Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 122

Tarko complete novel - Chapter 122

Tarko complete novel Chapter 122: Tarko complete novel Chapter 122. ****** ********* ****** Acikin wanan yanayin ne aka,sallamo malam daga,asibiti inda ya…

3,198 words

****** ********* ****** Acikin wanan yanayin ne aka,sallamo malam daga,asibiti inda ya dawo gida da zama na kwana biyu Don Yaya Abubakar yace sai ya dawo zai mayar da shi gida dakan shi, idan yazo, Sai haba haba nake da iyayyena,da,su kazo daga gida tare da malam da matar shi,, Malam ya murje yayi kyau sosai zakace ba shine ya tayar muna da hankali irin haka ba, Sai godiya,da,saka,muna, albarka yake tare da,kara muna,nasiha duk kan mu duk wace taje gaidashi zai mata nasiha akan rayuwan zaman aure da kuma hakkuri da abokan zama, Sai dai a,bangaren Salawatu da Fatima duk irin nasihan da malam ke masu kallon azzulumin tsoho suke mai, wanda bai kaunar jikan shi dasu sai dai yar uwar shi kawai, Sadiya ce ma ita bata faye dauka abu da zafi ba sosai hakan yasa,taje gode wa nasihan shi dayje mata, Malam din yana matukar mamakin ganin cewa jika shi na cikin shine Allah yaiwa wanan irin falalan haka, Hakan yasa yakan kara fada,min idan muna mu biyu koda yaushe Aminatu ki dinga,kara lurar da,dan uwan ki hanyan alheri ma,yan uwan shi a gida saboda duk abinda kabawa wani shine rabon ka na lahira, Nakan cewa malam din in Allah yaso zanyi kokari naga na yi hakan An shiga,kasuwa an masu sayayya sosai don nasaya masu duk wani abinda nasan zasu so su tafi dashi, gida daga nan, Ranan da yaya ya iso washegari suka kama hanya tunda safe zuwa Birnin Kebbi, Mutanen gida,sunyi farin ciki sosai ganin dan tsoho mai ran karfe yadawo gida lafiya,sabanin yadda,aka,wuce dashi ruwa ruwa rai a hannun Allah,, Taje gida ya,cikw da yan uwa,da,abokan arziki masu zuwa,gaida malam da yi mashi sannu da,zuwa A wanan zuwan ne Yaya Abubakar din ya gyarawa,malam dakin shi inda yasa aka,kara,gyara gurin ya,saka,mai sabbin kayan daki masu kyau, Wanan zuwan sai da ya,gana da iyayyen Fatima akan zancen yaran da,yace tadawo dasu gida, Aliyu ya bore masu ita da mahaifiyar su saida aka tura wani dan uwan su yatafi ya dauko yaran gwanin ban tausayi, Duk wani tashin hankali da Fatima ke kokarin yi dani a,gidan ban yarda na biye mata munyi tashin hankali ba, Bakin cikina guda da na zama ina a cikin sanadiyar barin yaranta,a,gidan don duk gurin da ta zauna zance sai tace ai saboda nice aka, tura yaranta gidan su, Wanan dalilin ne yasaka,ta tashi tsaye akaina tana ta dan shige shigen ta da uwar ta,tare da yan uwan ta ke masu a can garin mu, Mun tafi mun sauke farali nida Fatima a,kasa mai tsarki tare da,wasu daga,cikin yan uwan mu daga,ciki har da,Yaya,mustapha da,su baba Hamza da ba shaibu, A can nai sabbin kawaye duk da,ba,damuwa,da,sha,anin su nakeyi ba amma duk inda zasu tafi sai mun tafi tare da,su, Dayake da,Anty mariya mukai tafiya tana manne dani akoda yaushe, Mama,Sa,adatu da Dije suka zauna,min da yara a daki na har na,dawo, Naiwa maigida tsaraba,important abubuwa masu kyau da,nasan maza suna amfani dashi a,rayuwan su, Nayi wani dan fresh dani kamar ba,aikin hajji na,tafi ba,gashi haskena ya kara,fitowa, sosai, Mun samu maigidan baya,kasan don yai tafiya zuwa kasan Thailand haka,muka samu damar kara dan kimtsawa kafin Allah ya dawo, dashi lafiya, Sai dai akoda yaushe muna,waya dashi sosai don yakan kira yaji motsin mu, Yarinyar da Baba Hamza yake son ya aura tazo gaidani, dazasu koma sai yake cewa zai dauki motar gida ya mayar da ita gida, Amma,sai Salawatu tace wai bazata bada key ba don keys din a hannunta suke gaba daya, Tun lokacin da,bamu nan muna saudiya, ita kuma,Sadiya,ta,tafi Birnin Kebbi ganin mahaifiyar ta bata da,lafiya, Naje part din ta,da kaina bayan sun fada,min cewa, tace bazata bayar ba, Nake ce mata haba dai don Allah kiba da,key ya mayar da,wanan yarinyar gida kafin yamma tayi, Sai cewa,tayi bazan bayar ba,don ba,dole,sai da motar gidan nan zai mayar da ita,gida,ba, Cikin murmushi nake cewa haba,may yakawo wanan maganan don Allah yi hakkuri, ki basu yanzu zai dawo ba zai dade ba insha Allah, For god sake Meenatu ki kyaleni ba zan bayar ba a,saman side drawer din ta na hago keys din moran don haka na,dauka batare da,najira may zata ce ba na juya abina ina,cewa zandawo dashi dazaran sun dawo insha Allahu acikun ba,a, Fitan su yai daidai da,fitowan ta daga daki a,fusace tana cewa kina ganin cewa ke har kin isa kishigo har dakina,ki dauki abinda,aka,bani ajiya kibawa wani banza ce ya fita da,shi, Nace haba Salawatu bafa,wani guri zasu tafi nisa don dai kawai yarinyar tazo gurina,ne shine yasa nace kibada key akai ta amma,kiyi hakkuri don ina,ce ko dawasa kikeyi ai da,farko shiyasa,na,dauko kets din, Bari kiji Meenatu duk tsiyar bazan bar gidan nan ba tunda,bake ke aurena,ba, Kinzo kin gwada min cewa ke kin isa a gidan nan da har zaki shiga dakina ki dauko key kiba wanan munafikin yaron, Ni ba abinda zaki iya yimin Meenatu don wallahi nafi karfin ki ko may kike tsan mani na,wuce nan Meenatu don haka ki kama kanki dani wallahi, Nace cikin zafin rai ke dan Allah ki rufa,wa mutane baki yanzu may abin fada a nan kina,dai fadane kawai don son jan fitina, Naga,ko shi mai gidan yake gari yana bawa ,Hamza keys zuwa,gurare da dama, Tace dallah mallama rufa muna baki nagane cewa, hassada kike yi kawai d,bakin ciki don keys din suna gurin na, Kallon mamakin na juya akan abinda ta furta zancen ta na tsaya yi, don wanan abin da ta fada duk halaiyanta,ne, Ni dai ko fada ko wani zance can na bacin rai ya hadani da kishiya ban tsayawa mayar da,martani, don Anty Amarya ta fada min cewa, Tsayawa fada da kishiya kuna,sa,in,sa shike sa kaji zancen kazafi da sheri wanda har ka mutu kana tuna shi, A haka ake samun daman fada,ma zancen sheri wanda ake son isar ma dashi, Tace amma idan kina da matsala da kishiya share ta,kawai ba fada ba gaba tankar baki san tanayi ba,yafi komai zafi da cin rai a gareta don zaki barta da zancen ta yana nukurkusan ta ita,daya har ta gaji ta,sake rai, Hakan naso nai wa Salawatu din don tun dawowan mu da na kula da cewa duk wani abu tayi kakagida dashi sai na,sa mata ido, Wanan kaddaran ma don banda yadda zanyi ne saboda motana tun kan mu tafi saudiya bata da lafiya, Murmushi nayi ina mai son na,shige nabar gurin don gudun rudin shedan don ni kaina na fahinci idan ina wani dan fitina dasu irin shariyan da nake masu yana bala,in ci masu rai don su sunfi bukatan mu tsaya a tsakar gida muna jefa wa juna magana, A lokacin da na juya don na,shige part dina sai naji tana biye dani har da har da taba hannuwan ta tana cewa wallahi Meenatu babu yadda zakiyi dani a gidan nan, Don duk tsiyar ki ba zan bar wanan gidan ba kuma,dole nayi yadda raina yake so kina kallo agidan dan uwan naki, Dake da duk yan uwanki masu bakin cikin gani na agidan nan suna cewa wai na mallakeshi, idan zaku mutu ne ku mutu in kuma zakuyi rai kuyi, Amma zama daran a wanan gidan kuma Abubakar muna tare yadda raina ke so, don nagane cewa ke kawai yan uwanku ke kauna da zama a gidan nan, Na kalli Salawatu nai murmushi nace, ai yan uwana basu bakin ciki akan kowan ku don da sunayi da baki kai war haka a gidan nan ba , Din gidan da kike gadara da maigidan duk nasu ne don haka idan sun so bari ki gidan ayau din nan dole kibar shi wallahi Salawatu ba sai an kwanaba, Ina fadaar haka na,shige na barta na tana haushi tankar sabuwar karya har dare tana mitan abu guda ,, Hamza ya dawo da key din nabawa Maimu nace ta mayar mata azatona bazata karba ba amma sai naga ta karba,, Maimu ke cewa wai tace dolema a mayar mata inba tsoro ba, nace fita zancen mahaukaciya kawai, Muna nan a haka da ita ba mai shiga harkan wani har yarana duk ta,share su muma dama ba damuwa mukayi da harkan kowa ba agidan, Don Alhamdullahi nafi karfin yarana,duk da kanana,ne, ban sakar masu ba akan shiga wani part na gidan ina taka tsantsan da abina, Nasan cewa zance na nan Salawatu ta kulla a,ranta har zuwa dawowan maigidan don tun a,waya na fahinci wani abu a tare dashi, Mama sa,a sukan yi mamaki irin yadda nake zaune a cikin wa yan nan jiga,jigan mata har kuma nake iya tabuka wani abu, Take ce min ai su a zaton su nice za aita zalunta don ni karamace sosai acikin su, Amma tun zuwan mu duk gidan mu suka fahinci cewa nima,wata abuce a zuciyan maigidan namu irin yadda mu, amullan mu dashi a cikin taron buki yaje don komai sai ya,saka a nemoni, Mama Sa,a tace shine ta kara wanke zargi a zukatwn mutane masu saka idanuwa da,fadi shace, Mirmushi kawai nai mata don mama ba sa,ar yina bace da zan zauna ince mata ai gashi gashi, don ance gani ya kori ji ai,

****** ********* ****** Kwanan mu goma,sha daya da,dawowa shima ya dawo daga gurin tafiyan da,ya tafi, A lokacin da ya iso gida muna daki dani dasu Mama Sa,a sai dai yadan dauki lokaci bai samu shigowa gidan ba, Aisha ce tazo tana,sanar dani dawowan Baban nasu abinda yadan sani kara dan kimsa jikina, kenan na dan gyara,fuskana,na saka dan kamahi a hannuwana na,shafe jikina Yana zaune saman kujera fuskan shi dauke da,murmushi Fatima daga gefen shi itama,acikin murmushi fuskan nata, yake, A hankali nake tako na tankar wacce bata so fitowa ba a lokacin, Na karaso gurin adaidai lokacin da yake ce mata ai nazaci kuma bazaku saka hakorin gold din bane, Fatima tana cewa ai tunda kace kana son na saka shiyasa gaba dayan mu muka saka, yace har biyu kikasa ke tace eh amma ita Meenatu guda ta sa kawai, A lokacin ya dago kai yana kallona yayin da yake jin wani sanyi ya na rantsa mashi zuciyar shi,, Bai san abinda yasa idan yaga wanan yarinyar Meenatu yake jin samun natsuwa da nishadi, a cikin rayunwan shi ba,, Ganin ya,mayar da hankalin shi gareni yasa matan falon watso min wata irin fitinanniyar harara, ta gefen idanuwan su, Yayin da Fatima ta karashe zancen da su keyi a cikin yar zafin rai, tare da jan yar guntuwar tsuki bata tsaya sun karasa maganar ba ta mike tana cewa bari ta,duba,abu a kitchen, Ranta a bace ta mike tabar gurin tanacewa wanan anyi yarinyar iska da tazo bai iya boye feeling din shi a kanta gaban kowa, Tace nidai wallahi ban son wanan yarinyar da Salawatu a gidan nan don duk yan iskane damadama, ita Sadiya din, amma ko ita babu dama dazan samu wallahi duk waje road zasu, Nakoma daga bayan kujerun da,suke a zaune nadan yi masauki daga tsaye can bayan cushion din Nai mai sannu da zuwa a cikin jan kamshi tare da dan basarwa Irin kallon da yai min shiya dan dimautani sosai, don nasan irin kallon da ke nuna sha,awa Amma sai na basar tankar ban fahince shiba, nan ya dan rikice ya rasa may zai ce wani irin kallon yake yana cew a cikin daburcewa yake fadin kamar wace batai aikin hajji ba, Salawatu ta sake wani dan gajeren tsuki mara sauti tabar falon, Murmushi nayi don dama daniyya nai mashi wanan abin don kawai suji haushi, a ransu, Yaya Abubakar wanda na gane cewa ya riga da,ya shagaltu gurin son na matso kusa dashi, bai masan cewa sun bae falon ne don haushi ba sai dai giftawan su kawai yake gani Muryan Aisha,ce kecewa mummy Amira ta fado daga,gado ta,fasa bakin ta, Abinda yasa shi saurin dawowa acikin hayancin sa kenan muka,kwasa zuwa,dakin don ganin yarinyar, Salawatu wace take labe tun shigewan ta,don ganin yaya zai yi dani,idanuwan ta , suka kada don kishi su kayi jawur, a lokaci guda, Abin yarinyar nan tsoro yake, bata, tana aiki a kai amma kullun kamar kara saka kaunarta, ake azuciyar maigidan nasu, Wani irin kishin Meenatu ya kara turnuke zuciyar ta tace a,fili zanyi maganin ki yar iskan yarinya,, A yadda,girkin gidan mu yake duk ranan da yazo wace keda girkin dukka gida itace mai masaukin shi sai dai idan har wani uzuri na,daban ya gifta sai adan daga kafa, Yau din ma Salawatu ce zatai girki idan tafita sai Fatima daga Fatima sai Sadiya sai ni, Wanan daman ne ya,sa Salawatu, fara aiwatar da nufinta na ganin cewa sai na samu matsala a tsakani na da maigidan ko ta halin kaka, a gidan, ****** ********** ****** Tun ranan da Salawatu tai girki washegari ban gane kan maigidan ba agai don sai wani basar wa yake min, Ganin hakan yasani nima na dan lafa da,duk wani kulawan da nake bashi, don gujewa wullakancin maza, idan sun hau, Saboda ban san abinda akafada mai agamay dani ba wanda har yasa shi a cikin wanan halin,, Ance ba,a yanke hukunci a cikin fushi haka kuma baka bada hakkuri alokacin da rayuwan mutum yai matukar baci, Don haka naja daga gefe ban saka kaina daga duk wani al,amarin gidan sai abinda ya shafeni kawai,, Muna a cikin hakane, har zuwa lokacin da girki ya zagayo a kaina alokacin na riga da na,shirya daga taron duk wani challenges din da zan samu daga gare shi, Da kuma irin taron da zan mai idan har ya bukaci hakan daga gareni don kaza Anty Amarya ta turo min daga sokoto, Wanda na shige kuryan dakina na cinye shi ni kadai kamar yadda ta umurceni da yi, Ranan da na karbi girki a gidan nai duk wani abinda,na,saba ga girkina, Ga idanuwan kishiyoyi a kaina suga yadda girki nawa zai kasance tsakani na da maigidan wanda babu shiri yan kwanakin nan a tsakanin mu, Ko kudin girki a ranan Maimu yabawa da takawo min daga kofan part dina ya juya abinshi zuwa inda zashi, Tsab na gyara gidan kamar yadda na,saba inda kuma nai girkina irin na gargajiya, Ban samu haduwa dashi ba,sai a dinning gurin cin abinci daidai lokacin da ya zauna zai fara serving din kan shi, Nafito saye a cikin wani dogon riga mai fitar da,shape din mutum yanada zubin duwatsu agaban shi har iya nono, Sai kamshi dana dan murza a jikina don na yarda da akace kamshi yana motsa sha,awan maaurata, A hankali na dan rankwafo daidai saitin gurin da yake ina kokarin karban serving spoon din daga hannuwan shi, Idanuwan yan sa idawan gidan kyam a kan mu suna kallon yadda,zuwa na kusa dashi zai wakana, Har Sadiya wace ke nunawa a fili da baruwanta da kishin kowan mu, Amma a badili tafi kowan mu kishi azuciyar ta, sai dai tana boyewa don azauna lafiya, Ita ko Fatima dama kamar Salawatuce kawai bata bukatar gani wata kishi a,gidan gaba,daya bata da zabi, Ina gama zuba mai na juya zuwa part dina batare da na tsaya ba,again, Bayana ya bida kallon yayin da nake shiga part dina batare da yace uffan ba har nashige ,abina, Ya mayar da fuskan shi ga abincin shi yafara ci a hankali batare da ya,tsaya sauraren kowa ba ,don abincin yai mashi dadi sosai a baki da idanuwan shi, ma Saboda tuwon farar shinkafa nayi da miyar kuka wanda kamshin kayan yaji da daddawa ke tashi ga kassan rago danayi a cikin sa sai kamshi ke tashi,

Sai da na tabbatar da cewa ya kammala duk wani abinda yake a,falon ya,shige part din shi, don kwanciya, Yan mintuna nashirya inda naiwa su mama Sa,a sallama ita,dasu Ramatu nadauki yar jakar da nake sa kayan bukatuna a ciki idan zan tafi turaka, Nashiga,bakina dauke da sallama inda na hango shi zaune saman kujerar dake dakin hankalin shi yana a kan system din da yake aiki akai, Sallamata yasa shi dago kai don yaga ko wacece tashigo dakin, Naga ya mayar da kanshi da, ga,abinda yakeyi, batare dayace uffan ba, Hakan ya,sani sanin cewa ya sha maganganu iri, iri a kaina,duk yadda akayi, Direct gurin da muke aje flask din ruwan zafi na nufa inda na,aje flask din dake dayan hannun nawa a hankali, Na nufi gadon wanda yasha gyara yai kyau lumilumi dashi nadan kara kakabewa kamar yadda sunna ya koya muna, Nadan kwanta daga gefen gadon a hankali tare da jero adduoi dana sani, Tun ina jin motsin shi yana yan abubuwa har barci yadan fara daukana a hankali, Acikin barci naji muryan shi yana cewa, 'Ke, Meenat tashi muyi magana, dake, Fada min may ye a tsakanin ki da Hamza ne wai ? Acikin mamaki na bude idanuwa duk da tambayan ya girgizani amma,sai nadaure na mike ina cewa A,uzubikalamati tamat min sherin min halak,,, Acikin natsuwa bayan na mike nake ce ma shi Hamza wani Hamza kuma,? Yace a cikin daure fuska wani hamza kika sani a nan gidan wai ? Nace a cikin natsuwa zama nake dashi kamar dan uwa albarkacin sunan baba Hamzan mu dayake dashi , Katseni yayi da cewa ke, Meenatu, ki fada min kafin naji daga bakin wani kuma, Innalillahi wa,inna,alaihim raj,un na karanto yayin danace a cikin natsuwa banda,wani alakan daya wuce haka,a tsakani na dasu sai kuma zaman makwabtaka damuke da yan gidan su wanda ya zama muna zumunci yanzu, Yace a dan hasale ance a koda yaushe, ko da,dare ne, yana part din ki wani lokaci wai har da matan banza yake shigo min gida, Shine ke har da zuwa gaba gadi daukan key ki har dakin Salawatu ki bashi ya fita da mace da motana,,, Nace acikin natsu shashan ci ba tarbiyan gidan mu bane balle nayi shi yanzu dagirmana har da yara a tare da ni, Don duk tarihin gidan mu babu mai abin assha daga cikin mu, Ina,fadan haka nace nima acikin bacin rai dama wani abin aka zarga min ba wanan ba, Sai naga yadan furza iska yana cewa hakane amma shin may ye gaskiyan maganan , Yaya kukayi da,Salawatu akan keys din motar dake wurinta, da kika,shiga har dakin ta kika,dauko, Ban boye mai komai ba na kwashe yadda duk mu kayi da,Salawatu na fada mashi a tsanake, Shiru yayi a cikin matsanacin tunane akan zancen yayinda ni kuma nake zaune a bakin gado gaban shi nai shiru ina,sauraren abinda zaice, Sai naji yai shiru har zuwa wani dan lokaci yana ajiyar zuciya, yace ni za,a rainawa wayyo haka amma bari Allah ya kaimu gobe lafiya, Daga haka ya mike ya nufi wardrobe din shi yayin da ni kuma na koma,na kwanta tare da,juya bayana, idanuwa suna a rutse, Tunanen abinda zancen shi ke nufi na keyi, don abin ya ban mamaki, sosai nace a raina, Ana nufin kenan, sheri ko ince zargi a kai min a gurin Yaya Abubakar, Ban san ya akayi har karso saman gadon ba sai ji nayi yadan kankamay ni, yana,sauke numfashi a hankali ya yana cewa, a cikin wani yanayi Iam so sorry for treating you dis way, Kamata yayi ace nayi bincike kafin nayi wani hukunci a kan zancen, Dama dagani har shi kowa yana bukatan dan uwan shi don haka,sai ban wani dauki zancen da zafi ba kawai na,sakar mai da komai,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull