Tarko complete novel - Chapter 128
Tarko complete novel Chapter 128: Tarko complete novel Chapter 128. ****** ********* ****** Tana zaune a cikin dakin ta da,waya a hannun ta sai zuba takeyi…
2,308 words
****** ********* ****** Tana zaune a cikin dakin ta da,waya a hannun ta sai zuba takeyi akan zancen abinda yafaru a tsakanin su , Sam bata,san da shigowan shi ba a,dakin irin kalaman da suke fita daga bakin ta,ne suka bawa,Yaya Abubakar mamaki anan yaji tausayin Meenatu ya shige shi don ita a tsakani da Allah ya fahinci tana zama da su gaba dayan su Don har yau ba zai iya cewa akwai wani ranan da ta zauna a tare da,shi akan zancen daya daga cikin su ba, Gyaran muryan da taji azaton ta lokacin ne zai shigo dakin nata amma tana daga kai sai ta ganshi a tsaye fuska a murtuke, Wanda hakan ya sata fahintar cewa yaji duk hiran da suke a,waya tare da Salawatu shu,uma,,, Bai ce mata komai ba a yadda take zato har safe tana sauraren zai mata magana akan zancen, sai dai shiru har zuwa lokacin da ya fita zuwa office,, Zuwa lokacin ne ta samu daman yin waya da Salawatu tana sheda mata cewa ai hiransu a kunnuwan shi yake a dare jiya, Itace ke cewa Sadiya din kawai ki share shi kamar kema abin bai damay ki ba ai yasan gaskiya ake fada ba karya ba, Hakan yasa Sadiya sake rayuwan ta har ta,samu dan sasauci a ranta, ta,dan sake rai,, Yaya Abubakar yana shiga office sai duk yaji abin duniya ya,damay shi, irin munanan kalaman da Sadiya take sakewa saboda zafin kishi a kan zurian shi yai yawa,, Malam tsoho ne ya,fado mashi a rai, alokacin don haka ya,daga waya yakira shi don ya labarta mai, Tiryan tiryan yakewa malam bayanin irin halin da yake ciki da iyalin shi da kuma irin munanan kalaman da daren jiya ya riski Sadiya tana fada akan iyalen shi, Murmushi malam tsoho yayi har sai da,Abubakar din ya ji shi a,cikin waya Yace Abubakar wanan shine, girma, ita girma tana zowa bawane batare da,sanin sa ba, Ire,iren wa, yan nan matsalolin zasuyi ta zuwa a gurare daban daban ,, Allah ya na,son bayin shi masu hakkuri da dubaiyya, a rayuwa, Don haka shawaran da zan baka anan shine kayi hakkuri ka kyaleta har gaba don gaba yana da yawa in har halinta ne zata kara watarana a lokacin sai ka dauki mataki a kai, Amma yanzu idan har ka kyaleta abin zai tsaya mata a rai sai taita zama a cikin zullumi, taga cewa zaka iya mata magana akoda yaushe,, Nan dai malam yai mashi nasiha akan rayuwan zama da matan zamani yai matukar jin dadin wanan nasihan na malam tsoho din sosai, Hakan ya sashi mantar da komai a ranshi yana harkokin shi sai dai zuwa yanzu zaman shi da,sadiya din ya,samu sauyi sosai don ba yarda a tsakanin su kuma, Ni Meenatu tun ranan da akai zance Allah yai min yaki na,kuma,gode mai sosai, ban kara bi ta kan zancen ba agai , Sai dai yanzu duk hankalina yana akan yara da abubuwan dake gudana a gidan ,, Ga maigidan ya hau cewa sai wanan yar aikin tabar mashi gidan shi don bazai zauna da ita ba, Nidai nawa kawai ido don uffan ban ce ba akan zancen don da na jefa kaina zan samu matsala,da,Yaya irin yadda naga ya hau, akai,, Wanan cikin yazo min da sauki sosai ba kamar wancan karon ba duk d ina dan kafa kafa,da kaina don gudun abinda kaje ya dawo, min, Nakan dan yi aiyuka kamar yadda na,saba yi a baya sai dai ba,sosai ba don gudun wahala, Yau ma kamar kullum bayan na gama duk wasu aiyukan da zan iya na,shiga dakina don na,dan huta, kafin maigidan ya,dawo, Karatun Alkur,ani maigirma nakeyi a, hada kasa kasa, cikin wata murya mai dadi, idanuwa na a rufe suke a lokacin, Ban san shigowar shi dakin ba a lokacin yana tsaye a kaina yana dubana a cikin so da kauna, Yana kuma sha,awan irin son addinin da nake dashi wanda ke nuna aslina na zama yar musulmai gaba da baya, Bai katseni ba sai sauraro na da yake a cikin sha,awa har na kai karshen suran , Sai na,danji kamshin turaren shi da,sauri na,dan bude idanuwana a hankali, Yana tsaye da alama ba shigowan shi gidan ba ke nan don ganin sauyin kayan dake a,jikin shi sabani tufafin da ya fita dasu zuwa office, Muna hada idanuwan mu ya,sakar min da murmushi, hannuwan shi, ya mika alamar na kama mai, Nadan kama ya tai maka min wurin zaunawa da kyau daga kwanciyar da nake, Yace ashe alaranmiya tana nan tana jan kira,a ne a daki nadawo har nayi wanka zan fita banga kin fito ba shine na leko ai, Na,danyi murmushi tare da dan kara gyara zamana ina cewa inda babu irin ku ko Yayana, zamu zama alarammiya, Ya daga,min gira cikin cewa ko ? Haka ma zaki ce min ko,? Nace cikin murmusawa hakane mana Yaya acikin rausaya kaina, Hakane mana Yaya don kai kowa yasan cewa babban malami ne kilama kai zaka gaji malam idan ya kaura,, Sai naji ya,saki dariya a cikin nishadi yana mai takowa zuwa garen inda ya dan kai zaune daf dani yana mai kallona, Yace dazun munyi waya da Mustapha yake ce min yau jikin malam ba dadi amma nace su kai shi asibiti a,duba muna shi, Da sauri na dago kaina ina kallon shi a cikin tashin hankali, Nace a wani irin murya subbahanallahi o,o Allah wanan dan tsohon wanan ciwon kuma ya kara tashi mai again, ? Yace haba may ye na tayar da hankaline haka bayan ko dazun munyi waya mustapha din ya fada min cewa,sun dawo gida anbashi magani ance yasha kwana uku su koma, gida Nace ni ina ma son naje gida don na duba mutanen gida saboda na,dade ban tafi gida ba, Ya mike yana cewa ina planning din hakan don nima ina,son zuwa amma sai naga yanzu tafiya kamar zai maki wuya don yanayin da kike a haka, Nace acikin dan marairaice murya don Allah yaya ka,bari na tafi na,duba malam don hankali yana gida,duk kwanakin nan, Yana tafiya yake cewa kinga kada ki daga hankalinki don na fada maki yaji sauki sosai yana gida, Nace a wani murya wallahi yaya malam tausayi yake bani Allah abubuwa sun mai yawa ga tsufa yazo mai sosai, Yace a cikin murmushi koni na tsufa balle malam wanda ya sharuwa har ya gaji, Ajiyan zuciya nayi ina ina cewa ko sun sha ruwa ai muna son su don suna da ranan su gare mu su ma, Yace ai,shi malam sun samu kira mai kyau gashi kuma rayuwan shi yayi shine a cikin taimakawa addini, Ya samu ya rayu acikin diyan shi da jikokin shi har da yayan su,, Yana fita daga dakin na mike tare da dan rolling din kaina da gyale na fito don zuwa duba Ramatu da yara da nake tsanmanin sun kusa dawowa daga islamiya,,, A falo na samu Sadiya tana waya nafito sai da na kawo daidai inda take nake cewa sannu da zama Anty, daga haka na shige a bina,,
****** ********** ****** Yau kwana uku da zancen ciwon malam wanda a koda yaushe muna waya dashi ina jin yadda lafiyan jikin shi yake, Idan na kirashi zamu dan dauki lokaci mai tsawo dashi muna hira a waya wanda maganar shi a koda yaushe kamar nasiha ce a gareni, Aminatu kiyi hakkuri da abokan zaman ki, don dole suyi hassada dake, don ke Allah yai maki baiwan da bazasu tabq samun irin shi ba, Kinga na farko ke yarinya ce karama acikin su na biyu ke yar uwar maidane na uku Allah ya azurta ki da zuria masu albarka, Ki fada min ta yaya bazasuyi kishinki ba akan su gashi kuma ance ta fannin ilimi dukka biyu kin dara su,,,, Dole akoda yaushe su dinga kawo maki sara da,suka da,sunar kishi , Aminatu ke wata babban Tarko ce dana haka a gidan nan wanda sai bayan raina mutanen gidan nan zasu gane cewa wanan auren naki da dan uwanki akwai manufa agare shi, Ki zauna da kowa da zuciya guda koda kuwa zama na rana gudane zakiyi da mutum, Aminatu koda yaushe ki kasance mai taimakon mijiki akan duk wasu al,amuran shi na rayuwa gida da,waje don ke tashi ce shi nakine, Nakan ce acikin dariya insha Allahu malam ina kokartawa kamar yadda kake umurtana da yi, Wani lokaci zai ce na bashi yaran su gaisa musan man ma Alhussaini wanda shine takwaran shi,, Yanzu yarana Amir yana da shekara uku da yan watani da haihuwa su kuma kananan su da shekara biyu da, rabi a duniya, Ba,wasu manya bane amma ga tsana irin na,kishi matan gidan mu su dora masu,, Yau tun dawowan shi na lura da cewa bai a cikin yanayin shi kamar da akwai abinda ke damun shi, Nayi tambaya amma sai yace min babu komai kawai shima bai san may yasa shi tun safe jin wanan yanayin ba, Haka na zauna na zuba mai abinci yadan tsankwara ya tashi baici irin yadda ya saba ci ba da farko, Naga dai yana dan fita waje yana waya sai ya dawo, ashe da Yaya mustaphane suke waya akan jikin malam din, Ranan hakana muka kwanta babu wani dadin rai ganin yanayi shi nima ban matsa mai ba na kwanta abina, Yayi barci amma ni sai barci ya kaurace wa ido sai faman juyi nakeyi kawai, Sai tunane nake na,saka wancan na kwance wancan din, Sai musalin sha biyu da rabi ranan daren jumma,a ce ranan alhamis da,dare,, Karar waya ya tayar damu gaba dayan mu a lokaci guda muka bude idanuwan mu, Jin da nayi ya ambaci sunan Yaya mustapha yana cewa Mustapha lafiya dai ko ? Yasa gabana faduwa daga inda nake kwance jikina ya,soma rawa, A hankali ya juyo ya kalleni yaga idanuwa biyu sai naji yana cewa Allahu Akbar Innalillahi waina alaihim raj,un,,, Da sauri na mike zaune ina cewa may yafaru ne Yaya ? A hankali naji ya jawoni zuwa cikin jikin shi sai naji ya matse ni kawai ajikin shi, Maimakon yai magana,sai naji yadan sa kuka a hankali yake cewa Meenatu sai dai muyi hakkuri Allah ya karbi ran malam yanzun nan, Kamar a mafarki naji maganan don munyi waya dashi da,safe da yammane da nakirashi har wayan ta katse va,a daga ba sai nai zayon cewa yana tsangayar shi gurin bada karatu,, Kan ayi salla asuba har mun gama shiri gabadayan mu har yara don bamu kara komawa barci ba, Su ma mutanen Abuja ranan zasu shiga Birnin kebbi bisa ga umurnin da aka basu, Duk wandaya ganni a ranan dole na bashi tausayi haka shima maigidan duk a rude yake, karfe karfe shidda na,safe jirgin mu ya tashi zuwa Abuja muna isa muka kama hanyan sokoto kuma, Sai daman kiran wayan Yaya Abubakar akeyi ind yake cewa yana hanya insha Allahu zuwa sha daya muna gida,, Ina zaune daga gefen shi duk na shige mai ajiki don ni kaina karfin hali nakeyi kawai a lokacin Wayan shi tai kara yadauka naga yana kokarin gyara,zaman shi kamar a,fili yake da mai kiran nashi Sai dafa baya na fahinci cewa Baba na ne suke waya dashi inda yake ce mai famu tafe gaba dayan mu ai, Sun gama wayan bayan ya kashe yake ce min Baba ne ke tambayan lafiyan ki, Nace cikin kuka yanzu Yaya shike nan malam ya tafi ya barmu ke nan, Cikin natsuwa tare da kara gyara muryan shi yake cewa, ai shi ya godewa Allah, Meenat, Yayi irin mutuwan da ake so mutum yayi ya mutu alokacin da duniya take da matukar bukatar shi, A cikin natsuwa da,sanyin jiki na kalleshi nace cikin kuka Yaya munyi rashi a rayuwan mu malam ya wuce kaka a gare mu uba ne a wurin mu, sai na sakuka bai hanani ba illa dan bubuga min kai kawai da yakeyi, sadiya tana daga dayan gefen shi sai cewa tayi kawai hakkuri za,ayi don hanyan kowane mutuwa, Mun isa Birnin kebbi goma da rabi na,safe don aikin jirgi ke nan, don munyi sammako mun samu jiragen safe, Tun a kwanan uguwar mu muka fara ganin motoci bila,adadi, ga mutane ta ko ina, Jama,a cicike har ba masaka tsunke a gurin sai bin mu da kallo akeyi, baba,Wadda sai kuka,shima yakeyi, Motoci hudu muka iso dasu don a Abuja suka taso muka hadu a,sokoto dasu, A take naji kamar numfashina zai dauke don tashin hankalin da nagani a ranan, kafana bana jin zai daukeni zuwa cikin gidan mu, A hankali naji Yaya Abubakar ya rugomoni zuwa jikin shi muna tafiya a tare sai kuka muke gaba dayan mu, Sauran mutanen da mukazo dasu suna,biye a bayan mu suma acikin tashin hankali, Jama,a suka taso zuwa gare mu don gani Yaya Abubakar ta iso suna faman cewa sannunku da zuwa, barkan ku da hanya, sannuku da hakuri malam ya rigamu mutumin kirki da,sauran su, Kowa da irin abinda yake fada muna shi dai yaya sai amsawa yaje amma hankalinshi yana a gareni don rike yake dani zuwa cikin gida, Ga cincirondon mutane amma haka yarikeni muka,wuce direct part din malam tsoho inda muka,sanu anyi mashi sutura ana batun fita dashi ai mashi sallah akaishi gidan shi, Muryan Yaya mustaphane ke cewa Meenatu bazata iya ganin gawan malam ba yadda take wanan kukan haka, yace ke Safiya tafi da Meenatu cikin gida har a wuce, Gida ya rude sai kuka ake yai munyi babban rashi a,rayuwan tarihin gidan mu, Muna shiga part din Baba musa don shine kysa dana malam din kuma,aciki mutane yan gidan mu suka taru, Na kaea saje wani kuka mai saurin ban tausayi take gurin kuma ya dauka masucewa Meenat dole yau kiyi kuka don shakuwar ki da malam tai yawa, Yau malam yai tafiyatai ya bar mu nace cikin kuka malam Allah ya gafarta maka ,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA SEENABU
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣2⃣2⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SUBBAHANALLAHI WALHAMDULLAHI, ALLAHU AKBAR,,,,