gurin malam tsoho Alhamdullahi don ya ci abincin shi, sosai nan na zauna ina wade mai lemo don ya sha , Bayan na gamane nafito don na,dauraye plate din da na zuba mai abincin a cikin sa, Fatima din na hango tana shiga gurin da zai sadaka da likita, kamar na kyale ta amma,sai na,karasa dauraye plate din na,bi bayan ta, Tana zaune tana hangoni caraf idanuwan mu suka hadu amma,sai naga ta kawar da kanta a gefe, Kamar na koma amma,sai na daure na karasa acikin sakin fuska nake cewa maman Aina jikin ne kuma,? Kallo mai kama,da harara ta,sake min ranta a bace take cewa, wanan kuma,ai matsalata ce aiko, Cak naja na tsaya guri guda,ina kallon ta acikin mamaki, itin yadda ta,wani daure fuska tamau, Idanuwana ya gaza gaskanta min cewa wai Fatima ce ta murde fuska take min wanan cin fuskan a,gaban jama,a, Likitane zai shiga office din shi ya,riskemu a hakan ya,dubi inda nake tsaye yakai kuma,duban shi a gurin da take zaune,yace ya dai madam ko jikin ne yai tsanani da yawa haka, Tace cikin daga hannuwa No bari dai mu shiga daga,ciki kawai, kara kallon mamaki nake mata, don idanuwana still sun kasa gaskanta ta, Yace cikin dan son ba,a kodai ta rakokine don a duba lafiyan ku tare, Ranta a bace tace don Allah likita bari hadani da wanan kada, ace na kuma taba yar dangi a ja min magana, Likita yadan sake kallon sai naga yadan sake guntun murmushi ya shige office din shi ya kada kan shi a hankali, Batare da nace mata uffan ba na,juya zuwa inda nafito rai na cike da takaicin wanan tozarcin na Fatima a,gare ni, Baba Wadda na samu na fada mai yadda muka kwasa da Fatima din shine ma har yake zancen a gaban su Inna Asibi matar Baba tsoho da sauran yan uwa, Malam wanda yake a,kwance saman gado yana,sauraren hiran da,Baba Wadda,keyi,, Har sai da kowa ya,gama fadar albarkacin bakin shi sanan malam din yace Aminatu ho yaki nan zauna yana min nuni da gefen bakin gadon da yake gurin da na,saba zama idan zan bashi abinci ko nazo gaishe shi, A cikin natsuwa bayan na zauna yake cewa ki kwantar da hankalinki kamar kullun kiyi nazari da abinda nake fada maki, Yace kinga matan nan da Allah ya hada,zaman ko dasu, na amsa mai da cewa a hankali eh malam, Yace a koda yaushe kiyi kokarin sauke hakkin makwabtakan su dake kan kanki, don ba mijin kine kawai keda hakki a,kansu ba harda ke ma da Allah ya hadaki zama dasu, Dakin yai tsit muna sauranshi, yace, yace kamar yadda suke mata haka kema,mace ce yar uwar su, don haka kada ki bari shedan ya,dinga samun galaba akan ki yana tuzuraki wajen aikata mugun abu akan yar uwar zaman ki, Shi wanan rayuwan duniyar dakike gani dole ne watarana ko su barki ko ki barsu walau mutuwa ko rabuwa acikin daya sai hakan ya faru daku, Malam yace Allah yai maki albarka,da har kika ganta kika tafi gurin ta da zuciya guda, Ko ma may take nufi a kanki a kanta zai koma don ke baki kulafuce taba a ranki,, Shi mijin ku kan shi da nake mashi nasiha akan zama da iyalin shi, ai ya,fada min cewa yanzu gaba,dayan ku ya,fahinci halin rayuwan ko wacen ku, Kinga ke nan kowace mace da irin halin ta ake zama da ita ashe, don ya san halin kowace dafa cikin ku kuma a hakan yake zama da ku, Shi aure da kike gani rayuwa gare shi duk lokacin da ya kare tau babu makawa ranan nan ana,rabuwa walau da rai ko a mace, Yace don haka ba,agajiya da hakkuri jeki ki zauna da kowan su lafiya kuma kiyi wa kowa adalci, Nace malam dukkan su ina zaman amana,dasu amma,su basu kauna na malam, dama ma Sadiya don gaskiya bazance ga abinda tai min ba don koda sun zuga ta daga baya takan gane ta dawo hanya, Malam yace cikin murmushito kinga ai gashi da bakin ki kin fadi su ma din idan har kina kyautata masu suna zaluntar ki watara sai kin nemay su kin rasa a gidan don halin su ne zai koresu, Don haka kiyi alhreri ga kowa don kema ki girbi alheri a rayuwan ki san nan shi mai hakkuri da juriya bazai taba tabewa ba a rayuwan shi don zakiga komai nashi sai gaba gaba zai tayi, Don haka kiyi hankali dasu ita da har kika taka zuwa inda take tai maki wullakanci dake da ita ai alkalin ku Allah, Don haka kiyi hankali da su saboda a kwai hakin su kusan uku a kanki kamar yadda kema naki uku yake akan su, Na farko hakkin musulunci nabiyu hakkin kishi sai na uku hakkin makwabtaka, wanda yanzu, shine kika sauke mata amma,rashin sani da,rudin shedan ya hanata ganewa, Kada ki fasa,ko kice kin daina kula,su Allah ya sauwaka makuzafin kishin dake cin ku gaba dayan ku, Muka amsa da,cewa Amin malam nakara da cewa nagode malam, Bai amsa min ba,sai lumshe idanuwan shi dayayi tare da dan kada kan shi alaman amsawa, Dan shiru ya biyu baya can nace malam to ka kara min addu,a mana Ya,bude idanuwan shi yana dan kallona,yake cewa,su wadancan dana baki da farko fa ,? Nace mai ina yin su yace to ki matsa dayin su don sune ginshikin adduoi, Salati, Hailala Istigifari da hamdala, zaki iya karawa idan da hali lahaula da,kulhuwallahu kafa dari, dari, Don kinga lahaula kawai da,zaki rike da kin sha mamaki a,rayuwanki don rigakafin dari ba daya takewa duk mai yawan karantata,, Dakin yadauka da cewa ai malam muma,sai mi lazamci yinsa ke nan, Yace ai ba ita kadai nakewa nasiha ba,a,gurin nan gaba,daya duk wanda ke gurin nakewa wanan nasihan, Mun dauki lokaci a dakin muna hira don ni azatona idan ta gama abinda takeyi zata shigo ta gaida malam har nabar asibitin banga tashigo ba Ina,isa gida naga motar ta,agurin da take parking hakan yasani gane cewa ta dawo gida ke nan, Nima na,samu gurin parking dina ina cewa acikin raina,wanan irin soyayyan na matan yayana mijin kawai suke so bada yan uwan shi ba,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull