Tarko complete novel - Chapter 137
Tarko complete novel Chapter 137: Tarko complete novel Chapter 137. Watan haihuwana ya kama don haka nake ta saka ido kullun don jiran haihuwa, A wanan…
3,218 words
Watan haihuwana ya kama don haka nake ta saka ido kullun don jiran haihuwa, A wanan lokacin Maigidan baya samun zama kasan nan sosai saboda yanzu ga aiki ga business da yakeyi wanda ya fara dauke mai hankali, Yar gurin Fatima yar da take ji da ita kamar kwai sanyi yasa jikin ta ya tashi sosai, Don haka maigidan ya nufi Abuja babu shiri don duba lafiyan yarinyar, Fatima tayi matukar kidimewa hankalin ta ya tashi da,wanan ciwon na yarinyar Don bata taba irin wanan ciwon ba don likita har ya kai ga ya sa mata dan roban numfashi a hancin ta, A yadda muke jin labarin jikin yarinyar naso na tafi Abuja din don na duba bata, Amma sai Mama Ladi ta hana inda ta shiga yin min fadan cewa ban san ciwon kaina bané da,tsohon ciki zan ce zani tafiya, Nan tashiga zage zagen Fatima da yan uwanta tana kira masu mugunta da mugun abu,, Dakina,na koma,saboda bazan iya,sauraren yadda Mama take cin mutunci ba, don bata sa lokacin daina fadan ba, Ina zaune a dakina ina waya,sai ganin nayi an daga mun labulen daki, a cikim masifa tana cewa baya don na hanaki zuwa gurin wanan mara,mutuncin yarinyar shine yau kike fushi har kin ki fitowa ki dubani ,,, Idan da sabo na,saba da fitinar mama tun ina yar karama balle kuma na yanzu da take a matsayin sarakuwata, Saurin ajen wayan nayi ina cewa cikin dan sakin fuska mama ai na,sauko na,amu kina,barci shine, nadawo nima na kwanta yanzun nan shine farkawana daga barcin ai, Bata samu cewa komai ba sai juyawa da tayi afusace, tana mita a fili akan kowani yaro baka da daman kai mai fada yi fushi da kai, Tana fita nabi bayan ta da kallo ina tabe baki nace a filli Allah ya sauwaka,, Van fito ba har sai da,na gama,komai kamar yadda,na saba na,sauko a,kasa nai sallah magrib da isha,i na, Gaba,dayan mu muna zaune a falon gidan har Baba Wadda wanda,kan zauna kawai don takalan mama Ladi fada, suyi takwasa,muna dariya, Wayan Yaya Abubakar ne ke kirana da sauri na karbi wayan daga hannun yaron dake kokarin miko min, A yadda naji muryan shi yasani saurin faduwan gaba ina daga wayan yake cewa hello Meenatu yarinyar nan dai Allah ya karbi abin shi yanzun nan, Muna asibitin bamu ma fito ba Salati na saka mai karfi tare da saurin cewa Innalillahi wa, innaalaihim rajji,un, Gaba dayan su sai hankalin su ya dawo gareni don jin wa muka rasa may kuma ke faruwa don jin Salatin mutuwar da nayi, Na juya inda mamatake zaune ina cewa Mama Allah ya karbi yarinyar nan yar gurin Fatima, Su Ramatu da su Baba har maimu suka saka salati atare, Nan kowa ya fara fadan albarkacin bakin shi a cikin ji mamen yar suna cewa Allah ke nan ba ai maka dole, Wanan yar da Fatima ke ji da ita tankar kwai yau itace Allah ya karbi abin sa, Yarinyar da ko a hannun wa take zakaji Uwarta tana ce ta dawo daki ko ta ce a gaban mutum idan na kara ganin kinzo gurin wani sai na dake ki, Mama Ladi tace af aiku duk mai saukine Wadda nifa daukar manya wanan Yarinyar take min , Salati muka sa nace haba mama hauka take da zatai maki wanan zargi din idan ke manya ce ai da da mu zaki fara ba jikokin ki ba, Tace duk irin wullakancin da,suke min har ita wacan da ta wuce wace bata shan ko ruwan gidan mu sai dai tazo da ruwan bature a gora, duk kallon su nake yi don in har nai niyar su bar gidan nan dole ne su barshi a lokaci guda,,, Don na kawar da zance nake cewa Allah sarki yarinyar nan ta wahala wallahi, Ga yarinyar da son mutane Ramatu tace wallahi ni yarinyar tana bani tausayi don a koda yaushe zaka ganta a takure, ne,, Ina daga zaune na dan mike ina cewa bari na kira Fatima din naji ta, Wayan ta yana ta ringin amma bata daga ba har ya katse na sake kira again sai gab da wayan zata tsinke ne ta dauki kiran nawa, Kuka take gwanin ban tausayi nace Fatima ashe abinda ya faru ke nan cikin kuka take cewa, Meenatu sai kikagaji Baby ta yi tafiyan ta tabar ni ko , Tausayinta ya kamani nace kiyi hakkuri Fatima kiyi mata addua Allah da ya bamu ita ya karbe ta yafi mu son ta ne, Don haka sai addua Allah ya gafartawa musulmi Allah yai mata Rahaman sa , Ki daina kuka haka please kinga gaki da ciki a jikin ki kada wani abu yazo ya samay ki, Tace na gode Meenatu, nagode kwarai, ki fadawa Alhussaini abokiyar fadan shi ta tafi ta barshi, Wani irin tausayin ta ne ya,shiga zuciyana dama zancen dole nakeyi kawai don nimq yar ta shiga raina sosai wallahi don ita ma yarinyar tana sona don wani lokaci ko barci nake zan farka na ganta kwance a bayana either tana barci ko tana wasa, ita kadai, Dana tashi zata kawo min karan Alhussaini ne idan kuma nakirashi zan mai fada sai tace aa mummy bafa haka nace ba, sai na basu sweet ko biscuits wanda ban rabuwa dashi a dakina don yaran saboda na kanaje ne don koda yaro yana so sai na dauko mai, Ban yarda da dabiar cewa nabawa yaro kudi a hannun shi yaje ya saya abu da kan shi ba don nimw ba haka mahaifana sukai min ba, Dabiar cewa abawa yaro kudi a hannun shi yatafi ya kashe yana daya daga cikin gudun mawar lalacewan matasa a yau, Don sai kiga yaro yanzu komai kankantar sa zai iya kashe naira hamsi ko dari a lokaci guda, Uwaye don Allah mu gyara da kan mu don a lokaci muke yanzu Duk abinda kika san cewa yaron ki yana ra,ayi zaki iya sayen shi idan da hali ki boye a dakin ki idan kuma babu hali idan zaki saya mai kada ki bashi kudin ki aika a sayo mai sai ki bashi, Insha Allahu zaki ga yaro ya taso a cikin natsuwa kumq ba kashin kudi, a tare da shi, Wani sabon bala,i mai lalata al,umma shine idan yaro zai tafi makarata ace wai an bashi kudin kashi, Wa iyazu billahi wallahi wanan kudin kashin da uwaye ko ubane keba yara wani sabon masifane wanda bamu sani ba, Idan da hali yar uwa a cikin hira zaki iya tambaya danki ko yarki irin abubuwan da ake sayarwa a school din kiji may yafi ra,ayi daga ciki , Sai ki saya mashi su yau idan zai tafi bashi billisuwa gobe bashi kankan, jibi bashi balbalo haka dai zaki tayi, insha Allahu zaki taimakawa rayuwan danki daga halaka Don idan kince kudi zaki bawa yaro idan bai sai wanan abin ba sai yasayo wani fitinar a wajen makaranta, Ko kuma idan yan uwa sunga danki mai zuwa da kudi school ne zaiyi sabbin abokanai masu cusa mai wani mugun akida ta daban yaro ya lalace ke uwa baki da labari,,, Allah ya sa mu dace ya shirya muna zurian yasa masu albarka duniya da lahira,,,
****** ********* ****** Muna a cikin jumamen rasuwa yar mu ne da kwana,biyu na tashi da nakuda, Ramatu ce tafara gane irin halin da nake ciki lokacin don haka ta samay ni a daki take cewa anya hajiya bazamu tafi asibiti ba kuwa don ina tsoron haihuwan ki a gida, Cikin dauriya nake ce mata tabari naga irin yadda hali zai yi kafin lokaci, Duk yadda na so na daure hakan baiyi ba don nakudun ya taso min sosai, don haka Ramatu ta fadawa Baba Wadda inda ya fadawa abokin Yaua Abubakar watau Nasir ,, Shine yazo da matar shi muka tafi asibiti inda acan ne suka karbe ni acikin sakin fuska duk da,babu musulmi ko mutun daya a cikin su, Amma sai faran faran suke da mutane zakace a arewa muke zaune, ba kudu ba, Ban cika awa daya a asibitin ba Allh ya saukeni lafiya inda na haifi yarana maza su biyu masu kama sak da mahaifin su, Daga gurin da nake kwance nake tambaya may na haifa su kace min twins brothers, Na mayar da kaina saman pillow da sauri fuska babu annuri, a cikin sa ko kadan, Dayar nurse din take tambaya may yasa bani farin ciki sai nace mata cikin murya ba bu walwala, Nake cewa baby girl nake son haihuwa don mahaifin su yafi son baby girl arayuwan shi, Ni kuma,sai maza nake haihuwa akoda yaushe, ba mata da yawa sai mace daya, da na samu yayin haihuwan yan uku na,, Yaya Abubakar ya na can gurin karban gaisuwan yar shi labarin haihuwana ya samay shi na haifi diya biyu, Yashigo cikin gida da murna ta yadda bai iya boye farin cikin shi a fili, Suna zaune a falo ya samay su yana fada masu zancen haihuwan nawa cikin jin dadin shi, Sadiya tace fuska a daure tau yan biyun aka kara haihuwa kuma ? Lalai abin nayi ne wai susan kafa,da,galma, ashe kafin wani lokaci gidan nan ya cika da diya, har ba masaka tsunke,, a gidan nan, Bai yi mamakin jin haka ba daga Sadiya don yasan irin zafin kishin da takeyi akan Meenatu da yaran ta, Don haka sai yake cewa zai bi jirgin yamma ya koma don ya je yaga yaran da aka haifa, Fatima,wace sai a lokacin ta,samu yin magana sai cewa tayi da ya fi don ita wanan tariga da ta mutu ko, an karta ,,, Ranan hankalin su yai matukar tashi sai kowan su ya shiga sake bakar magana waya,ke tashi koaa yana fadawa dan uwanshi zancen cewa Meenatu takara haifo tagwaye again, An makale shi an hanashi shakat a rayuwa an hana sauran abokan zama hakan ma yan uwan shi, Sadiya ce ke wanan wayan da yar uwan ta, Anty nata ta ce mata Sadiya ki godewa Allah da irin mijin da ya baki, T Yanzu ke inda Abunakar ba wanda yasan ya kamata bane da yanzu fa baki gidan nan, Ki duba kiga irin abubuwan da yafaru amma ya dake yabar komai ga Allah, Ya nuna bai ma saka ki a cikin zancen ba yanzu shine zafin kishi da rudin shedan ke son ingizaki ruwa, Wai har kece mai bakin ciki da karuwan da yasa mu aduniya Anya Sadiya kina ko da tunane a,ratuwan ki ina wanan zancen yafito maki haka, Duk irin abubuwan da bawan Allah nan yake maki amma wai shine zaki bari shedan ya,rude ki, To wallahi ki kama kanki yanzu ke idan da,wata ce duk yaran da ake haifa mashi aike ce mai renon su ki nuna kin mafi uwar da takawo su duniya son kaunar su, Amma kassh wallahi Sadiya nayi mamakin jin haka daga,gare ki kin kuma bani kunya, Idan zaki gyara ki gyara din shine mafitan ki saboda dai kin san cewa sai Allah haihuwan ki a,gidan nan ,, Wanda laifin mahaifitar mune don an ce,tsafi gaskitan mai shi, Duk da jikin ta yai sanyi amma tana jin kyashi da hassada a,rayuwsan ta har lokacin,, Shi sai faman mamaki irin wana zafin ratuwan na mata yakeyi don duk yadda yaso ya daure da halin su yana ji bazai iya ba gaskiya Haka ya kamo hanya har a cikkn jirgi yana tunanen rayuwa ,, Daga cikin su babu wace ta,iya mai Allah ya raya koda na munafunci ne, saboda zafin kishi irin na matan shiyan mu, A cikin dare ya iso gida alokacin mun dawo daga asibiti ina dakina zaune tare da mama Ladi tana dauke da dayan yaron wai tana,shafa,mai Mankade wanda aka hada da Tafarnu, aka,soya guri guda ya daskare, Sai Alaidi pure one wanda take shafawa yaran a hanci da baki, don sanyi kadaya kama su, Ramatu tana daga gefe daya muna kallon mama wace ta hana kowa yiwa yaran komai, Ina kalon ikon Allah duk da banji dadin irin yadda mama ta hana Ramatu sakat da yaran, Da yake ita Ramatu mace ce mai hankali don haka,sai kawai ta,sakawa mama ido duk abinda tace sai tace toh, kawai,,
****** ********** ****** Ya shigo dakin dauke da,sallama a bakin shi idanuwan shi kar a kan dan jaririn dake a kafan mama tana shafa mai, mai a jiki,, Yake cewa cikin dan nuna farin ciki a fuskan shi, mama ashe munyi baki ne a gidan baya na, Tace eh ikon Allah ke nan wata, ta tafi wasu, kuma sun zo, kasan Allah shi kadai kayin wadda yaso,,, Gurin da nake zaune ya fuskanta yana mai min kallon farin ciki Ya, kike hope normal kike dai ko, ba wani matsala, atare da ke by now, Na ce a cikin dan lumshe idanuwa na lafiya kalau muke dagani har yaran, Daga gurin da mama take zaune nadan saci kallon ta,naga yadda ta dan tsuke fuskan ta azuciya na nace kai mama hoo, halin dai yana nan, ashe , Idanuwan shi yana,a,dayan yaron wanda yake barcin shi hankali kwance daga gefe na, Nace ya karin hakkurin mu baby ta tafi ta barmu abinta, shike nan, Abinda yasa shi sauke ajiyan zuciya ke nan yace yarinyar ta wahala da yawa wallahi, yake ko abinci a hanci ake bata, Daga inda nake zaune nace subbahanallahi yar karamar yarinya ke nan take wanan bautan Allah, Allah ya jikianta ya,sa ta huta, ku kuma iyayyenta Allah ya kara maku hakurin rashin ta yace Ameen, Azuciyan shi yace Allah sarki hali ba daya ba ita uwar yar tana can tana bakin ciki da samun naki karauwan ke kuma ki na nan kina danuwa da rashin yar ta har kina mata addua, Mama wace da kyat ta samu tamike daga zaune don kawai taja hankalin shi zuwa waje take cewa yayin da takai kofa dama sai nace ba,,, Bata furta komai ba hakan yasa shi bin bayan ta suka fita, zuwa kasa a tare, Murmushi nayi a fili ina cewa kai mama ho har yanzu dai ana yadda ake ke nan dai ba, a barin hali, Suna fita yana bayan ta take cewa shine baka bari ka kwana ba ka biyo hanya da daren nan, Mai sunan malam ka,rage tafiyan dare dan Allah don yanzu lokaci ya canza, sosai, Yai murmushi yace mama ai bada mota bane jirgine na ke shigowa shi yasa,kika gan ni,ai, Tace ni gwanda da kadawo yau din ma don wa yan nan yan jakar uban, banga amfani tsayawa a gurin su ba, Kamar bai gane may take nufi ba yace mama,su waye kuma dai ? Tace wa yan nan matan naka mana marasa mutunci ai gara da ka,wuto kabar su tunda basu da kirki ko kasan don babu wace ta bugo waya har yanzu daga cikin su,, Bai samu cewa komai ba don shigowan su Baba Wadda gidan inda,sukayi kicibis a falon gidan, Nan suka zauna ana mai jajen rasuwar yar shi da kuma yi mai barka haihuwa duk a lokaci guda, Ramatu ce ke ta faman kai komo akan mu tana kula,dani da yara, don mama bazata iya wanan ba saboda ba lafiya a jikin ta , Sai dare lokacin da ya shiga daki kiran wayan Fatima ya,shigo mai inda yake cewa, a sake Ya dai Fatima na barku lafiya, Sai ji yayi tana cewa wanan cin amana ne ai a filin Allah ko sadakan bakwai din yarinyar nan ba a yi ba zaka juya ka koma don kawai an fada ma cewa matarka ta haihu, Wallahi duk dai abinda mutum yayi dashi da Allah a,rayuwan shi, Da karfi yace Look Fatima kin san ban son irin wanan zancen na gani iyakar mutum, Na fada maki sharadina cewa, ban son irin wanan haukan kishin a gida na, don ba zan iya lamuntar hakan ba, Don haka in har kinga kina da matsala ko zaki je gidane inda za,a baki kulawan da ban baki, Tace ai ba kai zaka gwada min hanyan gida ba babu inda zan tafi da cikin ka ajikina haka, ba,, Rayuwan shi gaskiya ya baci don wanan abin yana sako mai tarin bacin rai a rayuwan shi,
****** ********** ****** Kamar yadda na roki Yaya Abubakar tun kan na haihu cewa yayi hakkuri naje gida muyi bukin sunan mu a cikin yan uwana da abokan arziki da farko yaso ya ki zancen, Amma dana dan kara tausa murya tare da ban baki sai ta hakkura da zancen tafiyan, Don nace mai idan mun tsaya a nan mutane da yawa zasu so zuwa gurin sunan kuma kaga ba,wai muna da wuri waddatace bane da zamu tara bakin mu a ciki, Kuma kaga mutanen garin bawai sun saba bane da irin al,adan mu na hausawa da irin zancen nan har na samu nai convincing din shi ya yarda kwana mu biyar a can muka,garzayo zuwa Birnin Kebbi a sokoto air port muka sauka, Inda Uncle dina yazo ya kwashe mu a gidan shi muka fara sauka, inda naga yadda yai sabon gidan shi mai kyau, Saye nake a cikin wani tsararen jallabiya wanda matan kasan Asian ke sawa, idan mace takai, mace, Tsaraban da aka,sayo muna a tafiyan da yayi zuwa kasashen Arab ta tsakiyane yazo da kayan, Anty Amarya ta ce kai wanan ko ashe Meenatu tace kuwa haka ? Gaskiya ban da abinda zance sai dai nace Allah ya gafartawa Malam Tsoho yakai Rahama ga kabarin sa, A take idanuwa na,suka dan canza kala don jin sunan malam tsoho da ta ambat Anty tace gaskiya babu wanda zaice wai kece ke haihuwan wa yan nan yaran haka duba fa sai kace Anty su ce ke, Nace kai haba Duk yadda muka,so muyi hira ba time don haka muka bari har ta shigo suna BK din, Mun so yin hirar gadamar amaryan sune amma kumw ba time, Dama shine hiran mata idan an hadu ko wace na kokarin fadawa nata labarin abokiyar zaman ta,, Idan baki hadu da abokiyar hiran alheri ba,sai ta kaiki tabaro gurin bada shawaran banza Nidai Alhamdullahi hiran mu da Anty bana boka bane ko malam sai dai yadda zamu burge kan namiji da kissa da kisisinan mu na mata kawai, Mun huta muka kwasa sai Kebbi mun samu yan uwa suna jiran isowar mu, Tun da daren ake shigowa ganin mu naso na zauna a dakin mahaifiyana amma sam su anty safiya suka hana dole na,sauka a part din mu, Ina shiga Salawatu tafado min arai mai fadan gurin zama yau gashi cikin ikon Allah bata gidan, Sam banson zancen ta don kawai irin tozarcin da tai min na kishin hauka zuwa ganin tsiraicin mu, har a gado, Fuskan kowa ya,shigo a kaina don ganin irin yadda gaba daya rayuwa na ya canzs na zama wata irin matar manya, Mama Ladi tace wai sai a gurin mu zata sauka amna su anty Safiya suka hana suka ce ai ba itace ta saba zama dani ba idan na haihu don haka sai dai Mama Sa,a da gwagona Habbi zasu zauna dani sai Dije wace take, wanka a lokacin, Ba karamin daga suka,sha da mama ba amma fir sukaki yarda niko nasan dalilin sin zamata da mu don tagane wa idon ta,duk wani shige da ficen da za,ayi a part din mu, A gajiye muke don haka ranan bamu tsaya wani dogon hira ba sosai nai barci duk wanda ya shigo sai a fada mai ai nayi barci ko,