Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 121

Tarko complete novel - Chapter 121

Tarko complete novel Chapter 121: Tarko complete novel Chapter 121. ****** ********* ****** Malam ya,samu sauki yanzu sosai zuwan Yaya Abubakar ya kara,…

2,967 words

****** ********* ****** Malam ya,samu sauki yanzu sosai zuwan Yaya Abubakar ya kara, sashi sake jiki don yanzu har likita yana zancen sallaman shi amma,sai yaya yaroka da cewa abarshi har yakara,dan murmurewa,sosai, Anty Sadiyace ta karbi girki a zuwan shi don haka yau nice zanyi girki a gidan, Bayan na idar da komai da nasabayi idan nice da,duty ko ina,sai kamshi ke tashi duk da,dai suma,suna nasu kokarin idan zasu karbi girki, amma dai dole ne akwai banbanci a cikin sa, Rana sau daya na,samu shiga asibiti gurin malam aiki ya, tareni ban samu komawa ba, Don har malam saida ya bugo min waya yana min sherin cewa saboda mijina yazo yau shine na yardashi a gefe, Cikin dan tausa murya nace malam.yi hakkuri wallahi hankalina yana gurinka nima nasan yau ban ma,adalciba, Cikin dariya yake cewa, ai nagane ku kedashi yau dai kin gwada min cewa shine na karfe ke nan duk mukasa dariya , Na tabbatar da,cewa, yanzu ya idar da komai don banganshi a falo zaune ba, Ina,saye da wani dogon riga baki na daura dan kwalin shi na rufe kaina dashi, Hannu na yana dauke da,fruit wanda na yanka mai a plate, baisha ba yace sai zai kwanta, zai sha, Yana saye da jallabiya fara kal ajikin shi, yana zaune a gurin da yake zama idan zaiyi karatun Alkur,ani, maigirma, Haske lamp din daya haska mai ne yadan haska idanuwan shi, ida hankalin shi gaba,daya yanaga abinda yakeyi, A hankali na aje plate din na,samu guri can dan nesa kadan dashi na zauna tare da dan jingina kaina saman pillow , A hankali na fara,shiga a vikin tunanen rayuwan duniya tun ina,sauraren shi har nadan yi nisa da,sauraren nashi, Dif naji batare da nasan yakai ayya ba da,sauri nadago idanuwa na,sauke su a gare shi, Ashe shima ya zubo min nashi idanuwan yana kallona, acikin nazarina, Kasa jure irin kallon da yake min nayi inda nai saurin kawar da idanuwa na, May kike tunane haka hae ya dauke maki hankali irin haka ya jefo min tambaya a lokaci guda yana kokarin jawo plate din fruit zuwa gaban shi, Cikin sauke ajiyan zuciya tare da,dan yin har da idanuwa nake cewa ba komai ina dai tunanen idan malam ya koma gida ko zai kula da shan maganin shi kamar yadda likita yace, Yadauki fruit zuwa bakinshi yana cewa ai su babane zasu kula da wanan don dai ba,son shan magani yakeyi ba, Nayi saurin mikewa zaune daga dan kishingidar danayi danufin zuwa waje, sai naji muryan shi yana cewa ina kuma zaki tafine ? Nace cikin murya kasa kasa cup zan dauko wanda zakasha tea, Koma ki zauna yace cikin dan murmusawa yana cewa so kike nafi nan kiba kenan ashe, ? Na girgiza kaina ina cewa ai baka da,almar kiba da yawa Yayana don kaga duk iyayyen mu ba masu kiba, Yace cikin dan sake ajiyan zuciya ai abin badaga nan ba ke dai Meenatu , Wayar shi ce tai kara alamar kira yashigo mai ke nan, Gaba dayan mu gurin da wayan yake muke duba sai naji yayi yar tsuki kawai, Naga ya dauki wayan, ranshi a bace, yana cewa wai yaya akayine kuma? Ta fahinci bai so daukan wayan nata ba amma,sai dai ta,daure rai a bace take cewa , Ina cikin wani haline don kaina ke ciwo kamar zai tsage min naji yadan yi huci yace baki sha maganin kiba ke nan ko ? Ko may take fada ban sani ba don dai ina,dan nisa kadan dashi, ,Sai naji yana,cewa sama, sama OK gani nan saukowa kasa, yanzun nan, Mikewa naga yayi ya,sauka zuwa kasa inda nabi bayan shi da kallo a cikin tabe baki don dai nasan daga cikin matan shine keda wanan matsalar, Na mike don kara dn gyara dakin kafin yadawo,, A dakin ta ya,samay ta,zaune ta,wani dunkule guri guda wai ita bata da lafiya, Tana ganin shi wani kishi ya kara turnuke ta tana ji tankar ta,shake shi, saboda wani irin bakin kishi da take ji, a ranta, Yace mata kwaso min maganin nagani idan da wanda zaki sha aciki, sai kisha kafin safe mu koma,asibiti, Sai cewa tayi kana nufin baza mu tafi yanzuba kenan sai gobe da,safe, Tafara dan guna guni tana cewa tunda ciwon ba ajikin mutum yakeba aidole ace nabari har safe, Ranshi a bace yake cewa look Fatima wallahi yadda na,gajin nan babu inda zan tafi da,daren nan, don haka idan zaki sha magani kisha har zuwa safe don ni zan tafi in kwantane, Tacd cikin bacin rai ni bazan sha ba tunda dazun nasha kada yai min yawa har yai min lahani a,jiki, Yace to ba inda zan tafi yanzu, Tace haka ma zakace yace eh hakan nace, ya wuce yana cewa idan kinga dama kin sha ruwan ki, Tabi bayan shi tana,jefa mai harara, tare da jan tsaki tana cewa jarababbe kawai tunda yana tare da mace ai ba inda zaka din, Karaf a kunen shi amma sai yadaure bai ce mata uffan ba yaja mata kofa ya koma part din shi,

****** ********** ****** Yasamu har na kashe light din dakin na kunna dumlight, mai ruwan blue, Ina kwance duk da,ba barci nayi ba amma sai mutum yai tsanmanin cewa ina barci ne, Naji yana jan tsaki yana cewa, har kin kashe light din ne sai nace batare da na juyo inda yake ba, Nake cewa ai ina ce ko fita zakuyi ne yanzu shi yasa na kashe light din, Ya dan saki guntun tsuki yana,cewa zazzafan kishin Fatima ya baci wallahi, ban san ita da,wanan mahaukaciyan wanda yafi wani hankali ba akan kishi, Ni dai ina,sauraren shi kawai ba tare da na ce mai uffan ba, sai dan kallon sa nakeyi, Ya,shiga,bayi yafito yana ce min doctor mansur ya fada min cewa baiga abinda ke damunta ba kawai damu ta,dan sawa ranta, Sai alokacin nai magana nake cewa ba ance cikine ke wahal da ita ba hakan, Yana kokarin kawai kwance yake cewa doctor yace bata da komai tare da ita, Doctor ya fada min cewa taimaki rashin mutunci a gaban shi ai, Nace a ciki murmushi wanan ai matsalartane doni ban iya abin zubar da mutunci a,gaban jama,a, Shima bai ce min uffan ba sai kallona da yakeyi kawai, tare da dan sauke ajiyan zuciya sai naji yace ai doctor ya fada min komai a kai, Nidai nadan juya ina gyara kwanciya yayin da naji hannayen shi a saman jikina ya fara dan sarrafani yadda ranshi yake son yi,, Bayan komai ya lafa ne a tsakanin mu nake tunanen ashe maganar malam gaskiya ce don gashi doctor da ban tsanmani ya fahince mu ba ya,fada mai, Allah ke nan inji malam da yace nidai na nufe su da,alheri a,duk zaman mu Da,safe sai da ya gama,shirin shi sanan suka tafi asibitin shi da ita inda tun a hanyq ya,fanci babu abinda ke a zuciyan ta kamar yadda doctor yafada sai kishi kawai, Don tana wani kokarin jan hankalin shi da hira sai yai banza da ita, kawai, Abinda yasa itama taja bakin ta tai shiru don ta fahinci bai son maganan, Ina tsaye a falo da,suka,dawo sai nake cewa sannun ku da,dawowa kamar dai yadda malam yace na dinga masu abu a,sake da,zuciya guda, Abinda nasan cewa zan samune a gurinta na,samu watau harara, da fuskewa, Murmushi kawai, nadanyi daga gurin da nake tsaye inda na shiga kitchen na dauko mai goran ruwan sanyi da cup, Bai tsaya shada cup din ba ya kafa bakin goran a bakin shi ya kwankwade su gabadaya, ya,aza min goran a,saman tire, Sai yake cewa shirya yaran nan mu fita da,su please Da sauri na kai mai kallo a cikin mamaki nake cewa ai banice mai fita dasu ba,wanan satin, Fatima ce, Yace wace bata da lafiya ina zata iya fita dasu kuma? Duk karshen wata yake fita da yaran shi idan yazo inda,kowacen mu da lokacin da take futa da yaran, Inda a,wanan fitan ya fahinci cewa ko wace mace dahalin rayuwanta a yaran nashi, lda ya fahinci cewa ita Fatima diyanta kawai na ta sani duk inda ake tana haba haba dasu ne kawai, Salawatu kuma bata iya dawainiya da yara sai yake gani don bata haihu bane killa bata son yara, Sadiya kuma ita bata,son hayaniyan yaran bawai bata,son su bane kawai dai bata saba da harkan yara ba, Amma idan zamu fita da yaran in nice har diyan Fatima suna nuna farincikin su akai, Kuma idan mun fita gaba dayan su ina haba haba dasu ne ban taba nuna ban banciba, Nikan umurnin maigida nabi inda nashirya tare da umartan yaran part din ya,dasu fito mu fita tare, Jikina yana,saye da,wani jan lece mai kyau da tsada na sa mai farin gyale mai stone duk jikin shi, nai daurin baya mai kamar a,daure butterfly a tsakiya , Kna tsaye ina jiran fitowan mai gidan kamar yadda muka,saba fita a daidai lokacin da yafito yana kokarin sa aninin hannun rigar dake jikin shine, Ita ma,Fatima tafito daga dakin ta tana cewa yara sun ce wai kince su shirya zaku fita,dasu, Nace a,cikin dakewa don dama nasan cewa za, arina a hakan, nima fuskana a daure kamar nata nace a,gadarance Eh maigidan ne yace mu fito mu fita tace cabdijam Meenatu har abin naki yakai gashiga hakkina irin haka a gidan nan,,? Ina tsaye ban kai ga bata ansa ba yafito yana cewa, ni naba da umurni mu fita tare, Don ke baki da lafiya kinga ko bazan bar yarana ban fita dasu ba,saboda baki da lafiya ke, Kallon shi tayi kamar zatai magana,sai kuma,tai shiru don ta fahinci Tarkon da ta hakane ya kamata, dumu, dumu, Wani irin kallon haka zakai min tai mashi sai yake cewa yadda kanki ke ciwo har a cikin dare baki iya barci ai gara ki samu hutu sosai tukun, Yana kaiwa daidainan ya juya inda nake sawa, Amira dan top saman kayan ta,don ita bata faye don sanyi ba,sosai, Yana cewa oya mu tafi ko kada yamma yai muna don har gurin malam zamu tafi, dasu su gaidashi, Na bi ta gabanta a cikin wani irin tako na kasaita na,wuce ina mayar mayar ta da martani abinda tai min jiya,da,dare, Nan muka fita batare da yaranta ba,muka,barta a cikin tashin hankali, inda uwar tsegun Salawatu tana labe tana kallon duk draman da,akeyi a,falon gidan, sai dariyan dakutawa tayi a boye,, Mina fita daga haraban gidan na sauke ajiyan zuciya batare da ya,dubeni ba yake cewa may ke faruwa kuma, Nace ni dama nasan cewa wanan fitan sai an samu matsala da Fatima tunda turned din ta ne, Yace amma ai cewa tayi bata da,lafiya bata iya barci don may za,a fita da ita bata da lafiya, kuma, Kamar da gaiyya don wanan fitan va karamin abu yasaya wa yaran ba,har mada na,Fatima,da basu tafi din ba,nasa ansaya masu suma, Saboda mun biya,asibiti sai dare muka,shigo gida don malam ya tsare ni da sherin cewa Yaya Abubakar yazo ya hanani na kula dashi daga karshe kuma yana,wa yaran wasa, Mundawo duk na gaji amma falon gidan kanar babu kowa don duk suna,cikin part din su alamar kowa ma ta hau ke nan, Nashige part dina ina cewa a raina kai kishi ho, kishi kumallon mata, idan baka iyaba sai a kar ka abaro,

ZEEE MAKAWA YELWA SEENABU

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣1⃣7⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

HOLY FRIDAY ALLAH IS OUR PROVIDER, LET,S ALJANNAN FIDDAUSI BE OUR RESTDENT IN,HERAFTER ALLAHUMA AMEEN,,,

Duk wani abinda mutum zaiyi arayuwan shi yayi don Allah ya,kuma,bari don Allah, Na aikawa Fatima,da,yan abin lashe, lashe da,muka,sayo na yara,har ba,da yan wasu abubuwan wasan yara, Amma,sai Fatima ta kwasata,dawo min da,su har dakina,da ka ta, Fitan tane Yaya Abubakar yagani daga part dina a,fusace yai mamaki don haka ya,dakatar da ita yana,cewa, lafiya ya,akayi ne kuma, Kamar bazatai magana ba,sai kuma yaji tace kaya na mayar mata, Da,mamaki ya,ke duban ta yace a cikin wata murya mai nuna tambaya da cewa, kayan may fa ? Ciki ciki take ce mai kayan da,ta aiko min da, su na yaran da kuka,sayo, Kika mayar mata da kayan bayan ta aiko maki da nasu kason, Baiyi magana,ba ya,shige part dina a fusace ina daga kwance ina,bawa yara nono naji an bankado min labule azatona ko itace ta kara dawowa, dakin, a lokacin, Yana tsaye a kofan dakin fuskan shi a,gurin da ta,zube min kayan tafita, Ni kallo guda,nai mai na fahinci a kwai matsala sai yake cewa kwaso kayan nan ki biyoni falo, Nakira Maimu tazo takama yaran ni kuma na mike tare da kwasan kayan zuwa falo kamar yadda ya umurce ni , Na samay shi zaune yana kokarin rage volume din TV dake aiki a falon shi kadai, Kusan duk lokaci guda muka fito daga dakunan mu zuwa falon atare , Gurin yai tsit na dan wani lokaci sai zuwa can yadan dago kanshi a hankali ya,dubi gurin da Fatima take zaune, yan cewa, Kara maimaita abinda kika fada min akan zancen kayan dana sayawa yaran ki yau, Da,sauri ta,dago kai tana kallon shi don jin kalman da yai magana dashi na cewa yaran ki, Shiru tayi ba tare da ta,ce ma kowa uffan ba sai shine ya kawar da shirun da cewa tau ki sani tunda,bazakiyi magana,ba Duk wani abinda zan saya a gidan na yara insha Allahu bazan sai wayaran ki komai ba tunda ke baki san ana maki ba Gaba,dayan mu muka,dago kai muna kallon shi sai ci gaba da,cewa yayi, ni bazan dauki wullakanci ba wallahi, A hankali tace aini ba kai na mayar wa,da kayan ba da zakace hakan,, Ita wace kika mayar wa itace ta,saya masu ko ni dazaki ce hakan, Tace itama acikin daga murya ai da kai kasaya masu sa,sai ka basu da hannun ka badai, ita,ta aiko min dasu ba, Ta karashe maganan cikin dan hasala tare da juyar da kanta wani gefe, Ni Meenatu na,shiga uku, dama don nice na, bayar abasu kikace basu so sun yafe din, Sadiya,daga gurin da take zaune take cewa may ke faruwane wai haka dai, Fatima tayi maza tana cewa kin san nice ya kamata na fita,da yaran nan wanan time din,, Amma,wai sai kawai gani nayi Meenatu zasu fita,dasu wai na,shirya yaran nace su tafi tunda ba,gaskiya a zancen Yanzu bayan sun dawo, shine ta,aiko ma yaran nan wai nasu tsaraban, Kallon ta kawai yake rai a,bace, batare da tai magana ba yayin da Sadiya ta juya gare shi tana cewa, Amma,dai wanan fitan ai na Fatima ne dama may yakawo hakan kuma, Kamar ba,zaiyi magana,ba,sai yace, Look