Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 127

Tarko complete novel - Chapter 127

Tarko complete novel Chapter 127: Tarko complete novel Chapter 127. ****** ********* ****** Tafiya ne ya,taso wa yaya Abubakar na tsawon sati uku don haka…

3,094 words

****** ********* ****** Tafiya ne ya,taso wa yaya Abubakar na tsawon sati uku don haka ya,shiryahar da mu yatafi aiki a kasan Spain Mun sauka a babban airport din su na Madrid inda wa yanda zasu tare mu suka kwashe mu zuwa masauki, Ranan dagani har yarana mun sha kallon kasar turawa, Wanan tafiyan yai min dadi sosai don hutune sahihin shi mukayi a can daga ni har maigidan mun mori junan mu sosai a can, Don naga so tarairaiya da kauna a gurin shi kamar ace ni kadai tal matar shi a,duniya, Hakama bangaren yara na,suma sun samu kula,sosai don dama tafiyan saboda Amirace akayi damu don adiba lafiyan ta, Da farko kasan India yaso ya kaita saiga,wanan tafiyan na kasar Spain ya taso mai don haka sai muka kwas muka nufi can din, Wanan tafiyan yai matukar tayar da hankalinabokan zamana dan gaba dayan su sai suke gani ai kamar na mallake hankalin maigidan ne nida yarana, Don haka suka dauki karar tsana,suka kara dorawa a kan mu kishi kyashi hassada da bakin cikina sai ya karu a saman wanda suke min da farko, Na fahinci hakan ne a lokacin da Sadiya ta,bugo mai waya na karba don mu gaisa amma sai ta katse layin wanda nai mamaki kwarai da wanan abin da tai min, Yana daga gefe zaune tankar wanda baisan mai ke faruwa ba alokacin yayin da,nabi wayan da kallon mamaki, Nace a raina lalai wa tan nan suna da ja dani don haka ya zama wajibi na kama kaina, da su gaba dayan su duk da dama can kowa tashi ta fishe shine, Yace daga gurin da yake zaune har kungama wayan ban taka mai ba sai ma daure fuskan da nayinace ban taba zaton Sadiya zatai min wanan irin wullakancin ba haka amma zamu kwata ai, A,satin mu biyu da suka rage muna a kasan na daura dammaran yaki da duk wace ta shiga hakkina ta ruwan sayi, Nai amfani da wanan daman tafiyan da na,samu gurin matar dashi komai na wata diya mace a duniya sai ni, Hakan ya sani fahintar cewa ashe shi gwarzon mazaje ne mai iya soyayya da dauke hankalin diya mace, Kaunar da yake gwada muna nima ya sani nuna mai tsantsar kauna wace har yake ji har cikin ranshi dama ace a duniya ni kadai ce matar shi, Don ya fahinci na banbanta da sauran matashi a komai na rayuwa, hakan yasa shi jin bai taba gajiya da kasancewa dani A cikin dan lokaci rayuwa ta canza mai ya manta da wasu mata a gida sai ni kadai yake jin na iya gamsar dashi , Duk da inajin jiki amma haka na daure don Yaya Abubakar ba karamin namiji bane Don kawai na nuna masu the differences is clear sai nake daurewa da bukatar shi koda kuwa yazo min a lokacin da ban ra,ayin karban bukatar shi,, Sai daga baya na,fahinci cewa ashe hakan ne ke kara min daraja da daukaka a gurin shi, Na fitar maida sha,awan ko wace mace a ranshi sam ya manta da cewa akwai wasu a gida, ta ni da yarana kawai yake yi,,, Tsoron Allah kawai ke,sani damuwar shi da tambayan ko ya,buga waya yaji labarin su suna lafiya? Idan na cika damuwa yakan kira wata daga cikin su don yaji sabida idan bashi ya kirasu ba basu samun shi, Sai a wanan lokacin na kara godewa Allah da Anty Amarya don duk wani training din da ta dorani akai wanda ba boka ba malam sai dai adduoi da kuma yan dabarún mata su nake a wanan kasar kuma Allah ya tai makeni har na,samu nasaran shawo kan namiji kaman Yaya Abubakar a kaina,

Tsafi gaskiyan maishi domin abokan zamana suna can cikin tashin hankali cewa na,asirce maigidan yazo da taimakon malam tsoho baiji ko ganin kowa sai ni da yarana ,,, Salawatu an samu abinda ake so don sai shige da fice akeyi don fanin an shiga tsakani na da maigida, Niko nasan cewa za,arina don haka ban wasa da adduoina don komai ritsi sai na zauna nayi wa yara da kuma kaina don neman kariya daga shedan, Wanan karon har Sadiya da bata faye irin wanan abubuwan ba saida shedan ya rude ta ta afka shirka, A haka sukai ta surukullen su, basu yarda dacewa komai na Allah bane, Nayi wani irin kiba nai haske na murje nai kyau sosai ga,wani irin waye dana karayi,

****** ********* ****** Zaune yake a gaban laptop dinshi da alamar aiki yake sosai don kan shi a duke yake ,na shigo dauke da wasu kayan da na,sayo na yara, da muka fita ina,son na nuna mai, Sai da na dan zauna nake cewa amma da mun koma zamu wuce zuwa Abuja ko ,,don lokacin komawan mu yayi,, Barin aikin da yake ya,dago ya kalleni yana cewa Abuja Abuja yin may kuma,? Nace acikin mamaki ka manta cewa yau saura sati guda mu cika wata ukun da zamu yi a porthercoth tare da kai wata tazo,, Yace a cikin daure fuska ban san wanan lissafin ba ni don haka ki fitar da zancen a ranki,, Shiru nayi ban tanka mashi ba yace in kuma kun gaji da zama dani ne sai ku shirya ku koma, Saboda kin daukeni wanda bai san ciwon kanshiba zaki maidani wani wagili na bi can, Ya kike son karatun yarana ya kasance idan ina yawan canza masu makaranta, Da sauri na kara kallon shi don jin may yace watau ta karatun yara ke nan zai fake a rashin komawan mu Abuja, Mun dawo gida lafiya inda na samu su Ramatu lafita,sai faman washe baki takeyi wai na canza mata gaba daya na koma kamar wata yar Lebanon,, Mun dawo da sati gudane ni dai sai ido kawai na tsura mai ina sauraren yadda zancen komawan mu Abuja zai kasance, Shiru har ana batun sati na uku amma ba zancen tafiyan mu gida, Gashi har ya tafi Abuja yai weekend a can ya dawo shi kadai, batare da kowa ba, Ranan muna zaune, tare dashi a falo aka kirashi a waya sai daga baya na fahinci da Baba musa suke waya, Don naji yana cewa Baba na fada ma dalilina na barin su anan don bazan yarda karatun yarana ya tabarbare ba saboda haka idan sun shirya kamar yadda na fada masu cewa su dinga zuwa suna wata uku suna komawa, a tsakanin su,,, Abinda yasani gane cewa matan shi sunyi karan shi ne akan rashin komawan mu can tare dasu,, Haka dai sukai ta magana akan zancen wanda daga karshe naji Baba din ya yarda da zaman mu a na tare da shi dindin din, Wai sai dai mace tazo tayi wata uku ta zauna damu idan wata uku ya cika sai ta koma wata tazo kuma,, Zancen ya jowa tashin hankali sosai a tsakanin shi da sauran matan shi don sun nuna rashin amincewan su da hakan, Sai dai babu yadda zasuyi don ya riga da ya yanke hukuncin da hakan,, Umurni kawai ya bani cewa, na koma dakin sama,gaba daya da,yara sai nabar na kasan, Ba daman na tambaya don ba fuskan hakan don haka muka, kwashe nida yarana zuwa sama, da Ramatu da Maimu, Hakan ya,sani shan jinin jikina cewa akwai dalilun yin haka watakila akwai abinda zaiyi da dakin, Kamar sati daya, sai ga Sadiya ta shigo garin Baba Wadda da,Baba Hamza ne suka dauko ta daga airport,, Irin yadda naga yanayin ta,bayan mun tare ta,sai kawai naci gaba da harkokina na,share zancen ta kawai, Na kuma jawa yarana kunne a kan shiga harkan ta, ko na yar aikinta ba,da umurnina ba,, Don ita ma tazo da yar aikinta tare da yan kayan bukatunta nayau da kullun, Bayan tayi girki ta tafitane na karbi girki inda nai komai kamar yadda na,saba, Saidai ga yan kwanakin nan sam banjin dadin jikina sai yawan kasala da nake ji akoda yaushe, duk inda na,samu barcine, Yashigo dakin bayan magriba ya samay ni a kwance yake tambayana may yasa ban fito na bashi abinci ba kamar yadda na saba kullun, Nace cikin wata irin murya mai nuna yanayi yau sai nake jin jikina ba karfi tare dani, Yadan kai hannun shi zuwa jikina inda yaji jikin nawa da dan dumi, Yace wai may ke damuwanki ne duk kwanakin nan haka nake ganin ki, A cikin wani yanayi na bashi amsa kamar a cikin shagwaba da cewa nima ban san ni ba nadai dauka ko wahalané hakan, Yace gobe zan ba Hamza kudi yakaiki asibiti a,dub lafiyan ki zai fi agane, Washegati bai mantaba yabawa Hamza kudi muka tafi asibiti sai dai sun bukaci na kawo fitsarina don gwaji, Cikine dani wata biyu a,gwajin su don haka suke shawartana dana dan dinga samu hutu a kai akai, Ina cikin wanan yanayin ne na cewa ina da shigan ciki a tare dani ga kuma sabon fitinan kiyoshi a kaina,,,

ZEEE MAKAWA YELWA SEENABU

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣2⃣1⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

YA, HAYYU YA, KAYYUM

Wanan cikin yazo min a,bazata don banyi tsanmanin samun ciki a yanzuba,sam, Maimakon nai farin ciki da samun shi sai kawai na shiga tashin hankali da fargaba saboda tuna irin yadda nasha wahala a,baya, Tun ina yi aciki zuciya, har na dan fara rama duk yadda naso na boye a raina saida aka gane hakan irin yadda na ramay a lokaci guda,, Zaune nake a dakina bayan sallah la,asar Yaya Abubakar ya shigo dakin nawa yana saye a cikin wasu kananan kaya ajikin shi, A hankali daga gurin da nake zaune na dan dago kaina nake cewa sannu da dawowa, Yace tun da na shigo banji motsin ki ba shine nace bari na haunaga ni ko lafiya, Nace cikin dan sakin fuska ina nan zaune dan banson yaran nan su cikani da ihu, Murmushi ya dan baiyanar a fuskan shi yana cewa wanan kuma da rashin son magana yazo shi, Nayi murmushi kawai don jin may yake cewa don nasan cewa zolaya ce, yake min, Ya ce yanzu ya jikin naki I hope kin danji sauki sosai dai ko don ban son ganin ki a,wani yanayi A jiyar zuciya na,saka ina cewa sauki kan yanzu ai sai ranan da na haihu kuma, Yace haba dai wanan wani irin magana ne ai ba dole bane koda yaushe abin yazo maki kamar kullun Nace to ai dole ne Yayana ni yanzu duk tunanen irin yanayin da zan shiga a,cikin wanan cikin nakeyi, ,, Ya ja tsaki yana cewa kawai ki sa a,ranki cewa lafiya lau zaki renon wanan cikin, Nace ni Yaya yanzu sai nake jin zancen ka da kamar dadin baki kake min don ka kaini kabaro ko Yayi murmushi yana cewa yanzu dai ni ban son wanan shiga dakin da kike ke kadai nafi son naga kina walwala, ya karasa,da,sakin yar murmushi yana,mai juyawa da,nufin fita daga dakin,,, Zaman mu da,Anty Sadiya agarin porthercothe zamane nq kowa tashi tafishe shi mukeyi don tana gwada min babu ruwanta da mu gaba daya, Hakan yasa nima na,share zancen ta sai harkokina na keyi abinda na gano shi kan su a hade yake a kaina Ban damu da hadin kan su gareni ba,don nasan cewa ko a tsakanin su babu wani shiri wanda zai dore, mai tsawo sunq yine kawai don wani manufa,,

****** ********* ****** Muna zaune a,falo don yau nadan tashi da karfin jikina, don haka na,sauko na zauna a falon kasa, Sai ga Aisha ta,shigo falon da gudun ta tana kokarin boyewa a,bayana, Yar aikin Anty Sadiya ce ta biyo bayan ta a fusace ga dukkan alamu inda ta samay ta zatai mata mugun duka ne, Aisha wace ta tsaya a baya na kadan tace wallahi ni idan kin kara buguna sai nace Allah ya isa, Na dubeta a cikin mamaki nake cewa may ke faruwa ne haka har da duka kuma,? Tace akan may zata dinga zuwa gurin da taga nayiwa Anty shayin kayan ta kuma na fada masu tun farko cewa kada wanda ya tafi backyard,nayi shayi agurin,, Nace wanan kuma sabon dokan yaushene aka saka shi a gidan nan ne wai da za,a ce kada yaro ya fita harabar gida,, Tace a cikin tsiwa to Anty ta tace na fadawa yara kada su taba mata kayan ta da aka,shanya,, Nace tau tunda har ta zo nan jekiyi hakkuri bazata kara tabawa ba ai don zan mata magana, Sai tace walle in tafito sai na bugeta don sai da na fada masu gaba dayan su kada su taba muna kaya , Nace to tunda ba zakiyi hakkuri ba ki tafi idan ta fito sai ki kashe ta tana juyawa Maimu tana shigowa ita ma rai a bace take cewa wallahi Anty wanan matan ta matsa wa yaran nan da zagi da duka komai sukayi sai ta dinga zagin su har da,dukan Amir tayi jiya,wai ya,shiga falo tana guga,,, Duk da raina ya,baci amma afili sai nai murmushi ina cewa ai maganin su ke nan don basu jin magana, Mai ta bude baki da nufin yin wani magana nace haba Maimu ya isa ma idan sun ga tana dukan su ai zasubar abin da bata so din,, Maimu tana fita dakin na juya inda Aisha take tsaye tana sauraren mu nace mata a cikin jan ido, Idan na karajin kun shiga tsabgan su a gidan na sai na baki kashi da kai, Saunawa kike son na fada maki cewa ku fita har kan wanan mutane, a gidan nan ,, Yarinyar a cikin kaduwa take ce min Allah mommy ba je gurin ba haka take muna da mun fito ta dinga hararan mu tana zagin mu, Nai mata fada Nikan har na mance anyi wanan zancen a ranan don ban sashi a,raina ba, Bayan Yaya ya dawo daga gurin aiki ya zagaya dakunan mu yana duban mu kamar yadda ya,saba yi muna, Ya koma kasa saboda ranan a kasa yake gurin Anty Sadiya itace da girki , Don haka ranan a dakin ta yake da zama kenan nikan sai mu kaci ga ba,da al,amororin mu, Sai da dare bayan duk mun gama abinda mukeyi ne Ramatu ta shigo take ce min wai ana magana dani a falo,sam ban kawo komai a raina ba don haka na mike zuwa falon kasa din, Ya na zaune saman kujera two seater tun daga nesa na gano bacin rai kwarai a fuskan shi,, Alaman cewa yaji wasu magan ganu iri, iri amma dai kuma ina isowa naga yadan rage bacin ran nashi,, Nace mai a cikin sakin fuska sannu da hutawa Yaya na juya gurin da take, zaune nace Anty sannu da hutawa ta amsa min a gitsere da umhumm a ciki ciki, Ina zama naji muryan shi yana cewa Meenat yaya akayi kika bari yaran nan sukewa Sadiya rashin mutunci haka, A cikin natsuwa nace Innalillahi, wa,inna,alaihim raji,un, na ce rashin mutunci daga wa yan nan yaran kuma har nawa yaran nan suke da zaauyi rashin mutunci ai sai dai rashin ji ko Ya fahinci may nake nufi don haka sai ya dan juya,gurin Sadiya yace ba,rashin mutunci kika ce yaran suna,maki ba ? Sadiya tace a cikin wani hasala, rashin mutunci mana tunda sun iya zagin babba suje gurin ki ki tare masu, Kallon mamaki nai mata nace zagi kuma Anty daga cikin su waya zage ki har yazo guna na tare mai kuma,? Nace a cikin natsuwa bake ba ko dan aikin gidan nan bazan yarda yara su zzage shi ba balle ke uwar su,, Nace matsala dai Atika ta samu da Aisha kuma da tazo gurina tabiyo ta zata dake ta,nai mata magana shine ta nemi tai min rashin mutunci kuma still na bata hakkuri don a zauna lafiya, Nan nai mashi bayanin duk yadda abin ya faru da bayanin da Aisha tai min na dukan su da Atika din ke yi, Shiru Yaya yayi na dan lokaci mai tsawo ba,tare da,ya,ce uffan ba saboda rayuwan shi ya, baci jin Atika ta,saka,mai diya,gaba ta hanasu, walawa, Duk sauraren shi muke kamar ba zai yi magana ba ina zaune daga gefe a cikin natsuwa ina sauraren shi, Anty Sadiya tace ai yanzu tunda baki bukatan kowa anan zaki iya yiwa mutane kage da sheri, don kawai a baki guri da Yayan ki k8 mamaye guri, Da sauri naga ya dago kai ya kalle ta yace ita Meenatu din ce take son abata guri ta zauna da diyanta kawai ? Tace a gadarance eh mana nufinta ke nan duk wanda ke a gidan nan ya zauna a under control din ta tunda suke da gida, To bazan yarda da wanan ba wallahi don yadda take da iko haka ma muma muke da iko a gidan, Yace cikin daga murya tunda har kince hakan tau sarara kiji abinda zan ce yanzu, Ita wanan yarinyar da kikazo da ita take takurawa yarana ki sani gobe nake bukatar tabar gidan nan, Tunda gida dai na Uban sune don haka bani bukatar zaman ta,a gidan nan, Ta samu yara a gidan su har ta dinga hattaran su haka ta takura masu ta hanasu shakat, Ita uwar su bata kawo karan ana takurawa diyan ta ba ke zaki iya kawo karan yar aiki ta samun takura, Sanan ita Meenatu dakike cewa wai bata bukatan zaman kowa a gidan nan, Wanan zancen ba gaskiya bane don Meenatu bata adawa da zaman ku anan garin, idan badon ita da ta tayar da hankalin ta ba akan zuwan ku da ba abinda zai sani wanan system din na retation da kukeyi, Zaman ta tare dani da diyana ya wadatar dani anan din a cikin kwanciyan hankali, Yace na dade da,sanin cewa baku kaunan zuria na Sadiya da babu abinda zai sa har ki fifita yar aikin ki a kan yarana ki basu daman wullakanta min yara a cikin gidana, Ya juya inda nake zaune yana cewa yanzu ai kinga abinda naki hasashen ya jawo maki lokacin da nace ban yarda wata tazo nan ba ku zauna anan don karatun yarana, Kika tayar da hankalinki a gidan nan har muka rasa gane kanki wai ke kina fushi,,, Sadiya tace a cikin wani irin murya kawai dai ni yanzu na gane cewa sai abinda Meenatu taga daman yi agidan nakawai mu bamu dana cewa don haka kake son korar min yar aikina, Yace dakata kiji wanan matar bazata zauna min a gida ba don Allah kadai yasan irin cutar min da,diya da takeyi, Shiru nayi a raina ina cewa Allah ke nan an kawo karana don ai min cin mutunci bayan ni ake cuta, Sai gashi Allah yai min gata ya mayar mata da aniyar ta, ance yar aikin nata, ta mara mutunci tabar gida,,,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull