Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 135

Tarko complete novel - Chapter 135

Tarko complete novel Chapter 135: Tarko complete novel Chapter 135. ****** ********* ****** Yaya Abubakar bau shigo gida ba a ranan sai dare sosai balale…

3,331 words

****** ********* ****** Yaya Abubakar bau shigo gida ba a ranan sai dare sosai balale ya,shigo gurin mu ba don haka nashige part dina da yarana muka rufe tun takwas da rabi nadare, Abinci kawai yaci ya shige daki don ranan a dakin Fatima yake,, Rayuwan shi ba dadi barci ya gagare shi sai sakawa da,warwarewa yake daga kwance, Fatima wace tasha kwalliyan shirin kwanciya sai karairaya take amma bata samu wani kulawa ba don haka tabawa kanta hakuri, Barci ya fara dauka ta taji muryan shi yana cewa Fatima inda ta farka firgigit tana cewa Naam a,zaton ta ko harka ne, Sai taji yana cewa ki fada min yadda akayi Salawa ta shiga har dakin Meenatu dazun, Nan Fatima tashiga fada mashi karya da gaskiya, wai ina kwance ne naga Salawatu a kaina ta fara dukana shine nake ihu sukaji suka,shigo dakin, Allah ne ma ya tsare Ramatu ta hawo saman da tai mata dan karen duka babu kowa a kusa, Har Allah yaba ta sa,a tana waya da wayanta tafito da gudu shine ta rufe ta ta baya kasamay mu a hakan don tace idan tafito sai anyi kashin kai a lokacin, Tace dama ai tace sai ta yi sanadin cikin nan ya fita daga jikin Meenatun wai,, Baice uffan ba sai gyara kwanciyar shi dayayi tare da furza iska, yana mika,,har barci ya dauke shi a hakan,, Washegari Ramatu ta,sakani a gaba akan nai wanka naci abinci tare da kara,bani shawara na,saki jikina kada na,sa,damuwa a,raina ko kadan, Acikin ikon Allah na,samu walwala,akan,shawaran Ramatu din da takw ce min na mayar da komai ba komai ba na,saki jikina, Don har na fito falo na dan zauna da yarana mukayi breakfast tare dasu da dan hira, kafin su wuce zuwa school,,, Ina gyarawa Alhassan aninin rigar shine maigidan yafito dauke da yar case din shi a hannuwan shi idanuwan shi kar a kaina kamar mai son gane, wani abu a gurina, A sanyaye nai mashi ina kwana ciki ciki, batare dana bude murya na ba sosai, Ya amsa shima, fuska ba yabbo ba fallasa da lafiya a takaice batare da ya tsaya ba,, Ko breakfast bai tsaya yiba ya kwashi yara,suka fita zuwa school, Ban wani dade kwarai a falon ba,na kwasa zuwa sama nadan kwanta don na mike jikina, Shigewa na yayi daidai da zuwan Abuwa wace akaiwa kiran gagawa na,tashigo taji may yafaru,,,, Sun kai wani lokaci dakin a tare suna kullawa suna,warwarewa,a tsakanin su har tsawon wani lokaci, Kamar yadda kowa,yasa yadda mai suna,Abubakar yake da,da,hakkuri da sanin ya kamata hakama,wanan Abubakar din namu yake, da hakkuri a rayuwan shi, Don haka a hankali yake son ya zantar da hukuncin wanan al,amarin a gidan, shi, Amma ni a bangarena ina ganin cewa bai dauki wani mataki ba don haka kawai sai na,kulle zancen a raina,ba,wani walwala a tare dani, Yai ya kasance jumma,a kamar kullun ina kwance a dakina rigingine, saman gado sai haye ke dan tsiyayowa daga idanuwa, a hankali, Ban san shigowan shi dakin ba sai ganin shi a bakin gadona nayi a tsaye hannayen shi a cikin aljihun wandon shi yana mai kura min ido cikin kada kai, A hankali na bude idanuwa da sukai, nauyi dishi dishi, don kuka, Ganin shi danayi a tsaye yasani kokarin yunkurawa na tashi zaune, Sai kin halaka kanki zaki bar wanan kukan haka ko,? Ya zauna daga gefena yana duban fuskana a hankali, na kawar da kaina daga gare shi,, Yace ban san may yasa kika sawa kanki wanan zancen a rai ba har yakai ga ramar da ke haka gashi duk kin wani ramay kamar wace tai ciwo, Don Allah Yaya Abubakar ka kyaleni ka tafi can gurin yan barikin matan ka,,, Ido ya kura min inda yake kallon yadda yau nake mai magana kamar bani bace, Meenatun da ya sani, Kalaman nawa sun bashi mamaki sun ruda shi ya gane cewa ga,duk kan alamu yau ina a cikin tsananin bacin rai, Don haka sai ma ya,rasa ta inda zai faro dani ta yadda zamu fahinci junar mu a zancen, Sai dan sheshekan kuka nake a hankali a ciki ciki gwanin ban tausayi dani gani na koma,wata jagwab ga ciki ya kara mayar dani wata kala can daban, Aranshi yaiwa Salawatu Allah ya isa wanan hadin fadan da tayi a lokaci guda, don duk yadda yaso ya nuna hakkurin shi wanan karon abin ba zai yi ba, don ta kaishi makura sosai wallahi, Wanan masifan da taja mai inda ba Meenatu bace watace da baisan inda zancen zai tsaya ba, Kanshi a dafe daga gurin da yake zaune yana tunanen wanan sherin na Salawatu haka don yasan da niyayya taimai hakan, Kanshi ya adafe sai tunane yake a cikin tsananin damuwa tare da neman mafita akai, don wanan karon takaishi makura ko, Meenatu yarinyar mai hakkuri da sanin ya kamata duk wani abinda yake tana kokarin shanyewa a rata amma ga wanan zancen ya tsaya mata a rai, Ina daga gurin da nake zaune shima yana daga kwance gurin da yake din yana kallona a cikin mamakin yadda nake kuka, Dakin yai tsit dukkan mu kowa da irin damuwar da yake damun shi daga cikin mu , Ya kara cewa Na ce kiyi hakkuri dan Allah saboda kada kiyiwa kanki illa,hakana, Bana,son wanan damuwar don zai iya saki a cikin wani matsala fa, Ki bari zan dauki mataki yadda ya kamata na dauka insha Allah, bawai hakane zai sani daukan mataki ba Maimakon naji sanyi ga zancen sa sai ma kara tunzurani da kalaman shi su kayi, nace da karfi a cikin kuka ba sai ka dauki mataki ba ka barta ai ta,shigo duk lokacin da ta bukaci hakan, Wallahi Yaya na tsani wanan aure na tsane wanan mugun rayuwan da kuka jefani, a cikin sai na kara,fashewa,da kuka, da karfi, A take jikin shi ya dauki rawa a lokaci guda ran shi yai mumunan baci da jin kalamaina, Nan shima ya fara bani amsan zance na a cikin fushi yana cewa ai tunda kin tsaneni sai ki dauki mataki a kan haka, Nace maki kiyi hakkuri a kan zancen nan Amma sai kara tayawa kanki da hankali kikeyi, kije kiyi duk abinda zakiyi a kai, Yakara kura min idanuwan shi a cikin fadan yana cewa dubi duk yadda fitina yasa ki wanan mugun rama haka Meenatu da babu ruwanta yau itace ta jajirce mashi haka da masifa, Kan gaskiya Ranan haka muka kwana kowa rai da zuciya yana suya, saboda bacin rai, Washegari haka yafita daga dakin nawa a cikin rashin walwala a tare dashi, don da a,zaton shi zai iya shawo kaina mu shirya,,, Har yakai kofa zai fiylta nake cewa ban son na kara kwana,a gidan nan a matsayin matar ka wai, Shut up, Meena ki iya bakin ki tun jiya kin ishe ni da zancen banza kawai ni ina a matsayin mijiki kuma yayan ki zaki zauna kina min wana surutun haka bai kamata ace wannan surutu ya fito hakaba daga bakin ki don karki manta cewa ni mijin ki ne fa, ko ki nadon fadawa fushin Allah ne a hakan , Dakatawa nayi ina sauren shi kamar mai jin abinda yake fada amma a raina sai cewa nake dubar shi kamar wanda yake maganan gaskiya har zuciyar shi, Ranan mun kai wani lokaci a daki bamu fito ba sai fafatawa muke dashi , Nacire kunyan shi na,fada mai magana,son raina,wanda ban taba zaton zan iya fada mai irin haka,ba, Don har cewa nayi dama ance a gurin dadiro suka hadu da Salawatu sukai zaman bariki, shine ta like mai sai da ya aure ta,, Yace a fusace kamar zai dakeni inda yayo kaina idanuwan shi a waje yana cewa Ke enough Meenatu kikama bakin ki wallahi kona fafasa ahi yanzun nan, Ganin irin yadda ya juye min a lokaci guda ya sani jan bakina nai shiru don nasan yadda ya hasala zai iya makeni din, Ashe dama da farko kyaleni yayi don mu sulhunta sai da yaga da gaske nakeyi ya hawo min kamar mayunwacin zaki,

****** ********* ****** Muna a ciki muna masifa suko matan gidan suna,daga waje suna balain kishin cewa mun kai wani lokaci a,sama bamu fito ba wai, Basu san cewa muna can muna ta faman madifa ba a tsakanin mu nidashi, Saida aka kira wayan shi wani amin nin shi da muke a kwatas gudane ya kira shi din, Shine har ya shirya yafita yabarni a cikin bacin rai inda nima na tashi na gyagije kamar bani ba na,fito don na,duba yarana, Ba,Salawatu ba har Fatima da na fito sai da naga sauyin fuska a gare ta amma da yake yar duniya ce sai take cewa wai har kin fito nace eh nafito sannu da gida, Na fita don gaisawa da su Baba Wadda ita ko Salawatu tun wanan zancen bamu magana a tsakanin mu dama, da ita,,,

A haka abubuwa sukai ta guda gidan babu zaman lafiya dama saura sati biyu su bar gari don haka, wani yammaci da yashi ana kwana goma cur da fitanar mu yake ce masu su shirya zasu koma wanan weekend din, Aikuwa nan wani sabin fitinw yafara a tsakani su dashi inda ita Fatima ke cewa,ba inda zata tafi don yar ta tafara karatu yanzu a nan port din, Amma sai yace aiko a Abuja akwai makaratan da ma yafi na port din kyau da komai na karatu, Sai kuma take cewaai ita bata karasa hutun ta ba,sai nan da sati biyu don tai tafiya anan din, Ganin zata fara caza mashi kai dama yana a cikin wani sai yake ce mata idan takara tankawa a yau zata bar garin, Dole tai shiru badon taso ba,ta juya zuwa dakin ta tana guna guni a ranta don ba dama tafurta a fili, Salawatu hankalin ta ya tashi sai shige da fice sukeyi da Abuwa inda bokayen ibo ke cin kudin su suna yaudaran zu, An mata alkaaarin cewa ko ta tafi zata dawo don a karshe ma ita kadai zata zauna a Abujan batare da kowa ba kamar farko,, Ina waya sosai da mutanen gida yan uwa inda suke ce min idan na haihu zasu shigo port su sha buki nakan ce masu Allah yanuna myna lafiya, Har gobe mahaifita takan min nasiha akan yadda,al,amari yake a yanzu duk da ina,cikin tashin hankali basaini daga,waya na kira gida na fada masu ba, shima Baba Wadda na roke shi da kada ya fada don sirin mune, Zamu iya shiryawa da mijina,watarana,suko iyayyena,dana,fada masu irin halin rayuwan da nake a,ciki bazasu taba mantawa ba, Shiyasa ba,a,son mace tana fadawa iyayyen ta laifin mijinta don abin yana masifan tsawa a,zuciyan su har su dinga kallon miji dashi suna,samun sabanin rayuwa, Hakan yasani kin fadawa kowa irin halin rayuwan da nake a ciki da maigidana nadaure ina,shaye abina har mu kai ga,mafita a kai, Duk da abubuwa sundan yi sanyi sai shirin tafiya,masu tafiya ke yi hakan bai sani na huce wanan zancen a raina ba don haushin Yaya Abubakar nakeji sosai idan na gan shi kan zancen,, Ina Falo zaune da yarana muna hira acikin dariya,suna,min gasan karatu yashigo ya,samay mu a hakan yana ganin mu sai yadan ji sanyi a ran shi, don ya dade bai gan mu a hakan ba, Yana zama yana jawo Amira zuwa jikin shi na mike nabar falon zuwa dakina ba,shiri, Yabi bayana da kallo har nashige ziciyar shi tana mashi kuna ina,shigewa ya saki wani gwauron numfashi a fili, Yakara rugumay yatinyar ajikin shi cikin ran shi yana cewa ya rasa yadda zai bullowa wanan al,amarin, Don ya kamata ace nasauko zuwa yanzu amma baiga alamar hakan ba gareni, Sam ban yarda ko guri guda na zauna dashi ko salawatu wace ma bata da lokaci sai shige da,fice takeyi a gidan kawai, Ranan tafiya yazo mukai Sallama da Fatima sama sama ba kamar yadda na zata ba amma tace min bazata dade ba zata dawo, Salawatu ko kallon juna bamuyi ba da ita nabar falon zuwa sama bayan na gama sallaman da su ko,,,

****** ********* ******* Sun isa Abuja ana koda ruwan sama Lawal mijin Fattu ne yazo ya tare su inda,suka,shiga gida a jike don ruwan da ake mai karfi, Tun kan su shiga dakunan su suka,fara sauke masifa a tsakanin su yana jin su yake cewa zai maganin su ai, Salawatu tana,kokarin bude kofar dakin tane yake ce mata,ta,dakata tukun sai sun dawo tukun, Ta,zaci wani guri zasu tafi da murnanta tabishi zuwa unguwan da yace, din, Ganin uguwar da yazo da itane ya bata mamaki don a,uguwar sune ya kai ta ya Parker mota akofan gidan ya,bude, yasa,hannu a,serve din mota yafito da farar takarda ya mika mata yana,cewa ga wanan da check a,ciki na amfanin ki, don haka,ban son wani fitina agai kayan ki zan sa mota gobe ya kwaso maki, insha Allahu, Tace a cikin wani murya ban fahince ka ba gaskiya yace wanan takarda na,sakine nai maki so bamu da aure dake yanzu don na yanke igiya biyu daga cikin auren mu dake,, What ? What the you mean by that,? May nai maka,zakai min wanan hukuncin hakane wai,? Ya dubota ido a cikin ido yace I can't staye with you anymore saboda abinda kikai wa family dina na tozarci, Idan na zauna dake a haka na,shiga hakkin wace kika zalunta don haka,naga na,sauwaka maki shine alheri a,gare mu baki daya,,, Kamar ta,baba takoma a lokaci guda tana cewa ka tai makeni for god sake kada kai min haka shetin shedan ne bazan kara,ba, Yace will you stop that kada ki manta fitanki da Abuwa matar da na hana ki hurda,da ita amma kikaki kuka,tafi can Akwata, bayan dam gurin wani bokan ku har can natura aka biku don in samu evidex a kan ki na kuma samu don har wankan da boka yai maki saida,aka,dauki min photo shi a,waya, Shiru tayi kamar ruwa yaci tana cewa na,shiga uku I don die wooo, God help me woo iam dying today ,,,,, Yasa hannun shi ya bude kofan motan yace get out in my car noses woman, And kada ki fara naga kafanki a gidana nabawa security alernt a kanki ko, Nan yaja mota yatafi ya,barta ta sa hannu bibiyu akai tana,rusa kuka kaman karamar yarinya,,,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA SEENABU

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣2⃣6⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH GAFURUR RAHIM,,,

Tashin hankali mai kama da bala,i shine ya faru a wanan ranan a gurin salawatu, Motar shi na barin gurin ta,sa a hannu a kai tafara rusa kuka kamar karamar yarinya tana cewa tashiga uku ta lalace ita Salawatu ina zata sa kanta,, Ita wallahi karyane sam bai isa ba basu rabuba dakin ta zata komadon in shi ya saketa ita bata sake shi ba, Kururuwan tane yafito da mutanen gidan su da makwabta nan da nan guri ya cika da jama,a suna son jin ba,asi itako sai faman kururuwa take tana cewa sam bata saku ba wanan ma zancen karya ne kwai,,, Da kyat da boni suka samu ta,shiga gida saboda dare yayi gashi anyi ruwan sama gurin yayi tsit babu mutane a waje lokacin, Ranan wani irin barcin wahala tayi a rayuwanta tsakiyan mutane sunfi su goma a,daki daya maza da mata, Kuma a kasa saboda babu ko katifan kirki a dakin , Tun a,daren nadama yazo mata a,rai tayi da ta,sani ta zauna lafiya tayiwa kowa biyayya sau da kafa,a waye lafiya, Amma gashi shedan da son zuciya sun rude ta,sun hanata samun ribar duniya, Ta manta da irin yadda ta aha wahala a baya kafin ta,samu wanda zata aura, Da kuma irin yadda ta,sha gwagwalmaya kafin ta,samu Abubakar yace yarda da zancen auren shi da ita, Kwana juyi da soshe soshe ta kwana a,dakin ga kwari na ta hawan su,,, Mace ke nan yar gaba da baya yau kina a,cikin daula gobe kina acikin wahala, idan mijin ki ya mutu ko kun rabu dashi, Sai ki koma kina dan rabe rabe a dakin uwar ki ko cikin yan kannen ki kuna,sa,insa da junar ku, Duk inda kika,samu kanki kiyi hakuri ki bi a hankali ki zauna lafiya da kowa da Allah ya hada ki dasu,,, Maganan da wata kawarta ta taba fada masu ke nan ita da Lubna da sukaje gurinta wai ta taimaka masu idan tasan gidan wani boka ko malam,, Shine take basu shawara da su daina wanan harkan si zauna lafiya da kowa don samun gurin hutu har su tai maki wani nasu su ma, A lokacin bala,in haushin wanan kawar nasu su kaji amma sai gashi yau ita, da kan ta, take tuna wanan shawaran a ranta a daidai lokacin da zancen ya zama mata dana sani,,, Ya Abubakar yazo gida a gajiye rai kuma a bace duk abin duniya ya jagule mai a,zuciyar shi, Yasamu babu kowa a falo don haka ya rufe kofa ya kashe wuta, sai ya haye sama abinshi, A can ya samu Sadiya a kwance har tayi barci ta gaji da jiran shi ko, Sai da ya gama duk wani shirin shi ya koma ya kwanta zuciyar shi fam da,tunane sai dai yana ji kamar an cire mai wani kaya a kafan shi, Bai iya tabuka komai ba, a daren don irin yadda rayuwan shi yake a,bace, Washegari sai zuwa sha biyu suka fahinci cewa Salawati bata a gidan tunda dare Koshi sai da su kaga an bude dakin ana kokarin kwasan kayan dakin wasu masu kama,da jami an tsaro suke kwasan kayan, Yaya Abubakar bai mata keta,ba don har motar ta,saida ya,bata abinta da,duk wani abinda yasan shi ya,saye shi, Salawatu ashe tun safe tazo gidan amma,sai maigadi ya tare ta yace bazata shiga ba don an bashi umurnin yin hakan ko, Duk yadda taso maigadin ya barta,tashiga don tabawa maigida hakkuri amma maigadi yaki yarda da,shiganta gidan, Dole takoma tana sharan hawaye tare da,tarin dana sani a zuciyar ta yau abinda tafi karfi gashi yafi karfin ta,gaba daya,,, Ko wan su da mamaki yake kallon irin yadda ake kwasan kayan a na fita dashi waje Wa yan,nan jamian sune suka,kai mata kayan ta hargida,tare da,takardan shedan kwasan kayan nata, Wanan shine karshen zaman Salawatu sa idawa a,gidan matar dada tun shigowar ta hakkuri maigidan ke faman yi da ita, Haka kuma kishiyoyin ta,babu wace take so ko kauna da zuciya daya babu dadi a tsakanin ta da kowan su, Idan har kaga ta juya gurin mutum to tana son a kullawa wata,sheri ke nan a gidan ita shine hadin kan ta,,, Tana ganin kayan nata hankalinta ya kara dagawa, ta rasa may ke mata,dadi don, kaman ta sa hannu a ka ta yanka ihu,,, Fatima ce ta bugo min waya a lokacin ina barci ina ganin wayan ta na mike ina mata ya gajiyan tafiya ya suka samu mutanen gida, Batare da ta bani amsa ba take cewa, kedai ai kinji abinda ya faru daiko ? Nace a cikin sauri subbahanallahi, may ya faru Maman Aina, ? Tace cikin dakatawa hmmm bari ke dai ai wallahi abin farin ciki mutumiyar ki dai sai kikaji an tafi ko ? Nace wake nan dai ? Salawa mana, tabani amsa a takaice,, Cikin mamaki nace an tafi ina kuna daga komawan ku ? Tace sun rabu mana har an kwashe kaya yau babu ko tsinken ta a gidan nan, ai, Innalillahi innalillahi wa,ina alaihim raj,un, Yaushe ? May yai zafi haka ? Subbahanallahi may yafaru kuma ? Duk a cikin rudewa na jero mata wanan tambayan a lokaci guda, Sai take ce min aike dai bari wallahi tun shigowan mu garin nan ya sallami yar banza ya korata gidan su, Kai kai kai shiko dai yaya shine har da kwashe kaya idan Allah yasa akwai sauran zama fa a tsakani tai sauri tace Allah ya tsare wallahi ba dai gidan nan ba kan, Ai tabarshi har abada ke nan yar banza mutumiyar kawai, Subbahanallahi nake maimaitawa a raina cikin nuna rashin jin dadina har layin ya katse, Gaba daya,sai na rude duk na,shiga damuwa a lokaci guda na koma wata silent banda kuzari a jikina,, ****** ********* ******

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull