Tarko complete novel - Chapter 129
Tarko complete novel Chapter 129: Tarko complete novel Chapter 129. Yaya Abubakar ya dade tsugune a kan gawar malam tsoho yana kwararo mai addu,oin irin da…
2,817 words
Yaya Abubakar ya dade tsugune a kan gawar malam tsoho yana kwararo mai addu,oin irin da ake bukatan mutum yaiwa mamaci, Yana idar wa ya,mike a cikin kuka yayin da jama,an dake wurin suka dauki kabbara a lokaci guda cikin, natsuwa, Wanan ne ranan da muna ji muna gani akatafi da dan tsohon da mu kafi so dakauna makwancin shi na gaskiya Allahu akbar mutuwa tana a kan kowa amma sabo akewa kuka, Duk wanda ka duba daga yan gida har makwabta yan uwa da abokan arziki acikin kuka suke cikin yanayin tashin hankali, Ina dunkule yayin da naji mutane sun mike gaba daya cikin kabbara suna fadin Allahu akbar malam yau shike nan Allah ubangiji ya karbi bakuncin ka, Nima na yunkura na mike ina mai raka tsohon da addua abinda a yanzu yafi kauna da bukata a gare mu bisa ga yi wa mamaci kuka,, Muna jin dirin motoci sun tashi alamar a,gama yi mashi sallah, gida,ya kara rudewa da kuka sai dai ba,wai kuka ihu ko kururuwa ba, Gurin gaba daya yai tsit baka jin maganar kowa matan gidan mu da suke a tare a,part din Baba Musa suka fara fadin sannu da zuwa Meenatu , Yau malam yatafiyar shi yabar mu sai dai hakkuri don wanan rashin dake da mijiki sai kunfi kowa jin shi, Sai dai hakkuri kawai don yau so ya kare suna fadar haka ne don sanin irin sabon dake tsakani na,da malam din dakuma tsaksnin shi da Yaya Abubakar wanda bai iya boye feeling din shi gare mu, a gaban kowa, Na,dan daga kai daga inda nake zaune idanuwana sun kada sunyi jawur saboda kuka gayar tasbahana da na,sawo a,saudiya mai kyau da tsada a hannuwana ina dan ja a,hankali duk da istigifari nake amna zuciya na tunanen yau malam ya kara sheda wanene Allah a rayuwan shi yafi addabana sai addu,an fatan dacewa da rahamar ubangiji nake mashi,, Shiru kake ji bamu masu wani magan ganu a gurin sai tasbaha a hannun kowa ana nema wa mamaci gafara da kuma rahamar ubangijin mu Allah, Muna nan zaune a cikin jimami kaina yana duke don ina ji kamar zuciyana zai tsage gida,biyu, Naji anacewa ina hajiya Meenatu ga yaranta nan kuka,suke wai suna bidan ta, Daga inda nake can cikin rufar matar baba musa a tsakiyan yan uwana nadago idanuwa a karo nabiyu ina mai duban inda yaran suke fitowa, Ramatu da Maimu ne tafe min dasu gwanin van sha,awa duk da acikin tashin hankali muke bai hana a gane cewa yaran birni bane yaran dan kamannin su da ya nuna hakan, Nake cewa cikin wata irin dakysassan murya Ramatu kuje gurin Mama Saira a hada masu abin karyawa, Mutane kowa yashiga cewa Aklah sarki basu karya ba ni dai ban iya magana mai tsawo su Anty Safiya ne ke cewa daga pothercoth suke yau fa kowa sai mamaki ana kokarin dauko hira sai kawai na kara fashewa,da,kuka mai tsuma zuciya take gurin ya kara samun natsuwa, Ina nan zaune gwagon mu dake aure a Jega ta,shigo tana,cewa taso ki shiga daga cikin wancan shiyan ki daina kuka haka Meenatu wanan rashin na kowane amna ansan cewa naki yafi, Don malam ko kafin ya rasu saida yai zancen ki da mijinki da Mustapha ba a dade ba Allah ya aiko mai da manzon shi,,, Nace a cikin kuka bari na shiga gurin su Dije duk da ina jin wani iri a raina kamar idan na shiga zanga malam bai mutu ba, Dakin uwar gidan malam din na fara,shiga part din nasu sai kanshin turaren da,akai mai amfani dashi yake Mukallal Badar collection,,, mutane ne yan uwanta da makwabta wa yanda suka kwana biyu a dakin na karasa har gab da ita na zauna sai dai ban iya magana ba a lokacin sai hawaye, Nadan jima a zaune a dakin suna cewa nayi hakkuri dama wanan irin ranan kowa ke jira suda suka rigamu basu yi sauri ba mukuma da muka rage bamuyi nawa ba, Na mike a cikin kuka ina share hawayena na nufi dakin Dije wanda yake makil da yan uwanta da yaran su, Dije tana hangoni take cewa yanzu ake fada min cewa wai kun iso ashe sannun ku da zuwa tana kokarin gyara min gurin zama a kusa da ita, Na zauna nai shiru ina mai zubar da hawaye kawai dakin ma gaba daya shiru akayi ,Dije tace sai hakkuri hajiya Meenatu malam yai tafiyatai ya bar mu, ki bar kukan haka don shi da bakin shi yace bai son kuka jiya jiya da,safe yake fada muna hakan , Ina share hawaye nace Allah sarki malam naso nazo na ganshi wallahi sosai wallahi amma nisa da yanayin jikina ta hana, Ya dai tafi yana sa maku albarka dake da mijinki yana kara nanatawa da kuyi hakkuri a,rayuwan ku, yi zumunci dayan uwanku ko Samira da Iliyasu abinda ya fada masu ke nan da suka,shigo jiya, Nace cikin kuka acikin dasassashen muryana nima jiyan da,safe da mukai waya ya fada min hakan, Tace ai malam bazaka dora mai mutuwa ba,sam don da kafan shi da,bakin shi har ya,tafi,, Mun yi shiru gaba dayan mu dakin kowa da,abinda yake sakawa a zuciyan shi wanda bai wuce idan taka tazo ya zata riske ka ba, Part din Mahaifana na koma inda yan uwa suke shigowa,daya,bayan daya suna min sannu da,zuwa,da kuma ta,aziya, Ina dunkule don sam banjin dadi idanuwa na arufe naji muryan Anty Rukaiyya tana cewa hajiyan tayi barci ne,? Ramatu dake zaune daidai kaina take cewa anya sai nake ga kamar idonta biyu, Nace Anty idona biyu sai dai bana jin dadi ne sam har jiwa nake gani idan na mike, Tace subbahanallahi au kuwa kisha magani kinji zai fi ko zaki samu sauki, Tace dama wai zancen abincine da za,a dafa ga mutane a zazaune nace ko zamu hada kudi mu yaran gida,ne ? Cikin wani irin yanayin murya nace bari na kira Yaya Abubakar naji, may za,ayi, Koda na,daga waya muryan shi a dakushe yake don baka,jin muryan nashi sosai, don tsananin bacin ran da yake ciki, Nace a cikin dan kwantar da muryana Yayana dama zancen abinda za,a dafa ne a gida don ga jama,a a zaune, Yace a yar muryan nan nashi sorry please yanzu zancen da mukayi da mustapha ke nan za,a kawo komai, Na fadawa Anty Rukaiyya yadda mukayi dashi a,wayan tace to bari mu mayar wa kowa da kudin shi ke nan nace gaskiya, Kafin wani lokaci girki ya hau anfara dafawa,a,can part din Baba Hamza, ake dafuwan, Tun shigowan mu garin ina part din iyayyena kwance don banjin dadin jikina, Maimu ce da Ramatu suka shigar da duk wani belongings dina a dakina suka gyara saboda suna da yakinin cewa zamu kwana biyu a garin, Duk da mamana tana yiwa yaran kokari amma Ramatu da Maimu basu yarda sun bar yaran na yawo a cikin mutane ba, Bayan nai sallah La,asar ina dan gishingidi da tasbaha a hannu na ina ja a hankali idanuwa na a lumshe , Sai a lokacin naji muryan baba wanda tun da nazo bamu hadu ba sai yanzu, dashi, Bude idanuwana yayi daidai da Isowan shi dakin mahaifiyata, Na mike zaune a hankali ina cewa sannu Baba yace Aminatu sai hakkuri yau kin rasa malam dinki a take naji idanuwana sun ciko da hawaye, lokaci guda suka fara diga, Babana yace ai danaje gaidashi yake ce min kayan tea din shi sun kusa karewa amma, yasan kafin su kare zaki yo mai aike ai, Yace dake da maigidan ki Allah yai maku albarka kuma nayi kokari ko bashi na dinga kwantar maki da hankali a kan zaman gidan ku,,, Shiru Baba yayi ya kasa ci gaba da zancen da yake yi sai naga yana share kwalla shima, yana cewa Allah dai yai wa malam rahama na amsa da Ameen baba, Nasan Baba yai rashi mahaifi mai kama da,aboki agareshi don duk dare ya dawo daga gurin aikin shi suna tare da malam din suna hira, Baba na yace mutane sunyi yawa ban samu ganin ki ba tunda kuka,zo gashi ance baki da lafiya, Yanzu ma na,shigone don naiwa mamanku zancen girki da za ayi din gaki da yara da mutane Nace Baba ai ba sai anyi komai ba don a kwai abinci ga kuma tuwon semo can a nayi na dare, Yace amma dai a gara a,dafa ko kadan ne naga zaifi nace ko yanzu ga shinkafan da aka dafa na rana basuci ba, Bayan futan Baba na ne na mike jikina ba karfi na nufi part din Mama Ladi don tun da na,shigo ban je ko ina ba,, Sai a lokacin ma na tuna,aida abokan zamana muke tafe garin don bangan su ba tunda muka,zo, Mamane a part din ta da yaranta suna harkokin su har da dariya nai mamaki yadda mutuwar bata huda,su ba, Babu kowan daga cikin kishi yoyina a gurin mama din,, Nashiga da sallama na gabadayan su idanuwan su ya,dawo a kaina nake gaishe su a cikin murya mai sanyi, Mun gaisa ne na juyagurin mama ina gaishe ta, ta amsa min ba yabo ba fallasa,, Na,samu guri na zauna ina kallon irin yadda suke ta harkokin su hankali kwance, Ramatu ce ta kirani a waya tana part din mu don haka na mike jiki ba kwari na barsu , Ina fita mama ke cewa yar mulki sai yanzu taga daman zuwa gaida mutane ita, Samira tace kwance take bata da lafiya tuncan haka dai tazo, Mama tace bata da lafiya may ya samay cikin kaguwa taji amsa sai Anty Safiya ke cewa ina ganin fa kamar ciki ne , Mama tace ciki hmmm lalai an samu guri ita kadai ta zataita haihuwa ko kuwa, Yanzu dai ai dada mai surukulen ya tafi sai ayi mugani don dama shi ya kama mata, takewa mutane yadda taso, Mariya tace aiko ni dazun da taka kuka saida na fadi a raina nace ai dole taka kuka tunda shina malamin ta, Anty safiya ce tace kai haba haba jama,a wani irin magana na haka miya kawo wanga zancen kuma, Ciki dai na kuma na dan uwan muna itama yar uwar mu ta, Da wa yanga mata nashi suyi ta haihuwa basu kallon mu da mutunci da ita da take namu wani yafi, Dazun fa yar gurin Fatima zaki dauka amma Fatima ta hana tana cewa wai yarinyar bata yarda kuma nasan karya na, Zancen zaman ki da hajjana da ake cewa tare kukq maita ke da hajja, din shina yasa ta hana maki yar ta, Nan Mama ta hau fada tana zage zage tana cewa mi akai da irin su Fatima irin tsiya,
****** ********** ****** Na samu mata part din mu da Salawatu da Sadiya tare da yan uwan Sadiya a dakin Sadiyan ita kuma Fatima tana dakin ta da yan uwanta sunzo mata gaisuwa, Dakina na,shiga na,samu yarana an masu wanka Maimu ke ce min Anty ankawo kayan tea amma,saida suka bude naki sannan Salawatu ta canza millo ta saka maki nescafe, zallah, Nace kyaleta bazai karata da komai ba nan daga waya na kira brother na Aliyu mai bi ma,Asamau na'ce yazo ta hado min wani kayan tea don nasan halin yarana, da,shan tea, Allah gafurul rahimu yaya ya shigo part din mu saiga Aliyu ya dawo min da,sakona yake kallon sakon da yaji yana cewa fa canji nace jeka da,shi, Yaya Abubakar wanda ke alwala yake cewa ba,na, aiko da kayan tea din ku ba dazun shiru nayi wanda hakan ya tabbatar mai da,akwai magana, Har daki na biyoni yadaga labule yana cewa dake nake magana ina kayan tea din da nace a shigo maku dashi dazun nace ba millor kuma kasan yaran shi suke sha ba nescafe ba, Ya juya yafita rai a bace nace can ku gane sayayya sosai aka,sayo muna na daki, Ranan ba wani zancen barcin dadi a gareni don dana kwanta zan fara mafalkin malam sai na falka, Mutane yan uwa da,abokan arziki ta ko ina sai zuwa suke ta,aziyan malam daga ko ina, Abokan aikin Yaya daga Abuja sunyo tawagan su suma sunzo gaisuwa har Bk,, Iyayyen Maimu sunzo min ta,aziya daga tarasa naji dadi don har da tsaraban su sukazo muna nai masu abin arziki suma, Anan suke min zancen wai suna son idan ta,samu miji zasuyi mata aure nace ba matsala idan sun tashi sai su fada min, Ta tafi tare dasu zata kwana a can idan Allah ya kai mu washegari ta dawo, Anty Nani ta zo tana son wai ta koma tare da mu amma fir naki yarda nace ta bari kawai Ramatu zata iya muna komai insha Allahu, Anyi sadakan ukun malam a ranan ne kowa ya watse don komawa inda ya fito mu kuma yan gida aka tara mu a daren aka kara yiwa juna ta,aziya tare da kuma kiran hankalin kowa akan zumunta da kuma taimakawa junan mu, Naso Yaya Abubakar ya barni na dan kwana biyu a gida amma Baba na ya hana fir yace may zan tsaya nayi Malam dai ya riga ya tafi don haka na shirya na tafi da mijina da,sauran yan uwana, Ban so hakan ba amma babu yadda zanyi dole na,shirya na kwashi mutane na muka koma inda muka,fito Sai dai na roka ina son yabar ni, in dan kwana biyo a Abuja kafin na koma fatakwal din, Na,samu ya yardan min da hakan don haka idan mun tashi ni Abuja zan tafi daga BK, Zancen cikina a Birnin Kebbi su Salawatu suka samu labari don haka ta kasa boye bacin ranta a hakan,, A Abuja sa yada magana takeyi wanda ke nuna farin cikin mutuwar malam din tana cewa,ai yanzu sai ayi su gani tunda malamina ya mutu, Abokan arzikina na Abuja sunzo min gaisuwan rasuwan malam din sun kuma yi min murnan samun ciki, danayi, Amma na nuna,masu cewa banyi farinciki bani sai Anty Barister take cewa isan baki so ciki a yanzu ba sai yaushe ? Sai bayan kin tsufa lokacin abubu sunyi maki yawa,akai , Yanzu ne daidai lokacin haihuwan ki idanniin gana sai ku zama abokan shawara,dake da diyan ki, Anty Soloon tace wai may ma zai saki cewa haka bayan wanan cikin yazu ya kaiwa abokan zaman ki ko ina nasan kila har fitinan shi sai sunyi da maigidan ku, Sundan jima a tare dani suka tafi suka bar mu wanda a yanzu ban son zama guri daya saboda damuwan da nake ciki ga cikin jikina har ya turo zani ko, Yaya Abubukar ya tafi ya bar mu a Abuja shi da Sadiya sai dai ya,sa ta canza yar aiki don ba zai tafi da Atika ba kamar yadda yace , Don itama Sadiyan saura yan sati ta,dawo don turned din ta ya kare soon, Ga Fatima tace ita bazata Fatakwat ba indai har ba,dani za,a yi retation system din wata uku uku ba, Don haka aka bar zancen zuwan ta sai shu,uma Salawatu ke shirin zuwa, zama da mu, Na samu Yar gurin Fatima bata da lafiya again tun bayan dawowan mu daga gida take ta fama da rashin lafiya yarinyar haka take kamar sicklar ce ita, Sai naga uwar tana wani share zance na ta cin kamshi dani babu sakin fuska mai tsawo a tsakanin mu, Sauki guda yanzu ita Fatima halinsu ya banbanta da,su Salawatu don bata yarda ace wai anyi hadin kai da ita, Gashi ganin da sukai min tun a Birnin Kebbi duk ya saka su a rudani da tsorata, Saboda gaba daya sun gaa lokaci guda na canza ga kyau ga iya dressing din shiga ta manyan mata masu aji, Ga kuma ciki na uku a jiki na wanda hakan yin Allah ne bana mutum bane, cikin ya kara min kyau da girma, Wanqn abin yai matukar tayar masu da hankali gaba dayan su a kaina, Sun san cewa yanzu kan akwai aiki ja a gaban su a kaina dan abubuwa sun bamvamta dana farko, Itako Antyna Anty Amarya da suka shigo gaisuwan malam tsoho ta gani gefe guda tajani tana cewa haka nake son ki diya ta yanzu kan komai Alhamdullahi don ja damu sai an shiriya aiko mutun ya mai da kanshi abin kwarai a,duniya wani alfarmane ga ubangiji, Don mutum zai zama mai mutunci da kamala a idanuwan kowa tare da kima, Sai a lokacin naga amaryan da Uncle dina ya kara nagane irin su Salawatu ne matan office masu lakewa mazan mutane su aure su ko da tsiya koda arziki, Don da ganin wanan auren ba auren Allah da Annabi bane don matan ta dan manyanta ko, Ita ko Mummy da ta hada kai da ita don su cutawa Anty Amarya da tashigo yanzu ba wani jittuwa a tsakanin su sai fada da tonon asiri wa junan su,, Shiyasa idan an yi amarya manya kance kada ki yarda da hadin kai don idan amarya ta zama yar gida dake zata fara masifa taso ta turaki waje don ta riga tasan sirin ki ko,