Tarko complete novel - Chapter 15
Tarko complete novel Chapter 15: Tarko complete novel Chapter 15. ****** ******** ****** Ba wani issashen lokaci yake da shi ba so,sai saboda tafiyan da ya…
3,336 words
****** ******** ****** Ba wani issashen lokaci yake da shi ba so,sai saboda tafiyan da ya taso mai a gagauce zuwa England, Don, haka ya zo gida, a bazata don yai masu sallama duk yadda yaso ya wuce batare da yazo ba saboda baida issashen time, Amma sai ya ga haka bazai yuyuba ba agare shi dole ne yai squeezing din time din shi ko na kwana gudane, Azaune yake cikin daren da ya iso agaban malam suna dan ganawa, Bayan ya gama fadawa malam din dalilin wanan tafiyan da zaiyi zuwa kasashen ketare, Malam din yai mashi addu,a tare da fatan alheri, Malam ne ya jefo mai tambaya akan cewa ya zancen maidakin shi Sadiya, Abubakar ya dan gyara zaman shi a hankali ya ce a canzata zauna har zuwa lokacin da zan dawo, Ita da wa ke nan zata zauna acan din ? Batare da wani damuwa ba yace wata,ce yar uwar ta zasu zauna tare, "Tau, Inji malam wanda yaji zafin wanan zance na jikan nashi, A ce mutum bai shawara da kowa acikin yan uwan shi, Yanzu duk yawan yan uwan shi amma ace wai sai an fita waje an samo, mai zama da matar shi,, Duk yadda malam yaso a lokacin yai magana irin wacce, za, a fahita abin ya kakara, Sanoda yasan cewa bazasu fahinta ba a yanzu don haka ma ya ja bakin shi yai shiru, kawai, Abubakar zaune a dakin mahaifiyar shi mama Ladi suna bankwana, Sai addu,a da fatan alheri take kwarara ma dan nata, Can kuma ta dan kashe murya tankar akwai wani wanda zai jin may zata ce a wanan lokacin, May ake ciki akan zancen auren da naji ance zaka kara wai ? Shiru Abubakar yai mata a wanan lokacin tare da dan dukar da kanshi a kasa, Tau, saurara kaji koda kai wani aure ka kokarta ka kula, da matar ka sosai, Don ban son ace kayi aure ka wulkanta diyar aminiyata, Saboda ban son mu samu matsala da uwarta akan wanan auren ? A cikin ladabi ya ansa mata da cewa, insha Allah babu abinda zai faru a kan haka, Sosai mama Ladi taji dadin ansan da dan nata ya ba akan diyar aminiyar ta, Zancen auren yar, uwar shi Samira wanda za,ayi baya kasan mama ta kawo a lokacin, Abubakar yace ba kudi kukace na aiko maku dashi wanda zaku sai mata kayan daki dashi ba, Ma kin san fa yanzu babu kudi sosai na riga da na yi duk wani planing akan tafiya na, ko, Cikin dan marairaice murya mama tace amna aikasan dole ne sai mun kai kayan gara irin wanda mutane zasu sheda ko ? Shiru yay tare da sa hannun shi a cikin aljihun shi, Inda ya ciro kudi hannu suna rawa mama ta mika ta karbi kudin daga hannun shi,, Tafiya yake yi alokacin zuwa sashen amaryan mahaifiyar shi wanda kusan a manne su ke da junan, su, said ai yar katangar da akayi a tsakanin su, Tunane yake yi wai may yasa mama tafidamuwa da Safiya fiye dashi, Yadda mama take nuna mai tankar Sadiya ce ta haifa a tsakanin su ba shi ba, Duk irin mugun rayuwan zaman auren da suke yi a tsakanin shi da Sadiya mama bata taba ganin laifin hakan ba sam, Saidai ita gurin ta kawai a gyarawa Sadiya rayuwanta sai kuma zancen ya ba da kudi aiwa gidan su Sadiya abu, A haka yai sallama da duk kusan wanda ya kamata yai sallama da shi a wanan lokacin ya yi saboda safe zai wuce,
Da Baba samaila suka gana akarshe inda yake fadawa Baba samaila kudirin auren shi da yadawo daga England insha Allahu, Inda baba Samaila yai mai alkawarin cewa zai tsaya mai akan zancen auren har komai ya tabbata, Mama Saratu tana jin duk zancen da sukeyi a lokacin, Don haka take mamaki da cewa wanan karon akan mace Abubakar ke niyar saba, wa mahaifan shi, A nan taji muryan maigidan ta inda yake kara nanata wa Abubakar da ya kwanatar da hankalin shi yabawa Yarinya hakkuri, har zuwa dawowan shi Sai a lokacin ne Abubakar ya tuna da cewa ai Baba samaila yana da yara masu dan girma akwai Ibrahim da kuma mace ai, Wanda gaba dayan su baya jin duriyan su acikin zurian gidan nasu,
****** ******** ****** Wata uku ke nan yanzu da suka wuce rabon Meenat da zuwa gida birnin kebbi, Sai,dai a ko da yau,she suna waya da yan uwan ta sosai, Musan man Samira wace ke aiko mata da kudi ta na siyo mata abubuwan bukatu a garin sokoto, Zaune ke da yar wayar ta a hannugama wayar ta ke nan da Abdullhameed, Wanda zuwa yanzu sun rage irin hurda da su keyi a da dashi, Wanda ita sam hakan bawai ya damay ta bane don tasan cewa yanzu take don abune mawuyaci tafi batare da ta dawo da sabon yyi ba, Duk da TV dake a dakin su yana aiki kamar y tsage mutanen ciki su fito, Hakan bai sa Meeenatu daga kai ta kalli TV ba ita hankalin ta, na ga wayan ta , Text take karantawa wanda duk kusan yan kwanakin nan mai text din na yawqn damunta da turowa, A hankali har ta iso inda meenat din take zaune daidai inda take a zaunen, Takai hannun ta, a hankali ta dafa ma ta kafadar ta, Hakan yai sanadiyar dawo da ita acikin hankalin ta Tadago kai suka hada ido da uwar dakin nata watau Anty amarya, Ajiyan zuciya Meenat ta sauke tare da dan yin yake a fuskanta, Da ganin dariyan bai kai ciki ba tadai yi shi ne kawai, Gefen ta amarya ta samu ta zauna tana cewa Meenat auren yan uwanki ya matso banga kina wani shiri ba akai, Ido meenat ta lumshe kadan sanan tace anty ina ga fa sai kila ne ma in samu zuwa don ina da test awanan lokacin, A ,a ke ko meena za ai buki a gidan ku kuce bazaki samu zuwa ba nan da birnin kebbi, Anty Amarya ta dubi meena da kyau tace sai dai in akwai abinda zai hana ki zuwa Fuska meena ta bata tace Anty kin san fa yar wajen mama Ladi ce fa da diyar baba shaibu, Ni wallahi Anty ban son tozartawa sam wallahi saboda hakane kawai ban sa zan tafi ba, Murmushi Anty tayi tace zaki tafi mana don in baki tafi ba basu ji dadiba musam man samira din, Ai badon ita mama ladi zaki tafi ba ko ? Ido ta tsurawa wa meenat din inda yarinyar ta ba ta tausayi sosai, Yarinya kamar meena ace bata da kwanciyan hankali saboda kawai hassada Hannu ta sa ta dauko ledar dake gefen ta kayane tafara ciro daga ciki Kayane har kala uku Anty ta a mata wai tasha buki da su, Baki bude Meena ke kallon uwar dakin nata wace a ko da yaushe tana ko karin ganin farin cikin ta, Sabanin mummy wace ji takeyi tankar ta shake meena din yanzu Wai ta yiwa dan uwan ta sheri, don ta bata mashi suna,
ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 ²³ and ²⁴
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH-AL-BAARI
Gaisuwa gare ku da fatan alheri masoyya wanan novel TARKO,,, Allah ya sada mu da rahamomin sa na wana ranan,
Ga irin al,adun buki na garin birnin kebbi, a, da sati biyu ne, amma i, zuwa yanzu an rage zuwa sati ko kwana hudu, A cikin wa "yan nan kwanakin ne ake gudanar da abubuwa da dama, Musali zuwa gyaran dakin amarya kafin a sakata a lalai, Daukan darasin amarya ga malamar da zata koyar da ita, zamantakewa aure, mutane daban daban zasu dingawa amarya huduba kala kala, Tun buki da sauran sati biyu za,a fara gyara amarya da kayan hadi na gargajiya masu kyau da ma,ana, Hakan ya kasance a gidan malam tsoho wanan satin, Don jikokin shi biyu da akasa a lalai a lokacin wanda duk dangi na kusa da na nisa sun iso wanan gidan, Sai hidima kawai ke ta kankama akowani sashe na gida, Sashen Baba Samaila ba wasu bakine sosai suka zo ba, Don bukin ba na yan dakin su bane sanan ba wai wani zaman lafiya bane a tsakani balle yan uwan su na sashen mahaifiyar su su zo masu kara, Wana sai in Allah ya gwada muna auren yar lelen baba watau Meenatun sa,
Duk wanan abin dake gudana hankalin Anty Samira yana gurin yar uwar ta Meenat, Shakuwan Samira da Meenat ya samo asaline ga tashin da Meenat tafara yi a gurin Baba Buhari, Watau a hannun mama Ladi wacce ta yayye ta daga nono, Sai dai daga baya da matsi yai matsine Baba samaila yashafawa idon shi toka ya karbe diyan shi wacce aka mayar tankar boya, Mutane da yawa sukan ce wa meenat yar dakin Samira don samira bata yarda aiwa meenat wani abu, idan ta na gurin, Haka ke sa mama kara jin haushin yarta Samira akan yadda take nunawa meenat zumunta mai karfi a tsakanin su, Samira wace, itace ta saka meenat a cikin manyan yan matan gidan da karfi da yaji badon ta isa ba, Kuma babu yadda zasu yi dole suka kyale Meenat ta bi su don masifan Samira,
Masu zuwa gyara dakin amare yau suka tafi don su gyaro mata inda duk da samira ce babba itace ya kamata a fara gyarowa Amma sai mama tai tsaye tace sam sai andawo gurin gyarawa Murja nata tukun, Hikimar mama da yin hakan shine, wai kada a fara jerawa Samira kaya suga wani abu suce suma zasu sayawa yar su, Don haka mutane sun san masifa take so dole aka nufi gidan murja dake bayan Owando aka fara gyarawa, Sosai ba laifi gidan murja yayi kyau don mijin yayi kokari, Yaro ne matashi yana aikin gwaunati a gidan taki, Andawo cikin murna da sambarka tun a kofa mama ta kasa hakkuri sai tambaya takeyi ya aka ga gidan na murja, Yar guda ce Safiya ta ja ta zuwa gefe tana cewa ha dai Innar mu shin mi ki ka yi haka wai ? Da Samira,da murja ai duk guda na ko? Ansa mama Ladi ta bata da cewa a gurin ku suke guda ko? Nikan a guri na ai diyan kishiyoyi na, na, To Allah shi kyauta innar mu, Amma don Allah ki ko karta ki boye kishin ki a kai, Diyar ta guda mai suna habiba itace tazo gurin da suke tsaye tana cewa, Innar mu ke ji dai ko kwatan Samira murja bata kama ba ko, Ai da sunga an fara fitar da kayan Samira nasan du girgiza zasuyi, Habiba had ke ya,? Shi ita Murja wai ba yar uwar ki ta ba ? Ko yar uwata ta hwa,? Sai inki nawwa in kama ta ? To Allah shi kyauta inji safiya, wacce ta kula da cewa baza su daina abinda su keyi ba,
Jeran samira abinyaba wa mutane mamaki sosai don an nuna mata gats an, nunawa mutane cewa ita yar dangi ce,,, Don kamai da akewa amare masu gata anmata agidan ta, Sai,dai matsala guda shine, Murja tafita samun miji na kwarai sosai kuma tafita samun gidan aure, Gara na gani na fada aka kai masu wanda malam tsohone da kan shi ya hada masu wanan garan , Sai,dai ita mama ladi wacce ta kara akan wanda malam din yai masu,
Zaune take tana gyara yan yatsun kafan ta wanda suka sha zane, Da kwalliya, anty amarya ce takira mai mata zane har gida tazo ta zana masu ita yar ta da zasu,yi wa meena rakiya gurin buki, Kitso da kumshi yar asali akai masu zanen dashi, Wayan ta Nokia da ke gefe yai kara, da sauri takai hannun ta ta dauka ANTYNA SAMIRA, Shine baro baro ga screen din wayan ke boring, Murmushi meenat ta sa,ke tana cewa sai Anty na Da Assalamu Alaikum kamar kullun ta daga wayan tana mai yi wa antyn ta dariya, Amma Meena walleh ke ban mamaki ace har anfara program baki taho ba, Gashi nasan cewa Anty amarya zata ba da sakon da ta ce ki kawo min, Ba hakana na ba Anty Samira, Tsayawa nayi in rubuta test yau gobe tun da safe in sha Allahu zamu tahowa, Ke da suwa na zaku taho ? Ni daina kataho mana, mtss taja tsaki aza nayi da Anty amarya zaki tahowa, To ai ke san mama bata gaiyyace su na ba, da sun taho ko da yini na, To goben sakko zakiyyi ko ? Awo, insha Allahu koda sha biyu kayi muna cikinkin garin birnin kebbi to da ke kyauta gaskiya, Don dai kesan kuna na hannun damana ga wagga harkan, Kai anty Samira, ga manyan yan mata mi akai da yan kananun yara iri na, To ke dai ji na hwada maki sai ke taho ke nan, To Anty samira agaida gida,,, Ajiyan zuciya Meena tayi gami da lumshe idon ta, Allah sarki Anty Samira yanzu zata bar gidan mu ke nan ta fada acikin sabon rayuwa, Ita ma , watarana irin haka zaizo kanta ranan da zata bar gida tabar baba da maman ta da yan uwan ta zuwa gidan auren ta, Ajiyan zuciyar tayi don tasan cewa akwai aiki ga irin haka don ba karamin tashin hankali bane , Aure sha kan yaro inji manya, masu karin magana, A lokacin ne anty ta zo da leda ga hannun ta tace munyi waya da samira wai in baki sako ki kai masu shine na hado har da ita dayan amaryan tunda duk yan uwanki ne, Godiya Meenat tai mata, a cikin mutun tawa,
Karfe sha daya da rabi suna Ambursa, kafin, sha biyu cif sun shigo gida, Tun a kofan su meenat ta gane cewa buki ake sha a gidan su, Saboda bakin fuskokin yara da manya da bata sani ba da ya cika katon iccen dake kofan gidan nasu, Acan kuma dan nisa da gidan su gidan makwabtan su kidan D,J ne ke tashi yara da yan mata suna ta kwasan rawa, Murmushi Meenat tayi don tasan cewa malam tsoho ke nan ya hana a kunna masa kida a kofan gida,,, Saboda diyan Anty amarya Meenat tazo shi yasa uncle ya bada motar shi wani dattijo driver makwabcin su yakawo mashi su, har birnin, kebbi, Idan kuma sun gama buki sai ya dawo ya kwashe su komawa gida, Cikin wani yadin Swiss material blue colour take, dinkin dogon riga mai dogon hannu, shara,shara, Sai farin gyale dan karami, wanda tai rolling din kan,ta da shi,, takalmin masu dan tu,du,, ta saka a kafan ta,, Kayan jikin na ta sun matukar karban jikin ta sosai sai dan farin glass da ta, saka a idon ta don kare, kurar hanya, a idon ta, Yaran cikin gidan su ta samu,su kwashe mata kayan su, zuwa cikin gida, Gurin da rufar malam tsoho yake a ciki,ta nufa tana rike da hannun yan kan,nen ta da suka nace sai sun biyo Anty zuwa buki gida, birnin kebbi, Ita kuma anty amarya saboda ta mayar wa Meenat da mahaifiyar ta da irin ko,karin da suke masu wajen zumunci ta yarda aka tafi da yaran ta, Da sallamar ta da murmushi manne a fuskan ta ta karasa zuwa gurin da yake zaune, da littafi mai rubutun warash, a hannun shi yana dubawa, "A hho, malam ; Har ya ce in,gwaiyya kan shi a duke azaton shi daga cikin yan jikokin shi dake agari ne masu shige da fice, suke gaishe shi, Sai kuma yaji muryan kamar na wacce ya dade da sani a da can, Da,sauri ya dago kai daga kallon littafin da ya ke yi na, Risala,,,, Ameenatu shin ? "Ke ta atta tahe yanzun ? Awo malam nita a,daidai lokacin da suke cire takalman kafar su don karasawa gurin malam din, Har kasa gwiwa bibiyu suka rusun na ita da yaran da ta zo da su yusura da didi, Gaisuwa sosai sukayi da tsohon kakan nata inda ya ke tambayan ta mutanen sokoto,, Yaran da take tare da su ya kallla yara masu kyau da su bulbul dasu gwanin ban sha,awa,, Nan yake tambayar ta diyan gurin kawun ta ne wa yan nan yaran ko,? Meenat taba shi ansa da fadin en malam duk kan su diyan amaryan shi ne da take gurin ta,, Ya jinjina kai irin na manya tare da kara masu sannu da hanya, Daga haka ta mike ta na rike da hannun yaran har zuwa sashin su inda takeyi tana gaisawa da duk wanda ta hadu da shi wanda ta sani,,, Mama Saratu tai murna kwarai da zuwan diyan yan uwan ta gurin ta, Alokaci guda aka fara gwada wa yara gata da kauna,
Meenat bayan ta huta tamike tsaye tana cewa mahaifiyar zata ta gaida mutanen gida sai taga su anty samira, Jinan Inkyau, sunan da take kiran meenat da shi ke nan, Kiyi nisa da maman ku Ladi don bata jin kunyar tozarta ki cikin mutane, Balle ma mama ai nasan sai tayi babu mutane ma tai mun balle yau ga jama,a,,, To ki dai bi sannu ban son abin magana sam a rayuwana, To mama insha Allah
Kusan duk sashen da ta leka suna gaisawa cikin mutunci dakuma yi mata sannu da hanya, A kofan shiga sashen mama Ladi suka hadu da Samira wace ke shirin fita daga lungun nasu, Ihu samira ta sa don murnan ganin Meenatu alokacin Ihun da ya jawo hankalin mutanen dake daga cikin sashen mama Ladi, Mama ladi wace take zaune tare da yaran ta suna kokarin hada kudin sayen robobin rabawa mutane, masu zuwa walima yau, Gaba daya hankalin su ya koma gurin su Samira da meenatu da suka makale junan, su don murna, Wacce tta ayar can ? Inji habiba antyn Samira sai Safiya ta ba da ansa da cewa killa kawar ta ,ta taho ko ? Caraf mama tace wacce kawar ta Amenatu ta fa diyar baban ku Samaila, Gaba dayan su lokaci guda suke cewa, Amina shim? Yanzu Amina ta, ta,koma haka ? Mama Ladi tace, badole ba tunda iyayyenta sun sake ma duniya ita, Wai wata yar bariki karikon ta matar kanin uwar ta, Daidai lokacin da Meenat ta karaso zuwa gurin da suke zaune , Har kasa Meenat takai tana gaida su a cikin ladabi, Sai cewa suke yi Shin Meenatu, ke ta haka ? Yaushe rabon da mugan ki a idon mu , Dariya kawai meenatu tayi gami da mikewa tsaye a lokaci guda,
Rungomota Samira takara yi tana cewa gaskiya kamata yayi in fushi da rashin zuwan ki da wuri haka? Anty Samira na fada maki test nayi jiya shi ya hanani zuwa da wuri, ok, haka ne kin kuru, Bakomai tun da gashi kin zo yau din kinga ai ayi wasu events da ke,, Ok Meenat barin je in fara shiri kin san yau zamuyi kauyawa day, A gurin program din ne take jin cewa wai za,a hada Aisha ko,yar wurin baba shaibu aure da Yaya Abubakar idan yadawo,daga England wurin karo ilimi, Meenat azuciyar ta tace aiko da mai shi ta shiga uku,,,,, ****** ******** ****** Anty Sadiya wace mijin ta ya bari Abuja zaune ya wuce zuwa England, Daga can ya kara turo mata da kudi ta hannun Salawatu, Wanda zata tafi birnin kebbi don halartar bukin kaunar shi Samira da sauran sisters din shi, Inda ya bata sakon wasu kudi don ta karawa mama,Ladi idan taje, gurin bukin don buki akwai cin kudi sosai tun dai irin bukin mutanen su na hausa, Wanda za,a kashe zarahi kamar ba gobe kuma ? Isowar Sadiya garin nasu gidan mahaifiyar ta Hajja ta nufa direct, Duk sha,anin da akeyi bata leka ba sai yau da za,a yi sisters day, Ko shi bata so zuwa ba saida yan uwanta suka dinga mata korafi da cewa halin nan nata baida kyau ace mutum yazo buki a gidan mijin shi amma bai taka ba ko sau guda, Wanan ne dalilin halarta da tayi yau a tare da yan uwan ta su biyar, Jama,a sai wani kallon ta sukeyi, don ba wani canji a tare da ita,