don't take me, as a young, nafiki sanin abinda nakeyi, Jiya cikin dare ta buga min waya,cewa sai nazo na kaita asibiti bata da lafiya , Nasauka,na,ce tasha magani tabari yauda safe mu tafi da,safe ina masallaci take kirana wai ciwon ya matsa mata, Mundawo asibiti kuma kina zaton zan tafi na kashe kudina a banza ne wai, Koko saboda bata da lafiya,bazan kai yarana yawo ba, kamar yadda nai masu alkawari, Daga,gurin da,Salawatu take zaune tace ai wanan ma ba hujja bane tunda bata,da,lafiya ba,sai a tafi da the next person ba, Sadiya tace gaskiya Fatima kinyi kuskure don kinga bai kamata tun farko kice wai yaran ki basu tafi ba, Kuma an sayo masu tsaraba kince wai basa,so saboda may zakiyi haka, Tace ke dakata yaranki ko nawa ni keda yarana kuma,nace bazasu karba,ba, Yace good yara,nakine ba,nawa ba don haka ki shirya,su ki mayar dasu gidan uban su ko gidan ku, Don bazan zauna kina tayar min da hankalin iyali ba saboda diyanki, ya mike yana cewa kinji abinda na fada maki, Nan Fatima tashiga daga murya tana fadan bakaken magan ganu tana cewa,dama ba yau ba tasan cewa ana,bakin cikin da zaman yaran agidan nan, A,daidai lokacin ya,sauko sai yake cewa ana,bakin ciki dasu zata,kwashi kayan yarana ta ba yaranki, Da,sauri tajuyo tana kallon shi yace yes kayan nan ni ban sayowa,yaranki ba xon nasan ke yar cin mutunci ce dama nasan zakiyi hakan, Ya juya gurin da,nake zaune acikin mamaki yana cewa ai yanzu kingani ko ban fada maki cewa ban sayo dasu ba, Yace daga yau idan har na isa gareki kada na sake ganin zan fita kin hado min da,wani abu daya danganci Fatima, Kema na,cire ki daga harkan yarana daga yau ban son wani abinda zai kara kawo min fitina a gida, Abin ya kara batawa Fatima rai tace ai suma,suna,da gatan su kawai dai don mutuwa ce da ta raba su da nasu mahaifin, Yace ai ni na san komai zaki iya fada don haka dai na fada maki ki mayar da yaran nan gidan mahaifin su, kafin na,dawo garin nan, Yana fadan haka yasa kai yafita zuwa waje da zai tafi yabar mu nan a zaune cikin jimamay, Sadiya tace ni wanan abin wallahi banga abin tada jijiyoyin wuya ba akai idan kuma zaikiyi wa kanki adalci Fatima da baki ce wai manager bai kokari akan yaran nan ba, Takuma juya gurin sadiya a hasale tana cewa ninace bai kokari dasu, in ma baiyi ya bari mana ai suma,suna da,gidan uban su ko, Salawatu tace hmm kidaiyi a hankali ki samu ya sauko don komawan su gida kema kin san hasaranki ne, sosai, Nikan na kira Maimu nace tazo ta kwashe kayan zuwa,daki dasu sai cewa Fatima tayi ai dole aje aci haram tunda ankai ga yadda akeso, Diyan matsiyata,su samu guri suce su zasuyiwa mutane wullakanci, Najuyo zanyi magana amma,sai Sadiya take ce min wuce kawai Meenatu kada ki tsaya sa,insa don girman Allah, Nayi maza nace ai ba,sa,insa zanyi ba zan fada mata cewa dan matsiyata ne tabiyo zuwa nan ko ? Wanan matsala na Fatima shi yahana,mu ganin farincin maigidan har ya,koma,bakin aikin shi batare da ya,sake rai ba,don yana a kan bakan shi na,cewa sai Fatima ta mayar da yaran gidan su,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull