Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 132

Tarko complete novel - Chapter 132

Tarko complete novel Chapter 132: Tarko complete novel Chapter 132. ****** ********** ****** Tafiyan Sadiya yazo tare suka tafi da ita don haka muka rabu…

3,095 words

****** ********** ****** Tafiyan Sadiya yazo tare suka tafi da ita don haka muka rabu da ita a cikin mutunci, Sai a lokacin ne take ji a ranta abubuwan da tai min a lokacin da tazo da batayi su ba saboda wanan dawowan da mukayi bata da yar aiki a tare da ita komai namu a tare a keyin shi kamar farko, Hakan ya sa ta jin dadin zama damu kamar kada ta koma Abuja, din, A can ne rikici ya kaure a tsakanin matan shi don Fatima tace ita sam bata yarda da zancen zuwa da Salawatu ba sai dai itace zata tafi, Wanan zancen ne har ya jawo masu mumunan tashin hankali, a tsakanin wanda suka dinga tonawa kan su asiri da abubuwan da bai sani ba a gidan, Yana daga sama ya sauko kasa rai a bace cikin tsawa yake cewa wai may ke faruwa ne haka,? Babu komai inji Salawatu take ce mai acikin huci tana mayar da numfashi, Fatima tayi maza tace akan zancen tafiya Fatakwat ne zaki ce mai babu komai, Yace kamar ya zancen tafiya fatakwat kuma Fatima tace ai tasan cewa nice zan tafi amma sai ta haushiri wai itace zata, Da can baya da kika tafi waya hanaki ke da yanzu don nace zan tafi har ki sani baki, Cikin daga hannu Yaya Abubakar ya maza ya katse ta da ce wa may ya kawo wanan zancen yanzu, Salawatu ta kalle shi a cikin natsuwa da yake ta iya makirci tace ni dai banda magana,da ita tunda ba itace mai tafiyan ba Shine yanzu ta samay ni take cewa dani wai ita ce zata tafi tare da kai don dama zuwan tane, Shine don nace ai ni kaine kace na shirya idan Sadiya ta dawo sai na tafi tunda nan a gaban mu tace idan har Meenatu bazata dawo ba ita bazata ba, Shiru Yaya Abubakar yayi na dan lokaci mai tsawo saboda ranshi ya baci sosai a lokacin, Gaba dayan su gurin shiru sukayi don sun fahinci rayuwan shi a bace yake sosai a lokacin, Ganin sunyi shiru yasa shi cewa, dago kan shi dake kasa ya dube su daya bayan daya yace idan hakane har an rasa wanda zai bar wani ya tafi sai ku shiyar mu tafi gaba dayan ku idan wata ukun yayi sai ku dawo, Daga haka yabar falon ranshi a bace don yasan hakan da yace zasu tsaya a tsakanin su, sulhunta kan su akan zance, Yadda yai tsan mani hakan bai samu ba don gaba dayan su, sun hau don haka babu wace ta jaye zancen, tafiyan daga cikin su, Bai ce masu uffan ba don haka suka shirya zuwa tare, Sun iso muna a cikin dare don haka nice ranan mai masaukin baki na tare su a cikin mutunci da haba haba, Bayan mun shigar masu da kayan su a dakunan su inda sai kallon girman gidan suke da mamaki, Salawatu itace farko sai Fatima daga ciki dakin da Sadiya ta fita a cikin sa akwai komai a cikin dakin, Muna shiga part din mu Ramatu tace uwar dakina akwai magana a gidan nan don da ganin wanan tafiya akwai rikici a cikin sa don haka mu namu shine ido kawai, Yanzu ban son fitina Ramatu don haka zanyi iya bakin kokarina naga na gujewa duk wani abinda zai kawo tashin hankali a tsakani na,da kowacen su,,, Washegari ma mun masu abin karya kumallon safe inda tun a nan maigidan ya zaunar da mu cewa mu tuna cewa nan bariki ne don haka,baya son hayaniya a,gidan shi kuma duk wace tai mai hayaniya a gida saboda kishin banza zasu hadu da ita, Haka mu ka zauna mu uku saboda tujara kowa tana jin dan uwa a,rai kamar zata shake yar uwar ta,,,,, Sau dai babu halin nunawa a fili Fatima wace tai sanyi da yawa yanzu muke dan zaman shiri da ita sama sama don ba kamar yadda mukai zama da Sadiya,ba da tazo, A tare yaran mu ke zuwa makaranta duk da ita yarta sickler ce yau ciwo gobe lafiya, Wani magani da uban ya karbo ma yarinyar saboda warin shi uwar bata so wai yana hawa mata kai nice nake daurewa duk da ban so na,shafawa yarinyar a jikin ta, ko ina,sai na shafe ta dashi tas kafin ta kwanta, Wanan abin da na kewa yarinyar ya kawo shakuwa a tsakani na da ita tun uwar ta na dan sayi dani akan yarinyar uwar ta gaji ta,saka muna ido ranan da take da duty a gurin mu yarinyar ke kwana,, Wanan abin da Salawatu tagani shine ta dauki fitinan duniya ta sawa kanta cewa wai mun hada mata kai ni da Fatima don muna yan gari guda, Can ta hade da matar wani director kusa da gidan mu gidan su yake don haka suke kawance, Nasan da matar tun farko matar batai min ba don ita irin matan nan ne masu sakaci da addinin su sosai matar dai muna musulmaine ita, Da zaran maigidan ya tafi office zata fita zuwa gidan ABUWA, sunar matar ke nan yan yaren lokoja ce matar, Daga haka har suka fara fita yawon shiga da fice irin na matan da basu dogora ga Allah ba, Duk gurin da, suka ji cewa, akwai wani hatsabibi ko hatsabibiya sai sun kai kafan su gurin, Tashin farko har abin ya fara tasiri a kan maigidan inda hankalin mu gaba daya ya tashi, Fatima ce ta fara samuna da zancen cewa wai kuwa na san abinda yake gudana a gidan nan yanzu fa,duk marance sai Salawatu sun fita da maigidan zuwa unguwa , Idan sun dawo kúma zakifa sun shige dakin ta har tsawon wani lokaci kafin ya fito,, Duk da kishi gaskiya,ne ga mace amma sai na dake kawai nai murmushi nace kai maman Aina ke nan halin wanan shu,umar matar ne kuma baki sani ba, Ai al,amarin ta sai Allah shine kawai zai shirya ta daga sherukan ta don ta riga da tai nisa ga kaucewa ita Nace idan za,a soni a,soni don Allah idan kuma baza,a,soni ba zan hakkuru har randa abin zai dawo a kaina don al,amarin na miji mai mata kamar tashin tsuntsune, Watarana yausaka akan idan ya motsa kuma sai ya tashi akanki dake dashi sai watarana, Ido ta kura min tana cewa ban fahinci may kike nufi ba k8na nufin kice mi ke baki irin yan shige shigen nan ne ko kuwa, Nace eh to inayi irin na shan hakin maye da sauran kayan mata, ni bayan wanan ban wani zuwa gurin kowa wallahi Allah Ga Allah na dogora gareshi nake kai kukana ga duk abinda ya shige min duhu, Wani irin kallon mamaki Fatima ke min yayin da take kokarin zubar da miyau daga bakin ta don na fahinci tana da dan karamin ciki ne ita ma, Nace ba dole sai kin yarda da zance na ba amma ni nasan cewa Allah ba zai bari Salawatu ta cuce mu ba, Duk yadda shu,uman cin Salawatu yaso ya kama maigidan sai kuma ya kubce daga sherin ta, Ance al,amarin namiji mai mata baida tabbas a kullun akan mace daya, Abin kamar tsuntsune yau idan anayi da ke sai kuma ya tashi ya koma ga waccan dake dashi sai watarana, Hakane muma al,amarin gidan mu don maganar Fatima gaskiya ne sai dai ban yarda na,sawa zuciya na cewa Salawatu ta rinjaye mu ba don nima ina iya kokarina gurin kai kukana ga Allah ubangiji subbahanahu wata,ala, Ance wai tsafi gaskiyan maishi don ba laifi tana yadda ranta ke so a kai, amma sam dagani har Fatima wace a yanzu muke da dan fahintar junan mu saboda sanadin yaran mu, Wani lokaci nakan tuna da malam tsoho sai inyi kuka don nasan cewa na fikowa rashin shi don da yana da rai da yanzu ya bani shawaran yadda zan bullowa wanan al,amarin na Salawatu, watau sabon sallon ta, da tazo muna dashi Abinda yazo min arai yau shine hiran mu na karshe da malam din da nake cewa malam ni har yanzu tsoron wayan nan kishiyoyin nawa nake ji, cikin murya mai rauni nake cewa duk sun girmay min Don duk sunfi karfina wallahi zama kawai nake da su don haka kuke son ganina, Malam yai murmushi tare da,dan yin jim.kamar may son yin tunanen wani abu can yace amma basu fi karfin mijin ki ba ko ? Yace indai har suna tsoron mijin ku to dole ne suji shakkar yi maki wani abu don hakane na dauko daga gare shi nai maki hikimar da,zai sa shi bi ta kanki, Sam banyi tsanmani ke yar wanan gidan kuma haifafan Kebbi har zakiji tsoron kishiya ba Don hakane na hadaku ke dashi saboda na san halin kowan ku hadin naku yai wa kowa daidai saboda hakkurin ki Mijin ki shine gurin ki a duniya da lahira, don haka kamar yadda Allah ya rufa maki asiri kika samay shi a,sauwake ta kissa da da dabarun ku na mata haka ma zaki kara rike abinki gam, a hannun ki ,bawai sai kin rike shi ajikin ki ba kowa yasani, Har kice zaki hanashi zuwa wajen wata matar da ke da hakki a kanshi, Ki barshi da wanan don jikinshi ne ai Ki bari yayi yadda yaso yaji dadi son ranshi da,wata, ya morewa rayuwan shi don Allah ne ya halat ta mai yin hakan Gurin ki ke kawai shine kiyi kokari ki rike zuciyar shi inda duk yaje kece abin tunanen sa, abin farin cikin sa, Indan har zaiyi magana wanda ya,shafi alheri a cikin matan shi sunan ki zai ambata don kece yasani maishi,, Wanan zai sa duniya da sauran matan su zaci cewa wani asiri kike ta yi wanda zai iya saka zukatan su ga hauka don basu san sirin ba,,,, Ina kaiwa nan da tunane na sai na sauke ajiyan zuciya tare da lumshe idanuwa nace a fili Allah yajikan ka malam , wasu yan hawaye masu dubi suka biyo kumci na, Na furta a fili cewa lalai malam kayi gaskiya don haka zan mike na kara kaimi gurin ganin cewa na kara cusa kaina ga zuciyar maigidan tako wani hanya muddin bazan kaucewa Allah ba, A kan Fatima na fara aiwatar da shirina don haka sai na kara dan janta a, jiki don na fahinci nata al,amarin akwai sauki, Idan har taga wani abin bacin rai nakan nuna mata cewa ta mayar da,shi ba komai ba ta shanye, Tun bata iya ba har tafara koyi da hakan sai muka mayar da Salawatu kamar mahaukaciya, Duk irin shu,umancin da zata gwada wanda zatayi don ran mu ya baci sai mi hade mu shanye mu mayar da abin ba komai bane, Tankar bamu san cewa tanayin abin ba balle mu kulla har kan ta sai kumahakan ya fara bata haushi saboda ba hakan taso ba, Matsala guda ne shine bamu yarda ta shiga hakkin mu ko kadan don a ranan girkin mu mukan yi kokarin ganin mun kanainaiye, maigida ta yadda baida lokacin ta sai namu kawai, Wanan abin yana matukar batawa Salawatu rai don sam bata taba tsanmanin cewa za,a samu natsuwa a tsakani da Fatima ba irin yadda tasan cewa ba shiri a tsakanin wanda indan an biyo gaskiya itace duk umulabaisin hakan a tsakanin mu saboda anyi ance din ta da yai yawa,,

****** ********* ****** Shirye nake a cikin wata doguwar riga baka mai dan fadi a kasa sama a dan tsuke wanda ya baiyanar min da surar cikina wanda kusan wata biyar da dan kai zuwa yanzu, Na fito ne da niyar tambayan shi ina son fita zuwa gidan su kawata yar Yola wace tazo min har sau biyu bayan rasuwan malam tsoho din Zaune yake a falo da waya a hannun shi, da alamar wayan da yakeyi mai mujin manci ne sosai don ita madam din tana daga gefe a zaune cikin sauraren shi, Tunda na fito yake kallo har na sauko kasan yayin da yai min kur da idanuwan shi, Yana a cikin wayan amma hankalin shi yana a gare ni tun da nake saukowa daga stairs din sai gab dashi na zauna a hannun masagalin kujeran da yake zaune a kai, Naji lokacin da ya saki yar yajiyar zuciya tare da dago kai gareni firgigit, Yace wanan shigar haka kuma,sai ina nadan rausaya kai ina cewa wanan kallo haka yayana ko so kake nayi tuntube na fadi, Ya girgiza kan shi yana cewa ke din ce da wani batta da,kama kina,wani tafiya kamar mai tafiya a gajimare, Shi yasa ai nake maki kallon mamaki don da mutum zai ce Meenat sai ki ce ke ai duk jikin ki ciwo ne, Nace haba dai Yayana ni ai yanzu abin tausayi ce duba fa yadda,duk na koma a lokaci guda, Mikewa Salawatu tayi tabar gurin a cikin bacin rai, Na bita da kallon harara ta wutsiyar idanuwa ina cewa a raina sai dai kare ya mutu da haushin kura, Har ta kai kofa sai ta juyo tana cewa idan ka gama kada ka manta da zance na please, don ina jira ta fada fuska a daure, Tare da tabe baki ta, ta juya zuwa cikin dakin ta sai dai zuciyar ta tankar ta buga saboda wani bakin kishin da take ji nawa a ranta, Nace cikin dan murmusawa Yaya yau ina son zuwa gidan yan Yola ne na mayar da kafa nima, don zuwanta biyu ban tafi ba ni, Yace cikin murmushi yau kice min yawo zaki fita ke nan yai daidai da fitowan Fatima daga dakin ta, Tun kan ta karaso take cewa yau fita zakiyi ke nan nace cikin dan wasa da keys din motana eh wallahi, Zandan tafi nan na,dawo tace ashe bari na biyo ki sai mu fita don ina son sayen abu dama, Yace da izinin wa zaku fita,din nace a cikin dan kwantar da murya ai muna,afuwan please, Ya girgiza kan shi yana cewa dama dai kuna da inda zaku tafi ke nan ni fa ban fahinci wanan wayyon da ake muna ba na kabawa, Na mike tsaye ina murmushi nake cewa, ai kafi kowa sani don kai ka hada shi, Yara na kwaso tare da Ramatu muka duru a mota guda amma sai da muka rufe par din mu kafin mu bar gidan, Bayan fitar mu ne tafito a kufule tana cewa kaga dama na fahinci cewa da sanin ka ake min hadin kai a gidan nan, Gashi yanzu a gaban ka,sun fita batare da sun bukaci na bisu ba,, Mikewa,yayi shima ran sa a bace yana cewa ban son zancen tsegumi saunawa kike fita a gidan nan su basu fita,ba, Kuma na fita tare dake basu damu da cewa wani abuba sai yau da,suka fita da yaran su, Tace to dama kasan cewa zamu fita don haka sai mu tafi ke nan Yace ba inda zani yanzu don motana,suka dauka suka fita dashi, Ta juyo cikin nuna halin su na yan duniya tana cewa oh hakama zakace min ke nan ? Ya gyada kai Eh babu inda zani sau naga sun dawo zanfita don bazab bar gida babu kowa ba, Ai dama kai indai zance na Meenatu ne baka iya, boye feelings dinka,akai gaban kowa,sai ka nuna hakan, Ji fitowa take muna magana da kai amma duk kawani rude kama daina waya saboda ganin ta, Yace cikin dakewa wanan kuma matsalar ki ce don ni ban daina,waya ba sai da na gama, Meenatu bakuwatace da zan rikice don na gane ta tace saboda kai baka san yadda kakeyi bane ai , Ya dan maida kan shi a bayan kujera tare da dan lunshe idanuwan shi yana ma lashe laben shi na sama yace, Duk surutunki ya isheni a kai wallahi tace eh ai dole kace hakan don ba yau ka fara wullakantani ba a kanta Yace daidai shigowan baba Wadda gidan shout,up my friend kin cika min kunnuwa da yawa, Meenatu dai Meenatu dai haba wanan wani irin rayuwa ne ke a koda yaushe dai cikin an maki laifi wake baki rike girman ki ne for god sake, Don haka ki bace min da wanan zancen banzan naki ya isheni haka, Duk abinda kikaga dama kike a gidan nan daga ita har Fatiman sun kawo ido sun saka maki don kawai a zauna lafiya dake amna still hakan bai maki ba,sai kuma kin kawo wani tsegumi akai, Tsaban fitina tagani a idanuwan shi wanda hakan ya sata saurin juyawa don barin falon Sai sukayi kicibis da Baba wadda wanda take da tabbacin cewa yaji zancen nasu, ko,, Ido a rufe ta juya zuwa dakin ta inda ta fada saman gadon ta cikin tashin hankali Don bata tsanmaci haka ba daga gare shi a kan Meenatu don tana ganin cewa yanzu ta rufe babin Meenatu din har Fatima a gare shi, Idon ta a rufe ta kira wayan ABUWA tana fada mata yadda yai mata cin mutunci yanzun nan a kan matan nashi, a cikin kuka,, Cikin takaici ABUWA din tace, sam ban san irin wanan shedaniyar yarinyar ba yanzu zata ce duk abinda akayi aka bata taci bai shigeta ba, Salawatu tace a cikin wani irin murya ni ina duban yadda nake narka duk wani abu nawa amma wanan shegiyar yarinyar taki bar min Abubakar ni kadai, ABUWA tayi murmushi har za,a iyajin ta acikin wayan tace kyale ta kawai ai za,a yita yakare don zan gwada mata dani take wasan ,, Don haka kada ki damu zan san abinyi kwanan nan isha Alkah sai tabar maki shi don babu inda zaki, koma sai dai ita ta koma, tabarki a nan din, Wanan zance na Abuwa yaiwa Salawatu dadi sosai a rai don dama tai hakane don ta suku tai mata abu mai muhinman ci wansa zai kawo rabuwa tsakanin Meenatu da maigidan, Don dai tasan cewa yanzu dai babu malam tsoho wanda a da nake kuri dashi yake min aiki na mallake miji,,,,

Shi ko yaya sai da ta wuce sai kuma yaji baiji dadin abin da yai mata ba to amma ai itace bata da hakkuri ko kadan , Yana gida har,sai da mu ka,dawo a lokacin kuma yamma tayi da kayan mu niki niki ashe ita fatima kindarmo tatafi samowa a gidan kuma sai mukayi sa,a an kawo masu sai muka zo dashi Mu ka kuma tsaya a wani shago mukai yan sayayya abubuwan bukatun mu, Duk inda mukabi saboda shigan mu sai su ce,, hausa woman's,,, Na hausa people woo,,, Sai su bimu da kallo duk sai Ramatu ta rude tana cewa Hajiya mu tafi gida don ban yarda da kafiran nan ba saboda,ba abin yarda bane don a kasar su mu ke,,,,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull