Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 133

Tarko complete novel - Chapter 133

Tarko complete novel Chapter 133: Tarko complete novel Chapter 133. ****** ********* ****** Sosai Salawatu da ABUWA suke shige shige har na tashin hankali…

2,600 words

****** ********* ****** Sosai Salawatu da ABUWA suke shige shige har na tashin hankali amna,su a,ganin su babu wanda ya fahinci hakan, don su mayar da mutane wawaye, Duk da tsohon cikin dake a jikina bai hanani yin ibadana ba ina kai kukana ga Allah buwayi gagara musali, Kuma a fili bamu rage maigidan da komai ba don duk wani hakkin shi muna kokarin sauke mai su, Ganin yadda nake yawan ibada ya,sa itama Fatima tadan fara mai da hankali gurin yin nafilfili da sadaka da karatu saboda itama ta sauka,, Dama haka rayuwa take komai ana samun canji akan shi, don na zamay wa Fatima alheri din na tsamota daga aikata miyagun halaiya yanzu zuwa na alheri,, Nice yau da girki bayan mun dan gama abinda mukeyi na barsu a falon na koma dakina don na kimtsa jikina, Don yanzu ina da ciki saboda haka ba wani dabaran mata da zanyi don haka sai na sha zuma da madara kawai, Na shiga bathroom wanda tun karfe hudu nake tsarki da ruwan dumi, Kafin wani lokaci ni kaina na shirya a cikin wasu kayan barci masu masifan kyau, Ban san cewa ya shigo part din namu ba wanda dakina muke zama dashi idan har ina da girki a gidan, Watau tsohon dakin shi na farko da yake zaune kafin a fara system din retation a gidan Inda nake zaune ina waya a bakin gado ya nufo yana mai min kallon sha,awa har ya zauna gab dani, Nce bayan nagama wayan har ka,shigone yaya yace eh don ina gudun kiyi barci gashi snce idan mai tsohon ciki tai barci ba,a,son a tasheta don a lokacin akewa yaton cikin ciki halitta wai, Nai murmushi nace haba dai Yayana ai ba yanzu zanyi barci ba don ban ko dauko ma ruwan flask ba , Yace saboda may nifa bani son yawan hawa da,saukowanan dakikeyi gaki da lalura ajikin ki, Nace dama nashigone nadan kimtsa jikina sai na koma na daulo yace cikin kamo min hannuwana ki huta yau na hutar dake , Na dakatar dashi ina cewa cikin girgiza kai aka riga da ka saba da hakan bari kawai na dauko ma shayin ka, Yayi saurin dakatar dani ta hanyar matseni a jikin shi yana cewa, ban son yawan saukan ki huta hakana please, Ban mashi musu ba nakoma na zauna inda ya dan shiga fara lalabana a hankali,,

Fitowan ta ke nan daga daki sai bata ganshi a falon ba gashi kuma tana sin ganin shi kafin ya kwanta, Don haka ta yanke a,ranta tabishi sama kafin yakwanta don yau yayi saurin kwanciya saboda tara da yan mintina shi kuma yakan kai shadaya saura yana aiki a,system din sa, A hankali ta hawo saman namu inda bakajin komai sai karan na,uran dake aiki a gurin, Ko dakin yarana da alama,suna ciki a natse baka ko jin motsin su don Ramatu ta natsa min su ko, Saboda haka dakin kwanciyana ta nufa wanda take zaton yana a ciki a lokacin, Ta sa hannuwa ta hankalinta a kwance ta murda handle din kofan a daidai lokacin da,,,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA

SEENABU

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣2⃣4⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

AR'RAHMANIN RAHIM,,,,

Tura kofan ta yayi daidai da lokacin da Yaya Abubakar yake a cikin jikina yana aiwatar da sunnan ma aikin Allah a kaina Jin shigowan mutum a dakin ne ya sani da ban fice a hankalina ba,sauri duban kofan dakin, Innalillahi na iya fadi da sauri, Abinda shima yasa shi yai saurin duban kofan dakin ke nan Salawatu ce ya gani a tsaye tana cewa wai Sorry please, Yace cikin tsawa get out, Stupid idiot, Noses A, you out of your mind ? Gashi a saman jikina bai sauka ba gata kuma bata fita,ba,wai tana cewa wallahi Oga ban san cewa kana cikin condition bane, ai da,,, Salawatu get out please, I dont want to see Your face,, Ta juya simi simi cikin tashin hankali idanuwanta a,rufe bata ma,san ina take takawa ba sai tafiya takeyi,, Da Ramatu su kai karo a hanyan sauka ta kauce mata ka dan don kada ta bugeta,, Ramatu ta bi bayan ta da kallon mamaki don ganin irin yadda ta fita cikin hayacin ta ita ma hankalin ta a tashe yake don tana zaton ko wani abune ya faru, wanda har ya kai, Salawatu shiga bedroom di na ,, Ko ita da muke a tare da ita a koda yaushe bata shiga dakina idan har ba nice da kaina,na,bukaci hakan ba Musan man ma yau da tasan cewa,nice da,maigidan a part dina, bata tsayi a wahe da wuri take gama aiyukanta ta shige daki,,, Don haka sai Ramatu tai zargin cewa babu lafiya yau don dai Alhaji yana dakin, Kuma ga wanan shu,umar matar ta shigo masu da fitinar ta, ****** ********* ***** Yaya Abubakar yana ganin Salawatu ta,fita daga dakin yai tsuki tare da, cewa No,Sciens Yana kokarin komawa a jikina nai saurin ture shi daga jikin nawa da karfin Allah, Allah ya bani sa,an samun hankada shi gefe guda namike a cikin kuka naja zani na dake gefe guda na,shige bathroom da kuka, Wani irin tsuki yaja tare da kara kwantawa flat a saman gadon nawa da duk muka ya mutsa, yana mai huci da furza iska daga bakin shi , Yakai wasu yan mintina a hakan a zaton shi zan fito daga cikin bayin a lokacin amma sai yajini shiru, Hakan ya bashi daman sanin cewa ina ciki ina kuka ko wani abu, Shiru shiru baiji fitowan nawa ba daga bayin sai ya dan mike ya kai zaune tare da tokare habar shi da, hannayen shi biyu, Yana yi yana duban hanyan shiga bathroom din ko zan fito, Jin shirun da yayi ne yasa shi mikewa zuwa kofan bathroom din yana dan kwankwasawa tare da kiran suna na, a hankali,,, Amma yaji shiru ba amsa abi da ya kara harzuka mai zuciyar shi ke nan, Ina shiga bathroom din na zauna saman zinc din toilet din ina mai rusa kukan bakin ciki da takaici da kunci a hankali, Sai tunanen irin wanan abin tozarcin rayuwan da yau Salawatu tai min a duniya, na Abinda ban taba tunanen shi ba acikin diyan musulmai hausawa yan asali, yau sai gashi a gareni ni akaina,ni Aminatu Samaila, Manya Birnin Kebbi, Jin muryan Yaya Abubakar danayi a kofan bayin yasani kara rusa kuka acikin ban tausayi Muryan shi naji yana cewa ki bari na shiga na tsarkake jikina please,, Hakan da naji yasani fitowa daga bayin ba tare da na tsaya na kalli gurin da yake tsaye ba, na fito na dan gega ta bayan shi zuwa cikin dakin, Ya bini da kallon irin yadda nake rusa kuka gwanin ban tausayi, Take ya kara jin zuciyar shi na kara cakushe mashi da bakin ciki, Can saman side drawer gado na koma na zauna ina mai zubar da hawaye zuciya ta sai tafasa takeyi tana saka min abubuwa da dama araina Ina a gurin zaune har yafito daga bathroom din daure da towel a kunkurun shi, da wani dan karami a hannun shi yana goge ruwan kan shi, dashi a, hankali, Ina kallon shi naji wani irin haushi da takaicin shi ya kamani a lokaci guda naji ina danasanin auren shi a yau din fiye da ko yaushe, Don inda a garin mu nai aurena da,babu wanan zama kamar na arna ko dabbobi, da bani ba mata irin su Salawatu yan bariki,,, Shigowan shi dakin yayi daidai da mikewana zuwa bathroom din na fada wankan nima, na gyara jikinq Bayan nafito na sa hijjab dina na tayar da salla batare da nai mai magana,ba A gurin da na idar da sallah nake a zaune sai kuka nake duk yadda naso na daure na,daina fitar da hawayen bakin ciki, dake fita min a idanuwana, Yaya Abubakar yana daga gefe bakin gado a zaune yana kallona acikin dan jijiga kafuwan shi, a kasa, Ya,rasa ta irin hanyar da zai fara,mata magana a kan zancen, don ya fahinci, bata da niyyar sauraren shi , a lokacin Yakira sunana a hankali ba tare dana amsa ba na daga kai na kalle shi, a cikin jajayen idanuwa da suka rine min a lokaci guda , Yace ki zo ki kwanta har da,safe don kin san kina,da lalura kada ki sakawa kanki damuwa haka, har wani abu yazo ya samay ki Haushi da takaici suka kara,rufe ni watau bai ma,san zafi da munin abin da akai min ba yau a gidan nan har yake bukatan nazo na kara kwantawa dashi, Maimakon na tashi sai na dan kara ji gina kaina a,gefen mirro din da nake zaune a gefena a hankali in mai ajiyan zuciya irin na wanda yai kuka da yawa, Tsuki naji ya saki tare dan bubuga hannayen shi biyu guri guda, a hankali, yace Shittt, Zuwa wani dan lokaci abin ka ga na miji da bai san takaici ba sai naga ya kai kwace yana mai gyara kwanciyar shi tare da jan bargo zuwa jikin shi, A zato barci yake ashe abinda ban sani ba ya dai kwanta ne kawai amma rayuwan shi a tafashe yake mai , Sai tunane ke zo mai kala kala,shidai yasan cewa a iya tsawon rayuwan shi bai taba aikata zina ba, Baita neman mace da sunan zaman banza ba ko sigari baya son jin kamshin, sa Iskanci da duniyanci baitaba bashi sha,awa ba a rayuwan shi, Sanin shi da yayi da ra,ayin son shiga jikin mata da yawa a zuciyar shi ya,sakashi yin aure aure don ya kauda sha,awan shi, garesu akoda yaushe, daga zinace zinace ke nan,, Amma,sai gashi yau, matar sunan shi yake a tare da ita,amma,shedan ya,turo shedaniyar matar shi, har daki inda yake sunna da matar shi ta riske su a tsakiyan ibada,, Bubu shakka,wanan matar ba abokiyar zama bace a rayuwa don bata san addini ba a rayuwan ta sam, Gaba daya lissafinsa ya dagule mashi ya kasa fahintar komai zai iya,aiwatar wa a kan Salawatu din a haka zuwa tsakiyan dare barci ya kwashe shi, Ranan a kasa na kwana saman salaya na duk da ba,wani barcin kirki na,samu nayi ba amma hankalina ya kasa kwanciya da nai barci da kyau, Sai faman juyi nakeyi na,kasa koda runtsa idanuwa na,sai tunane abubuwa kawai, ****** ********* ****** Washegari motsin fitowanshi daga bayi ne ya farkar dani daga,barcin da nakeyi, firgigit na,farka,tare da,sauke ajiyar zuciya , A cikin wani yanayi mara dadi yake duba na tare da,cewa ki tashi haka a kasa kada jikin ki yai maki ciwo, A hankali na mike zaune ina mai dan gyara habar zanin dake a jikina tare da,son na mis,tsike idanuwana daga dan barcin da ya kwashe ni a lokaci, Zuba min idanuwan shi yayi yana dubana a cikin damuwa yana ji tankar ya,rugumoni a jikin shi ya lalashe ni sai dai babu fuskan yin hakan saboda ko kallon inda yake a zaune bana yi, balle Yace a cikin wani yanayi tare da dubana yake cewa ki tashi kada ki makara ga sallah, Na yunkura na tashi na nufi hanyar bathroom ta inda yake tsaye yana gyara bottom din jalabiyar jikin shi,, Har ya,dawo ya,shirya ina zaune ina adduoi batare dana,mike daga inda nake zaune ba, Ki tashi rana yanayi ki duba yara ko sun shirya yake cewa a lokacin da yake tsaye a gaban mirron dakin yana kokarin daura nicktie a wuyan shi,,, ,, Ramatu za tai masu komai ina Al,azakakar ne ni sai na gama zan fita, cikin daurewa na furta mai hakan, sai dai murya ta tana nuna damuwa acikin ta, Murmushi ya saki tare da takowa zuwa inda nake a zaune ya tsareni da firgitattun idanuwan shi da,suka,sauya kama yau din,,don bacin rai Ki daure ki tashi ki duba,shirin su kada yaran su tafi basu ganki ba don sun saba da,sallamar ki a kullun, Wasu irin hawayene suka soma zubo min daga idanuwa na, ina mai girgiza kai nace ai zasu shigo nan din kafin su tafi, na sani, Abin breakfast dina fa ya tambaya yana mai kewa daga inda yake a tsugune, Nace nasan yanzu Ramatun ta kanmala komai da ya,kamata koda ban fita ba, Zai kara magana nace cikin kara narkewa da kuka,don Allah Yaya ka rabu dani hakana ban son magana yau, Na karasa fada tare da kara rushewa da kuka inajin kunan zuciya a cikin raina, A take kukan nawa ya,shige mai zuciyan shi tare da tabo mai rayuwanshi, Irin yadda yaga ina kuka ya sakashi, jin tsana da kiyayyan Salawatu a ran shi Sai naga ya mike da sauri ya nufi hanyar fita waje da jakar shi a hannunshi, Zuwa yan mintina sai ga yaran sun shigo dakin suna min sai sun dawo sai sun dawo, na ansa masu da kyat, da cewa sai sun dawo suma yaran basu gane kaina ba ranan suka fita jiki ba karfi, Banji shigowan shi ba,sai jin shi nayi yana kokarin juyo fuskana gare shi, tare da dago fuskana don mu hada idanuwan mu,,, Nan na,soma cewa tare da fisge fisge ka sakeni dan Allah Yaya ban son haka please, Maimakon ya sakeni sai matseni a jikin shi yayi tare da cewa shi zai fita in bari na,saurare shi, Gam ya matseni yadda ban iya motsi dole na hakkura sai kukan da nakeyi, murya a hargitse abinda yasa shi sakeni kenan don ba zai iya sauren kukan nawa ba,,,

****** ********* ****** Ita ko Salawatu tana shiga dakin ta wanda ta samu da kyat ta isa dakin nata, Fadawa tayi saman gadon ta ragwab, hankali a tashe, idanuwan ta a,rufe, Tana tuna cewa, wai Abubakar handsome gentle one in town shine kewa, Meenatu wanan irin mahaukacin soyayyan da ta samu yanayi, Idanuwan ta ta runtse tare da hade wani irin bakin miyau mai daci, Ta koma tankar wata mahaukaciyar kasuwa mai warin daddawa, Bata zaune bata tsaye duk abinda takeyi tana ganin yadda ta samu Abubakar yana,wa Meenatu abinda bata taba tsan manin zai iya yiwa wata diya mace shi ba a duniya,, Ta kasa daurewa ta dauki waya ta kira ABUWA tana sheda mata irin abinda tagani yau a gidan su, ABUWA tace cikin daka tsawa may kaiki wanan aikin Salawa wanan ai rashi girmane gare ki, Kiga abinda zai tayar maki da hankali a banza ya hanaki barci da tunane,, Tace ba komai yasa ake gujewa hakan ba,sai don ganin abinda zai tayar maki da hankali, Zaki ga ko da abin bai kai irin wanda yake maki ba sai kekiga ai yafi wanda yake maki ke din, Salawatu tace aima yafi nawa din don wallahi baki gani bane tace aiko bazan gani ba ma ni, So,sai tai wa Salawatu nuni da rashin dacewan hakan lokacin sai daga baya ta dawo hanyan su na yan bariki kuma tana cewa, Ashe kin sha kallo yau ke nan TV gare ki a banza ba,saye, Salawatu tace hmmm bari ke dai tawa ai ni ba zancen TV ba yau baki ga yadda Oga ya wani koma,a,jikin yarinyar nan ba, ne,,,, Tace, ni yau abin ya bani mamaki sosai wallahi wai Ogana ne a haka tare da,wanan yarinyar, Ashe haka yake mata ni a zatona fa tun da bashi ita akayi babu wani abin da yake mata na soyayya kawai dai suna zamane ya dan jagulata ya tashi ashe abin ba haka yake ba, ABUWA tace ashe baki san namiji ba ke nan ke abinda kika raina shi a gareshi ai zinare ne, wai guban wani abincin wani,,, Wanan bai dace ba gaskiya baki kyautawa rayuwan ki ba don kin gano wa kanki abinda zai hanaki barci yau,, Sun kai wani lokaci a tare suna hira akan zancen barcin ya kaurace masu a idanuwan har zuwa asuba,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull