Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 136

Tarko complete novel - Chapter 136

Tarko complete novel Chapter 136: Tarko complete novel Chapter 136. Kwanan shi uku yajuyo ya,dawo portharcout shi kadai sai yar jakar kayan aikin shi a…

2,885 words

Kwanan shi uku yajuyo ya,dawo portharcout shi kadai sai yar jakar kayan aikin shi a hannun shi, A lokacin ina zaune a falo tare da Ramatu ina saye da,wani fatin lace mai aikin zare dark blue dinkin bubu nayi dashi da zani, kamar na matan Niger,, Fuskana,ba yabo ba fallasa a cikin sa sai dai ban daure shi urin tam din nan ba, A lokaci guda mukai mai sannu da zuw shima ya amsa mu da daga hannayen shi gurin karbawa dace yyahwa, Na mike da kyat irin na masu ciki na dauko mai goran ruwa da cup hade da drink na juice din mixed fruits , Yana zaune ya rike goshin shi da dayan hannuwan shi kamar wanda yake a cikin damuwa, Murya kasa, kasa nake cewa a hankali ga ruwa ya sauke hannun daga saman goshin shi yana furza iska, Yakar bi ruwa batare da cup ba ya kafa kai ya kwankwade goran ruwan gaba daya ya aje goran saman dan ture din dake rike a hannuna, Yace na tafi da juice din wanan ma is OK yakara mayar da jikin shi a saman kujeran da yake zaune a kai, A lokacin yaran suka shigo ta kofan baya suna mashi sannu da zuwa tare da rugumay shi a cikin kauna da so, A zatonq da Sadiya zai shigo amma sai na gan shi shi kaidai don haka sai nai tsan mani ko sai daga baya zata biyo shi ta, shigo, Na haye sama da yar jakar da,ya,shigo dashi inda na barshi da yaran sun ta hiran su kowa na fadin complain d8n shi wa uban nasu, Ramatu tazo shigewa yake ce mata ta gyara dakin su na kasa su koma a ciki ita da yara, Ruwan wanka na hada mai tare da kara gyara dakin don ya kara daukan ido, badon komai ba sai don sanin cewa mazan yanzu sun fi son dakin macen da koda yaushe a gyare yake, Dakuma macen dake kokarin canza launin a binci wa namiji din, Na sauko yana zaune nake ce mai na hada ruwan wanka a sama ya amsa min a kasalance da cewa ok, Daga sama Ramatu take cewa Hajiya abinda yasani mikewa na hau saman ke nan na barsu nan shi da yaran, shi, Nan Ramatu take sheda min cewa, wai, yace su kwashe zuwa kasa ita da yara gaba daya, Sai nake cewa acikin dan murya kasa kasa ina ga,dai akwai matsalane a gidan don kin ga ai baizo da Sadiya ba don da tace muna wai zata shigo tare dashi ai,, Bayan yai wanka yafita duk ina can tare da Ramatu muna hada kayan yaran, Sai dare ya dawo ya,samu muna cin abinci a tare da yara na, da sauran mutane, Ya haye sama nadan wani lokaci sai gashi ya sauko a cikin wata jallabiya mai yar gajerar hannu,a ya tako daga matakala sannu a hankali ya na,waya acikin wani yanayi, Yana cewa, na riga da na fada maku cewa is over now ba sauran wanan zancen a raina so please bana son a kara kirana kan wanan zancen please, Daidai lokacin ne yakara so gare mu yana cewa, cikin muryan shi ta rowa ina nawa abincin Amir, ? A hankali na tsamay hannuna da niyar zuwa na,dauko mai abinci amma sai yake ce min na zauna Ramatu ta dauko mai, Ramatu ta dauko abincin takawo mai nan na zuba mai daga gurin da nake zaune, Har dare muna falo zaune ana hira inda nai waya da Anty Amarya daga baya kuma kamar hadin baki sai ga Mamana ta kirani again, Na dauki wayan ina murmushi nace mama ina kewan ku wallahi yanzu nagama waya da Anty ai, Cikin hausan mu na mutanen Kebbi take cewa duk kuna lafiya dai ko ? Cikin girmamawa kamar munaa fili nake cewa lafiya kalau mama ya sauran mutanen gida tace walle duk lafiyan su kalau, yar baba, Tace Maman ku daina bata da lafiya kwanan jikin nata ya tashi kuma, amma ban sani ba ko sun fadawa shi mijin naki, Da sauri na,daga kai na dubi gurin da Yaya Abubakar yake zaune idanun shi time to time suna a kaina, Nace subbahanallahi injin da sauki dai jikin nata ko ? Mama tace min gaskiya tana jin jikin amma taji sauki yau na gani, Da sauri naga yadago kai ya kafe ni da idanuwan shi, Mama take ce min yaya yaran duk suna lafiya dai ko Nace lafiya kalau muke mama, Tace tau yar Baba nasan ki da hakkuri don Allah ki kara aksn wanda kike dashi da farko don kinga yanzu girma ne ke fara shigan ki tunda kin fara tara iyali, Balle kuma gaku tare da kishiyoyin zamani don haka ki rubunya hakkurinki akan na farko kin san mazan zamanin nan su ma sai da hakkuri , Nace insha Allahu ma, Tace to Allah yai maku albarka na amsa a cikin sanyin rai da Amin mama, nagode ina gaida Baba,, A haka mukai sallama da ita na kashe wayan ina mai duban gurin da yake a zaune sai yake cewa waye ba lafiya nace mamace wai ba lafiya akace, Yace Mama ba lafiya shine aka rasa wanda zai fada min duk cikin su, sai mama Saratu ta bugo waya tafada min, Shiru nayi ina kallon shi inda naji ya bugawa yaya mustapha waya yana mashi masifa ranshin bugo mai wayan da ba,a yi ba a gida , Anyi cewa a kawo ta asibiti ta jirgi gobe zasu kaita sokoto tazo abuja gurin likitan ta, dake ganin ta, Inda ya kuma buga waya Abuja wa lawal yana sheda mai za,a shigo da mama Ladi din ga gobe insha Allahu, Yaran sunyi barcin su a nan falo gurin mu don haka na kira Ramatu nace tazo ta kwashe su zuwa,dakin su,,,, Nice na,fara,shiga, daki inda nai wanka,tare da,dauro alwala,kamar yadda na,saba indan na,shiga wanka zanfito sai nai alwala,don ya kara min hasken goshi, ga idon jamma,a, Ina zaune a gaban mirro ya shigo dakin da alamar a gajiye yake saboda irin yadda na ga yanayin shi, Bathroom ya,shiga na tsawon wani lokaci ina kwance a saman dogon kujera ya fito daga bathroom din idanuwan shi kyam a kai, Sai da yagama,duk wani abinda zai yi shine ya tako zuwa inda nake kwance duk da a lokacin bq barci nayi ba to amma idanuwan nawa sunyi min dishi dishi saboda nauyin barci da ya fara kama su, Ganin shi a,gabana yasani dan lumshe idanuwan nawa jin hannuwan shi da nayi a saman jikina yasani, saurin kokarin mikewa zaune, Lokacin da nake kokarin tashi zaune ne naji ya kwanto jikin shi zuwa jikina A take naji wasu hawayen bakin ciki suna biyo min fuskana a hankali Muryan shi naji yana cewa please Meenatu ya kamata ki sassauta wa rayuwan ki hakana, Don duk wani abinda zakiyi nasan a kan gaskiyan ki kike don an tabaki , To amma tunda abin ya wuce ai yakamata ki sake hakana ko zaki samu relief a,rayuwanki ke ma, Ki saki ranki hakana ko na,tare dake zasuji dadin zama dake ban san kuma hukuncin dakike so yanzu na dauka ba, Kinsan dai bake kadai aka,tozarta ba har ni nake gani nafiki tozarta a nan amma shi musulmi ba,a son shi da riko da yawa haka, Yakare zancen a cikin dan tausa murya irin yadda mai ji zaiji tausayin shi, Acan kasan zuciyata na soma jin dan sanyin zancen shi a raina ko dn ma yadda mutum kamar Yaya Abubakar yake magiya a kaina, Na bude bakina zanyi magana a karo na farko da ya fara zancen shi, yana mai kura min idanuwa nace, Ni abin yaki fita min daga raine akoda yaushe na tuna ina ganin abin yazo min sabo a rayuwa, Yace to ina mai rokon ki daki cire wanan zancen a ranki don kada yazo yai maki illa gaki da ciki a jikin ki, tsoho, Sannu a hankali na soma jin wani sanyi a zuciyana yana sauka a hankali, Da kyat na tursasa zuciya ta na samu har na dan manta da komai da ya faru ya samu ya dan samu kaina, Ganin yadda,na,sauko a lokaci guda yasa dadi da farin ciki ya baibaiye shi a lokaci guda, Bakomai yasa shi yin hakan ba gare ni sai don sanin da yayi cewa Meenatu yarinya ce mai yawan hakkuri, Kuma wanan karon da ta hau an tabata ne sosai don ko shi sai da kyat ya,samu zancen ya fita mai a rai, Washegari ya tashi kamar wanda aka jefa a rahama don ranan sayayya yai muna abubuwan bukatan mu komai normal, Sai da daren ranan ne yake fada min cewa daga wanan lokacin ya daina system din retation a tsakanin matan shi, Da sauri najuyo ina tambayan shi ko lafiya da hakan , Yace ra,ayin shine yin hakan banda abin cewa akai don haka,naja,bakina nai shiru kawai, Yake ci gaba da cewa Fatima da Sadiya ne a gida zai so ace ya gama ginan shi na Birnin Kebbi sai dayan su ta koma can da zama daya tana Abuja, Nace ita Salawa fa sai ce min yayi bada ita,ba nace ke nan anan zata zauna tare da mu ko ? Yake cewa bata tare da mu yanzu so a tsakanin ku ne wanan anan ma shiru nayi tankar ban fahince shi ba,sai dai a,raina nake cewa kenan zancen Fatima gaskiyane ke nan,

****** ********** ****** Jikin Mama Ladi ya matsa gashi ba wani kulawan kwarai take samu ba,daga gurin su Sadiya da Fatima , Ranan naji yana fada sosai dasu a,waya cewa wai kwana biyu batasha magani ba da likita yashigo dubata ne yake fada mai hakan, Ina daga tsaye sai nake cewa idan abin yazama hakane a dauko ta ta zauna nan tare damu mana inaga zaifi sauki, Ya,shirya zuwa Abuja acan ne ya fa irin ko inkulan da mamake samu agurin matan shi, ga rashin kunya daga Fatima wace ya lura da cewa ko yarta bata bari tazo kusa da mama din don wani manufa nata da bai sani ba, Inda ya gane hakan shine yana zaune a falo da mama sai yarinyar ta sheko zuwa gurin shi amma sai Fatima tai sauri taja yar nata da mamaki yake ce mata saboda may zaki rike taki barta mana tazo, Tana wani kamay kamay zance ne yake cewa cikin fada sake ta nace tazo sai take cewa wai zata shiga da yar ce ta bata magani, Mama tace a,a kyale tada yarta ko zatai kukan jini ne bazata taba barin ta tazo kusa dani ba kada na cinye mata "Ya, Saukin abindai ba ita,kadai bace jikata a gareka ina dasu da yawa kuma,sai yadda nayi da abina, Rayuwan shi yai mugun baci a ranan baicewa Fatimq komai ba ita kuma batai azancin barin yar tazo gurin su ba, Haka ya tunzura mashi rayuwan shi sosai har yake fadawa Lawal wanda yanzu suke Aminai a tsakanin su Lawal ke cewa kyaleta aidai duk abinta jikan Mama za,ace ba jikan wata ba can, zancen yai matukar tsaya mai a rai sosai, Da kwana biyu da zancen mu aka,iso da mama wacce ga tsufa ga ciwo a tare da ita, kuma babu kulawa na musan man, Idan ka ganta sai tabaka tausayi sosai don duk ta zagwanye ta ramay sosai dole na zage a gurin kula da mama din , duk da nima din na tsufa amma,ni din ce na koma kanta Mama sai faman saka muna albarka take dani da mijina da yaran mu da ko yaushe suna a jikin ta a tare suke komai da ita wanda hakan ba karamin dadi Yaya din ke ji ba, Don da wuya ya shiga gurin ta bai samu daya daga cikin yaran a manne da ita ba ko suna barci a,side din ta, Maganin Safe nice, na rana ma nice, da dare ne Ramatu take kama min don na huta ga abinci maigina jiki muna mata akai akai sosai,, Watan haihuwana ya kama naso na koma Abuja na zauna har na haihu amma yaya Abubakar ya hana, Yanzu a tsakani na da mama Ladi babu wani hattara sai haba haba koda yaushe, da albarka, Idan bata ganni ba zata dan tako zuwa falo tana kiran Ramatu tace yau ko dai uwar dakin ki za,a haihu ne, banji duriyar ta ba, a waje, Yaya Abubakar ya tafi weekend Abuja ya samu yar gurin Fatima jikin ta ya tashi suka je asibiti a daren aka basu gado, Abinda ya hana shi samun dawowa kamar yadda ya saba kenan yadan dora wasu kwanaki a kai, Yarinyar a yadda yakw cewa tana,jin jiki kuma likita ya,fada masu cewa yar sickler ce don haka ya dora yarinyar a hanya, Fatima ta dinga masifa wai ita bata gane wa yar taba tu kuma ance mata kila mayu ne suka kamata don haka tana tuhuma yarta ta narike ne a hannu, Ranan yai mata kaca kaca inda yake cewa idan bazata kai yarinyar shan magani ba sai ta bari amma fa alamar yarinya ba lafiya,zaki wani lauye zance saboda bakin canfinki, Muna zaune yanzu lafiya inda yan uwan mu a gida suna a cikin wadda ta gashi duk shekara sai ya samu wanda suka tafi saudiya don sauke farali, Allah ya saukeni lafiya na haifi yara na maza biyu masu masifar kama da junan su, Na haihu da kwana biyu yar gurin Fatima Allah yai mata rasuwa ita kuma, daga can muka,kwaso zuwa Birnin kebbi don nasamu za ai suna a gida wanan karon, Rasuwar yar bai hana yan uwana yin shagalin su ba don sun san cewa Fatima ta camfa gidan mu wai mama manya ce itace ta kama mata diya, Mutuwar yar ya tayar mata da hankali sosai mun sha shagalin mu da yan uwa na munyi rabon gift da sauran abubuwa masu mahinmanci wanda mutane sai sam barka suke muna, Yana tare da Lawal Fatima ta bugo mai wayan cin mutunci tana mai zagin fitan arziki wai dama tasan cewa yar bata damay shi ba tun farko ai ba,sai ya nuna baya kaunar ta ba, Inda take shiga ba nan take fita ba gurin cin mutunci wai tasan cewa itace tai hasara tunda shi yana da wasu yaran da yake gani, Akan haihuwan Meenatu har ya manta da mutuwar yar da kwana biyar ke nan har ya bari akai shagalin suna haka mai yawa babu abinda ya damu kowa sai ita da tai hasara ce tasan ta rasa "Ya, Murmushi yayi batare da ya,bata amsa ba don bai son bata ranshi a lokacin yana tare da mutanen shi na arziki, Har take cewa zata shigo mota ita da yan uwan ta su dawo BK idan an gama sai ta koma, don ba zata zauna tana hadiyan bakin ciki da tskaici ba ita daya a gida sai yarta da tazo mata, Gashi ance mata yana can yana bushashan shi acikin farin ciki kamar baiyi rashi ba, Kashe wayan yayi da abin ya ishe shi saura yana mai hadiye bacin ran zancen ta,, Washegari kawai ta shirya suka kamo hanya ita da yarta a hanya sukayi accident yar nata ta kare a hannu da kafa ita kuma ta kare a hannu wanda yai sana diyar fitan cikin dake a jikin ta,, Asibitin Sokoto akai kai su an bugo wa yaya Waya a lokacin yana tare da wanta Aliyu ake sheda mai abinda ya samay su, Ya mikawa Aliyun waya ya karasa jin bayanin ranshi in yai dubu ya baci daga shi har Aliyu din, Inda yake cewa acikin kunar rai na yi da ita cewa zan shigo ai suna tunda har mun riga da munzo gida amma da anyi suna da kwana,biyu zamu dawo Abujan insha Allahu, Yace a cikin takaici tun zuwana Fatima a waya take tana ci min mutunci wai dama tasan bana son yar ta don haka dole na nuna farin cikin rayuwana a fili, Yace shi babu inda zai tafi sai dai Aliyu ya tafi shi kadai da kyat su Baba suka samu kan shi suka tafi dashi don ganin yanayin da suke ciki, A gaskiya sunji jiki sosai gama ita da abin yazama ma biyu duk ta fita hayacin ta, Dole ganin yanayin ta yasa shi saukowa inda ya,ba da umurnin a mayar da su asibitin Abuja,, Salawatu tayi binshi don ya mayar da ita amma fir yaki sauraren ta har Birnin Kebbi tazo gurin su Baba don a bashi hakkuri, Su Baba sunki sauraren ta sai Baba nane ya saurareta inda ya kira Yaya Abubakar yai mashi magana akan yayi hakkuri ya mayar da Salawatu dakin ta, Amma Yaya Abubakar yaba Baba hakkuri da cewa hakan shine kwanciyan hankalin iyalin shi don haka Baba yayi hakkuri inda ya bata jari kamar yadda taroka tafara business, Sai dai har yanzu hankalinta yana agare shi don takeganin babu namijin da ya kwanta mata arai kamar shi, Sadiya tana yadda take ba wani dadin rai a tare da ita don ita marowaciya ce ko yan uwan ta bata iya taimakawa balle Dangin miji bala,in aure, Hakan yasau daukan karar tsana,suka saka mata kowa sai sukanta yakeyi har suna cewa wai Salawatu tafi ta dama azuciya na ce baku san komai ba ke nan da baku fadi ba,,, Satin mu uku a gida mu ka kwasa sai porthercort da yarana don hutun su ya kare na makaran ta ko,

ZEEE MAKAWA YELWA SEENABU

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣2⃣7⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull