Tarko complete novel - Chapter 130
Tarko complete novel Chapter 130: Tarko complete novel Chapter 130. ****** ********** ****** Tun zuwana Abuja ban fita ba sai yau din nan nake son fita,…
3,581 words
****** ********** ****** Tun zuwana Abuja ban fita ba sai yau din nan nake son fita, don zuwa important wurare, Saye nake cikin wani super exclusive mai kalar danye kore da ratsin jar kala , Daga sama na dora gyale irin mai tsada nan na matan mayan , sai dan kamshi mai, taushin shaka, Takalman kafana mai dan hill da stones masu ruwan golden, ja,,, Sam ban san da zaman su a falo ba sai fitowana nagan su zaune girshi a gabana share su nayi ina tafe da yarana, da su Maimu a bayana, sai hayaniya mukeyi, Gaba dayan su duk suka,bimu da kallo a lokaci guda, saboda munyi matukar kyau duk da kishi bata bukatan kwalliyan kishiya, Nace au kuna nan a she cikin dan kada keys din motan dake a hannuna, Nace zamu san shiga gari sai mun dawo daga haka muka bar gidan, Tsaki salawatu taja race inda bamu san asalin mutum bane sai yai mina yanga, haka, Fatima tace to ai asalin su daya da wanda ya aje ki ni ina mamakin yadda kuke ganin laifin Meenatu ita kadai haka, Ita fa ba yinta bane yin maigidan ne don shine mai wanzar da komai ba ita ba, Fatima ce ke wanan maganar duk da zafin kishin da take ji akaina bai hana ta fadar laifin maigidan da take gani ba, Nice ke jan motar Ramatu tana dayan gefen nawa, yaran suna baya zaune, Uguwar su Ramatu muka nufa don muyiwa mutumin dake kula mata da yara jajen hasarar da yayi a kasuwa, Mutumin yaji dadin ganin mu inda na,bashi dan wani abu mai tsoka su dan kara, Daga gidan muka wuce uguwar su Anty saloon mun kai wani lokaci agidan ta muka,nufi gurin Anty Barister, Na dawo gida a gajiye tun a,bakin get mai gadi ke fada muna cewa Fatima tana asibiti da yar ta, Kamar na share kada na tafi amma sai naga rashin dacewan hakan don ko banza ai diyar dan uwana ne, Tare da Maimu muka shiga asibitin inda muka samu Fatima a,cikin tashin hankali tana ganina take cewa Meenat ki taimaka min babu wanda yazo tun zuwan mu gashi likita yace sai an mata test, Na karbi takarda naje nadawo haka naita sintiri a,sibitin inda akace nemoniaer ke damun yarinyar kuma, An bamu magani sai tara na,dare muka,dawo gida a gajiye, Ba laifi don yarinyar ta samu lafiya sosai sai barci takeyi, Ina dakina na fito daga wanka sai ga Fatima din tashigo tana cewa tazo ne tai min bangajiya, Nace haba dai ai ba komai yaro fa na kowane ki dai kula,da ita saboda lafiyan ta tai godiya ta fita, A kofa suka hadu da Salawatu sai cewa tayi ai daji kunya wallahi don banzaci haka ba, Fatima tace ni banda lokacin ki don abinda ke gabana ya damay ni lafiyan yarinyana nake fata, Don haka abinda kike zato bashi naje yi ba nawa ya kaini, Ai ita Meenatun tafi kowa,sanin halin kowan mu basai na shiga yin sheri ba, kamar yadda kike yi, Ai,kuwa sai cacan baki ya fara atsakanin su kowana sakewa dan uwa magana mai zafi, Hayaniyar yai yawa har takai ga mun fito waje ni da Ramatu, nake basu hakkuri da cewa wanan ba girman su bane, ya kamata ace an daina wanan a gidan, Aikuwa Salawatu tayo cikina kamar wace ke a jirace dani tun farko tafara jefa min magana cewa , Na kama ksina don duk abin da nakeyi kyaleni kawai akeyi bawai nafi karfin su bane, Yanzu ai karya na ya kare tunda malami na ya mutu duk wani abinda nake takama dashi ya wuce ko, Cikin murmushi nake ce mata aini yanzun ma nake don wanda nake takama dashi yana nan daram don ko ita da shi take takama, Tace a cikin kaguwa wana kenan nace mata a gadaran ce da ALLAH mana, Sai tai shiru tana cewa ba wani wallahi duk karyane inda ma bamu san gaskiyan zancen bane, Nace mata to shike nan zaki ko fani don Allah yafiki yafi mugun nufin ki ai Fatima tace shi dai dan sheri baiji dadi ba wallahi, Ni ba irin Sadiya bace da zaki uya,sawa a kwana a lokaci guda ni wallahi ke kin san nafi karfin ki Salawatu, Nidai na shige kawai abina ba tare da na tsaya kara sauraren ta ba don1 na mayar da ita wata yar daba ko, Ramatu ke cewa hajiya ki daina kula wanan mara asalin da bata san Annabi ya faku ba,, Ina shiga muka rufo part din mu don dama dare yayi a lokacin don har yara sunyi barci ko, Maganar ta,sun balain sosa min zuciya sosai don irin yadda ta,aibanta min kakana mai mutunci da dara a gabana wai kuma kakan nata mijin ita ma, takewa wanan irin kazafin, Nasa a,raina babu wani hanyan da zamu shirya nida ita ko don wanan can fuskan da tai min, akan malam tsoho, Ita ko Salawatu tana shigewa part din ta takira sadiya tana,sheda mata irin cin fuskan da tai min yau din, Tace ai bata da laifi maganar Fatima gaskiyane dubi u yadda yake wani washe baki idan ya ganta a gaban shi, Sadiya tace ai ke baki ga komai ba sai kinzo zama zakiga tarairaya da zaran yaga kamar tai fushi ranan babu fita a gare shi sai idan yaga ta,sauko, Salawatu tace lalai yarinya ta samu guri zan gwada mata ita karamar yar kauye ce, Sam yanzu shi inba Meenatu ba baida tunanen kowa a cikin mu sai dai nata da yaranta, Salawatu tace idan na shigo zata san kwanan wasa don wallahi duk yadda zanyi na barar da gwanatinta a gare shi wanan karon sai nayi,
ZEE MAKAWA YELWA SEENABU
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸
ZAINAB IDRIS MAKAWA
FA,INNA MA,AL USIR, YUSURRA,,,,, INNA, MA,AL,USIR YUSURRA,,,,
Satin mu guda zaune a Abuja muka shirya komawa Fatakwal gurin Yaya Abubakar wanda zuwa yanzu yakira waya akan na dawo mai da yara saboda karatu yafi a kirga Tafiyan safe mukayi don haka mun samu gyara ko ina na gidan wanda ya koma tankar babu, kowa acikin sa, saboda kuran da yayi,, Sadiya wace take nuna vata so dawowan mu ba,saboda wai yara sun cika gida da hayaniya, sun damay ta, Nace a raina O,o ni Meenatu yanzu kuma yaran sune abin gujewa kuma, ni dai na godewa Allah da ya bani yaran, Don haka na natsasu ta hanya hauwa sama dasu gaba daya don gujewa baki,,, Na,samu suka fara barci da guda gudan su har gurin ya lafa tsit yadda take son jin gidan Nasan ba laifinta bane don bata saba da hayaniyan yaran bane, Sai da yamma maigidan yadawo daga office tun a kofa yake kiran yaran da cewa Yaran Uncle suna ina ne, wai, Babu kowa a falon sai TV dake aiki ana wasan kokuwa a cikin sa kawai, A hankali ya daga kai yanawa ko ina kallon tsab don fahintar ko bamu dawo bane, Sai dai idanuwan shi sun sheda mai cewa mun dawo din don irin yadda ko ina na falon gidan ke kyalli da haske ga kamshi yana tashi, Abinda ya haddasa mai sauke wani irin sanyayan ajiyar zuciya ke nan,, Tare da dan lumshe idanuwan shi a hankali ya dan fara takawa zuwa saman bene inda muke da yaran, Still ba,wani hayaniya da ya tare shi har ya kai kofan dakin namu inda a lokacin ne Maimu ta fito don zuwa kasa gurin Ramatu, dake kitchen tana girki, Sannu da dawowa Uncle tace a cikin dan kaduwa ya kula da akwai yar kaduwa a tare da ita don haka yadan tsaya daga baya yana cewa ko tana ciki kuwa tace eh uncle, Ya turo kofan ya,shigo da,sallama ina zaune a kasa da alaman tun da,nai sallah nake zaune a,gurin na mike kafafuwa na, don naji dadin zama da kyau, Acikin fara,a nake cewa sannu da zuwa Yaya,na yace cikin dan sakin murmushi C U kinga daman dawo ke nan yau ko, ? Nace ai ban gama abinda na keyi ba ne ko yanzu ma na dawo ne gudan kada muyi laifi, A hankali ya tako har inda yara suke kwance suna bancin gajiya inda Amira take ya nufa yana dan taba ta a hankali sai ta bude idanuwanta da,suke cike da nauyin barci tace Daddy,, a cikin wani irin yanayi, Ina daga gefe ina kallon su sai suka bani tausayi don a kwai wani irin shakuwa tsakanin uban da ita Amira, Hannu ya mika ya,dauko ta tsab daga cikin yan uwan ta ya nufo inda nake zaune, K8n dauke min uwata kin hanata ganin Daddy ta ke babu abinda ya damay ki ko ? Nace a cikin murmushi nima ai an hanani ganin nawa Daddy din Baki da tausayi Meena don nasan cewa wanan yarinyar duk inda kuke acikin damuwa take ita, Nace ai ita ce tasawa kanta mukan free muke muna ta harkokin mu sai naji yace, Zaman fitinan da kukeyi acan duk kun ruda min gida ban san ko sai yaushene zakuyi hankali ku daina wanan kishin naku ba na hauka, Da sauri na dago kai ina kallon shi a cikin mamaki don nasan zancen dan hayaniyar da akayi can abuja tsakanin mu shine har ya samu labari, Yace kina mamaki ne ko kin manta cewa, gidana ne duk abinda ke faruwa a kunnuwa na suke, Yanzu ita Fatima wace tace da farko bazata zo ba ta dawo da zancen zuwa kuma, Saboda kin bata mamaki kina kula da harkan ta duk da ita tana gwada maki tsana a fili amma hakan bai sa kin shareta ba, Tace taje asibiti da yarta babu wanda ya bita sai da kika dawo ko gida baki shiga ba kika bita can din,, Nace kai duniya duk a ina ka samu wanan labarin haka Yayana, Kafin yai magana Aisha ta farka daga barci tana cewa sannu da dawowa uncle, yayin da ta mike zuwa gare shi, Na fara nauyi a lokacin don haka da kyat na samu na mike inda muka sauko kasa gaba dayan mu har yaran, Munkai wani lokaci a tare da shi da yara kowa da abinda yake fada mai acikin hiran su muna zaune da Sadiya daga gefe muna dan hira jefi jefi a tsakanin mu akan abubuwan da ya shafe garin mu,
****** ********** ****** Tafiyan Sadiya yazo tare suka tafi da ita don haka muka rabu da ita a cikin mutunci, Sai a lokacin ne take ji a ranta abubuwan da tai min a lokacin da tazo da batayi su ba saboda wanan dawowan da mukayi bata da yar aiki a tare da ita komai namu a tare a keyin shi kamar farko, Hakan ya sa ta jin dadin zama damu kamar kada ta koma Abuja, din, A can ne rikici ya kaure a tsakanin matan shi don Fatima tace ita sam bata yarda da zancen zuwa da Salawatu ba sai dai itace zata tafi, Wanan zancen ne har ya jawo masu mumunan tashin hankali, a tsakanin wanda suka dinga tonawa kan su asiri da abubuwan da bai sani ba a gidan, Yana daga sama ya sauko kasa rai a bace cikin tsawa yake cewa wai may ke faruwa ne haka,? Babu komai inji Salawatu take ce mai acikin huci tana mayar da numfashi, Fatima tayi maza tace akan zancen tafiya Fatakwat ne zaki ce mai babu komai, Yace kamar ya zancen tafiya fatakwat kuma Fatima tace ai tasan cewa nice zan tafi amma sai ta haushiri wai itace zata, Da can baya da kika tafi waya hanaki ke da yanzu don nace zan tafi har ki sani baki, Cikin daga hannu Yaya Abubakar ya maza ya katse ta da ce wa may ya kawo wanan zancen yanzu, Salawatu ta kalle shi a cikin natsuwa da yake ta iya makirci tace ni dai banda magana,da ita tunda ba itace mai tafiyan ba Shine yanzu ta samay ni take cewa dani wai ita ce zata tafi tare da kai don dama zuwan tane, Shine don nace ai ni kaine kace na shirya idan Sadiya ta dawo sai na tafi tunda nan a gaban mu tace idan har Meenatu bazata dawo ba ita bazata ba, Shiru Yaya Abubakar yayi na dan lokaci mai tsawo saboda ranshi ya baci sosai a lokacin, Gaba dayan su gurin shiru sukayi don sun fahinci rayuwan shi a bace yake sosai a lokacin, Ganin sunyi shiru yasa shi cewa, dago kan shi dake kasa ya dube su daya bayan daya yace idan hakane har an rasa wanda zai bar wani ya tafi sai ku shiyar mu tafi gaba dayan ku idan wata ukun yayi sai ku dawo, Daga haka yabar falon ranshi a bace don yasan hakan da yace zasu tsaya a tsakanin su, sulhunta kan su akan zance, Yadda yai tsan mani hakan bai samu ba don gaba dayan su, sun hau don haka babu wace ta jaye zancen, tafiyan daga cikin su, Bai ce masu uffan ba don haka suka shirya zuwa tare, Sun iso muna a cikin dare don haka nice ranan mai masaukin baki na tare su a cikin mutunci da haba haba, Bayan mun shigar masu da kayan su a dakunan su inda sai kallon girman gidan suke da mamaki, Salawatu itace farko sai Fatima daga ciki dakin da Sadiya ta fita a cikin sa akwai komai a cikin dakin, Muna shiga part din mu Ramatu tace uwar dakina akwai magana a gidan nan don da ganin wanan tafiya akwai rikici a cikin sa don haka mu namu shine ido kawai, Yanzu ban son fitina Ramatu don haka zanyi iya bakin kokarina naga na gujewa duk wani abinda zai kawo tashin hankali a tsakani na,da kowacen su,,, Washegari ma mun masu abin karya kumallon safe inda tun a nan maigidan ya zaunar da mu cewa mu tuna cewa nan bariki ne don haka,baya son hayaniya a,gidan shi kuma duk wace tai mai hayaniya a gida saboda kishin banza zasu hadu da ita, Haka mu ka zauna mu uku saboda tujara kowa tana jin dan uwa a,rai kamar zata shake yar uwar ta,,,,, Sau dai babu halin nunawa a fili Fatima wace tai sanyi da yawa yanzu muke dan zaman shiri da ita sama sama don ba kamar yadda mukai zama da Sadiya,ba da tazo, A tare yaran mu ke zuwa makaranta duk da ita yarta sickler ce yau ciwo gobe lafiya, Wani magani da uban ya karbo ma yarinyar saboda warin shi uwar bata so wai yana hawa mata kai nice nake daurewa duk da ban so na,shafawa yarinyar a jikin ta, ko ina,sai na shafe ta dashi tas kafin ta kwanta, Wanan abin da na kewa yarinyar ya kawo shakuwa a tsakani na da ita tun uwar ta na dan sayi dani akan yarinyar uwar ta gaji ta,saka muna ido ranan da take da duty a gurin mu yarinyar ke kwana,, Wanan abin da Salawatu tagani shine ta dauki fitinan duniya ta sawa kanta cewa wai mun hada mata kai ni da Fatima don muna yan gari guda, Can ta hade da matar wani director kusa da gidan mu gidan su yake don haka suke kawance, Nasan da matar tun farko matar batai min ba don ita irin matan nan ne masu sakaci da addinin su sosai matar dai muna musulmaine ita, Da zaran maigidan ya tafi office zata fita zuwa gidan ABUWA, sunar matar ke nan yan yaren lokoja ce matar, Daga haka har suka fara fita yawon shiga da fice irin na matan da basu dogora ga Allah ba, Duk gurin da, suka ji cewa, akwai wani hatsabibi ko hatsabibiya sai sun kai kafan su gurin, Tashin farko har abin ya fara tasiri a kan maigidan inda hankalin mu gaba daya ya tashi, Fatima ce ta fara samuna da zancen cewa wai kuwa na san abinda yake gudana a gidan nan yanzu fa,duk marance sai Salawatu sun fita da maigidan zuwa unguwa , Idan sun dawo kúma zakifa sun shige dakin ta har tsawon wani lokaci kafin ya fito,, Duk da kishi gaskiya,ne ga mace amma sai na dake kawai nai murmushi nace kai maman Aina ke nan halin wanan shu,umar matar ne kuma baki sani ba, Ai al,amarin ta sai Allah shine kawai zai shirya ta daga sherukan ta don ta riga da tai nisa ga kaucewa ita Nace idan za,a soni a,soni don Allah idan kuma baza,a,soni ba zan hakkuru har randa abin zai dawo a kaina don al,amarin na miji mai mata kamar tashin tsuntsune, Watarana yausaka akan idan ya motsa kuma sai ya tashi akanki dake dashi sai watarana, Ido ta kura min tana cewa ban fahinci may kike nufi ba k8na nufin kice mi ke baki irin yan shige shigen nan ne ko kuwa, Nace eh to inayi irin na shan hakin maye da sauran kayan mata, ni bayan wanan ban wani zuwa gurin kowa wallahi Allah Ga Allah na dogora gareshi nake kai kukana ga duk abinda ya shige min duhu, Wani irin kallon mamaki Fatima ke min yayin da take kokarin zubar da miyau daga bakin ta don na fahinci tana da dan karamin ciki ne ita ma, Nace ba dole sai kin yarda da zance na ba amma ni nasan cewa Allah ba zai bari Salawatu ta cuce mu ba, Duk yadda shu,uman cin Salawatu yaso ya kama maigidan sai kuma ya kubce daga sherin ta, Ance al,amarin namiji mai mata baida tabbas a kullun akan mace daya, Abin kamar tsuntsune yau idan anayi da ke sai kuma ya tashi ya koma ga waccan dake dashi sai watarana, Hakane muma al,amarin gidan mu don maganar Fatima gaskiya ne sai dai ban yarda na,sawa zuciya na cewa Salawatu ta rinjaye mu ba don nima ina iya kokarina gurin kai kukana ga Allah ubangiji subbahanahu wata,ala, Ance wai tsafi gaskiyan maishi don ba laifi tana yadda ranta ke so a kai, amma sam dagani har Fatima wace a yanzu muke da dan fahintar junan mu saboda sanadin yaran mu, Wani lokaci nakan tuna da malam tsoho sai inyi kuka don nasan cewa na fikowa rashin shi don da yana da rai da yanzu ya bani shawaran yadda zan bullowa wanan al,amarin na Salawatu, watau sabon sallon ta, da tazo muna dashi Abinda yazo min arai yau shine hiran mu na karshe da malam din da nake cewa malam ni har yanzu tsoron wayan nan kishiyoyin nawa nake ji, cikin murya mai rauni nake cewa duk sun girmay min Don duk sunfi karfina wallahi zama kawai nake da su don haka kuke son ganina, Malam yai murmushi tare da,dan yin jim.kamar may son yin tunanen wani abu can yace amma basu fi karfin mijin ki ba ko ? Yace indai har suna tsoron mijin ku to dole ne suji shakkar yi maki wani abu don hakane na dauko daga gare shi nai maki hikimar da,zai sa shi bi ta kanki, Sam banyi tsanmani ke yar wanan gidan kuma haifafan Kebbi har zakiji tsoron kishiya ba Don hakane na hadaku ke dashi saboda na san halin kowan ku hadin naku yai wa kowa daidai saboda hakkurin ki Mijin ki shine gurin ki a duniya da lahira, don haka kamar yadda Allah ya rufa maki asiri kika samay shi a,sauwake ta kissa da da dabarun ku na mata haka ma zaki kara rike abinki gam, a hannun ki ,bawai sai kin rike shi ajikin ki ba kowa yasani, Har kice zaki hanashi zuwa wajen wata matar da ke da hakki a kanshi, Ki barshi da wanan don jikinshi ne ai Ki bari yayi yadda yaso yaji dadi son ranshi da,wata, ya morewa rayuwan shi don Allah ne ya halat ta mai yin hakan Gurin ki ke kawai shine kiyi kokari ki rike zuciyar shi inda duk yaje kece abin tunanen sa, abin farin cikin sa, Indan har zaiyi magana wanda ya,shafi alheri a cikin matan shi sunan ki zai ambata don kece yasani maishi,, Wanan zai sa duniya da sauran matan su zaci cewa wani asiri kike ta yi wanda zai iya saka zukatan su ga hauka don basu san sirin ba,,,, Ina kaiwa nan da tunane na sai na sauke ajiyan zuciya tare da lumshe idanuwa nace a fili Allah yajikan ka malam , wasu yan hawaye masu dubi suka biyo kumci na, Na furta a fili cewa lalai malam kayi gaskiya don haka zan mike na kara kaimi gurin ganin cewa na kara cusa kaina ga zuciyar maigidan tako wani hanya muddin bazan kaucewa Allah ba, A kan Fatima na fara aiwatar da shirina don haka sai na kara dan janta a, jiki don na fahinci nata al,amarin akwai sauki, Idan har taga wani abin bacin rai nakan nuna mata cewa ta mayar da,shi ba komai ba ta shanye, Tun bata iya ba har tafara koyi da hakan sai muka mayar da Salawatu kamar mahaukaciya, Duk irin shu,umancin da zata gwada wanda zatayi don ran mu ya baci sai mi hade mu shanye mu mayar da abin ba komai bane, Tankar bamu san cewa tanayin abin ba balle mu kulla har kan ta sai kumahakan ya fara bata haushi saboda ba hakan taso ba, Matsala guda ne shine bamu yarda ta shiga hakkin mu ko kadan don a ranan girkin mu mukan yi kokarin ganin mun kanainaiye, maigida ta yadda baida lokacin ta sai namu kawai, Wanan abin yana matukar batawa Salawatu rai don sam bata taba tsanmanin cewa za,a samu natsuwa a tsakani da Fatima ba irin yadda tasan cewa ba shiri a tsakanin wanda indan an biyo gaskiya itace duk umulabaisin hakan a tsakanin mu saboda anyi ance din ta da yai yawa,,