Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 131

Tarko complete novel - Chapter 131

Tarko complete novel Chapter 131: Tarko complete novel Chapter 131. ****** ********* ****** Shirye nake a cikin wata doguwar riga baka mai dan fadi a kasa…

2,488 words

****** ********* ****** Shirye nake a cikin wata doguwar riga baka mai dan fadi a kasa sama a dan tsuke wanda ya baiyanar min da surar cikina wanda kusan wata biyar da dan kai zuwa yanzu, Na fito ne da niyar tambayan shi ina son fita zuwa gidan su kawata yar Yola wace tazo min har sau biyu bayan rasuwan malam tsoho din Zaune yake a falo da waya a hannun shi, da alamar wayan da yakeyi mai mujin manci ne sosai don ita madam din tana daga gefe a zaune cikin sauraren shi, Tunda na fito yake kallo har na sauko kasan yayin da yai min kur da idanuwan shi, Yana a cikin wayan amma hankalin shi yana a gare ni tun da nake saukowa daga stairs din sai gab dashi na zauna a hannun masagalin kujeran da yake zaune a kai, Naji lokacin da ya saki yar yajiyar zuciya tare da dago kai gareni firgigit, Yace wanan shigar haka kuma,sai ina nadan rausaya kai ina cewa wanan kallo haka yayana ko so kake nayi tuntube na fadi, Ya girgiza kan shi yana cewa ke din ce da wani batta da,kama kina,wani tafiya kamar mai tafiya a gajimare, Shi yasa ai nake maki kallon mamaki don da mutum zai ce Meenat sai ki ce ke ai duk jikin ki ciwo ne, Nace haba dai Yayana ni ai yanzu abin tausayi ce duba fa yadda,duk na koma a lokaci guda, Mikewa Salawatu tayi tabar gurin a cikin bacin rai, Na bita da kallon harara ta wutsiyar idanuwa ina cewa a raina sai dai kare ya mutu da haushin kura, Har ta kai kofa sai ta juyo tana cewa idan ka gama kada ka manta da zance na please, don ina jira ta fada fuska a daure, Tare da tabe baki ta, ta juya zuwa cikin dakin ta sai dai zuciyar ta tankar ta buga saboda wani bakin kishin da take ji nawa a ranta, Nace cikin dan murmusawa Yaya yau ina son zuwa gidan yan Yola ne na mayar da kafa nima, don zuwanta biyu ban tafi ba ni, Yace cikin murmushi yau kice min yawo zaki fita ke nan yai daidai da fitowan Fatima daga dakin ta, Tun kan ta karaso take cewa yau fita zakiyi ke nan nace cikin dan wasa da keys din motana eh wallahi, Zandan tafi nan na,dawo tace ashe bari na biyo ki sai mu fita don ina son sayen abu dama, Yace da izinin wa zaku fita,din nace a cikin dan kwantar da murya ai muna,afuwan please, Ya girgiza kan shi yana cewa dama dai kuna da inda zaku tafi ke nan ni fa ban fahinci wanan wayyon da ake muna ba na kabawa, Na mike tsaye ina murmushi nake cewa, ai kafi kowa sani don kai ka hada shi, Yara na kwaso tare da Ramatu muka duru a mota guda amma sai da muka rufe par din mu kafin mu bar gidan, Bayan fitar mu ne tafito a kufule tana cewa kaga dama na fahinci cewa da sanin ka ake min hadin kai a gidan nan, Gashi yanzu a gaban ka,sun fita batare da sun bukaci na bisu ba,, Mikewa,yayi shima ran sa a bace yana cewa ban son zancen tsegumi saunawa kike fita a gidan nan su basu fita,ba, Kuma na fita tare dake basu damu da cewa wani abuba sai yau da,suka fita da yaran su, Tace to dama kasan cewa zamu fita don haka sai mu tafi ke nan Yace ba inda zani yanzu don motana,suka dauka suka fita dashi, Ta juyo cikin nuna halin su na yan duniya tana cewa oh hakama zakace min ke nan ? Ya gyada kai Eh babu inda zani sau naga sun dawo zanfita don bazab bar gida babu kowa ba, Ai dama kai indai zance na Meenatu ne baka iya, boye feelings dinka,akai gaban kowa,sai ka nuna hakan, Ji fitowa take muna magana da kai amma duk kawani rude kama daina waya saboda ganin ta, Yace cikin dakewa wanan kuma matsalar ki ce don ni ban daina,waya ba sai da na gama, Meenatu bakuwatace da zan rikice don na gane ta tace saboda kai baka san yadda kakeyi bane ai , Ya dan maida kan shi a bayan kujera tare da dan lunshe idanuwan shi yana ma lashe laben shi na sama yace, Duk surutunki ya isheni a kai wallahi tace eh ai dole kace hakan don ba yau ka fara wullakantani ba a kanta Yace daidai shigowan baba Wadda gidan shout,up my friend kin cika min kunnuwa da yawa, Meenatu dai Meenatu dai haba wanan wani irin rayuwa ne ke a koda yaushe dai cikin an maki laifi wake baki rike girman ki ne for god sake, Don haka ki bace min da wanan zancen banzan naki ya isheni haka, Duk abinda kikaga dama kike a gidan nan daga ita har Fatiman sun kawo ido sun saka maki don kawai a zauna lafiya dake amna still hakan bai maki ba,sai kuma kin kawo wani tsegumi akai, Tsaban fitina tagani a idanuwan shi wanda hakan ya sata saurin juyawa don barin falon Sai sukayi kicibis da Baba wadda wanda take da tabbacin cewa yaji zancen nasu, ko,, Ido a rufe ta juya zuwa dakin ta inda ta fada saman gadon ta cikin tashin hankali Don bata tsanmaci haka ba daga gare shi a kan Meenatu don tana ganin cewa yanzu ta rufe babin Meenatu din har Fatima a gare shi, Idon ta a rufe ta kira wayan ABUWA tana fada mata yadda yai mata cin mutunci yanzun nan a kan matan nashi, a cikin kuka,, Cikin takaici ABUWA din tace, sam ban san irin wanan shedaniyar yarinyar ba yanzu zata ce duk abinda akayi aka bata taci bai shigeta ba, Salawatu tace a cikin wani irin murya ni ina duban yadda nake narka duk wani abu nawa amma wanan shegiyar yarinyar taki bar min Abubakar ni kadai, ABUWA tayi murmushi har za,a iyajin ta acikin wayan tace kyale ta kawai ai za,a yita yakare don zan gwada mata dani take wasan ,, Don haka kada ki damu zan san abinyi kwanan nan isha Alkah sai tabar maki shi don babu inda zaki, koma sai dai ita ta koma, tabarki a nan din, Wanan zance na Abuwa yaiwa Salawatu dadi sosai a rai don dama tai hakane don ta suku tai mata abu mai muhinman ci wansa zai kawo rabuwa tsakanin Meenatu da maigidan, Don dai tasan cewa yanzu dai babu malam tsoho wanda a da nake kuri dashi yake min aiki na mallake miji,,,,

Shi ko yaya sai da ta wuce sai kuma yaji baiji dadin abin da yai mata ba to amma ai itace bata da hakkuri ko kadan , Yana gida har,sai da mu ka,dawo a lokacin kuma yamma tayi da kayan mu niki niki ashe ita fatima kindarmo tatafi samowa a gidan kuma sai mukayi sa,a an kawo masu sai muka zo dashi Mu ka kuma tsaya a wani shago mukai yan sayayya abubuwan bukatun mu, Duk inda mukabi saboda shigan mu sai su ce,, hausa woman's,,, Na hausa people woo,,, Sai su bimu da kallo duk sai Ramatu ta rude tana cewa Hajiya mu tafi gida don ban yarda da kafiran nan ba saboda,ba abin yarda bane don a kasar su mu ke,,,,

****** ********* ****** Sosai Salawatu da ABUWA suke shige shige har na tashin hankali amna,su a,ganin su babu wanda ya fahinci hakan, don su mayar da mutane wawaye, Duk da tsohon cikin dake a jikina bai hanani yin ibadana ba ina kai kukana ga Allah buwayi gagara musali, Kuma a fili bamu rage maigidan da komai ba don duk wani hakkin shi muna kokarin sauke mai su, Ganin yadda nake yawan ibada ya,sa itama Fatima tadan fara mai da hankali gurin yin nafilfili da sadaka da karatu saboda itama ta sauka,, Dama haka rayuwa take komai ana samun canji akan shi, don na zamay wa Fatima alheri din na tsamota daga aikata miyagun halaiya yanzu zuwa na alheri,, Nice yau da girki bayan mun dan gama abinda mukeyi na barsu a falon na koma dakina don na kimtsa jikina, Don yanzu ina da ciki saboda haka ba wani dabaran mata da zanyi don haka sai na sha zuma da madara kawai, Na shiga bathroom wanda tun karfe hudu nake tsarki da ruwan dumi, Kafin wani lokaci ni kaina na shirya a cikin wasu kayan barci masu masifan kyau, Ban san cewa ya shigo part din namu ba wanda dakina muke zama dashi idan har ina da girki a gidan, Watau tsohon dakin shi na farko da yake zaune kafin a fara system din retation a gidan Inda nake zaune ina waya a bakin gado ya nufo yana mai min kallon sha,awa har ya zauna gab dani, Nce bayan nagama wayan har ka,shigone yaya yace eh don ina gudun kiyi barci gashi snce idan mai tsohon ciki tai barci ba,a,son a tasheta don a lokacin akewa yaton cikin ciki halitta wai, Nai murmushi nace haba dai Yayana ai ba yanzu zanyi barci ba don ban ko dauko ma ruwan flask ba , Yace saboda may nifa bani son yawan hawa da,saukowanan dakikeyi gaki da lalura ajikin ki, Nace dama nashigone nadan kimtsa jikina sai na koma na daulo yace cikin kamo min hannuwana ki huta yau na hutar dake , Na dakatar dashi ina cewa cikin girgiza kai aka riga da ka saba da hakan bari kawai na dauko ma shayin ka, Yayi saurin dakatar dani ta hanyar matseni a jikin shi yana cewa, ban son yawan saukan ki huta hakana please, Ban mashi musu ba nakoma na zauna inda ya dan shiga fara lalabana a hankali,,

Fitowan ta ke nan daga daki sai bata ganshi a falon ba gashi kuma tana sin ganin shi kafin ya kwanta, Don haka ta yanke a,ranta tabishi sama kafin yakwanta don yau yayi saurin kwanciya saboda tara da yan mintina shi kuma yakan kai shadaya saura yana aiki a,system din sa, A hankali ta hawo saman namu inda bakajin komai sai karan na,uran dake aiki a gurin, Ko dakin yarana da alama,suna ciki a natse baka ko jin motsin su don Ramatu ta natsa min su ko, Saboda haka dakin kwanciyana ta nufa wanda take zaton yana a ciki a lokacin, Ta sa hannuwa ta hankalinta a kwance ta murda handle din kofan a daidai lokacin da,,,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA SEENABU

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸

ZAINAB IDRIS MAKAWA 1⃣2⃣3⃣ FA,INNA MA,AL USIR, YUSURRA,,,,, INNA, MA,AL,USIR YUSURRA,,,,

Satin mu guda zaune a Abuja muka shirya komawa Fatakwal gurin Yaya Abubakar wanda zuwa yanzu yakira waya akan na dawo mai da yara saboda karatu yafi a kirga Tafiyan safe mukayi don haka mun samu gyara ko ina na gidan wanda ya koma tankar babu, kowa acikin sa, saboda kuran da yayi,, Sadiya wace take nuna vata so dawowan mu ba,saboda wai yara sun cika gida da hayaniya, sun damay ta, Nace a raina O,o ni Meenatu yanzu kuma yaran sune abin gujewa kuma, ni dai na godewa Allah da ya bani yaran, Don haka na natsasu ta hanya hauwa sama dasu gaba daya don gujewa baki,,, Na,samu suka fara barci da guda gudan su har gurin ya lafa tsit yadda take son jin gidan Nasan ba laifinta bane don bata saba da hayaniyan yaran bane, Sai da yamma maigidan yadawo daga office tun a kofa yake kiran yaran da cewa Yaran Uncle suna ina ne, wai, Babu kowa a falon sai TV dake aiki ana wasan kokuwa a cikin sa kawai, A hankali ya daga kai yanawa ko ina kallon tsab don fahintar ko bamu dawo bane, Sai dai idanuwan shi sun sheda mai cewa mun dawo din don irin yadda ko ina na falon gidan ke kyalli da haske ga kamshi yana tashi, Abinda ya haddasa mai sauke wani irin sanyayan ajiyar zuciya ke nan,, Tare da dan lumshe idanuwan shi a hankali ya dan fara takawa zuwa saman bene inda muke da yaran, Still ba,wani hayaniya da ya tare shi har ya kai kofan dakin namu inda a lokacin ne Maimu ta fito don zuwa kasa gurin Ramatu, dake kitchen tana girki, Sannu da dawowa Uncle tace a cikin dan kaduwa ya kula da akwai yar kaduwa a tare da ita don haka yadan tsaya daga baya yana cewa ko tana ciki kuwa tace eh uncle, Ya turo kofan ya,shigo da,sallama ina zaune a kasa da alaman tun da,nai sallah nake zaune a,gurin na mike kafafuwa na, don naji dadin zama da kyau, Acikin fara,a nake cewa sannu da zuwa Yaya,na yace cikin dan sakin murmushi C U kinga daman dawo ke nan yau ko, ? Nace ai ban gama abinda na keyi ba ne ko yanzu ma na dawo ne gudan kada muyi laifi, A hankali ya tako har inda yara suke kwance suna bancin gajiya inda Amira take ya nufa yana dan taba ta a hankali sai ta bude idanuwanta da,suke cike da nauyin barci tace Daddy,, a cikin wani irin yanayi, Ina daga gefe ina kallon su sai suka bani tausayi don a kwai wani irin shakuwa tsakanin uban da ita Amira, Hannu ya mika ya,dauko ta tsab daga cikin yan uwan ta ya nufo inda nake zaune, K8n dauke min uwata kin hanata ganin Daddy ta ke babu abinda ya damay ki ko ? Nace a cikin murmushi nima ai an hanani ganin nawa Daddy din Baki da tausayi Meena don nasan cewa wanan yarinyar duk inda kuke acikin damuwa take ita, Nace ai ita ce tasawa kanta mukan free muke muna ta harkokin mu sai naji yace, Zaman fitinan da kukeyi acan duk kun ruda min gida ban san ko sai yaushene zakuyi hankali ku daina wanan kishin naku ba na hauka, Da sauri na dago kai ina kallon shi a cikin mamaki don nasan zancen dan hayaniyar da akayi can abuja tsakanin mu shine har ya samu labari, Yace kina mamaki ne ko kin manta cewa, gidana ne duk abinda ke faruwa a kunnuwa na suke, Yanzu ita Fatima wace tace da farko bazata zo ba ta dawo da zancen zuwa kuma, Saboda kin bata mamaki kina kula da harkan ta duk da ita tana gwada maki tsana a fili amma hakan bai sa kin shareta ba, Tace taje asibiti da yarta babu wanda ya bita sai da kika dawo ko gida baki shiga ba kika bita can din,, Nace kai duniya duk a ina ka samu wanan labarin haka Yayana, Kafin yai magana Aisha ta farka daga barci tana cewa sannu da dawowa uncle, yayin da ta mike zuwa gare shi, Na fara nauyi a lokacin don haka da kyat na samu na mike inda muka sauko kasa gaba dayan mu har yaran, Munkai wani lokaci a tare da shi da yara kowa da abinda yake fada mai acikin hiran su muna zaune da Sadiya daga gefe muna dan hira jefi jefi a tsakanin mu akan abubuwan da ya shafe garin mu,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull