Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 16

Tarko complete novel - Chapter 16

Tarko complete novel Chapter 16: Tarko complete novel Chapter 16. Ankon din pink lace akayi da blue din goggoro , Baba Samaila shine ya sayawa Meenatu kuma…

3,019 words

Ankon din pink lace akayi da blue din goggoro , Baba Samaila shine ya sayawa Meenatu kuma yabawa wata matar wani abokin shi soja ta dinka mata, Kowa kagani aranan cikin pink lace da gwaggoro blue,, Amarene kawai aka banban ta su da sauran mutane inda suka sa Fararen lace masu kyau da daukan ido, Meenat wace ta gyara jikin ta tsab tafito kamar wata tauraruwa, Don ba karamin kyau shigar yaiwa meenat ba don duk wanda ya ganta dole ya yaba da shigar ta ga kyau ga diri, da zati,,, Mutane sai zolayar ta sukeyi da tafito suna cewa wanan kyau haka meenatu sai kace kece amaryan, Murmushi kawai meenatu take masu duk wanda yace mata kai kin yi kyau sai tace nagode kawai,, Tun daga nesa ta hango matar yayan su Abubakar zaune tare da yan uwan ta, Yar su habiba tana tsaye tana magana da su, a lokacin, Gaba daya suka waigo suna kallon meenat din wace alamar hakan na nuna cewa ana yin zancen mutum a gurin, Gurin su ta nufa kai tsaye inda ta gaishe su cikin girmamawa, Ga mamakin Meenat sai taga Sadiya ta nuna tankar bata san ta ba, Hakan bai wani bata mamaki ba don sanin halin ko inkula da mutane irin na Sadiyan, Tana rike da hannun yan kannen ta suka kara gaba abin su, Anyi ta rawa da cashewa amma sam meenatu ta ki yarda tai rawa ko sau guda acewar ta su jikokin malam ne, yin rawa gare su zubar da darajan gidan su ne,

Washegari wankin amare don haka ranan buki ne sosai, Kamar yadda kowa yasan yadda al,adan bukin birnin kebbi yake ranan jumma,a ake wanke amare, Asabar ayi wanka, to shi wanan yasha bambam don malam tsoho yayi tsaye yace sai dai ayi wanka Alhamis, saboda shi jumma,a zai daura auren yayan shi, Inda yace mutane ne basu gane ba da,suke daurawa yaran su aure ranan asabar sabanin da da akafiyi ranan jumma,a, Inda yake cewa ta ya ya zakuji cewa an hana yin abubuwa a wanan ranan asabar din sai kuma hankalin ku ya gushe shedan ya rude ku, ku koma daura auren diyan ku a sabar din, Asabar fa wata rana ce da hatta wanki da yankan akai fa da kitso ko gyaran kai a hanemu dayi a wanan ranan don gujewa masifofi, Amma wai shine a yanzu jama,ar mu suka mayar wai ranan daurawa diyan su aure, Don haka shi yace jumma,a ce za daurawa su Samira da murja aure, Dole aka maida wankin amarya ranan Alhamis, a can G,R,A za ayi wankin amaren kamar yadda aka saba, Buki yakai buki inda jamaa yan uwa da abokan arziki aka hadu aka gwadawa wa yan nan ma,aurata gata duk kowani fannin both angwaye da amare, Meenat wace Allah ka,dai yasan yawan masoyan da ta samu a wanan shagalin Cikin ma tana boyewa bata faye fita fili ba sai can ba,a rasa ba,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 2⃣4⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAHA-AL-MUSAWWIR

Bayan an sauko daga sallah jumma,a ne, din,bin al umman Annabi suka taru a kofar gidan malam manya don sheda daurin auren jiko kin shi,,, Mutane da kauyu kan garin birnin kebbi, dama cikin garin sun shigo saboda sanayyan dake tsakanin su da wanan tsoho An taru inda tsohon malami, ya bukaci manya diyan shi da su wakilce shi, ga daura auren, Abin mamaki sai ga Malam din ya,bukaci Baba hamza da Baba shaibu da su matso gaba yace su yake son su fara karban auren, A take gurin yai tsit, ana sauraron tsohon dattijon irin yadda ga Baba Buhari a zaune amma ya gabatar da yan kan,nin shi a gaba, Anan ya umurci Baba Shaibu da ya amshi waliyancin dan shi Abubakar shi kuma Baba Hamza ya karbi na diyar shi Aminatu, A take jama,an gurin suka fara kalon kalo suna mamaki kowa da irin abin da ya ke fada agurin, A bokan Abubakar da suka zo daurin auren kan,nen abokin nasu, ta sanadin shi, sai mamaki suke yi a lokacin, Ba baki ba har yan gida sun shiga cikin rudani, saboda sam basu zaci cewa,, Ameenatu malam tsoho zai ce zai aurawa Abubakar ba, Saboda ai ba daki guda mahaifan su suke ba ,ga su , su da suke daki daya da mahaifin shi, ai, "ya,"yan su ne ya kamata a hada dashi, din, ba sai anyi wani dogon shako ba, har zuwa sashen Baba Samaila, Dole badon sun so ba aka daura wanan auren mutane na ta mamaki, Baba Samaila wanda yai mutuwan zaune saboda duk ilahirin jikin shi zufa ke fita, don tashin hankali, Shiko Baba Buhari sai cewa yayi Alhamdulillahi, Allah mungode maka da kabar muna,wanan tsohon namu maitarin alheri, Daga haka kuma akasa baba Samaila ya bada auren Samira, inda Baba Buhari tabada auren Murja, Wanan abin yai wa din,bin jama,a sha,awa irin yadda tsohon yai hikimar hadin kai a cikin zuri,ar shi, Sadakin kowace diya mace dubu sittin ne don haka kowace a ka mikawa waliyin ta, Daga haka masu sanarwa suka fara shedawa al,umman dake daga nesa, Maroka mata sukayo cikin gida suna guda da shewa yau Allah yayi an,daura auren Magajin malam Abubakar da Aminatu Samira da Aliyu, Murja da Dauda, jama,a sun sheda yau kun zama amaren angwayen ku,,,,,,,,

****** ******** ****** Meenatu da gwago Habiba wace suke cewa gwago Habi, ita kadai ce kauna ga mahaifin meenat din, Hira sukeyi akan yadda mamata hana aba gwago Habi abinci tun zuwan ta gurin bukin, Mama Saratu mahaifiyar Meenat tace gare ku wanan abin yake bako ko? Naga hakan ai kadan ke nan daga cikin halin mama Ladi, Baku ganin ko mariya diyar ta da yake bata da komai kuma a kauye take zaune ai kun ga bata hurdan komai da ita, Gwago Habi tace ai tayi abin ta wata rana sai labari don Allah bai manta da kowa ba, Muryan maroka matan da sukaji ya kaule gida shine ya dakata da su daga hiran da sukeyi, Kamar amafarki wata mai murya rarara, ta sake cewa yau Aminatu ta zama matar Abubakar inji Allah Samira matar Aliyu Murja matar Dauda, Gwago Habi tace ji mashiririciyar can abin da take cewa bata ko san sunayen amaren ba,,, Again wata mai babban murya daga cikin marokan ta,kara maimaita abinda ta farkon tafadi, Wanan marokiyar bata kara fadin zancen su samira ba sai ganin Meena Gwago Habi tayi ta mike zubur, Itama din mikewa tayi don mamakin abinda sukeji a na fadi daga wajen marokan, Guda mai karfi wata daga cikin dangin malam, tsoho da ta zo daga kauye ta rangada, zuwa sashen Baba Samaila din, Abin da ya kara tayar masu da hankali kenan gaba daya, Isowar matar tana wanan guda tare da,wasu daga cikin dangi yasa,Meenat cewa Ya Abubakar shin ? Sai ganin ta kawai gwago Habiba tayi tai kasa, a somay, Kururuwa jama,a suka sa wanda ya jawo hankalin sauran al,umman gidan, Ruwa aka zubawa,meenat din masu sanyi wanda yasa ta farfado cikin dan bude idon ta ahankali, Sai ganin jama,a tayi still, a kanta dafifi, abinda marokiyar nan da gudar matan nan ya fado mata a rai, Hakan ya kara,sata sumay wa again, a take duk gidan ya rude, Wanan karon duk jikin meenat a jike yake, da ruwa Amma shiru bata farko ba don haka aka fadawa maza a waje, Ba bata lokaci mahaifin ta ya sukkuce ta zuwa motar shi, Asibitin Sir Yahaiya ya nufa da ita, inda aka bata tai makon gagawa, Bude idon ta sukai arba da mahaifin ta wanda fuskan shi kawai zaka kalla kasan yana cikin mumunar ashin hankali a lokacin shi ma, Sannu Amenatu Baki ta bude da zumar zatai magana amma sai ta kasa saboda kukan da yazo mata, Muryan gwago Habi ce taji a lokacin wadda batasan tana gurin ba alokacin sai yanzu, Gwago Habiba tana cewa haba Amenatu kibi abin a sannu mana wanan irin tashin hankali haka, ? Mikewa take kokarin yi daga kwancen da take tana cewa Gwago Habi kiwa Allah ku cece ni ku ceci rayuwa na ban iya zama da mutum irin yaya Abubakar, Gwago Habi ce ke cewa Baba ya akayi haka ya faru ne yaya,? Bai kai ga bata ansa ba wayar shi tai kara, yana dauka yaji muryan Ibrahim yana cewa baba don Allah duk inda kake ka dawo gida ga mama Ladi nan tana tawa maman mu masifa da kidan zari a cikin gida, Da sauri Baba ya juya yana fadin ina zuwa habi ki kula da Amenatu kafin in dawo,

****** ******** ****** Tun a wajen gida yake jiwo muryan mama Ladi yadda ta ke budan baki, Wallahi wanan zancen baiko yuyuwa wanan ma ai karya ne, Duk muna funci da kilibibin da kuka kulla a gidan nan, Kan ku zai kare may ake da irin fulanin gwandu irin tsiya, Wallahi wanan sherin sai kusan yadda zakuyi da yar ku, Badai in hada zuri,a da irin ku ba wanan ma karya ne, Ke Ladi tajiyo muryan baba Samaila daga bayan ta yana kiran sunan ta, Wallahi ki kama kan ki ki iya bakin ki, Abinda kika sani ne in badon magabata ba bu abin da zai sa in hada wani alaka dake, Baki masan may kikeyi ba da baki zagi mutanen gwandu ba, Don ko mutanen gwandu sun gama maki komai a rayuwa, Sanan ki sani duk na karajin kin yi wani mumunan furci akan wanan abin yanzu zan gwada maki cewa karyan hauka ki ke yi, Nan mama lafi ta juya da fadin mahaukaci kawai wanda Alluran soja tai ma yawa a jiki, Nadai fada maku kusan yadda zakuyi da yar ku don ni dana yafi karfin lalataciyar yar ku,,, Juyawa tayi zuwa sashen ta a cikin masifa da jidali a bakin ta da zuciyar ta, Mama saratu tayi kuka sosai ta shiga cikin tashin hankali, Tana rike da hannun yaran da Meenat tazo da su daga sokoto, Su ma yaran ganin halin da antyn su ta shiga yasa su yin kuka da ihu,

Duk wanan abin da akeyi malam tsoho ya sane da komai amma kala bai ce ba, Don dama abinda yake son ya shawo kan shi ke nan agidan tun yana da rai, Baba Buhari wanda ke zaune, kusa da malam wanda aka hana shi shiga cikin gida don gudun masifan mama ladi Saboda shigan shi cikin gidan babban fitina ne tsakanin shi da matar nashi, Haka yasa malam tsoho ya hanashi motsawa ko nan da can, Daga gadon da meenatu ta ke kwance ba abin da takeyi sai hawaye da kiran sunan Allah, Baba yadawo nan meenatu tadage a kan don Allah amaida ita gida, bata jin ciwon komai ita, Ba mussu aka sallamay ta zuwa gida inda tun a hanya Baba Samaila yake fadawa, gwago habi yadda suka kwashe da mama ladi a gida, dazun bayan zuwan su asibiti, Maganar manya ce ita meenatu sai ajiyan zuciya kawai takeyi don abin ma izuwa yanzu ya wuce tunanen, ta, Tankar a mafarki ta ke ganin zancen wai ita meenatu ce yau wai mata a gurin yayan su miskili Abubakar dan mama Ladi masifaffa da ko mazan gidan su iyayyen su tsoron fitinar ta suke yi Saboda bata da kunya a cikin al,amarin ta sam, don haka ne ma kowa ke mata daukar mara mutunci, ko mara hankali,,, Daidai lokacin da take ajiyar ziciya yaji muryan mahaifin ta yana cewa , Duk iskanci ne da hankalin ta guri ta samu takewa mutane wanan iskan cin Yau ai badon ta gudu ba da taga karyan haukar da take kira min, Gwagwa Habbi ta ce kafita batun ta kawai yaya don babu yadda zata yi da mu acikin hidan mu, Bari kiji habbi, duk Ladi ta taba min diya wallahi sai ta gane kuren ta,

Duk wanda ke a kofan gidan a lokacin da aka dawo da meenat daga asibiti sai tabaka tausayi, Gwago Habbi tace kija mayafin ki zuwa kai don yanzu kina da nauyin akanki hakkin aure ya rataya a wuyan ki, Ita da kanta tasa hannun tana gyarawa meenat gyalen da ta dan yafa ajinkin ta, Wasu irin hawaye masu zafi suka fito daga idon ta, Yau don takaicin tsohon kakan ta ko kallon gefen da yake zama batayi ba haka tashige cikki rungumay a jikin gwagon ta. A sauran sassa gidan kuma wasu harda habaici suke sakewa wai ai dama mutum kurum kurum mugune, Yawan shirun mama saratu na mugun tane don itace tabi dare tabi rana gurin shige da fice irin nasu na fulani har tasa aka aurawa Abubakar yar su, Wasu kuma suce ai baba Samaila ma tsohon mugu ne don shiga dajin da yakeyi ba na banza bane, Ai mama kawai nata ya samay ta tunda ta hada irin mu acikin jikin ta yanzu, Wanan zancen nasu ya kara haukata mama Ladi sai,kawai ta figi mayafin ta sai wurin malam tsoho da kukan ta Tana cewa ita don Allah malam ya walware wanan hadin da yayi ya bawa Abubakar ko wacece amma dai Meenatu ba wace har gaba da secondary iyayyen ta suka tura ta har sokoto, Sai a wanan lokacin ne malam tsoho yai magana tun lokacin da take ta faman hauka a cikin gida da zafe zage, Cikin maganar shi irin tamanyan jiya yace, To Ladi haukar taki da akace kina dashi ne kika taho ki geada min har nan waje, Kunya taji tafara cewa ba haka bane malam gaskiya bazan taba yarda a hada min zuri,a da irin diyan su samaila ba, Murmushi Malam yayi ya ce ko kina da hujja akan hakan ? Shiru tayi yace to ki ta shi kije kiyi hakkuri, idan kuma baki hakkuri duk abinda zaki yi kije kiyi, aure ne kuma andaura babu mai rabawa sai mutuwa, Ganin duk kusan diyan malam suna gurin azaune lokacin yasa ta jan bakin ta tai shiru don tasan bazasu kyaleta ta zagi mahaifin suba agaban su, Gida duk ya rikice da surutu wasu naganin rashin dacewar haka wasu kuma basuga illa ga hakan ba,

Meenat kan tun shigewar ta dakin mahaifiyar ta bata fito ko kofa ba tana can kuryan uwar ta saman dan gadon kata kon dake dakin ta takure, guri daya sai kuka takeyi a cikin gumza, Ita ma mama saratu kukan takeyi zaune daga kofa saboda bata kaunar fitina arayuwar ta sam, Anty Samirace tashigo tun daga kofa take cewa ina matar yayan nawa nazo muyi bankwana kafin in wuce don nasan da wuya mu hadu anjima, Ganin yadda meenat take kwance bakajin sautin komai sai kukanta dake tashi a kuryan uwar, Dan dafata tayi cikin tausaya mata tace Meenat don Allah kiyi hakkuri ki daina wanan kuka har asan abin yi, Amma ni hakkuri kawai zan baki don kin san halin malam tsoho, Tunda yadaura ya daura ke nan sai hakkuri, Kamar ta yayafa mata fetur a take takarasa wani sabon sautin kuka a lokaci guda, Haka Samira tamike zuciyar ta sam ba dadi taiwa mama saratu sallama da gwago habi ta wuce ran ta a bace,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 3⃣3⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH-AL-BAASIT,,,,

Duk musumi na kwarai idan har,lokacin tashin sallah asuba ya yi Da zaran wanan time din yayi zaka ji tankar an tashe kane, daga barci komai nauyin barcin da kake yi, A irin wanan yanayin ne ni Meenat na farka daga barcin da ya dauke ni tun daren jiya cikin kuka da magiya, wa yaya na, Abubakar, Akan wasu abubuwa da tun muna yara ake muna horo akan su na mu kiyayyi yin su da wasu mazan Amma sai gashi yau yayana dan uwana jini,na yana kokarin yi min shi acikin wani irin yanayi, Farkawa na, nayi duk jikin na ya na,man, nauyi, don ban taba sanin irin wanan rayuwar ba,,, Na dade a kwance ina son tashi amma nauyin jiki ya hana ni,,, Gashi ina tsinkayo kiran sallah a can nesa da anguwar mu kadan, A cikin dauri ya na dan iya mikewa zaune daga kwancen da nake, Wani irin zazzabine naji ya ziyar ci jikin na wanda ya kara man nauyin jikin,a lokaci guda, Da taimakon bangon dakin na samu har na kai bayin kamar yadda Anty na cikin hikima tai man hiran wata yarinya da irin abinda yasamay ni a yanzu yafaru da ita, Heater ruwan zafi, na kunna, wananda shi ya taimaka man har na dan ji daman jikin na,wa, Sallah na gabatar inda nake zaune a takure na nade kafanna babu abinda nakeyi sai hawaye, shar, shar shar, Tiryan tiryan abinda ya faru da ni a,daren jiya tsakanin na da yayan mu mafi daraja da kima a idon kowa na gidan mu abubuwan ne yazo man, a,zuciya, wani irin tashin hankali naji, Kara runtse idon na nayi ida wasu sabbin hawaye masu zafi suna gangaro man a fuska, Macen kwarai ba, ta son jikin ta Meena duk halin da take ciki zata san yadda ta yi ta taimakawa rayuwan mijin ta, Don haka kada ki zama ragguwa a gidan ki ke ma ki zage ki zama cikin mata masu kwazo da fasahan aure, Maganar Anty Amarya ne ya fado man zuciya na cikin ire iren nasihan da take min a lokacin da nake a gida Don haka still jiki ba kwari na mike tsaye tare da nade sallayan da nai sallah akai wanda Uncle dina na ne yabani da zanzo,,,,, Kitchen na nufa inda na kunna gas, na dora ruwan shayi cikin daurewa, A rish din da na gani gefe guda cikin store har sun fara rubewa na zabo na fara herewa a hankali jiki na duk ba kwari,,,, Kafin wani lokaci gida duk ya gauraye da kamshin dadi, saboda sanadarin da sa acikin girkin, Da kyat na samu na kamalla hada komai saman dinning table, din don zuwa lokacin zazzabi mai karfi ya rufe man ido, Ban yarda na kwanta ba alokacin, sai,da nai wanka Na dauko wani bakin jallabiya mai laishi da yawan stone a gaban rigan nasa,, Ido rufe na fada gado jikin na,na rawan sanyi sai wani iri nake ji, du kuma a tsorace nake a lokacin,, Bargon dake a gefen gadon na na jawo na nade kaina a,ciki inda na rufe fuskan na lif, da shi,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull