Tarko complete novel - Chapter 124
Tarko complete novel Chapter 124: Tarko complete novel Chapter 124. ****** ********* ****** Kwanan mu biyu da yarinyar a,asibiti aka bami sallama,don jikin…
3,294 words
****** ********* ****** Kwanan mu biyu da yarinyar a,asibiti aka bami sallama,don jikin nata,yayi sauki sosai yanzu sai dan kwadayi da,takeyi kawai, Sadiya ta,shigo asibitin duba yarinyar tun ranan da akaba da gadon da yamma ta,shigo, Salawatu ce sai ranan da akai sallama tazo gudu guda batako kai minti biyar ba ta juya ta koma wai tana,sauri, Ranan da muka,dawo ina zaune a dakina na idar da,sallah magrib sai ga,Fatima,ta,shigo dakin da sallaman ta, Nakarba mata ina mai tambayanta,da cewa ya maijikin dai ina fatan dai ta,samu barci don naso shiga barci ne ya,daukeni dazun, Yanzu kuma ina zancen idan na idar sai na, dan shiga na lekata, Fatima dubini tare da busar da,iska daga bakin ya tana cewa a cikin wani irin murya Gaskiya ban san yadda zan maki godiya ba,a,gidan nan, Don kin min abin da ban taba zaton cewa zan samay shi agare ki bada farko, Sai gashi kin min abinda ko yar uwatace da muka fito a ciki daya,bazata iya yin min hakan ba, A cikin dare kika,sadaukar da rayuwanki muka bi hanya hakana zuwa asibiti, Meenatu ni ban san may zan fada maki ba gaskiya akan hakan, Murmushi nayi na dan girgiza kaina ina cewa haba Fatima kin manta cewa Baby nima yata ce , Diyar yayana ne fa diyar kuma abokiyar zamata don haka kinga, ashe dole na damu da damuwar yarinya,, Allah ya kara bamu hakkurin zama Meenatu nagode nagode kwarai wallahi, A cikin murmushi nake cewa haba,dai Allah dai ya raya muna yaran ya,sa masu albarka, Ta ce a,sanyaye Ameen ya Allah dama yaya Aliyu ya fada min cewa baki da,matsala idan na,fahince ki gashi naga zahiri sosai, A tare muka fito daga dakin nawa zuwa part din ta don muga yadda jikin yarinyar yake, Salawatu wace ke zaune tana wayata kura muna ido sai kuma,ta kawar da kai gefe taci gaba,da,wayan ta, Acan cikin zuciyar ta sai cewa tayi ai kuwa zamu ganku a fili a gidan nan, Ni dai dama ba,wani dogon shiri a tsakanin musai kawai na,share tankar ban san da ita ba a gurin
Bayan na,dawo daga dakin Fatima ne sai nake tunanen how, comes za,ace dakin Fatima a haka matar da na,sani a baya,dason tsabta sosi, Anya kuwa Yaya Abubakar ya,duba dakin nata yaga cewa,tana bukatan tai mako, Don haka na sawa rai na cewa insha Allahu zan mai magana,, Ya,iso garin kamar yadda ya,saba zuwa muna sai dai wanan karon yazo muna da tsaraba kala,kala, daga can din , A gurin rabon abubuwan da Yaya ya shigo muna dashi ne ina daga,daki naji muryan su fitina ya,kaure a tsakanin su, Abinda ya jawo duk hankalin wanda ke agidan ke nan a lokacin inda muka nufo falo don ganin may ke faruwa a lokacin, Shima maigida dayake daki tare da Sadiya a lokacin ya fito, a cikin fushi yake daka masu tsawa da,cewa Kai, kai kai, wai maye hakane please may ke faruwane anan ? Shiru sukayi gamu a tsaye cirko cirko muna kallon su ga kayan tsaraba agaban su, Yace tambaya nake may ke faruwa ne haka wai , Salawatu tace a,cikin muryan nan nata ni wallahi, baki isa ki saka min waigi a gidan nan ba,don kiji, Ita koma Fatima daga gurin da take a tsaye sai huci take, ta watsa wa Salawatu harara tare da jan tsuki tana cewa, Idan har baki dani ba bari kiji bude kunnuwanki da kyau ki saurare ni , Ni duk kar nake kallon kowa a,gidan nan don nasan maigaskiya,na,san macuciya don haks ni dadin bakin ki bazai rudani ba agurin nan, Kina gani kamar cewa bamu san zalunci ki ba a gidan nan tsinaniya kawai azzalúma mai shiga tsakanin masoya da karfi da yaji, Shigowanki duk kin canza dan bawan Allah kin mayar dashi dan bi can ko nan, Kinzo kin halatta rayuwanki a cikin kananan yara wai kina,kuntatawa mutane daga mugun sherin ki, Wallahi ta Allah ba,taki ba don bazaki taba iya raba kowa da gidan nan ba A zuciye ya Yaya Abubakar ya daka masu tsawa da cewa ban son hauka don wanan haukan xa tashin hankalin naku ya isheni a gidan nan Banda wani kwanciyan hakali duk lokacin da nazo gidan nan sai, weekend sai kun samu jidalin da kukai min, agida, Ni wanan halin ya isheni, zan dauki mataki akan duk wace take kawo min yawan fiti na, a gida Kai nagaji wallahi bafa ku kadai bane matana a gidan nan, Yabisu daya bayan daya da harara yana cewa kawai saboda baku da mutunci zaku mayar min da gida,gidan yan kokuwa, haka, Tsaban balain da kowan su tagani a idanuwan shi yasa gaba dayayin shiru batare da sun tanka,mai ba Kallon mamakin irin zagin da yake fita a bakin shi , take yi Lalai duniya mutum baida halarci yanzu Abubakar wanda ta sani abaya baida wace ya ke so da kaunar tankar ita, Yau gashi Allah yahada zaman su kuma gashi abin yazo da akasi sosai a tsakanin su, Abubuwan su na,daure mata kai sosai don duk wani abinda ya dace tayi akai tayi amma,abin yaci tura, Duk inda akace ga wani malami mai tashe a gari sai uwar ta ta,tafi mata don dai kawai a samu kan mijin nasu amma abu ya faskara, Yanzun ma abin duk yakara, tabarbarewa a tsakanin su don sam ba wani dadin zama da taje ji a,gidan, don tana iya,cewa kamar kada,yaranta,su bar gurin ta,sai abubuwa suka kara kwabe mata a gidan, Ya kara cewa a cikin tsawa wanan kayan da kukewa fada,badon ko wace mace na,sayo su ba don yara na,sayo masu zuwa makaranta da snack da irin wanan abincin, Da,guda daguda suka bi umurnin shi suka,watse a gurin rabon da ya hada su fadan, Har zasu fara tafiya yace Wait ban son na,kara jin wani hayaniya daga gare ku maka,mancin hakan, Idan ma,wani abin ne na zo dashi, ai bakece zaki sa a raba ba Sadiya ce ko Meenatu zasu ce araba a gidan nan, Salawatu tace a,cikin bacin rai tunda ka,fada,muna na yaranka ne ba shike nan ba sai abawa uwar yaran, Fuskan shi a,daure ba sauki a cikin sa ya kara tsare gida yace 'eh, na yarana ne, and so what, Ta zuba masa ido yayinda take jin zuciyarta ta shiga girgiza don ba makawa Abubakar ya canza mata fiye da tsanmanin ta, don haka sai ta,hade rai, tashige part din ta rai a bace, Tana tafiya tana cewa yanzu na fahinci cewa, yaran ka da uwar su sufi kowa a,gidan nan shiyasa kake kokarin wullakantani, Inda yabi bayan ta da kallo mai kama da harara, tare da girgiza kan shi don ta kaici, Daidai lokacin Sadiya wace take tsaye daga gefe tana sauraren ikon Allah take cewa , Wanan abin ma ai da,ake fada akan shi aina yarane, ko Ya juya don ya,shige yaji muryan yar aikin na Maimu fadi ba,a tambayeki ba tana cewa, Dama ita antyn Abuja zata kai dakintane shine maman Aina take cewa, ba a yarda,ba,sai a aje araba abawa kowa nasa, Na wurga mata harara daga inda nake tsaye ina cewa tau fadi ba,a tambaye ki ba, Ta dan yi kasa da kai fon kunya tashige ciki ta baya batare da ta kara tsayawa gurin ba, Zancen da Maimu tayine ya tsayawa Yaya Abubakar a rai yana tafiya yana cewa ita Salawatu dai komai ta handamay ita kadai a gidan nan Gaskiya irin wanan rayuwan na Salawatu baijin cewa zai ita,daukan su nan gaba, Gashi fitinan ta yai mashi yawa komai sai tace sai ita kamar ita kadaice mace a gidan,
****** ********** ****** Ranan muna tare da Yaya a, dakin shi, laptop din shi yake dubawa, Ina tsaye na dan zauna gefen side drawer kadan fuskanayana fuskantar shi ga abinda yakeyi, Nace Yaya dama ina ta,son nace ma don Allah ko zaka sayawa Fatima,wasu kayan daki don naga nata,sun dan samu matsala, Abin da yake a system din shi ya,bari yadago kan shi yana min wani irin kallon mamaki, Na,daure fuska na na nuna mai ba wasa a zance na ko kadan, Yace ba,a tare akai maku kayan ba da ita yaya akayi nata ya riga na kowa lalacewa, Nayi shiru ban tanka mashi ba yace ita,bata san yadda zata,kula da kayan ta bane, Nadago a hankali nace ba hakana,bane yaya kasan a lokacin dakinta,akwai yara masu wayo ina ga,shi yasa yafi na kowa lalacewa, Shiru yayi bai tanka min ba da alama zancen ya bata mai rai sosai, don naga ya kasa,furta komai, Na mike daga gurin da nake zaune ina cewa kayi hakkuri yaya don baidace ace wanan kayan sune kayan dakin matar ka ba acikin gidan nan, Daga haka nasa kai nafito daga dakin don zuwa na karasa sauran aiyukana danakeyi a waje Bayana yabi da kallo tare da,sauke numfashi yana mai furza da iska daga bakin shi a cikin takaici, Bayan kwana biyu da ya kara,shigowa,garin ne ya taramu a falo yake cewa yana son kowan mu ta,kwashe kayan dakin ta za,a canza kayan daki, Salawatu ta kasa boye murnan tace kai, thank you my dear wanan labarin yau yai min dadin ji wallahi, Yace No ni wanan ba ra,ayina bane ra,ayin Maman Amir ne gata,nan, Atake murnan taya koma ciki ta na ce wa gaskiya ai da shawara muka taru mukayi kafin a yanke hukumci ko, Yace OK ke bakya bukata ke nan ko, yace idan baki manta ba ina kece kika saka a sayo wa yan nan dake dakunan naku, Shiru mukayi yinda yace ita bata ce na,saya daku ba ma kawai a, Fatima tace na,saya Nine dai naga dacewan canzawa gaba dayan ku don hakan yana da kyau, Da sauri Fatima ta,dago kai tana duban gurin da nake zaune a saman ties ina gyarawa Amira kai a hankali na dukar da kai tankar banganta ba naci gaba da abinda nakeyi kawai, Muryan shi naji yana cewa sai kuma abu na biyu ina son kuyi shawara naji don zan fara zuwa da ku can saboda ina da bukatan hakan, Shiru gaba dayan mu mukayi babu wace tace uffan daga cikin mu sai Salawatu ce tace to a gaskiya ni shawaran da zan bayar anan shine, Yace shout,up my friend kece zaki soma magana ko su don ke baki a cikin wanan tsarin a yanzu, Na dago kai da,sauri daga parking din da nakewa yarinyar nace nima gaskiya bazan samu wanan abin ba,saboda yaran nan, Fatima tace a,a Meenatu zancen yara bazai hanaki zuwa ba kawai dai yanzu a kawo shawaran yadda za,ayi kawai, Muryan Yaya Abubakar naji yana cewa idan ke baki bukatan zuwa ni ina son zuwa da yara a kusa dani don shiru ya isheni haka a gidan, Banyi magana,ba sai dai a gaskiya na,sa a raina cewa bazan tafi ko ina ba don bazan iya wanan taulalin tafiyan ba gani da yara har hudu duk kanana, Ranan da dare mukayi fitina dashi a kan zancen tafiyan inda yaya yai min wullakanci tare da nuna min bacin ran shi a fili, Yace wani irin son kai ne gare ki haka da har ba zaki tausaya min nida yarana mu zauna a tare ba da zaki ce wai ke bazaki tafi can ba , Kina nufin idan har nace dake kawai zan tafi can din akwai wanda ya isa yace a,a, ne Na dago kai na kalle shi idanuwan shi sun yi ja sun baiyanar da bacin rai mai tsanani Har ya karaci fadan shi ban ce uffan ba akan zance don nasan cewa banda gaskiya to amma ai ina da dalilin haka, Don nafi bukatan ace suna nan arewa kodon su samu tarbita irin na yaran hausawa wanda shi al,adan ba haushe tafiya yake da addini sai dan banbanci kadan daga ciki, Idan kuma na kwashe su zuwa can kudu karatun addini fa, ?
ZEEE MAKAWA YELWA SEEENABU
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣1⃣9⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAHU GAFURUL RAHIMUN,,,,,,,
BAZAN TABA MANTAWA DA KU BA YAN UWA MASOYA MEMBES HUGUMA NOVEL GROUP, HUGUMA CONVERSATION, HUGUMA FIST CLASS,,, NITAKUCE HAR,ABADA DON DA BAZARKU NAKE RAWA ,,,,
Tafiya ya hau kan Anty Sadiya kamar yadda maigidan ya tsara cewa zamu dinga retetion a tsakanin mu n three three months, Don haka sai ban damu ba nake ganin cewa wata kilama kafin zuwana yazo abin ya canza, ai, Harkokina nakeyi bandamu da wani zancen tafiya ba inda ita sadiya sai shirin tafiya don bin maigida can kasar ibo takeyi, Kwana,biyu zai shigo Abuja kamar yadda ya,saba zuwa muna sai kwatsan tafiyaya riski Sadiya , Maihafiyarta bata da lafiya sosai tana asibiti a kwance inda sai kiran sunan Sadiyan take a lokacin, Sam Sadiya bata so zuwa ba amma sai malam tsoho ya bugo waya cewa duk abinda takeyi tazo Birnin Kebbi su gana da mahaifiyar ta, ALlAH ke nan shi kadai kayin yadda yaso don haka sai kwatsan tafiya yadawo a kaina ni Meenatu da iyalina, Wanan abin yai matukar tayar min da hankali sosai don abi yazo min a bazata ban taba zaton cewa hakan zai kasanceba, Hanakali na,gaba dayaya daga gashi hakan doka ne daga maigidan, Damu yafara,shigana akan zancen tafiya don in har akwai abinda na tsana to shine zancen zuwa kasan IBo da akeyi wai na tafi,, Badon komai yasa bana son zuwa ba sai saboda ina tsoron irin tarbiyan da yara zasu tashi acikin sa a,sakamakon zama acikin arna da zamuyi, Sai zance jama,an da nake zaune tare da,su don ban tsan manin cewa zamu tafi gaba dayan mu, A daren da zancen yazo min ranan na zauna da Ramatu da Antyn Nani harda Maimu, Nake cewa koda yake bawai na tabbatar da zancen tafiyan nawa bane, Amma dai duk da haka ya kamata muyi magana akai idan akwai wace taga cewa bina zai jawo mata wani matsala a rayuwa sai tai magana duk da ban san cewa ko da kowa zan iya tafiya ba, Sai ce min sukayi zasu tuntubi yan uwan su don suji, Ramatuce kawai tace min Uwar dakina ni ai bazance ba zani ba don zama dake shine rufin asirin mu, Idan har ban biki ba ma may zan tsaya nayi anan tunda bakya gari su yaran na duk mazane kinga ba zama suke dani ba idan ma har wani matsalane aiga waya sai muyi magana dasu, Naji dadin Ramatu sosai a raina don matar yar amnace ta san zama da mutane, Shiyasa sam ban yarda ko kadan na,samu matsala da ita don dai ahaife ta haifeni gashi kuma ita ba wata mai hayaniya bace, Hakan da na,sani yasani kara sakata a jikina tankar wata yar,uwata nake daukan ta, Wanda wanan itin zaman da nake daita yake ba yan gidan mu haushi sosai har sayran masu aikin nawa musan man Antyn Nani, Don sai tske gani itace ya dace nabawa urin damar dana bawa Ramatu din, Amma sai taga ni nafi saka Ramatu a,gaba fiye da ita dana fahinci haka sai nazauna da ita na fahintar da ita,sai ta sake zancen hamaiya a tsakanin su da ita, Ganin cewa fa tafiya tabbas ba fashi a gareni yasani samun maigidan don mu sulhunta ya tafi da wata can, daban bani ba don sam ban ra,ayin wanan tafiyan a raina, Saboda, kasan bai min ba a raina gashi kuma zan tafi nabar abokan arzikina a nan Can ko babu wanda na sani kuma gashi ance babu hausawa a kasan,
****** ********* ****** Na shirya a cikin wani lalausar material ja da fari wanda akai min dan wani dogon riga dashi, nai rolling din kaina da wani gyale mai laushi jan kala, shigar yai min matukar kyau sosai, A,gaskiya ni ba dabi,a na bace shiga turakar maigida idan har banice da girki ba, sai dai idan har wani abu mai matukar muhin manci ne zai kaini, Duk da Fatima ko Salawatu basu dauki yin hakan a wani shiga hakki dan uwa bane, Amma yau ya dayake ina,son yin siri tsakani na dashi don haka dole na,shiga part din nashi, ,,, Baki dauke da sallama yayin da nake tsaye daga kofa ina kwada sallama don naiman izzini, shiga, A lokacin yana tsaye a bakin mirror dakin shi yana kokarin daura agogo a hannun shi na haggu, Jin murya na yasa shi saurin juyowa da mamaki yana kallo na tare da bani izinin shigowa dakin, Saye yake a cikin wani farin yadda mai laushi da taushi dan kasar Pakistan, A hankali na karaso har gurin dayake tsaye a hankali inda tako kadan tsakani na dashi na dan ja na tsaya daga nesa, Cikin murya mai tsushi nace mashi barka da,warhaka Yayana ya amsa min fuska a sake tare da kokarin gyara kwalar rigar sa, Nace cikin kara tausa muryana dama nazone muyi magana dakai, ajan zancen tafiya na zuwa, can kasar, Sai nai shiru kuma,saboda na rasa may zan ce akan zancen da nazo dashi tayaya zan iya fada mai cewa bazan tafi ba, Muryan shi naji yana cewa Ummhummm ina sauraren ki ne fa, Nace cikin dan kara marairaicewa Yaya dama sai naga kamar da matsala a tafiyan nawa, don sai naga ,,,,, Sai kuma nai shiru yayinda ya juyo ya kura min idanuwan shi da na hango saurin su zuwa bacin rai a lokaci guda, Yace ke nake saurara daga ina matsalan ya taso da kike gani, nace yayin da idanuwana suka fara tara hawaye, Nace gani nayi cewa muna da yawa a part dina kaga yin tafiyana na barsu a nan akwai matsala kuma can din idan na tafi wa zai kama min wasu aiyuka daga ciki, Yace look Meenat ki fito stret to the point ki ce min baki zuwa yafi wanan kwana kwanan da kike yi a yanzu, A take sai naji idanuwa na sun kawo ruwa saboda wani irin rashin dadi da,naji a zuciyata don nasan cewa ban samu wanan damar ba Nace cikin kuka ni bance ban, zuwa ba kawai dai gani nayi ga yara ga kuma mutanen danake zaune da su, a part dina tare da ni,,, Yace daga cikin su akwai wace tace bata zuwane ? Nan ma shiru nayi ba amsa gareshi ta gefena ya dan bi ya gewaya zuwa kofa yana cewa ina son na san ko mutum nawa ne, tafiyan don a yanko tickets, yau din nan, Nan ya,barni tsaye tsakar dakin rai a bace na rasa yadda zanyi saboda takaicin da nake ji a lokacin, Bayan shi nabi jiki ba kwari ina tafiya a hannkali zuwa part dina,
****** ********** ****** Na kai wani lokaci zaune a dakina kafin na kira duk wani wanda ke tare dani a part dina, Nai masu bayanin cewa tafiya ya fado a kaina, don haka nake son ji idan akwai wacce bata da sha,awan tabini zuwa can sai naji, Gabadayan su shiru sukayi babu wace tace min uffan ina cikin sauraren sune Alhassan ya shigo inda nake ya zauna a jikina yana kukan yana son shan tea don shi wanan halin sai ince halin yaran dakinane shan tea a koda yaushe, Antyn Nani ce tace gaskiya hajiya bansa rai cewa zan samu binku har can kasan ibo din nan badon wani abun ba sai don haka kawai, Nace kefa Ramatu tace haba yo hajiya idan nace bazan tafi dake ba may zan tsaya yi a nan din, Ba wai ina da wata diya mace bane a tare dani da zance bazan samu zuwa ba, Tace yaran nan duk mazane ba zama suke a gari ba don haka binki yafi min kwanciyan hakali da zama a cikin wa yan nan kishiyoyin naki,, Don haka na juya gurin Maimu, nace kefa Maimu zaki tafi ko na mayar dake gida,? Tace Anty nikan ai zan tafi ko don naje naga gari nace acikin dariya kai Maimu Allah dai ya gyara da halinki ta fita tana dariya, Babana Wadda yace ai tashina tashin ki daughter na bazaki barni ba, sai shi ma Hamza yace balle ni, dani za,a tafi,