Tarko complete novel - Chapter 139
Tarko complete novel Chapter 139: Tarko complete novel Chapter 139. Ginan gidan mu an gama komai ansa furnitures ako ina nagidan gaba daya, Da mu kazo…
573 words
Ginan gidan mu an gama komai ansa furnitures ako ina nagidan gaba daya, Da mu kazo bukin Baba Wadda a ciki muka sauka gaba,dayan mu da iyalina da bakina , Sai a lokacin mutane suka san ko gidan waye a garin, Nan gulma ya tashi nidai yanzu Alhamdullahi don ba wani dan uwa da zaice bai samun kulawa daga gare mu, Duk abinda ya faru da,wani zanyi kokari naga naiwa yaya magana ya taimaka mai dashi don haka a,sannu matasan gidan mu sukai ilimi suka,samu aiyuka masu girma a Kebbi, Muna komawa daga bukin auren Baba Wadda Yaya Abubakar ya samu karin girma,agurin aiki inda ya,dawo Abuja a matsayin babban ma,aikatan su gaba daya, Inda kafin mu dawo tasa a kara gyara muna gida a dan canza fasalin gidan kuma again, Ganin zan dawo Abuja da zama yasa Anty Sadiya cewa ita zata koma gidan shi na Birnin Kebbi da zama, Yagane may take nufi don haka sai bai matsa mata ba , Mun dawo da kamar sati uku ta kwashe itama zuwa can gida BK da zama don tana ganin wai haka yafi mata sauki, Don bazata iya ganin yadda karamar yarinya tashigo gida ta,samu ci gaba tako wani fanni ita ta na zaune a hakana, Mama Ladi aka gyara mata tsohon part din mu ta koma ciki da zama inda aka hadewa mama, sa,a part dinsu ita daya, Da sannu ya gyarawa iyayyen part dinsu gidan yakoma mordern one kuma, Na zama wata big mama inda mijina akoda yaushe yana godewa Allah da malam tsoho wanda shine sanadin rayuwan mu a tare, Har zuwa wanan lokacin bani sakaci da addu,oin da malam yabani da kuma irin hakkurin da yakoya min wanda ke kai mutum ga,samun riban zaman duniya,,, a rayuwan bawa, in mace in namiji,,, Yaran mu sunyi wayau amma yaya yaki yarda mu kaisu koda makaratar kwanane balle kasan waje, karatu, A tare muke zuwa kasashen waje da yaran mu kwana biyu mu dawo gida bai yarda yakai yaro ko guda karatu waje ba don tsaro, Idan nai magana yakan yi murmushi yace Meenatu ke nan ni, a ina nai karatuna har Allah yai min wanan matsayin haka, Shi arziki duk inda kake idan Allah yanufe ka dayin shi zakayi shi insha Allahu,, Yan uwan mu suna jin dadina nida miji don al,amarin mu babu kyashi ko hassada a cikin sa, Ina business sosai na abubuwa da dama,wanda nima ban dogara ga abin hannun mijina ba, Muna yawan zuwa gida don dubo mahaifan mu inda idan mun tafi suke jin dadin yadda nakeyi masu, Watarana munzo shine baba musa yake cewa Meenatu inaga ni nafi kowa fatin ciki da wanan TARKON da malam ya dana muna a gida don ni gaskiya Alhamdullahi saboda nasamu yarana sun samu daga mijinki wanda ba komai ya kawo hakan ba sai hakurin ki da kikayi na aure wanda har yakai ga samun nasara akan TANKON da tsoho ya haka muna agida don da babu Wanan TARKON na malam da,duk wanan abin sai dai akaishi wani gida can muna ji muna gani, Dariya nayi tare da lumshe idanuwa nace Allah sarki malam Allah yajikan shi da,Rahamar sa,,,,,,
Karshe,,,,,,,
Don Allah yan uwa makaranta tarko ina fatan duk wace na bawa akan wanan labarin zata yafe min dafatan dakom dake cikin shi zai isa ga,wacce duk Allah yaba ikon karan tawa,
Nagode taku har kullun mai kaunar ku yar uwar ku ta musulunci,
ZAINAB IDRIS MAKAWA,,