Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 123

Tarko complete novel - Chapter 123

Tarko complete novel Chapter 123: Tarko complete novel Chapter 123. Washegari ban fito da,wuri ba,naiwa Ramatu waya akan ta,hada mai breakfast kamar yadda…

3,619 words

Washegari ban fito da,wuri ba,naiwa Ramatu waya akan ta,hada mai breakfast kamar yadda na,shirya,yi kunun gyada, Nakuma,bata umurni data gyara yara,su karya kafin na fito, Ai kafin mu mu sauko Salawatu ko Fatima,sunyi tsuki yafi sau barkatai, gashi kofa,a,rufe yake, Mu kuma barci muke aciki don kowan mu a gajiye yake ranan a can part din yaya nai wanka na kimtsa jikina acikin wasu atamfan super wax mai kalar kore da dan yellow flowers, Dinkin dogon rigane mai budaden kasa kamar fish tell, a gaban rigar a,sa stones dinkin kasan Dubai ne, Sai da na shirya na nufi gurin da yaya yake kwance dunkule acikin bargo yana barci, A hankali nake dan ta dashi nake fada mai cewa rana yayi don almost to eleven na safe, A hankali nake saukowa daga,steps din inda,sautin takalmana yake sake sauti a kasan stairs din, Salawatu ce mace ta farko dana fara arba da ita zaune wai suna hira ita da Lami Fatima kuma tana fitowa daga,kitchen alokacin, Idanuwan su kyam a kaina gaba dayan su suka juyo lokaci guda suna son ganin wanda ke saukowa daga,steps din, Kwaliya na shi yarikita masu zuciyan don kwalliyan na daga ciki sakon da,nake son isar masu, Acikin sauri suka fara dan fuskewa,suna masu kawar da kan su a gare ni,, Na dan sake wani irin lalausar murmushi nace, munafuka zaki gane kuren ki, Da, Fatima na fara haduwa nace mata a cikin basarwa ina kwana man Aina, Lafiya ita,ma ta dan amsa min a takaice kawai ba tare da ta tsayaba kamar yadda nima din ban tsaya ba, Daidai gurin su Salawatu nace ina kwanan ku suma,na,sa kai na ahige ban tsaya jiran jin may zasu amsa min da shi ba na shige part dina, kawai, Ina,shigewa Salawatu tace lalai namiji munafukine yanzu duk fushin da Oga yake ashe na munafunci ne, ni daga yanzu na daina yarda da dadin bakin namiji akan matar shi Diba ma don tasamu yadda take so a gurin shi yadda tawani yi kyau kamar watayar masar, Ban dade da,saukowa ba,shima din yafito saye a cikin wani farin yadi mai laushi wanda,akaiwa kwalliya da,wani farin zaren silver agaban rigar har kasa,, Tun yana a steps suka hada ido da,Salawatu wace ta wani hade rai saboda haushi da takaicin dake cin zuciyar ta a lokacin, Yasan wanan halin don sai yace kusan Sadiyace da Meenatu basu damuwa da fushi idan ya, kwana,da wata mace a,dakin shi har suka fahinci yai wani abu da mace sai kaga suna daukan zafi dashi har sai girki ya dawo gare,su zasu sake ransu dashi, Ta sakar masa harara ranta a bace take cewa ina kwana, cikin rashin sake fuska, Shima,fuskan shi ba,a,sake ba,sosai ya amsa da kun tashi lafiya, yasa kai zuwa part dina don ya gaida su Mama,Sa'a stilbayan shi tabi da harara har ya shige abin shi kai tsaye,

Ina shiga part dina na samay su a falo gaba dayan su ana ta hayaniya yaran na ganina su kayo kaina gaba,dayan su suna cewa mama Na rugumay su muka fada a saman kujera ni da,su, Sai da na zauna na,saka,su duk ajikina kowa da inda yake tabawa daga jikina don murnan gani na, Nima din ina rugumay da su gaba daya a jikina acikin so da kaunar su, Najuya inawa su mama da sauran jama,a ina kwana da yaya gida, suma suka karba min a cikin murna, Nake tzmbayan Ramatu da cewa kowa ya karya dai ko kuma ba matsalan komaiko, Tace Uwar dakina babu komai abincin rana ma yanzu haka na gama miya don sunce wai da miya suke so yau, Yana nan a kitchen din side din nan miyar shimkafa sai dan anjima na,dora a rice cooker nan ciki, Nai murmushin jin dadi nace Allah nagode ma nagodewa Ramatu da Inno, watau Antyn Nani sai duk suka,sa min dariya , Muna cikin hiran mu da,dariya,shigo dakin yana wani irin kamshin dadi fuskan shi a,sake kallo guda,zakai mai kafahinci yana cikin yanayin farin Mama,Sa,a sai addua taje mai tare da fatan gamawa da duniya lafiya, da,sawa zurian shi albarka Tana kuma kara mai nasiha ya rike amanar da malam ya bashi don dacewar shi a hakan, Matar shi dai tana mashi ran shi don batada matsalan nan da mamake cewa wai tana dashi gashi Allah baibata haihuwa ba, a gidan su kuma haka take zaune da mahaifin shi, Gurin da nake zaune yarana duk sun haye min jiki ya duba yana muna kallon sha,awa da kauna yake cewa Muje kibani abinci na karya nace ok gani fitowa dama Ramatu ganin ya,sauko ta nufi falon don hada dining din, A kusan tare muka fito part dina dashi muka nufi dininng din don karyawan safe, Ya fita ya barmu nida matan gida acikin yar futinan boye sai fushi ake dani don may zan kai har wani lokaci tare da mai gidan, Amma kuma shi zancen a boye ake turawa juna ba,a fitarwa a fili, Sai bayan four na yamma ya dawo gidan duk jikin shi a gajiye yske don wani kauyen suleja suka tafi, Ya tara mu gaba dayan mu a falon inda yake dan kallon mu daya bayan daya,idanuwan mu kyam a kan shi don jin makasudin kiran, namu, Gyaran murya yayi abinda ya mayar da hankalin mu gaba,daya,gare shi kenan Sai kuma yai shiru tare da dan bin mu da idanuwan shi daya bayan daya kamar mai nazari, Suna hada ido da Salawatu tai wani dan gyara zana tana murguda baki, ina daga gefe zaune kasa saman carpet, Nadan girgiza kaina a raina nace, yar duniya ke nan ta Allah bataki ba, Yace inason zamuyi dan magana,daku na fahinta yanzun nan don zan iya cewa tun tafiyana zuwa gurin sabon ma,aikatana bamu samu zama daku munyi wani magana ba irin haka ba, sai yau din nan insha Allahu, Juyawa yayi gurin da Salawatu take zaune yace da ban garin ina ganin kamar andan samu matsala a tsakanin Meenatu da Salawatu wanda yanzu nake son kafin na,wuce anjima na, dauki mataku a kai, Gyara zama tayi ta na wani wani kara murguda baki azaton ta zai min cin mutuncine akan shiga,daukan key nabawa su Baba Wadda, Ya juya a gurin Salawatu din da kyau yana fuskantar ta face to face yace, Ki kara fada min zancen da kika fada min dana dawo garin nan akan Meenatu , Shiru tayi yayin da,muma din shiru mukayi muna masu sauraren ta don jin may zata ce, Jin tayi shiru yasa shi dagowa yana cewa ki fada mana muna,sauraren ki don mi san abin yi, Tace a cikin wani irin murya ai na fada ma duk abinda ke faruwa abinda akayi kuma, Yace adan hasale ki fada min yadda kika fada, ranan, a gaban ta don takaraji, Tace ni may kake so nafada makka ne a kai gaskiya nama manta zancen da mukayi, Yace look mrs ki fafi abinda kika fadamin nace ban son ki bata muna taime, a zaune, Tace a dakina tashigo wai sai na bata key din mota tabawa su Hamza sukai buduruwan su, Yace ehhey sai kuma may kika fada min again ? Tace, may na fada ma kuma ? Yace sauran zancen da mukayi dake a ranan mana ? Tace cikkin dan kada kai gaskiya bazan iya tunawa ba don na manta da sauran,, Ranshi a bace yace may kikace min tsakanin Hamza da ita Meenatu din, ? Da sauri kowa ya,juyo yana sauraren abind yake fadi , Sadiya tace gamay da hamza kuma may ke faruwa a tsakanin shi da Meenatu kuma ? Fatima tace sunyi fadane da Meenatu da hamza din ? Yaya Abubakar yace muna sauraren ki sai ki fada min don zan dauki matakine yanzun nan bako sai andaga daga nan ba, Shiru gurin yayi babu wanda yace uffan kowa idon shi yana akan Salawatu din muna sauraren ta don son jin may ta fada may akaina, Jin shirun yai yawa bazatai maganaba yasashi sakin dan guntun murmushi, yace, Yace kin kasa fadane kuma bayan ni kin fada min da farkogashi yau ina son daukan mataki, Yace tun ranan da kika fada min zancen naso na dauki mataki akai Amma sai naga cewa daukan mataki a cikin fushi baida amfana daga baya yakan zama dana sani, ne, Tun ranan nake nazari akan zancen inda na fahinci cewa da wuya ace Meenatu taci amanata irin haka ? Badon komai ba,sai don sanin irin tarbiyan da tasamu daga gurin iyayyen ta duk da nasan cewa shi mutum yakan canza rayuwan shi wani lokaci can daban,, Sai ya,dan saki guntun murmushi yace Salawatu wanan zazzafan kishin naki yana iya saki kashe mutum idan baki daina irin sa ba, Yace ni da kaina nai nazari nakuma gane cewa duk sherine yasaki yin hakan, Da kinsa na batawa mutim dubu rai akan wanan nan mumunan zancen da kika shirya, Ace wai Meenatu tana hurda da yaro kamar Hamza wanda na sakewa a wanan gidan, Innalillahi su Sadiya suka,sake a lokaci guda ita da fatima, Fatima tace kai mutum mutum dan sherine har yaushe take da time din wanan ita da laluran yara yana sha mata kai, Salawatu tace wanan don Allah ya wuce duk sherin shedan ne dama, Nadago kai na kalli gurin da take zaune nace nabarki da kudiran ubangijin mu shi zai saka min agareki, Nace ni babu wace nake adawa da ita daga cikin ku duk a matsayin yan uwa nake daukan ku, Don idan yau wani abu zai samani kune mutane na farko da zaku fara bani kulawan ku, Hakan nima dole idan haka ya cika daku nice ta farkon baku nawa kulanwan, Duk zancen da muke shiru Salawatu tayi kallallahu batace wa kowaba, Yace don haka wanan zancen dake Meenatu kikayi aiya wadatar don shi Allah ba azzalumin kowa bane, Daga haka taron ya,watse kowa da,abinda yake fada a fili da boye sai da ya kara ja muna kunne cewa shi bazai lamunta da irin wanan cin fuskan ba agidan shi, A ran ya,sa kai ya koma gurin aikin shi don tdare doka aiki,

ZEEE MAKAWA YELWA SEENABU

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣1⃣8⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAHUMA AJIRNI MINAL, NAR,,👏👏👏

Kwata, kwata Salawatu tafi ta daga rayuwana saboda nasan cewa zata iya kasheni da sherin ta,, Wanan dalilin yasa Anty Amarya warning dina,sosai a kanta dagani har yarana, Tun tana wani dan fuskewa har tagane cewa nafita zancen ta takoma normal, Duk wani abinda zai shiga tsakani na da ita na daina shiga harkan, ta ta ko wani fanni, Amma,gaisuwa irin ta,addini munayi da ita wani lokaci har zata,ce ko ina da,abu kaza a part dina na bata, zatayi amfani dashi, Duk na fahinci cewa sherine kawai nagigagun bariki take son gwada min bata san cewa mu matan Kebbi da wayon kishin mu ake haihuwan mu a duniya, Amir ya isa sakawa makaranta,don haka wanan shigowan da uban yayi bai tafi ba,saida yaga ya,saka,a,makaranta, yafara zuwa, sanan ya,shiryayakoma, Abubuwa yanzu sai kara bunkasa suke wa Yaya Abubakar fiye da dacan baya, don yanzu yana da tatin dukiya mai yawa, Nagodewa Allah don tana taimakon mutanen gida sosai, don mutum ko ba acikin zurian mu yake ba idan rabon shi ya ratsa gare shi yana samu alheri daga gare shi, Gashi ya bude guraren saida abubuwa kamar motoci, gurin buga ruwan goruna, saida kayan motoci da injuma kalala duk a cikin garin Abuja, Ya,samo matasa masu yi mashi wanan business din daga can gida Birnin kebbi, ya zuba gurare daban daban su suna samun nasu rabon dagagare shi,, Business nakeyi ana saro min kaya daga kasar waje ina aikawa sokoto da Birnin Kebbi a sayar min da idan wata uku ya cika na hada kudi sai na kara turawa a,sayo min, nakara bayar wa, Sai sanar sayar da abubuwan kasar hausawa irin su yaji daddawa da busassan kubewa da bussashen karkashi, kifi bussashe sai ayi parked din su , Maman Biu itace ke min wanan business din a gidan su, kuma ana,saya sosai,, Nakan,yi business din hada kayan aure wa mai bukatan hakan daga ko ina,sai na hada ma komai da kake bukata na kayan lefe, Alhamdullahi do sosai abubuwa na,suke ci gabada yardan Ubangina Allah mahaliccin sanmai da kassai,

****** ********** ****** Barci nake amma sai nake jin ihu kamar a mafarki da sauri na bude idanuwa da aukai min nauyi a lokacin, Tabbass ihun a cikin gidan mu ne yake fitowa abinda ya,sakani saurin zuro kafafuwa dake a cikin bargo a rufe da sauri zuwa kasa, A falo na mu ka hadu da Ramatu take cewa, a cikin tausa muryan ta Hajiya, wanan ihun kamar daga gurin Maman Aina na ke jin fitowan shi, A tare muka fito falon inda mukayi kicibis da ita sabale da yar ta a kafada a cikin rikicewa take cewa don Allah ku taimaka min ku tai makeni kada ta mutu, please, May yafaru ? May ya samay tane wai, sai kuka take tana kokarin nufar kofan fita,daga,gidan Yar aikinta tana biye da ita, abayanta, itama din a rikice, take duk ta rude, Wai may kefaruwa ne Maman Aina, nace cikin dan daga muryana a rikice, Ta,dago jajayen idanunwan ta da,ruka rine sukayi jajir don kuka da tashin hankali, Jin yar ta,sabale mata a hannu yasa ta,saurin nufoni ganin ta nufoni yasa ni nima nanufe ta, Inda ta miko min yar na tara hannu na karbe ta dagahannun uwar, Idanuwan yarinyar a kakafe suke alaman ba rai a tare daita, Wani karata sa lokaci guda tare da zubewa kasa, tasa kuka, Da sauri na juya gurin Ramatu nace dauko min cibi da manja da gishiri da,sauri, tare da albasa, Dagudu Ramatu ta,shige kitchen ba,afi yan mintina ba sai ga ta da duk wani abinda nace ta dauko, Da,sauri na karbi spoon din na bude bakin yarinyar daidai tsakiyar nabar spoon din a gurin, Nace acikin tashin hankali Ramatu hada dan manjan da gishiri kadan ki miko min, Tana hadawa ta miko min na bude bakin yarinyar na tura mata shi ya,wuce, sosai, Nace daga albasan ki bani da sauri yauin da nashiga keta rigan dake jikin yarinyar wce take a hannuna kwance shabal, kamar ba,rai ido a kafe, Duk jikin yarinyar na,shafe da wanan albasan da aka dan dagaka min Sai mukaji yarinyar tai atishawa, a lokaci guda tare da fesa wani irin zawo mai warin, gaske,, Sai ta,sa kuka,sai dai duk muryanta a,shake yake bai fita sosai na kara daukan albasa ina kara,shafa mata har cikin kunnuwan ta saboda yadda jikinta yai mugun zafi a lokaci guda, Lokacin ne Sadiya ta bude kofan ta ta fito daga dakin ta tana cewa wai may ke faruwa ne, Nace Ramatu miko min waya nakira su Hamza muje asibiti yanzun nan, Sadiya tace bata da lafiya ne nace eh duk jikin ta yai mugun zafi shine conboltion ya kama ta, Munyi kiran waya duk layin su Baba a kashe yake na mike ina cewa bari na canza riga don wanan ya baci da kashin da tai min sai mu tafi asibitin, Sadiya tace yanzu karfe biyu fa da wani abu na,dare zakubi hanya mata da ku Abinda ban taba yi mata ba nai mata yau fon juyowa nayi nace a kaikaice, Allah zai kare mu, Nashige part dina don ta bani haushi a matsayin ta na uwargida wanan abin yana faruwa agida maigida bai a gari amma tana ji taki fitowa sai yanzu, Ni gaskiya sam ban son irin wanan rayuwan irin na matan gidan mu su kishi dai har da karamin yaro sai an saka a ciki al,amarin kishin gida, Nafito acikin dogon riga da hijab har kasa dauke da yar post dina dana,saka kudi a cikin sa da wayana, Nace wa Anty Nani tazo ta rufe gida idan mun tafi don da Ramatu zamu tafi saboda ita Fatima bata,da wani kuzari a tare da ita, Muna,gab da,fita,Salawatu tafito tana,cewa ina jin hayanita,samasam May kefaruwa ne wai, dan naji hayaniya daga,dakina, Sadiyace ke cewa,baby ce bata,da lafiya,zasu tafi asibiti wai, Da,sauri Fatima ta juyatana kallon Sadiya,din amma sai ta daure taci ga da tafiya Ramatu tana dauke da yarinyar a jikin ta, A hankali nake jan motan Fatima tana daga gefena a cikin tashin hankali, Ramatu da,yar aikin Fatima abayan motan dauke da baby din, Babu kowa,a hanyan sai kar nuka,da hasken fitilun titi daya haske ko ina,na,garin Muna tafe bakina da,addua har Allah yakaimu lafiya asibitin ba adauki lokaci ba akabamu gado a pediatric, Duk abinda akace a saya na,saye a cikin daren nan aka fara yiwa yarinyar treatment, Muna zaune zugum yayin da yarinyar ta samu barci,, Norse ta,shigo dakin tana cewa ku dan rage yawa kada ku hana ta barci please, Na mike ina cewa Ramatu tazo ta rakani nayo alwala don dare yayi a lokacin, asuba ya kusa, Norse din tace idan yarinyar ta tashi baki kusa ta,saka ihu fa? Najuyo na zuba mata idanuwana banyi magana ba, Tace a fusace cikin masifan su na malaman asibiti, Ba kece uwar yatinyar ba ina magana kin xuba min idanuwan ki kuma, Yar aikin Fatima ce ke cewa a,a wallah kishiyar ta,ta da diyan, A cikin mamaki ta juyo tana cewa kishiya ta kalleni ta kuma juya ta kalli, Fatima wace duk a rude take don fargaba da tashin hankalin da tashiga ciki, Muna gurin a zaune inda nai sallah ni da Ramatu har akai kiran sallah asuba , Inda mukabi massalacin asibiti jam,i muka kai wani lokaci a zaune muna addua, Muna a kofa zaune likita ya,shigo da safe don duba yarinyar Jin yace mu shigo yasa gabana,faduwa fargaban abinda ke shirin faruwa ya kamani a lokaci guda, Ina shiga,dakin yake ce min hajiya munq bukatan jini akarawa yarinyar nan, nan da awa daya zuwa biyu, Idanu na zare a tsorace ina cewa jini likita ? Yayin da ya kada min kai yace kwarai da gaske saboda haka sai a maida hankali akawo muna da,wuri Gaba dayabayan fitan likita shiru mukayi dakin kowa da irin abinda yake kiyastawa a ran shi, Nabude baki da nufin yin magana ke nan aka turo kofan dakin gaba dayan mu duban mu ya koma a kofan dakin , Nurse ce ta dawo dauke da takardan da likita ya kara,rubuta magani a,cikin sa tajuya zatafita, Har takai kofa ta rike handle din kofan ta juyo tana cewa au na manta ai likita yace na,fada maku ayi sauri fa a,samu jinin don yarinyar tana bukatan jini, Bayan fitan nurse din nabi kofan da kallo tare da,sauke ajiyan zuciya, na, Ina,juyawa don nai magana sai naga Fatima tana kuka gwanin ban tausayi, Nace cikin kwantar da muryana haba dai Maman aina may ye na kuka kuma anan dan Allah, Yanzun ni inda zamu samu jinin nan yafi damuna don shine abin yi da,sauri ake bukatan jinin, Na taka zuwa bakin gadon da yarinyar take kwance, ina mai kura mata idanuwa na na,tsawon wani dan lokaci, Nabude yar jakata na ciro wayana ina kokarin neman noban Hamza da Baba Wadda, Kira daya,ana biyu yadag,wayan da cewa Anty barka da,safiya ya su Amir, Nace Baba,dan Allah ko Baba Wadda yana kusa ka,bashi waya, Baba Wadda ya karbi wayan yana cewa Meenatu lafiya dai ko nace, Baba muna asibiti tunda dare wallahi, Subbahanallahi naji yana fada tare da cewa waye baida lafiya kuma nace mai baby ce yar gurin Fatima, Nan nake fada masu abinda likita yace sai cewa sukayi gasu tafe yanzun nan isha Allahu, Nace bari naje sayen magani kafin su iso mugani yadda za,ayi,, Leda tab da magani da su sirinji da su needle da carnular, Shigowa dakin duk ya mayar da hankalin su gareni ina,aje kayan nake cewa har yanzu yarinyar bata farka ba,ko, Uwar tace ta dan bude idanuwan ta sai kuma kuma ta rufe don da gani tana jin barci sosai, Sallaman su Baba mukaji abin mamaki su Baba Wadda ne tare da sauran abokanan su sunkai su goma nske gani duk da ban tsaya kirga yawan su ba a lokacin, Sai ya mai jiki suke kokarin yi muna tare da fatan Allah ya bata lafiya, Sai Baba Hamza ne ke cewa mutafi gurin awo a auna mu agani ko za,a samu jinin ko, Allah ya rufa muna asiri don asamu mutum biyu da za,a iya diban jinin su , Anan na biya nai komai da yadace, ayi kafin nabar girin, Ina,shiga,dakin da yarinyar take a kwance ne Fatima wacce ke dan kishingide rike da hannun yarinyar tai firgigit ta mike zaune tana cewa tau yaya anyi nasara dai ko an samu, Gaban ta na kara ina kokarin zama a saman farar kujeran roban dake dakin inacewa Yaya yarinyar ta farka,ne daga barcin halan don naga kin rike ta, Tace ta farka tana cewa wai abata ruwa da,sauri nace inji baki bata ba,don kinga ga,drip a jannun ta Tace min cikin kura min kumburarun idanuwanta da,sukai ja ai ban yarda an bata ba, Ina zama naji muryan Fatima tana cewa kin ko samu kin yi breakfast Meenatu, Nace cikin dan murmusawa bari har a,saka mata jinin mugani sai na je gida naiwanka idan na,dawo sai keki tafi ki dan watsa ruwan, Nace balle nasan Ramatu ta tsaya tayi aikine da kuma dan abinda ya,dace tunda tasan cewa muna nan,dole ta kawo muna abinci, Tsaki naji taja tana yayin da ta juyo inda nake zaune tana fuskanta na tana cewa yanzu Meenatu saboda tsaban kiyayya har zamu zo nan mu kwana amma ace babu wace zata,zo dubamu daga cikin wa yan can mata,, Nace ai zasu zo kin san sai sun gama kintsawa tukun kafin su shigo, Nace ai shi al,amarin ciwo yana akan kowa balle ciwo na yaro, don shi yaro ai na kowa ne, A yadda na lura maganata yadan sa jikin Fatima yai sanyi da zance na don haka itama taja bakinta tai shiru kawai, don dama bacin raine, ke damun ta da damuwa,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull