Tarko complete novel - Chapter 134
Tarko complete novel Chapter 134: Tarko complete novel Chapter 134. Washegari, Ranan ban fito waje ba ina daki saboda ban san da wani irin ido zan iya…
2,891 words
Washegari, Ranan ban fito waje ba ina daki saboda ban san da wani irin ido zan iya kallon Salawatu ba, dashi, ba salawatu gani nake kowa ma ya gan mu a haka ni dashi, Ba don komai ba sai don sanin darajan kaina danayi dakuma sanin cewa wanan abin sherin shedan, bai halat taba musulmi yaga tsiraicin dan uwan shi musulmi, Ita ko Salawatu sai ganin take cewa ai ya kamata ta hada idanuwa dani a ranan tai min kallon banza don tasan komai yanzu a kaina, tunda har tafa tsiraici na da miji, Niko, Har zuwa after two ban,sauko daga sama,ba zuwa kasa,, ina daki na a can , nai komai a ranan ban fito waje ba don haushi da kunya,ba, Don ganin kwam irin na Salawatu don ta sheda cewa, ina a cikin damuwa ne ko kuwa sai ta yankewa ranta hukuncin zuwa part dina a sama don taga irin halin da nake a,ciki,,, Ina kwance a cikin kuncin rai zuciya ta sai suya suke min idanuwa sun kada sunyi jajir don bacin ran da nake ji a ranan, Sau uku Yaya Abubakar yana kiran waya na,sai dai na kurawa, wayan ido amma ban dauka ba,sai ya kare ringing ya katse don kan shi, Shi ko a,zaton shi ko barcin da,ban samu yi daren jiya,bane nakewa ramuwa da ranan nan, Sai dare ya,shigo gidan inda ya dan leka dakin mun gaisa,sama sama dashi ba yadda muka saba,dashi ba, bai ga fuska,ba a,ranan gare ni ko kadan, Yafita dakin nawa kan shi a daure don dai yasan cewa bai man komai ba, don may zan hada dashi na,rufe tunda bashine ya kira Salawatu a lokacin ba, In ma tozarci ne ai har dashi taiwa don shi da ya ajeta har ta iya,shigo mai a lokacin da yake a tare da wata yana, hutawa, Shima duk ai yadda yake ji yau a ran shi kan wanan irin tozarci bai ko samu walwala a office din ba shi, ****** ********* ****** Kwana biyu, ke nan da faruwan wanan al,amarin daga shi har Salawatu babu kwanciyan hankali a tsaka nin su, don baida wani lokacin ta,duk yadda taso, Yau itace da girki don haka tai shiri na musan man don taron shi amma sai gashi da yamma ya shigo yana cewa zai yi tafiya zuwa abuja a can zai kwana, Tana ji tana gani ya bargarin ba tare da ya kasance tare da ita ba abinda bamu sani ba shine, yana acikin gari bai tafi ko ina ba ashe, Saboda kada ya kasance da ita ya dauko wanan plan din yana cewazai yi tafiya, Mun hadu da ita a falo dana sauko saboda Fatima shiganta biyu a part dina, a zaton ta banda lafiya kwana biyu shine ya sakani rashin walwala din da ban fita,, Danaga ta shigo har two times shine na sauko don na dan mike kafana kadan, Waje na fara fita inda yara suke zaune da Baba Wadda suna karatu addini, Na gaisa da, Baba Wadda yana min ya jiki kwana biyu ya tambaya ance jikina ba lafiya,, Nace cikin sake fuska kadan ai ba wani abu mai yawa bane na,samu lafiya , Zan dawo daga ciki nai kicibis da Salawatu tare da Abuwa zatai mata rakiya, A cikin raha da annashuwa suke, tafe kamar wàsu yan iskan titi, can don yadda suke shewa, Wani kallon banza na watsa mata tun daga nesa abinda duk ya karya mata ahurin mugun nufin da tai niya a kaina ke nan, Muna,iso gab da gab dasu Abuwa ke cewa a Hajiya Meenatu ashe kina ciki ina ce aiko kin fita unguwa ne, Cikin murya mai nuna bacin rai nace mata a kwai wani abune ko ? Tace a,a wai dai mu gaisa tun da ka,shigo gidan mutum kafita baka gaishe shi ba, Nace wanan ai ba komai bane idan akayi la,akari da irin yanayin rayuwan gidan mutumin in har ba na tsari kan addini bane ai sai ki ga kowa na,shiga inda ya ga dama a kowani lokaci, Wanan ba komai bane ko bamu gaisa a yau ba wata rana zamu gaisa ai don hakan ba bakon al,amari bane, Tace tau pa hakane kuma fa wanan gaskiya kika fada kuma ai, Su na dan barin gurin da nake Salawatu ke cewa wanan yariyar isan da akwai abinda na tsani gani a rayuwa ta yanzu ita ce, wallahi ban kaunata har cikin raina, ABUWA tace, idan baki kaunar ta ai mijin ku yana kaunar ta shi ko kin manta hakan, Murmushin takaici nayi tare da hade wasu bakun yawu a bakina nace Allah ya hausheni daga duk wani sherin ki,,, Fatima na,samu a falo zata shigo tana cewa yanzu nake batun na hau sama na duba ki don naga har yanzu baki sauko ba, Nace cikin yar murmushin karfin hali, ai na fito na nufi gurin yara ne don na gaida Baba Wadda kwana biyu bamu gaisa ba dashi,,, Tace a cikin zolaya surukina, malam Wadda nai dan dariyan yake kawai don nasan yadda suka saba ,, ****** ********* ****** Duk yadda zuciyata taso share zancen abin ya gagara don haka na kama kai na da,komai na gidan, Salawatu ta rasa gane yadda zata shawo kan maigidan don bata zaci cewa zai iya hawa haka ba akan zancen, Sai gashi yayi fushi irin wanda bata tsamani ba da ita don duk wani mu,amula ya dai na yi da ita, yanzu Ta samay shi a falo da dare ranan da ya dawo tana bashi hakkuri a cikin marairaice murya tana mai son mantar dashi daga komai, Amna ya daga mata hannu da cewa baida lokacin wanan zancen don Allah ta barshi ya huta a gajiye yake, Yace da safe zamu karasa daga haka ya tashi ya,barta a zaune yana rike da hannun Amira suka haye sama, Ko da ya,shigo daki ya samu nayi barci a gurin da naiwa kaina sabon makwanci saman doguwar kujerar dake dakin, Bai ce uffan ba don yasan cewa ko yace ba zan tanka mai ba don har yanzu a hasale nake dashi,, Washegari bayan fitan shi office ashe Salawatu bata san da fitan shi ba,saboda bai tsaya yin breakfast ba, Don haka ina a daki, naga mutum kawai ya shigo min ina daga kai naga ashe itace again tace min maigidan nake nema fa, Mamaki da takaici suka rufe ni a lokaci guda wanan wata irin dabban matace haka, ba,a gama wani ba,sai ga wani, kuma don haka Nace a hasale ya tafi gurin koyon sallama, sai naga ta juyo tana min kallon mamaki, Azuciyar ta tana cewa, wanan karamar yarinyar haka, tana son raina min wayyo, Banza nayi da ita bankara bi ta kan ta ba sai naga a hasale ta nufi hanyar bathroom kamar mai neman wani abu, Sai kuma ta juyo zuwa inda nake a zaune tace ki fada min ya fita ne ko kuwa, Na dago kai ina duban ta nace au, shi bai bafada maki cewa zai fita bane zaki tambayeni, Look Salawatu idan kika kara min irin wanan halin shiga daki babu sallama, wallahi zamu kwashi yan kallo dake a gidan nan, Salawatu tace cikin daga murya wallahi ki kama min baki don sai nai maki dukan tsiya babu mai fansaki kuma ko ya,dawo babu abinda zai min , A cikin rashin tsoro nace da karfi Bismillah shege ka fasa,, Ta yo kaina na mike kafin ta karaso nai cikin ta da karfi Allah yabani sa a na samu fuskan ta da duka, Da sauri ta dafe gurin tana cewa haba yau yarinya kin debo ruwan dafa kanki a gidan nan, Wayata ce tashiga ringing Salawatu takai duba ga wayan taga sunan maigidan ne sai ta dauka ina fadin miko min wayana idan ba kina son sabon balai bane, Alokacin irin yadda nake ji na manta cewa ina da tsohon ciki a jikina Ta dauko a daidai lokacin da yake cewa Kaunata may ke faruwa ne wai, Haushi da kishi ya kama Salawatu irin yadda taji yana magana yasa ta cewa, ba ita bace nice, Cikin wani murya na haushi da bacin rai yace mata may yakai wayan ta a hannun ki, give it to her maza ki bata wayanta naji , Kuma ki fita mata daga daki mara hankali dabba kawai, Nosens kawai, Wani haushi da bakinciki mai takaici ya rufe Salawatu, tace Oga saboda na shigo dakin Meena zanyi waya dakai kake fada min wanan maganganun, haka ? Ya ce Stupid ki bata wayanta ki fita daga dakin ya fada a cikin hargagi da hasalewa, Sai haushi ya kama Salawatu din tace itama a hasale bazan bata ba,sai ka saurare ni, ko kuma kazo ka kwaci wayan a hannu na, ka bata, Ta juya inda nake a tsaye sai taga bana nan hakan, yasa ta nufin fita daga dakin taji shi yana a rufe, Nan ta shiga dukan kofan dakin abinda ya jawo hankalin sauran jama,an gidan ke nan suka yo sama ganin irin yadda nake tsaye a hargitse cikin tashin hankali yasa su tambayan may ke faruwa ne wai kafin nai magana Ramatu take cewa, naga shigan ta dakin a hargitse shine naji fitina ya kaure a tsakanin su, Fatima ta dubi inda nake take cewa ai mu bude kofan muyi wa shigiya dukan tsiya wallahi, Fatima na juya ina kallo nace ai wanan ma abin da nai mata ya ishe ta don bazan bude taba sai lokacin da ya dawo gidan nan, Fatima tace aida anbari munyi mata dukan tsiya yadda bazata sake sha,awan shiga dakin wata ba izini ba, Isowan shi ne gidanba hargitse yake cewa wai may ke faruwa ne haka duk kun ruda gida da hayaniya, Ita daga ciki tana jefo muna zagida da asharr mukuma daga waje Fatima tana jefa mata irin namu zagin, na yan hausa,, Ya kara cewa Ya Salam wai may ke faruwa ne haka nake tambaya, Ku bude mata kofa may yasa kuka rufeta ne wai, wanan wani irin wullakancine ya juya inda muke a tsaye, Ina tsaye a gefe sai na kasa bashi amsa sai naji hawaye suna zubo min don wanan abin ya zama min bala,i,, Fatima tasa kuka a cikin kissa tana cewa, wanan wani irin masifane mata da ciki zaki bita har dakin ta kina shirin halakata, Yace cikin tsawa ban key din na mika mashi key din dakin ya karba ya bude dakin saiga Salawatu duk a hargitse tafito tayo kan mu da zuman bala,i, Ai ko mukai cikin ta muma da duka guri ya rude sai Ramatu ce tai kasa ta kira su Baba Wadda suka shigo a hargitse, Gaba daya mun jagula mai lissafin shi sai da su Baba Wadda suka shigo ne sanan ya samu suka taimaka mai gurin rike mu duk da haka duk mun jikartu sosai, Ya dubi inda muke yana huci yake cewa zaku kashetane, ? Meenatu ashe baku da hankali, zaku yi mata illa kuyi wa kan ku duk kuja min fitina, a garin mutane, Ya dubi salawatu wace ke ta faman huci tare da face majina tana kuka yace please stop that crying, Ina son kowan ku ta,shiga ta shirya zaku bar min gidana ne a yau din nan kafin ku ja min masifa a garin mutane, Na riga kowa fadawa dakina don aiwatar da abinda yace inda Ramatu ta biyo ni dakin, Yayin da nake kokarin bude wardrobe din kayana don na fara shirin kayana kamar yadda ya umurce mu da yi,, Uwar dakina ki dakata don Allah kada kice zaki debi kayan ki, kibari har muji may za,ayi, Fatima ma juyawa tayi zuwa dakin ta don ganin a cikin serious yake maganar shi ba wasa a zancen, shi,,, Salawatu ce ta saura ya juya gare ta cikin masifa yana cewa get out in my side, Ta wani shagwabe tana cewa oga kayi hakkuri ka saurare ni zan ma bayani, Yace cikin wani irin tsawa get out, my friend i dont want to hear you,,, Juyawa yayi ya fita daga gidan zai tafi yai muna buking din jirgi, sai ga su Baba Wadda sun tsare shi suna bashi hakkuri, Daga gurin da nake kwance naji karar motar shi alamar yabar gidan zuwa wani gu kuma, Nan na fada saman gadona a cikin matsanacin tashin hankali, ina ta rusa kuka gwanin ban tausayi ,, Ina Daga kwance, kaina yana min wani irin azabbaben ciwo, kamar ya tsage, Ina gurin a kwance har akai kiran Sallah la,asar sai a lokacin na mike na fada bathroom don na yi alwala, Abincin da Ramatu ta dafa muna yana aje daga gefe gudana har ya soma sanyi ko don tun safe aka aje min,,, A gurin da nai sallah nake ji na tashi zuwa kasa don na duba yarana don tun safe da,suka fita bangan su ba,,,, Ina fara takawa na soma jin dishi dishi a idanuwa na kaman zan fadi hakan yasani saurin bin bago don karna fadi, Maimu ce tashigo dakin don ta kwashe kwanoni dake dakina don wankewa, Tana ganin irin yanayi da nake ciki ai ta yanka ihu tana cewa mun shiga uku jama,a ku tausaya muna Anty zata mutu,,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA SEENABU kuyi hakkuri dani please yanayi ne ya kawo delay din rubutuna please nagode da fahintar ku gare ni ,
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣2⃣5⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
LA,ILLAHHA, ILLALLAH,,, WA,ADAHU LASHARI KALLAHU,,, LAHUL,MULKU,,, WALLAHUL HAMMDI,,,, WAHUWA ALLAH,,, QULLI,SHE,IN KADIRRR,,,,
JUMMA,AT MUBARAK MUSLIMS SISTERS ALL OVER THE WORLD,,,,
Ina dakina muna fama da Ramatu wace ke bani hakkuri akan kada nayarda na,bargidan mijina da sunan yaji ko tashi,, Baba Wadda ne ya shigo dakin hankali a tashe yake cewa Meenatu garin yaya hakan ya farune wai ? Maimakon na bashi amsa sai kawai na saka mai kukq irin mai tsuma zuciyan dan uwa, Yace Meenatu ashe ban isa naji damuwar ki ba je nan don nayi karami ki kirani da mahaifinki ko ? Cikin kuka nake cewa ba hakana,bane Baba wallahi ni al,amarin gidan nan ya isheni,, gaskiya, Baba ni bazan zauna gurin da babu addini ba sai al,amari kamar na kafirai, Yanzu Baba yadace ace wanan matar tana shigo min daki duk lokacin da taga dama ko taso a ranta koda ina kwance ne da,,,, Sai kuma na,sa kuka mai tsuma zuciya don bazan iya fada wa Baba Wadda wanan zancen ba kai tsaye,,, Ramatu ce daga gefena tace yo wanan anyi yar banzar mata ba shakka naga fitan ta daga dakin ku a yan kwanakin da suka shige, Nai mamaki nima kwarai dana ganta tafito gurin ku a wanan lokacin don sai da na kauce mata irin yadda naga ta fito daga dakin, Nace cikin kuka wallahi Ramatu kawai ina tare da Yaya sai ga wanan matar tsaye a kan mu kuma,duk da halin da ta gan mu a ciki amna sai taki fita ta tsaya wai bashi hakkurin cewa bata san a haka zata samay mu ba wai, Kuka mai tsuma zuciya na kara sawa a lokacin Baba Wadda yace wanan matar dama siffan kafirai ke gare ta, ai,,, Nan shima Baba Hamza ya shigo hankali a tashe sai ake mayar mashi yake cewa wanan anyi yar banza mara mutunci wallahi, Kowan su na fadan albarkancin bakin shi akan zancen ina daga zaune gefe sai hawayen dake ambaliya a idona don takaici da bacin rai, Nake jin kawai nabar auren da Yaya Abubakar na huta wa raina yafi min komai sauki arayuwana, Baba Wadda ya dubi inda nake zaune ina ta faman rera kuka yake cewa tashi ki share hawayen ki kidaina wanan kukan haka, Don babu inda zaki tafi sai dai ya kora munafikan matan shi su koma inda suka fito amna babu inda zaki tafi ke, Na ce cikin girgiza kaina a,a Baba barshi kawai na tafi gida tunda har ya iya bude bakin shi yace hakan bai ko tsaya tambayan yaya akayi tashigo har dakina ba second time,, Baba Hamza yace kwarai kuwa shine nima ke bani mamaki ai, Sukace babu inda zaki tafi fon anan suka samay ki sai dai su koma inda suka fito, Ramatu tace nifa ko ita wanan maman Aina din dake wani shige maki wai ita kamar ta Allah ban yarda da ita ba wallahi, Don duk ladabin shegune take yi saboda tana da wani manufa a hakan da takeyi din amma koma maynene nufinta Allah yafita ai, Da haka sukai ta bani magana har na dan ji sanyi a raina nace insha Allahu na fasa, Sun fita da niyan zuwa su sami Yaya Abubakar, inda yake, Ramatu tana a tare dani tana kara bani baki yadda zan kara kama kaina daga sherin kishiya, Fatima ta,shigo dakin da alamar barci tayi ita take cewa wai bai shigo bane na kalleta a fuske ina cewa banda masaniya gaskiya Sai take cewa ai bari shegiya sai tabar gidanvnan don ubanta don na fadi wallahi yadda taja min saki nima sai naga bayan ta, Da sauri Ramatu ta dago kai daga inda take rana min signal na kingani ko da manufa take komai nace, Wanan ai bakawa dan uwar ka fata amma dai aikowa ya tsaya matsayin shi bada shiga hakkin kowa ba , Hmmm Meenatu ke nan banga abinda zai sani jin tausayin kishiya ba wallahi tun dai wace bata da guri sai na nuna manufanta ga mugun nufi,, Shigowa Amirana yasani mayar da hankalina agareta na fita zancen ta sai dai a zuciyana ina cewa hmmmm, duk dai gautan ja ce sai dai in bata sha rana ba,,,