Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 138

Tarko complete novel - Chapter 138

Tarko complete novel Chapter 138: Tarko complete novel Chapter 138. ****** ********** ****** Washegari su Anty suka,shigo nan zancen shirin suna ya fara…

3,078 words

****** ********** ****** Washegari su Anty suka,shigo nan zancen shirin suna ya fara inda bamu yarda an bar dan ko wani part na gidan mu a baya don haka ba karamin karin hadin kai ya kawo muna ba agidan, Naji dadin hakan da Anty Safiya,sukayi shi yasa nake son Anty Safiya don halin ta daya da dan uwan ta, Shi matsalan Yaya Abubakar kawai don namijine shi inba ka ce mai aiko ya kamata ayi wa wani abu kaza ba bai damuwa da yayi Wanda akasarin maza haka halin su yake sai mace ce mai lurar dasu hanyan alheri saboda su basu da time din da zasu zauna har su san abinda wani yake ciki, hakan sai mu mata, shanu biyu aka tanadawa sunan banda raguna da za,a yankawa yaran, Dama kowa yasan hakan al,adan mutanen Birnin Kebbi ne yanka shanu da,suna koda kuwa yaro daya aka haifa, Don haka a cikin hiran mu na ke bawa Yaya mustapha shawaran cewa idan an yaka shanayen don Allah ya tabbatar da cewa duk part din iyayyen mu maza ya aika da naman arabawa kowa naman shanu guda a gidan guda kuma sai ayi sha,ani buki dashi, Munyi da maigidan cewa bazai samu zuwa gurin sunan ba don haka mukaci gaba da har kokin mu kawai, Sai may adaren suna sai kwai gashi a garin yazo yace wai tafiyan da zai yi an dage taron, Ya iso a cikin darene din haka ba kowane ya samu ganshi ba da daren , Da safe an tashi anradawa yara sunan babana da baba Musa wanda hakan umurni ne daga yannen mu maza, Daga ni har yaya Abubakar din babu wanda ya damu da zancen don may sukai wa yaran suna, Ya Abubakar yashiga gaida mama ladi a dakin tane take tambayan shi cewa an yaka shanun ne ko da ragunan yace wallahi bai sani ba amma a tambayi yaya Mustapha, Shigowan Yaya mustapha mama takara tada zancen amma sai yaya mustapha ke cewa eh an yanka har an fara raba, Tace a hasale akan wani hujja za a raba naman ba akawo mata ba, tagani ko akirata Mustapha yace wanan umurnin daga Meenatu ya fito a cikin fada tace ita Meenatu a bakin may take da har zata bada umurni irin haka, Da sauri Yaya Abubakar wanda da farko hankali shi yana a waya ya dago kan shi, Yace mama aiko Meenatu itace a bakin komai ba itace ta haihu ba, O ashe kaine ka bata wanan umurnin dama yace cikin daure fuska mama idan shanu kike buka zan sa akawo maki shanu guda kiyi yadda ranki ke so, dashi, Amma ban son ki ta da,zancen wanan naman har sauran jamaan gidan su samu labari hakan nama ai bazai hadaki fada da kowa ba, Amma ina sai da mama ta daga harshen ta har mutanen gida suka ji fitinar ta akan naman, Daga baya kuma tace wai sai an kawo mata shanu ta dawo kuma tace wai ya kawo mata kudin yafi sayen shanun kuma don taruwa za,ayi a cinye naman a barta, Yan uwa da abokan arziki sun cika gidan a lokaci guda ga abinci kala kala da akadafa muna, kowa sai sam barka, Na shiga na fita acikin dakakkun laces masu tsadan gaske wanda kowa yagani sai ya kara kallo na, Munyi rabon gift masu tsada wanda mutane ke farim ciki dashi kowa anbawa nashi gift din gwanin ban sha,awa Ya Abubakar yana acikin taro Fatima ta bugo mai waya tana cewa wai dama tasan mutuwar yar ta ba danuwan shi yayi ba don gashi taji ance yana can yana kashe kudi akan haihuwan Meenatu , Bai bata ansa ba,sai murmushi da yai mata kawai yace wanda ya, fada maki bai fada maki duka,ba, Ai kudin nawa na mika mata gaba,daya take busha sha dashi, Kuma,don yarinyar ta rasu ba,zai sa nadawo a kanki na tare ba, Indan kinga ba zaki iya zama ba na fada maki cewa ki dawo gida inda za,a kula dake,, Daga haka ya kashe wayan shi da tsuki batare da ya jira yaji may zata ce ba a karshe, Itako suna kashe wayan tai fushin zuciya duk da rana yayi amna tace,wa yarta da take zaune da ita su tashi su zo kebbi a ranan , Duk yadda yar uwar nata,taso su bar zancen tafiyan amma fir Fatima taki dole suka kama hanya, a hakanan, Sun kusa shiga sokoto da,daren nan sukayi accident a hanya wanda bata masan inda take ba, daga lokacin, Sai a, wayan tane aka,samu last called, din nomban Yaya Abubakar don haka akakirashi a lokacin suna wani unguwa da Aliyu ake sheda mai wai mai wanan wayan tayi accident, Yace a ina,sukace wai a nan gurin tureta Sokoto kuma suna a cikin wani yanayi, Dif ya kashe wayan ya kai wani lokaci bai baiyi magana ba, Sai can yake fadawa Aliyu abinda ya faru d yar uwar shi din, Duk yadda akaso yatafi yace bazai tafi ko ina ba,acikin daren nan, don bai aike taba, Can aka kara bugowa ana sheda mai wai cikin jikin Fatima ya,zube ga kariya da,ta,samu a kafa,daida cinyar ta, Ita kumayaruwar nata har guri biyu duk a,kafan ta subbahanallahi ranan gidan su Fatima duk ya rude da tashin hankali, Aliyu ne kefada masu cewa bama,da sanin Abubakar ta wuto ba , Ga kuma irin abinda ya samay ta a hanya gurin zuwa din , Da daren yan uwanta,suka tafi shikuma sai da safe su baba suka ci karfin shi ya tafi bai wani jima ba ya ba da kudi tace a dawo dasu FMC Birnin Kebbi, Ya,wuce abinshi zuwa portharcort kai tsaye don rayuwan shi duk a bace yake a lokacin,

Dan Allah kuyi hakkuri da wanan da fatan zaku gafarceni gashi nai maku bayani kamar yadda kuka bukaci nai maku din,

ZEEE MAKAWA YELWA SEENABU

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 1⃣2⃣8⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

(JUMMA,AT MUBARAK)

KOMAI YAI FARKO ZAIYO KARSHE INSHA ALLAHU BANDA IKON ALLAH,,,,,,

Fatima tana acikin wani yanayi wanda yakai taga shi wani hali, tasa damuwa sosai a ranta a lokaci guda,, Ranan da akazo da su Birnin Kebbi rana muka tafi dubata ni da,su anty Samira , Muna shiga dakin da take kwance tana ganin mu sai ta kawar da kanta gefe guda, Ta juya harshe a cikin yaren su na zabarma tana fadin kowa yafita batun mu, Mahaifiyar ta wace ke daga gefe zaune a saman tabarma itama ta daure nata fuskan, Ina ganin haka nace wasu anty su fito mu tafi kamar suna a jirace su ma ko minti daya bamu kara ba, a dakin muka fita muna mata Allah ya kara lafiya,, Barin dakin keda wuya anty Samira tace wallahi wanan matar batai min ba sam a rayuwana, Sai Anty Rukaiyya tace ni wallahi sam bani ra,ayinta don halinta bai min ba da ita da waccan da tafita, Anty Safiya wace muke zaune a gaban mota tare take ni tin farko ban ra,ayin wanan kin san junior dina ce a school ai kazamace fa sosai, a da can, Wai yanzu ta samu guri shine har da yiwa mutane wullakancin banza , Ina sauraren su yayin da nake tunkin mota a hankali nace haba Anty kishiyar kaunar ku ce fa shiya kuke kin ta, Haba dai Meenatu ta faye daukan kai sosai wallah kamar diyar wani da wata can, Nace kune baku fahinci Fatima ba, don ita zafin kishi ne da ita sosai, Wanda hakan shike sakata yin wanan irin halaiyar ita aduk lokacin dana haihu sai ta dau zafi da kowa kafin ta sauko, Anty Rukaiyya tace aiko zata mutu da haushi don insha Allahu bazamu hada zuria da su ba , Nace Fatima kishin ta yana iya,saka ta yin komai don ita a duniya bata bukatan ganin Yaya tare da ko wace mace a duniya sai ita kadai, In ma har ta fahinci ranan ya kwana da wata daga cikin matan shi tau babu zaman lafiya a tsakanin ta da shi a ranan Aiko zata mutu wallahi don da matan shi ta ganshi dasu kuma zata bar su, Muna,shiga gida mutanen gidan mu su ka yo kan mu don jin may ya faru da,Fatima, Sai anty Samira tace wallahi duk wace ta tafi gaida Fatima daga gidan nan babu ruwan wanin mu, Kowa ya fara fadin a,a wallah bamu zuwa bamu zuwa, A duk lokacin da na haihu nakan bada tsufin tufafina ga yan uwana da abokan arziki inda nakan bada turaman dana samu ga uwayen mu mata dama yan uwan mamana a gwandu,, Gidan da Yaya Abubakar yake ginawa a Birnin Kebbi ya kusa kai karshe don kadan ya rage ya kammala komai, Mutane basu san ko gidan na waye ba amma ginan yasha magana a bakin jama,a sosai, Satin mu guda nashirya tafiya komawa don zamu tsaya a Abuja mu kwana biyu kafin mu wuce fatakwat din, An tsayar da zancen auren Baba Wadda da Maimu na wanda zuwan Yaya Abubakar ya gabatar da komai na aure da ake bukata, Wanda har an saka lokaci nan da wata hudu masu zuwa insha Allahu, Naiwa mamana zancen ta sama min wata yar aiki don ita maimu yanzu aure zatayi, Amma sai Baba na yace ga gwagona,nan Habbi tunda ba yara gare taba mu tafi da ita don mijin ta yarasu ita kadai ce a gidan ta, Haka mukayi mukazo da gwagona Habbi kaunar mahaifina wace zamu zauna da ita don ita ma ba laifi tana da tsabta gashi bata taba haihuwa ba ita,

****** ********** ****** Sai dare muka isa Abuja don haka Fattu itace mai masaukin mu don mun samu ta dafa muna abinci sosai sai da mukaci muka koshi Mun ziyarci abokan arziki kafin mutafi muka dan huta muka kwasa bayan kwana biyu zuwa Fatakwat din,, Yarana sunyi wayo sai don kowan su yana samun kulawa sosai, Yanzu Yaya baya zama a gida koda yaushe yana fita gurin harkokin aikin shi ga kuma business da yake sosai, Abubuwan shi sai kara ci gaba sukeyi akoda yaushe, Idan natina da abinda Salawatu tai min har gobe nakan ji zafi a zuciya na,sosai, Gashi ita har gobe tana kokarin taga cewa Yaya ya mayar da ita gidan shi, don duk wani hanya da yakamata tabi tana bi,, Tun bayan fitan ta sau daya muka hadu da ita danaje Abuja gaisuwan mahaifiyar maman Antyn saloon da ta rasu, Salawatu tayi mugun tsoratan ganin yadda na koma a lokaci guda, ga iya dressing a cikin shiga irin ta matan manya ,irin rayuwan da ta,dade tana bukatan tagan ta acikin shi, Ita kanta sai da tasan cewa a yanzu ni ba sa,ar ta bace a gurin komai kuma, Tufafin dake jikina kawai ta kalla amai sai da ta raina kanta,, Ga zobbunan gold sun cika min yatsun hannu na wuyana yana,saye da wani diamond kiran Dubai, Kafana saye da wasu takalma masu dan tudu kadan sai yar karamar jakar dake rike a hannuna,, A tare da maigidan mukashigo gaisuwan da yarana na,goye manya ban shigo dasu ba, Tsadan shigana kawai ya isa yasa duk wanda yagan ni yasan ko ni wacece, Salawatu tana gidan gaisuwan amma tana ga in shigowana ta dan fara boyewa a cikin mutane, Ga kamshi duk a inda na zauna zan bar sako a gurin wanda ni ban ma san cewa ina wanan kamshin ba haka, Har lokacin Fatima tana gida tana fama da kafan ta sai dai izuwa yanzu Allah ya ba ta lafiya don tana tafiya zuwa ko ina, Nice da zan fita daga gidan don zan tafi gurin Anty Barister, nake neman ta don muyi sallama tazo tana dan kamay kamay tana cewa hajiya Meenatu har an fito ke nan ? Ko kuwa zaki dawo ne nake cewa gobe zan koma insha Allahu shiyasa zan tafi yanzu kuma jirgin safe zamu bi, Ina ganin bata san cewa da maigidan muke ba,a,waje sukai arba da juna inda yaga tai mashi wani irin mugun tsufa a idanuwan shi, Yana zaune a cikin wata tsadaddiyar motar shi yana jiran fitowana, daga cikin gidan, Ina fitowa yadan dago daga kwanciyar dayayi yana,sauraron kiraa, Ganin mu a,tare yasa shi tsuke fuskan shi tana gaishe shi da kyat ya ita amsa mata gaisuwar ta, Ya bode min mota daga inda yake zaune na zaga dayan hannun nashiga ina ce mata tau sai wani lokaci, Acikin kwantar da murya na nema mata alheri a gurin yaya inda da kyat yabata kyauta dubu dari biyu, Ko shi nice yaba na bata bai yarda ya mika mata a hannun shi ba , Takarba tana min godiya har zan zauna take cewa Meena sai na dakata take ce min nagode kwarai wallahi ki gafarce ni don Allah, Rudin shedan ne ya kaini ga abinda nai maki gashi kuma yanzu kin tai make ni baki kini ba,, Nai murmushi nace haba Salawa ai zaman kishi zamane na amna a tsakan kishiyoyi Duk wace ta cuci wata Allah bazai barta ba don haka ni ban taba daukan kishi a matsayin abokiyar gabata ba, Tace nasan haka dadadewa Meenatu kawai shedan ne yake rudina,a lokacin sai nake ganin ai auren ki da oga bana soyayya bane don haka dake har Sadiya ba wani son ku da yakeyi tunda aure ne na hafi akai maku dashi, Ashe abin ba hakana bane kyakyawan niya da kyawawan halin sjine tubalin dorewan aure mai karko, Murya Yaya Abubakar ne mukaji yana cewa wai ya haka kin san fa muna da inda zamu tafi, Tace min Meenatu ki tafi kada yai fushi ni k8n min komai don sadiya da hadu da ita,a kasuwa kyama ta nuna min a,fili ke ko gashi kin tsaya kin bata lokacin ki gareni nagode kwarai da kulawan ki a kaina, Nashiga mota zuciya ta babu dadi don sai naga kawai mutum yabi wanan duniyan a hankali don ba mutuwa ce kawai karshen mutum ba harda rayuwan komawa baya , Anan muka barta a zaune mutanen dake gurin suna cewa wanan ce dama kishiyar Salawa da ake fadin, Lubbuna tace, wanan ce mana tazauna da yarinya takasa hakkuri tanzu gshi tana gani sun mata kamshi dan goma ba ita,ba wanan daman kuma, Salawatu ta koma vikin jama,a tana daure zuciyar ta don irin yadda take ji a lokacin, Daga karshe ma,da taga zaman bazai mata ba,sai ta kwashi inata inata tabar gidan, gaba,daya, Muna barin gurin Salawatu nake cewa yayana da kayi hakkuri tunda ta saduda kamayar da ita dakin ta hakana pleas,,,, ban ksi karshen please din ba yace da karfi cikin juyowa ya fuskance da cewan , Wa? Ni Allah dai ya,sauwaka min ina zan kai wanan tsohuwar haka a gidana, Nace cikin dariya haba dai yayana a ina ka kaita da farko, Don Allah dai kayi hakkuri tunda har tagane kuskuren ta ai, ji yadda ta koma a lokaci guda dan Allah, Yace look daga yau ban son nakara jin wanan zancen a tsakanin mu idan ba haka ba zan saba maki fiye da tsan maniki, Nace Allah ya baka hakkuri yaya bazan sake ba insha Allahu nima, Mun shiga gurin Anty Barister anan muka,dan bata lokaci muka,dawo zuwa gida a gajiye, Sadiya bata wani damu da harkana ba nima haka tunda na fahinci bata kauna nane kawai a rayuwan ta, Irin shigar da nayi a,washe gari da zamu wuce yasa zuciyarta tukuki, Don komai nawa da gani mafi quality ne nake amfani dashi kyashi ya kara lullubeta a rai ta ce lalai wanan yariyar ta wuce inda nake tsan mani sosai, Ina mata,sallama ta amsa min a yatsine nawuce gaba na barta suna magana da maigidan, Yaya Abubakar yana karasowa a inda nake yake cewa sorry madam na bata maku lokaci ko ya karbi sheriff a ahannun yar aikin Kadi, suka,shiga mota na juya a ginshire inda sadiya take gurin mota nace tau da alheri anty, Don nasan sai kilane zata amsa min sallaman tun farko, Shiko yaya sai dan wasa yake dayaron a gaban mota yana cewa na gaya maki bazan dade ba zan shigo insha Allahu, yanzu ma gaisuwan nan ne yakawo mu bawai nazo bane weekend, Bayan tafiyan mu tashige daki tana kuka takira wayan yarta mutumiyar kirki tana kuka take sheda mata wai ita Ana mata wulakanci da yawa don anga bata haihu ba yanzu ace wai komai na yaran Abubakar shine mai masu, Cikin tsawa yar uwar tace mata amma dai ke baki da hankali wallahi ina ruwanki, Bazaki zauna matsayinki ba ga yar uwar ku nan tana yawon gararanba,da mota a gari tana,wani shiga da kananci wai ita matar mai kudi tafito Abuja, da zama, Idan haka kike so ke ma sai ki balgace auren ki dawo gidan maman mu ki zauna da ita ,ba shike nan ba, Ina ruwanki tunda baiyi watsi da zancen ki ba zaki dauki wahala ki saka a ranki waike kishi, Har da kokarin jefa yaranshi aciki wallahi naraba ki don idan yagane kina kishin diyan shi kin kade wallahi, Nan tauta zuba mata magana har ta gamsu tacewa yar uwar ta tagode zatayi kokari tayaki zuciyar ta irin yadda take jin rashin haihuwan ta a ranta, ****** ********* ****** Iyayyen Fatima sai aike suke mai wai yazo suna son su zauna dashi akan zancen zamanta a Abuja, Don tace idan har bazai koma da ita can fatakwat ba bazata koma ba ita, Yace idan bazata koma ba, taita zama gida shi bazai zo ba tunda baiyi fada da ita ba, Ga rashi mutunci a,waya koda yaushe da take zuba mai wata rana ta hadu da fushin shi ya ke cewa taje ya,sauwaka mata, saki daya again, Hakanlinta yai matukar tashi sosai dajin zancen shi inda ta,dawo bashi hakkuri amma fir yaki yarda, Aliyu yazo har fatakwat akan zance yace bazai mayar da ita ba nan take fada mai irin zaman hakurin da yayi da Fatima a gidan shi, Yace duk abinda yasaya mata da yan uwa sai ta sayar da nata, ga bin bokaye da malamai da ta dorawa wakanta, Ya fada mata cewa bai son wanan halin amma taki daina cin mutunci idan ta tashi har da iyayyenshi take hadawa ta,zage tas, Don haka,ayi hakkuri kawai kowa ya kama gaban shi kuma yace idan ta tashi wani aure yayi alkawarin zai taimaka mata da komai insha Allahu, Haka Aliyu yadawo BK jiki ba kwari ya,shedawa mahaufiyan su yadda sukayi da Abubakar din, Tai fada tai kuka tashiga wani yanayi tace mugun halinki ya kaimu ga hakan, Fatima sai da nace kiyi hakkuri tunda babu abinda kika,rasa a gidan yaron ga amma sai ki ka ki, yanzu ga abinda gari ya,waya muna ai,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull