Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 125

Tarko complete novel - Chapter 125

Tarko complete novel Chapter 125: Tarko complete novel Chapter 125. Sai da ya shigo cin abincin rana yana zaune a fali dauke da yar gurin Fatima a hannun…

3,413 words

Sai da ya shigo cin abincin rana yana zaune a fali dauke da yar gurin Fatima a hannun shi don itace ranan da girki na shigo falon Fuskana bai dauke da fara,a ko kadan na samay shi a zaune a hakali nake mika mashi sunayen su, Bayan ya gama karantawa ne yake cewa, ita mai renon yaran fa ko bazata tafi bane nace eh haka tace, yace OK sai a samu wata ke nan ko? Ban ce uffan ba ina daga gurin da nake a tsaye yar dake hannun shi take dan zillowa tana don wai na dauke ta badon komai hakan ya kasance ba si don duk a cikin mu ni kadai ce mai daukan ta tun uwan ta ba ta son ina daukan mata ya har ta yarda tabar ni ina daukan ta, Yau da yake ban a cikin wallawala sai na dan kai hannuwana a daidai kumatun ta na dan lakata kadan ina cewa ki zauna a nan bazan dauke ki ba dai, Daga haka na juya zuwa inda nafito rai a bace Yaya Abubakar yadan bi bayana da murmushi yana jijiga kai acikin jin takaici,

****** ********** ****** Ramatu ce ke shiri don ni komai ma na kasa shiryawa a lokacin don yanayin da nake a cikin sa, Ina kwance a daki waya a hannu na ina fadawa Anty Amarya yadda mukayi a akan zancen, Sai faman yi min nasiha takeyi tana cewa daga wanan kada na kara cewa wai don yara bazanyi abuba , Take ce min hakan yana mayar da mace baya ne a,gurin maigida don haka na zage a kan komai kada na bari a barni a baya daga yau, Nan take ta fada min yadda zan kara zagewa dakuma abinda zanyi idan har munyi tafiyan don kamar gasa ne tafiyan namu zai kasan ce, a can din Don kowa da irin halin rayuwan ta zata tafi garin a zauna da ita tace don haka kinga wace yafi jin dadin zama da ita itace zai fi sha,awan ta dawo, Nan na fahinci cewa zamane kamar na wani gwaji zamu tafiyi a can din don haka sai na shiga shirin daukan duk wani abin da nake bukata a lokacin, Ramatu tabani mamaki irin yadda ta shirya muna komai namu tsab duk abin fanin girki dana bukatuna da yarana duk ta,shirya muna shi yayi parked din su, Washegari da yamma muka nufi hanyan airport nida maigida dayara na,sai Maimu da Ramatu inda tun safe Antyn Nani ta kama hanyan zuwa gida Birnin Kebbi, Baba Wadda da Baba Hamza zasu bi mota da kayan mu gobe da safe already su ma kayan an hada,su a motan ko, Nai sallama,da mutanen gida da abokan arzikina na garin Abuja muka kama hanya, raina babu dadi a cikin sa,,, Bamu wani dade ba a airport din jirgin mu ya tashi sai garin fotakwat gurin aikin maigida, A cikin dare muka isa garin inda muka samu masu zuwa daukan mu suna jiran isowar mu, Gida ne mai girman gaske, irin ginan zamani mai daukan ido, sai raraba da idanuwana, nake gurin kallon daulan duniya, da zamu zauna a cikin sa, Da jagoran Yaya Abubakar wanda yake dauke da yar lelenshi Amira a kafadan shi muka shiga gidan,, Gaba dayan mu a falo muka zube daga mu har jakkunan kayan mu, A hankali ya shimfide yarinyar a saman dogon kujera dake a cikin falon, Inda yake cewa tau yau dai gaku Allah ya kawo ku sabon guri kuma again, Mun zo da abinci tun da naji cewa tafiyan dare zamuyi a lokacin munyi miya mai yawa da kuma wasu abubuwan bukatun mu, munzo dasu, Sama ya haye na,wasu yan mintina ya kirani cewa nazo,, Na tashi duk jikina a gajiye na nufi saman inda naga ya bi, Kofan daki biyu ne a gurin sai na hankalta da wanda yake kamar a bude daga ciki, Na tura kofan dakin ahankali kamshin turaren shi dayake yawan shafawa ne ya daki hanci na , Sai dai dakin ko ina kayane alaman dakin na bukatan gyara, a ko ina,, Yana zaune a bakin gado yai min umurni dana zauna nima a bakin gadon inda na zauna a hankali,, Yace min wanan shine gidan da nake ciki a yanzu don da a can baya ba,a nan nake zaune wani unguwa ne mai nisa da nan nake so nan din yafi min kusa da ma,aikatan mu koma ince nan gidajen ma,aikatane su, Don haka dakuna biyu ne a sama biyu a kasa sai daga waje a kwa dakuna biyu kamar boys quarters yake, na wanan gidan, So a can waje nake son su Baba Wadda su zauna don su mazane, Yanzu sai ki zaba wa su Ramatu inda zasu zauna mugani dake kuma inda zai zama dakin kina nan, Yana kaiwa nan sai ya mike ya nufi inda nake1 tsanmani kamar bathroom ne gurin kamar zai shiga sai yaja ya tsaya yana cewa ki tafi ki bawa bakin ki abinci, Da mamaki nake son sanin su waye bakin yace Ramatu da yaran ta, ko, Ni,dai na mike zuwa kasa na,samu yaran sun dan dunkule guri guda,nake cewa Baba Ramatu aci abinci, ko tace ai sunyi barci nace bari na ta dasu sai suci don kada,su tadamu da,dare a,garin mutane, Mun ci mun koshi sai hiran dariya muke Maimu tana ta bamu dariya muna kwasan dariya ya sauko saye a cikin farar jallabiyan shi, Daya bayan daya ya kalle mu a cikin farin ciki da jin dadi ya zauna, a tsakiyan yaran yana tambayan su ko sun koshi, Ni da Ramatu, muka mike zuwa dakin da za su, sauka aciki Ba laifi don mun samu dakin a gyare bed sheets ne babu a saman gadon don haka na,shiga part din yaya na dauko daya daga cikin bedsheet din shi na shimfida masu,, Daya bayan daya muka,kwashi yaran da kaya zuwa,dakin inda nida Ramatu mu kai wa kowa masaukin shi, Ita Amira da Aisha zata kwanta tare da Maimu inda su Amir da yan uwan shi suna tare da Ramatu,, Daga nan nai masu sai da safe