Tarko complete novel - Chapter 126
Tarko complete novel Chapter 126: Tarko complete novel Chapter 126. ****** ******** ****** Yau ya kasance ranan jumma,a don ni a gurina na kan girmamawanan…
3,081 words
****** ******** ****** Yau ya kasance ranan jumma,a don ni a gurina na kan girmamawanan ranan nan, ne tankar ranan sallah nake jin shi don hakan sunnah ne,,, Mu kan yi girki lafiyayye mu gyara gida mu saka kamshi ta ko ina na gidan, Mu kan yi kwalliya gaba dayan mu, kowa ya kure a dakan shi tsab mu saka sabbin kaya muna jin dadi, da murna, Idan yamma tayi zamu shimfida katon carpet a wani dan fili dake a wajen gidan, a,nan zamu zauna muyi ta hira ana ci a na sha tankar muna wani buki, Yau ma hakan ne ya kasan ce don tun safe muke aikin girki inda sai sha biyu saura muka gama komai, Yau nayi tuwon shikafa da,miyan alaihu, yaji agushi, da nama yanka mai kyau a cikin sa, Ga kunun zaki da zobo yana kamshin kayqn yaji gwanin dadin kamshi, kasancewa yau da maigidan zamuyi yinin jumma,a don sai satin sama zai shiga Abuja kuma, Na cewa su Ramatu kowa ya,shiga ya kimtsa jikin shi kafin su dawo daga school, Bayan na fito daga wankane na zauna a bakin mirron dakina ina gyara jikina, Wasu yadi na,saka na yan Mali yadin mai laushi dashi an,min dogon riga nai rolling din kaina, tsab da wani dan gyalen kayan mai laushi sosai, Motar yaran ne ya tsaya sun dawo daga makaranta, ina kokarin naga cewa, na daga kafin su shigo dakin nawa, da ihun su, suna cewa mummy, mun dawo sai rige, rigen zuwa hugging dinq sukeyi, Wanan dabiar su ce kullun aka dawo ana rige, rigen zuwa hugging din mummy, gaba dayan su,,, Na,rugumay su ina cewa Oyoyoyo Muhabbatina,,, Amira ce daga bayan su take dan takowa a hankali, kamar bata da sukuni,,, Ina daga zaune hankalina ya na a gare ta nace daga inda nake zaune Mama, na zo mana na mikq mata hannuwana daga inda nake zaune, A lokacin ne Alhasan ke cewa, mummy yau, Amira bataci komai ba a school, Da sauri na jawo ta zuwa jikina ina cewa mamana may yasa baki son cin abine wai,? Batare da yarinyar tace komai ba tafado bisa jikina tana cewa Mama, Na rugumay ta zuwa jikina ina mai tausayin yarinya a raina don a gaskiya idan har ana gadon suna tau wanan yarinyar tayo gadon sunan mamana Saratu wurin hakkuri, Mamana may yasamay ki ina kokarin taba mata jikin ta a hankali na ji yana da,dan zafi kadan, Alhassan yace Mummy naje naci abincin ta ne ? Na kwada mashi harara nace kaikan Allah yai ma,saukin wanan cin naka haka, yaron ya,ruga aguje zuwa kasa,, Nacewa sauran yaran kuje kuyi shirin zuwa Jumma,a kafin Uncle ya dawo gida, Suna fita na kara,rugumay yarinyar ajikina ina cewa, wanan halin rashin cin abincin ki yana damuna,wallahi, May ke maki ciwo ne mamana sai yarinyar ta dan taba cikin ta can kuma ta taba kanta, Narike hannun yarinyar yayin da nake mikewa ina cewa muje kasa na baki magani kisha, A daidai shigar mu falon gidan ne ya,shigo gidan hannun shi yana rike da yar briefcase din shi karama , Idanuwan shi kar a kan mu yayin danake tsaye da hannun yarinyar ina mai sannu da zuwa, Farin cikin shi a,kullun karuwa yake, idan har ua bude idanuwan shi ya ganshi a cikin iyalinshi sai yaji shi yana walwala, da jin yafi kowa sa,a, a duniya, Kallon yadda yarinyar take wani dan langabewa a jikina, don haka ya juya gareta yana cewa, yau may ya,samu mamana,ne, Nace cikin kokarin mika hannuna,don na karbi jakar hannun nashi, ina cewa ina ga dai bata da lafiyane ,don bata ci komai ba yau, a school, Da sauri yadan durkusa ya rage tsawon tsawon shi, daidai na yarinyar yana mai mika hannu shi gare ta ya kamo hannun ta yana cewa, mama may ke damun ki ne, ? Batai magana ba,sai dan kwantar da kanta ga jikin shi da tayi, kadan tana mai sauke numfashi a kafadan uban, Ina,daga tsaye gefe guda ina kallon su sai ya dago kan shi yana cewa,a debo min abincin in bata in gani ko zataci, Nace bari na kai jakar shi daki na dawo sai na, debo masu abincin, inda na hau sama na barsu a nan folon, Ina shiga sai na dan tsaya don na gyara mai kayan da zai sa zuwa sallah, Na kuma hada mai ruwan wanka don kada na,dawo dakin kumaidan na sauka, Ina,saukowa na hango shi zaune da ita yana dan rarashinta taci abinci, amma taki ci, Na sauko ina cewa bari na bata maganin zafin jiki mugani ya dago kai yana cewa da zata danci wani abu zaifi kafin tasha maganin, Nace mai daga inda nake a tsaye nake cewa ruwan wankanka is ready don time din zuwa massalaci yayi, Mikewa,yayi yana cewa karbeta ki bata ko zata ci idan na dawo sai na kaita, asibiti, Ina kokarin bata abincin ne, ai tuni idanuwan yarinyar ya cicciko da hawaye tana son tayi kuka, Ya koma ya duka a gabanta ya hankali a tashe yana cewa karkiyi kuka Mamana idan bakya ci sai a,bari kinji, Yadan sa hannayen shi yana dan goge mata fuskanta a hankali tare ce abarta please, Nace wa yarinyar zaki sha tea sai ta gyada min kai alamar eh zata sha din, Yace to a hado mata ko zata sha na kwadawa Maimu kira tafito da sauri tana cewa gani anty, Nace ki hado wa Amira yea kada ki sa sugar fa madara da millo kawai zaki hada mata,sai ruwan zafi, Na samu yarinyar tasha tea din sosai wanda hakan ne ya,dan kwantar min da,hankali, Sai na fahinci watakila bata ra,ayin abincin da aka dafa masu din ne,
****** ********** ****** Gaba dayan mu muna zaune a saman carpet waje, muna cin abinci inda Ramatu take ta fa ma da rikicin yara , Saukin abin ma su na tsoron mahaifin su don yakan tsawata masu har suji tsoron shi idan sun yi abinda ba daidai ba, Wayan shice tai kara z lokacin da yaks tsaka da cin anincin shi don haka yadan dakata yana mai duban laban da aka kirashi da ita a lokacin, Sai naga yadan gyara zama yana danna receive din waya tare da,fadar sallamu alaikum, Hankali sai na mayar gurin yaran gaba daya muna ta harkokin mu, sai naji shi a dan hasale yanacewa yaushe nayi daku cewa zan shigo this week ina last week ne nadawo daga can, Abinda ya jawo hankalina a gare shi ke nan ina dan sauraren zancen shi,, Ya karashe zancen da fadan na,fada maki sai satin mai sama zan shigo don haka ban son wani zance yarinya kuma a,kaita, asibiti ma ba doctor mustapha yana nan ba,,, Yana kashe wayan ya juyo da kallonshi inda nake zaune yana cewa na,dauke plate din abincin dake a,gaban shi ya koshi, Nace ai da ka kara ci don baka ci komai ba ai daga abincin, Yana kokarin wanke hannuwan shine yake cewa No na koshi ba zan ci ba kuma,,, Haka na,dauke plate din daga,gaban shi ina ma mai wayan wace nake ganin Fatima ce, zargin hana shi zama yaci abincin dana wahala gurin girkawa, Mikewan shi yai daidai da kiran wayan Sadiya tana cewa, Sai da yamma ne zai shigo garin ko kuwa, Yace cikin hasala wai dawa nayi zancen zuwa wanan week din daga cikin ku, Sadiya tace saboda naga anyi wanan maganan cewa ba a yarda ka,dinga yin har sati biyu ba,a gurin mace guda kawai, Yace ni keda kaina ba wani ba don haka babu wacce zata kafa min wani doka daga cikin ku , Idan har wata zanyi a nan bazo ba akwai wace zata tilasta min yin hakan ne ko kuwa, Don haka ban son yawan tsegumi wanda baikai ya kawo ba a tayar wa mutum da hankali ga banza ke da hankalinki har zaki biye wa wanan haukan,,, Daga inda nake nake cewa Yaya da ka tafi din tunda haka suke bukata, din, Will you shout up your mouth, wanan ba zancen ki bane,,, Simi simi na kwashi kayan abinci na,shige daga ciki raina a bace don gaskiya ban son abinda za,a zargeni akai koda yake a lokacin Salawatu ke zuwa har yakan shafe wata daya ma bai shigo ba, Mai makon nadawo falon sai na,shige ciki abina na dauro alwala ina sallah nafila, Ya gane fushi nayi sai ya,share shima ya shiga harkan shi a cikin system din shi sai yaran dake ta hayaniya suna kawo karan yan uwa a gurin shi, Bayan na,idar da,sallah ma ban sauko ba,sai da yamma kwarai na sauko a cikin wani dogon riga body hook, ina son inbawa Amira maganin ta tasha, A zatona yafita baya gida, a lokacin don naga yamma tayi sosai duk da dai shi ba ma,abocin son fita waje bane akoda yaushe, A sanyaye nai sallama a falon idanuna sunyi luhu luhu sun dan canza kala yayinda fuskana babu yabo babu fallasa acikin sa Ganin shi zaune rugumay da yarinyar a jikin shi ya dan sani shock amma sai na dake, nace Amira bari na dauko magani da kaya na sauya maki ko,, Ya dago idanuwan shi da su kai mai ja alamar rayuwan shi a bace yake shima har zuwa yanzu,,, Cikin wani murya yake cewa maganin ta fa, ? Nace a cikin dan sanyin murya harda shi zan bata yanzun din, Na,shige dakin gurin Maimu ta,dauko min maganin da kaya masu nauyi da,man shafin yaran na,fito inda,suke ita da,ubanta,, Na, dawo gurin su na zauna dan nesa dasu kadan na fara goge mata jikin t tare da shafa mata mai sai na bata maganin duk yana zaune a gefen mu yana ganin abinda mu keyi,, Alokacin ya mike zuwa sama kusan yan mintina yafito cikin jallabiya da alamar sallah magriba zai tafi, Daga inda nake zaune na dan zuba mai ido yana kokarin gangarowa kasa don fita, Yana isowa gurin mu yake cewa ina, Amir mu tafi sallah nace ya,shiga alwala yanzu, Yaron yafito suka fita tare yan uwan suna kukan zasu bishi amma baban nasu ya hana,su saboda sunyi kanana kwarai,,, Na zubawa bayan shi ido har suka fice yayinda zuciyata ke fada min yau da akwai fitina a tsakanin mu ke nan, Don naga yadda yake wani basar dani tankar bai sandani ba ma, a gidan, Mun idar da sallah isha,i, ne bayan nayi adduoi na na,fito don shirya mai abincin dare, a daidai lokacin ne ya shigo gida dauke da Amir wanda,da alaman barci ya,fara yi, Daga inda nake a tsaye yake cewa a kwantar dashi don ya,fara barci nake ce mai baici abinci ba zai ita tashi da dare don yunwa, Baiyi magana,ba sai ma,shigewa da,yayi part din nashi ya barmu a falo na,wasu yan mintina ya,sauko, Bai kai ga zama ba wayan shi tai kara,ya,dauka a zuciyana nake cewa dan kayan kiran waya, Ya zauna a kujerar dining na taso don na zuba mai abinci nan na fahinci da,Salawatu yake waya, a lokacin Naji tana cewa ance wai ka,fasa,zuwa,a cikin wanan satin sai ma,satin sama, Yayi saurin katse da cewa dacewa ban son jin wanan zancen don ban san may zayi maku ba haka,? Ina jin haka nai saurin dago kai na,dubeshi a cikin mamakin jin yana cewa wai may zai masu idan yazo, Ban karasa tunane ba naji ya katse wayan dayar guntuwar tsuki yana jawo plate a gaban shi,,, Ya dan juyo da nufin magana karaf idanuwan mu suka hade nai saurin sauke nawa kasa Ban tsaya ba kamar yadda na,saba tsayawa zuba mai abinci har sai yaci, nabar gurin yau kawai sai na tsuci kaina da,barin gurin don raina ya,baci,,,, Dakina,na koma duk abin duniya ya damay ni ba don komai, ba sai ganin irin bakin jinin da zai kara ja min a cikin yan uwa,, Ban sake fitowa falon ba bayan nai wanka na samu guri na zauna a,dakina, Sai zuwa dare sosai na,sauko zuwa gurin yaran don na,duba su inda na samu sunyi barci sai Ramatu ke yan hidimar ta,da Maimu, Ramatu yaran duk sunyi barci a,she ta juyo tana cewa kin fito ne uwar dakina Nace zan kwanta nace bari nazo na,duba,ko sunyi barci take cewa sunyi ita,Amira ma,bada dadewa,ba baban yakawo ta tayi barci a gurin shi, Na tabe bakina ban ce mata komai ba,sai naji tace, amma gaskiya uwar dakina bai dace ba yadda yau na fahinci cewa kinawa maigida, Murmushi nayi kawai nace a cikin kunan rai, amma Baba Ramatu kara jamin bakin jini yake son yi a gurin sauran abokan zama yanzu ace suna can suna duban hanyan shi yau din nan amma sai yace wai ba zai tafi ba, , Yo ke may ya shafe ki a kan wanan zancen tunda ba kece da ikon shi ba, Wanan matsalar su ce a tsaksnin shi da matan shi don haka kada ki jefa kanki a cikin wanan zancen, Shiru nayi ina,saurarenta daga karshe sai naga gaskiyar zancen ta amma kuma ai duk da hakan ina da ruwa acikin zance sai dai dayake banice da iko ba sai dai nai shiru,,, Nace a cikin murmushi nagode Ramatu, komai ai ya wuce, nai masu saida safe, na koma dakina,
Yana kwance har sha dayan dare a,dakin shi inda a kai, akai yake duban agogon dakin shiru baiga alamar shigowan Meenat dakin ba, Yaune karo na farko tun zuwan mu garin da nake kokarin raba,muna shimfida, Sai faman tunane barkatai yake yayin da yake dan daga,ido yana duban kofan shigowa dakin Gaba daya hankalin shi ya,dan tashi saboda ya kasa fahintar fushin da,na keyi gashi kuma,bazai iya tambayan ta komai ba a kan zancen, Ina zaune a gurin dana idar da,sallah ban daga ba don ban san abin yi ba don haka sai na zauna a gurin ina ta tunane kawai, Alaman nauyin mutum naji a kaina wanda hakan yasani daga idanuwa na ina kallon kofa, What happen? Don na ga har sha biyu ake zance banga kin shigo ba, don naga kamar a kwai matsala ko,,, Nace nima a,cikin dakewar murya babu abinda ya faru ina dai yan abubuwane kafin na,shigo, Ya,saki wani dan guntun murmushi tare da zuwa bakin gadon dakin ya zauna, Inda ya tsareni da,firgitattu idanuwan shi na dan wani lokaci sai naji yana cewa a cikin wani irin murya, Kin ban mamaki Meenat akan zancen da bai shafeki ba har zaki, dau zafi dani, Na dan dago kaina a hankali na, kalleshi yayinda na,sadda kaina a kasa ina cewa, Yaya ban son abinda za,ace nice na haddasa fitina akan zance don kaga suna nufin cewa a,nan kawai kake zama yanzu baka,son zuwa gurin su, baka ganin cewa hakan zai iya kara jawo matsala a tsakani dasu,, Yace matsala a tsakanin ni dake, kike tsoro ? ko tsakanin su dake ? Shiru nayi don banda amsa a baki sai a zuciyata sai naji yana cewa ban son kina saka kanki ga,abinda bai shafe ki ba, Nace a cikin sanyin murya ni kawai ban son al,amarin zargine shiyasa amma bawai ina sa kaina a cikin zancen bane,, Ina daga zaune a saman salayata naga ya mike yabar dakin yanufi nashi dakin, Bai dade da,fita daga dakin ba nabi bayan shi nima a cikin shiri na, na kwanciya,
****** ********* ****** Washegari safiyan asabar yana,zaune a falo breakfast yakeyi alokacin yara suna wurin daukan karatu, addini, Sai da na bari ya kusa gama karya kumallon nake cewa Yaya dama iba son fada ma cewa yau zamuyi baki a gidan nan , Da sauri ya dago yana ce min baki daga ina kuma zasu zo, Nace watace muka hadu a saloon da ita shine tace yau zata kawo min ziyara, Yace acikin canza fuskan shin Meenat ban son yawan kwashe kwashen mutane a gida na kiyi a hankali don yanzu ba kowane ake yarda dashi ba, Nace a Saloon ne muka hadu da ita shine ta karbi nombana yace na dai ce maki bana son kwashe kwashe tun kana kwaso na kwarai har ka hadu da mugun mutum nace in sha Allahu zan daina acikin ladabi daga haka nai shiru, da bakina, Nasan cewa ranan weekend idan har yana gari bai fita zuwa ko ina dashi zamu wuni a,gida don haka nake ta kafa kafa kada a,samu matsala idan sunzo,, Musalin sha daya na rana suka iso gidan na mu inda ta bugo min waya cewa a tare su a get din shiga quarters din namu, Baba Hamza yaje bakin get din ya shigo min, dasu,har kofan, namu gidan,, Mariya, da yaranta biyu sai mai gidan ta, ne suka zo ziyaran mu, Nan muka shiga taron su a cikin karramawa da abubuwan da muka tanadar ma zuwan su,, hiran duniya a tsakanin mu mukeyi da yanayin zaman wanan garin da muke a zaune, Tun shigowar su na hau sama na fadawa maigidan cewa Mariya da mijin tazo da kyat na,samu ya fito don su gaisa dashi kada mu barshi a zaune, shi kadai,, A hiran mu na fahinci yan uwa suke ita da mijin ta,amma ba hada su akayi ba,auren soyayyane sukayi a tsakanin su,, Taso taji wani dan labari a gamay dani sai dai ban yarda na fada mata komai ba a kaina, photo dake a falo wanda mukayi muda yara ta kurawa idanu, Take cewa yaran nan duk nakine ko kuwa nai murmushi daga gurin da nake zaune nace duk yarana ne mamaki takeyi don sai naga ta dan matsa daga inda takw zaune zuwa gurin photon wanda ni da Yaya da yaran mukayi, Sai nake mata bayani a,kan photo daga Amir har su yan uku da tagani take mamaki kan su guda gasu kuma,da kama,, Mun taba hira sama sama da ita har take gaya min rashin jin dadin garin da batayi , Nace to ai kinsan mu mata bamu da zabi sai na mazajen mu don haka hakkuri zamuyi har ranan sa Allah zai mai damu cikin yan uwan mu, Tai dariya tana cewa gaskiya ni har nace wa Yayana ya mayar damu gida, ai, Da sauri na katse ta da cewa wanan kuma baki daidai ba don zaman ku a nan tare dashi wani rufin asirine don mu mata zamu iya hakkurewa har na tsawon lokaci amma shi namiji sai kiga idan ba mai hakkuri bane ya,fada ga halaka, Nace don haka kawai samun lafiyan mace shine tabi mijinta a zauna lafiya, Haka ranan mu ka wuni tare dasu har zuwa yamma Ramatu da tai girki nasa aka saka masu don tace basu da abincin gargajiya kuma suna so, Munyi sallama da su kamar kada,su wuce saboda dan sabon da mukayi da su,