zuwa gurin Yayana, Na samay shi zaune yana bincike a system din shi inda na,shiga da sallama a bakina ya,dago kai yana dan kallona yake cewa sunyi barcine yaran nake cewa eh, Wanka na shiga na fito don ina tare da gajiya na danyi gyara sama sama na kwanta, duk da muna da gajiya tare damu bai sa Yayana ya kyaleni a daren nan ba, A jikin shi na kwana yadda ya keyi kamar a ranan ya fara,sani na a,ya mace,, Tun da safe na, sauko kasa don shirya mashi break fast duk da kitchen din yana bukatan gyara na,samu wasu yan abin buka cikin saboda dama yasan da zuwa daya daga cikin mu don haka yafara,sayen kaya stuff ya aje, Ramatu na samu a falo ta soma aikin ta nai mamaki kwarai nake cewa tun yanzu Baba tace to may nazo yi hajiya, Da taimakon ta muka hada komai kafin ya sauko gida ya kaure da kamshin dadi, Maimu taima yara wanka suka, shirya tsab Yaya Abubakar yai mamaki kwarai yadda har gidan shi ya koma na family man, Tare da yaran shi yai breakfast a ranan inda ina daga gefe cikin wani rigan 'yan Mali, Kallo guda za kai mai kafaninci farin ciki a tare da shi a lokacin yai muna sallama ya nufi gurin aikin shi, Da fitan shi duk da ina da gajiya naja Maimu mukayi wa dakin shi tsab ta ko ina,sanan na,dawo sauran dakunan yaran shima muka gyara tare da dayan dakin da aka kira da nawa har wanda akace na,su Baba wadda ne sai da Ramatu ta gyara shi, Ina kokarin shiga wanka kafin nai sallah azahar ne, yakira layina yana tambayan lafiyan mu,, Na dauki wayan ina mai cewa hello Yayana, yace ina fatan kin kwanta kin huta hakana ko ? Nace ban samu kwanciya ba har yanzu muna ta gyaran guri tun fitan ka, Yace No No ki kwanta hakana idan kinyi sallah ki huta, Ga Ramatu nan da dayan yarinyar nan zasu ita maki komai ai ki tafi bedroom ki kwanta , Murmushi zancen shi ya,sani nace haba Yayana su ma,ai suna da gajiya a tare da,su, Kuma ni ai mace ce ina son nai hidima a gidana na,samu ladan aure, Yace cikin tausa murya ai in hidima ne zakiyi shi sosai kaunata don yanzu zaki fara ma, Kunyan abinda ya,fada ne ya lulubeni, na kashe wayan ina dariya kawai, Ban samu kwantawa ba don yaran basu wani sake jiki ba,saboda bakunta, Muna falo da,su ya,shigo hannun shi dauke da yar brief case din shi inda da,gudu suka yi kanshi suna cewa Uncle yadda sukaji Aisha na kiran shi, Na mike na isa gare shi na karbi jakar hannun shi ina mashi sannu da zuwa, idanuan mu suka,hadu ya sauke min sakon dake a cikin zuciyar shi, Ina gaba yana bayana muka shiga dakin shi sai ji nayi ya janyo ni zuwa jikin shi ta baya Yana cewa cikin murya mai kama da,rada, may yasa dazun kika kashe wayan ban gama magana ta dake ba, Nace layin ya katse yakara manne ni da jikin shi yana,sunsunan wuyana yana cewa aikin da kika,zo yi ne nake shirin fara nuna maki, Kunya shine ya kamani inda na dan kwantan da kaina a kirjin shi, ina mai dan sauke numfashi, Don nasan ko wasu maaurata suna bukatan irin wanan yanayin a rayuwan su, Muna a haka yana dan aika min da wasu sakon nai a jikina inda har jikin sa yadan fara yin sanyi cikin dauriya nace, mai, Ai da,wanka kafara yi kaci abinci tukun don ko yaran kai suke jira, Ya dan sakeni yana cewa, yayinda yake kokarin sance necktie din shi, kina nufin har yanzu basu ci abinci ba ke nan, Cike da yar shagwaba nake cewa ai kasan halin mutumiyar ka itace tafara, cewa bata ci suma,sauran sukaki ci, Kwantawa yayi a bakin gado yana cewa wai Allah duk na gaji wallahi, nace to ka tashi kai wanka zakaji dadin hakan, Wani kallon sha,awa yadinga yi min daga inda yake a kwance ina tsaye a kanshi, Na juya don na,shige sai ya riko min hannuwana inda na,fado mai a jikin shi, Yace a cikin rada hannayen shi a,saman kirjina yace wanan aiki da kukayi a gidan ai yai yawa wallahi Naso na,dauko cleaners din office suzo su gyara ne a gobe sai gashi ke da Ramatu engine sarakan aiki kunyi, Yadan furza iska daga,bakin shi yana cewa ban son kina yawan aikin nan nazo da ke ne da yan aikin ki don mu huta, kawai, Nai murmushi nace gurin ne babu dadin gani i yaune kawai aiki yakare mai yawa, Da kyat na,samu ya dan sakeni ya,shiga wanka ni kuma na koma gurin yara a kasa, Ramatu tai wa yara,warning cewa idan ina tare da Uncle kada wanda yaje sama,sai in na sauko,,

****** ********** ****** Sai dare su Baba Wadda,suka iso a,gajiye mukai masu sannu da zuwa tare da basu abincin su, Sunyi murna,sosai nagani sabon gidan mu da,zamuyi rayuwan wani lokaci a,cikin sa Hutu sosai muke agidan kowa najin dadin zama garin ga ni,ima ba wani hayaniya acikin sa, Inda Baba Wadda ya fara koya wa yarana Alkur,ani maigirma tare da,sauran littatafai, Hakan yaiwa mahaifinsu dadi sosai inda ya,warewa Baba albashi don wanan hinman, A haka rayuwan mu ya,ke ta guda cikin jin dadi da annashuwa, sai murzan junan mu muke anidashi har naje ji a,raina kamar babu sauran wata diya mace mai sunan matar shi a duniyan nan, Zai zauna da yara karfe takwas zuwa tara da,rabi na dare, Sai ya,sallamay su mukuma,smu shige master bedroom goma daidai, daga lokacin kuma ba,wanda zai kara ganina sai safe idan Allah ya kai mu, Ya saka yaran wani makaranta kudi mai tsada a,garin har su Amira masu tasan ma,shekara,biyu, biyu sun shiga, makaranta kindergarten, school,

****** ********** ****** Ranan da muka cika sati biyu da zuwa garin sai Salawatu ta bugo mai waya tana cewa nace ko ka tuna cewa gobe ya kamata ace ka,shigo garin nan, Yace a cikin bacin rai ban tuna,ba,sai dai yanzu da kika tuna min Dama don banda,mata anan ne yasa nake tuna zuwa gida yanzun ko ina da ita Don haka bakece zaki nuna min zance zuwa sauke hakkina ba , Kashe lyin tayi tana mai cewa acikkin fada dama nasan irin wanan zaluncin ne yasashi kawo wanan shawaran, A lokacin na,shigo dakin dauke da bowl din fruits salad dana hada mai da,daren nan, Ya dan dago kan shi inda na hango bacin rai karara a cikin idanuwan nashi, Ganin haka yasani aje kayan na nufi inda yake a zaune inda naiwa kaina masauki a hannun kujeran da yake zaune akai, Nadan kwantar da kaina a saman kafadan shi ina mai dan shafan gashin kan shi da hannuwana guda nake cewa may yafaru ne wai haka, Ajiyan zuciya naji ya,sauke yana cewa yayin da ya kwanto da kanshi a gefen da nake muka hade kawunan mu ajunan mu, Yakara sauke ajiyan zuciya yana cewa wanan mahaukaciyar ce ta bata min rai Wai itace ke min tuni cewa nazo na bazu hakkin su hakana,,,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA SEENABU

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣2⃣0⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ARRAHAMANIN, RAHIM,,,

BARKA DA JUMMA,S YAN UWA MUSULMAI UBANGIJI ALLAH YA SADA MU DA RAHAMAR SA TA WANAN RANAN MAI ALBARKA,,, YA ALLAH KA YAFE MUNA KURA, KUREN MU,,,, JUMMA,AT MUBARAK

GODIYA GAREKU DUK KAN MASOYANA NAGODE DA KU KAI HAKURI DA IRIN DELAY DIN, DA ALLAH YA NUFI WANAN NOVEL DIN YA SAMU, BA KAMAR YADDA NAYI SAURAN BA A BAYA DON ALLAH KUYI HAKKURI DANI, DA FATAN ZAKU YAFENI,,,,,

Gaskiya Alhamdullahi don zan iya fada maki cewa ni Meenatu Samaila Manya Birnin Kebbi yanzu ne zan iya cewa nasan dadin aure arayuwa na, Bani ba har da zurian da Allah ya,bani suma zan iya cewa sun san zafin mahaifin su, Don a yanzu sai yai muna komai da zuciya daya batare da,tsoro ko fargaban shiga hakkin wata mace,ba, A,koda yaushe ina manne da mijina Yayana yana kwasan gara daga gareni, Yaran shi yasan halaiyar ko,wanin su yanzu saboda irin kusancin da suke dashi a tsakanin su, Zasu tafi makarata indan sun dawo sunci abinci suyi lesson , Karfe hudu zasu zauna da Baba Wadda su yi karatun addini, sai six zasu tashi,, Ranan alhamis da jumma,a ne kawai basu zama gurin karatun addini, Idan ranan asabar da safe suna zama karatun har in mahaifin su yana gari bai je Abuja ba, zasu zauna tare dashi da Baba wadda su koya masu nima da Ramatu muna zama daukan karatu don shi Baba Wadda mutum ne mai tarin ilimin addini Hakan ke sa malam tsoho yawan yin korafin rashinnzaman shi gida don ya gaje shi ga karatu,, Duk wani wanda muke tare a can suna matukar jin dadin zama da mu sosai don ba banbanci ko kadan atsakanin mu da su, Rayuwa muke da,su na one family atare, za ai komai gwanin ban sha,awa, Shi kanshi mai gidan yanzu da ka kalleshi zaka fahinci ya samu natsuwa a,tare dashi don hasken shi da tsayin shi duk sun kara haskawa, , Ina matukar jin dadin zama da Ramatu a rayuwa na saboda kasancewan ta mai zuciya guda, don haka muke rayuwa da ita har nake ji kamar da uwata nake zaune a gida, Don duk wani hanyan alheri zata sada ni dashi idan nayi ne sai tace da kinyi kaza idan nabari ne sai tace uwar dakina wanan abin kada ki sake yin shi nakan ce to Baba,,,

Ban san kowa agarin ba, don haka babu inda nake zuwa koda yaushe muna gida abin mu, Gurin gyaran kaine kawai nake zuwa har in nafita, gari, Yau ma kainayana bukatan gyara don kitso nake son ai min nida Maimu ne muka tafi saloon din Baba Wadda wanda yanzu yake kamar dangida a,gurin Yaya shile zuwa yin aike komai don suma suna da nasu albashin idan anyi biya, Matane a gurin yare kala kala, kala muka samu, kowa da irin abinda ya kawo ta gurin, Doguwar riga ce light green a jikina sai gyale danai rolling din kaina dashi, Tun shigowa shagon suke gulmana suna cewa Na hausa woman , all dis hausa people are, so beautiful, Gurin wata mace wace ake wankewa ma kafa gefen ta akwai kujera na zauna, Ban dade da zama ba wayana yai kara alamar kira, a daidai lokacin ne kuma yarinyar shagon ta iso gareni, Tana cewa, madam wetin you wan do ? Nace mata a takaice I wan plant my hair saboda tun a gida na wanke abina, Nadauki wayan ina cewa assalamu alaikum mama, ina wuni yaya gida da,sauran mutanen gida Da, sauri naga matar da ke can dan nesa dani ta kalloni har na gama waya idonta yana a kaina har na,gama waya da mamana wace ke min korafin cewa, na taimakawa yayana Ibrahim,,, Alhalin kuma Baba na ne ya hanani yin komai a kan zancen na yaya ibahim, din, Bayan mun gama wayan ne da mahaifiyata naji matan daga can tana cewa yar uwa ashe ke bahaushiya ce, Da sauri na juya inda take zaune ina kallon ta acikin mamaki , Cikin sakin fuska nake ce mata ina wuni tace lafiya lau hajiya, Tace anan garin kike da zamane kema, nace mata eh a,daidai lokacin da yarinyar shagon ta karaso gareni tana nuna min inda zan zauna, Na mike na barta ina ce mata sai anjima ko na nufi inda su ka nuna min gurin masu kitso, Dani da Maimu duk an gyara muna kan mu bamu samu masu kitso irin na muba da yawa don haka mu ka bar gurin da wuri,, Gurin da Matar take zaune take, cewa har zuku tafi ke nan, ni gashi yanzu zan fara gyaran kai, Nace eh sai kuma watw rana ko? Tace to ban nombanki don Allah ai zamuyi zumunci ko, ? Kamar kada na bata sai na tuna cewa tace don Allah don haka na bata, nomban inda a take ta kira nawa layin wayan, Baba Hamza ya dauko mu zuwa gida, inda muka,dan tsaya wani guri muka sai kayan miya fresh one,,, Na dawo gida a gajiye don yamma yafara a lokacin ban tsaya komai ba na ashiga sallah, A lokacin yara sun tashi daga makaranta islamiya wanda yanzu basu kadai ne ke karatun ba har da diyan wasu hausawa mutum hudu Ban tsaya komai ba na,shiga yan gyare gyarena da,aiyukan gida, Bayan kamar kwana biyu da zuwana,sallon har maigidan ya,dawo daga Abuja ranan talata, ina zaune ina karyawa bayan kowa ya watse ne, Naji wayana yana ringing alaman kira ya,shigo min na,dauka ina mamaki don ganin bakon nomba ina mai cewa sallamu alaikum, Aka karba min a dayan bangare da wa,alaikum mussalam, , Tace hajiya ina ta,son na kira ki don mu gaisa amma ban samu kira ba,sai yau, Nace cikin nuna bangane mai magana ba nace tau sai dai gaskiya ban san da wa nake magana ba, Tace lah bakiyi serving din nombata ba kenan ma,ashe tau Ramla ce wace kuka hadu a,saloon da ita,, Nace ayya Allah sarki sannu yar uwa wallahi banyi serving din nomban naki ba, Don Allah kiyi hakkuri kinji yar uwa tace ai babu komai kawai, dai dama na bugo na bugo ne mu gaisa don ranan bamu samu yin wani magana ba, kuna sauri, Nace hakane gaskiya don anzo daukana banda time a lokacin, Tace mu mutane Adamawa ne a cikin garin Yola,aikin banki mijina yakeyi shine aka turo shi nan , Naje gida inabawa maigidana, labarin haduwar mu a ranan shine yake cewa na tambaya ko a wani unguwa kuke za mu kawo maku ziyara, insha Allahu, Na amsa da cewa tau aiko mun gode sai dai a cikin raina ina tsoron kar maigidan yace na fara yi mai kwashe kwashe a gida, Muryqn ta naji tana cewa shine yace mu tambaya muji don yanzu watan mu shidda da zuwa garin nan amma bamu san kowa ba, sai yan kabilar garin nan, Nace muna a NNPC Quarters a senior Quarters din su muke zaune, a house nonba 2 muke da zama, Sai naji kafin nace wani abu tana cewa ,a a a ashe matar manya ce nake magana da ita nace kai haba dai, Tace insha Allahu zuwa ranan asabar zamu shigo gaida ku ni da maigidana da yarana, biyu, Na amsa da fadar Allah yakaimu tace Allahuma amin mun gode sai mun shigo din, Nikan tun a lokacin sai na manta da zancen wata mata kuma a raina,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull