Tarko complete novel - Chapter 25
Tarko complete novel Chapter 25: Tarko complete novel Chapter 25. ****** ********* ****** Tunda ya dawo sai yake ganin gidan tankar ba kowa acikin shi,…
3,092 words
****** ********* ****** Tunda ya dawo sai yake ganin gidan tankar ba kowa acikin shi, Yadda na tafi nabar shi da safe , shima yafita zuwa office haka yadawo ya samay shi, Yadan dade tsaye a tsakar falo yana kallon kofan shiga daki na, Kamar ya nufi can sai kuma ya juya zuwa, hawa saman part din shi, Har ya gama abinda yakeyi ya fito, ba motsin Sadiya, a falon, Alama ya nunamai cewa bazata girka masu komai ba ke nan yau, A fusace ya nufi dakin ta tana tsaye tana kokarin gyara gadon ta da,ya cikwikkuykuye, Bata iya ce masa sanun da zuwa, ba sa kawai tana kokarin ci gaba da abinda takeyi, Haushine ya kama yaya Abubakar mace kamar tunkiya, Bata san yakamata ba da bai kamata ba, Gefen mirror ta inda yadan saba tsayawa idan zai mata magana don ya jingina jikin shi,, Sadiya tadago ido ta kalleshi don jin yadda ya ambaci sunan ta, Ita azaton ta ya zo ne neman wani abu agurin ta don yaga yau ita kadai ce a gida, Tambayan da yai matane yasa ta saurin dago kai ta dan dube shi, Sadiya may kike nufi da rashin dafa muna abinci, da baki da niyan yi, Abinci zan dafa kuma kace bai yi kyau ba,? Idan nace bai yi kyau ba basai ki gyara ba ki koya ko zaki yi mai kyau, Gaskiya kada kace zaka kawo min wanan tun wuri bazan iya ba ni, Aiko dole ki iya don ba mai zama yana dafawa ki na ci,, Bari kiji in har kin samu Meenatu yarinya ce ko kuma tana yi maki a matsayin ta na yar uwar mu,, Wace zata zo gidan nan yanzu nasan ba zata daukan maki wanan akidar ba, Idan kace kar ta bani ko, Da mamaki ya kalle ta yace wai ko Sadiya kina da hankali kuwa ? Ki tashi ki fita ki girka muna abinda zamuci na dare, Kuma barin fada maki daga yau, bazan kara sayo maki take away ba agidan nan, Sai dai mu zauna ahaka idan ba za ki yi ba, Gani fuskan shi ba wasa yasa ta biyo bayan shi, don zuwa ta dafa masu abincin, Idomie ne ta dafa masu sai dai yayi yaji da yawa don bazai ciyu, bà sam, Dole drinks ya dan kara korawa sama ya samu guri ya kwanta, Zuciyar shi cunkushe da bakin ciki, don ya rasa may ke mashi dadi a ran shi, Shawara yake tayi akan yadda zai bullo ma wanan al,amarin na Sadiya,,, Ace, mace kamar Sadiya bata,san yadda zata tafiyar da gidan ta ba,, Amma wai har yarinya kamar Meenatu tasan yadda zata tafiyar da rayuwan shi acikin jin dadi batare da wani matsuwa ba, Dasafe ma ruwan tea kawai da burodi ta tanadar mashi, Irin abincin da nake muna na karyaw ne ya fado mashi arai,, Gefen da take zaune tana faman loda bread a cikin ya ya kalla yana cewa Harara yafara sakr mata sannan yace wai ke, Ko Irish din baki yiya soyaba ke nan Sadiya sadiya kiwa kan ki fada fa,, Wani jutar da kai tayi gefe guda kamar wace akai wa wani zance na daban, Tsaki ya ja tare da mikewa tsaye idon shi duk sun kada,, yana cewa kada kiga kamar kin min ne, Ya ce sam kan ki kiyiwa, do ke, ce zaki sha wuya nan gaba,, Daga haka yasa kai yabar gidan zuwa office abinshi,,,,
****** ********* ****** Falon yai shiru duk da yake dai sanyi safiyane, Uncle dina ne azaune, Tare da matan shi dukka kan su biyu, kayan da nazo da su ne zube a gefe gudan falon, Uncle ya kara min sannu da zuwa yaku ma tambayen ni akan kayan da nazo da su, Kamar yadda yaya Abubakar yai min baya haka na fadawa uncle dina, Shiru yayi zuwa wani dan lokaci, can yace cikin wata murya mai sanyi, Gaskiya banji dadin abinda Abubakar yai min ba, Ada dakike gidana shike bani abinda zan ciyar da ke ne ? Anty Amarya ce ta tare zancen da ce, Haba dai dear ba haka yake nufi ba , Idan har ka lura shi aganin shi ai yanzu yana da hakki akan Meenatu kuma nasan yana ganin hakan zai yi ya fitar da nauyin ta dake kan shi, Mummy ma tace nima dai abinda nagani ke nan ai, Uncle ya dan furza da iska may sanyi daga bakin shi yana cewa, Yanzu abinda za,a wanan shinkafa duk biyu zan turawa mahaifan ki suyi amfani dashi, Mai kuma sai ku diba ku bada saura akai masu Saratu, Zanyi magana Uncle yace min yadda ya ce haka za, ayi, da kayan dole na kyake ina kallo aka hada komai ya fita dasu zuwa tasha don ya turawa iyayye na, Sauran tsaraban da na sayo masu, naraba nabawa kowa nashi Atake gida ya rude da murna don kowa nasayo mai tsaraba mai muhinmanci, Sai da mukaxkoma daki ne nakara fitar wa da anty amarya da yaranta wasu tsaraban da na sayo masu na daban, Tsaye Anty Amarya take amma sai ta janyo, dan stol din mirror dakin ta zauna, Tana yi min wani irin duba nason jin bayani daga baki na, Kunya ne ya kamani amma sai na daure nake fada mata irin alherin da yaya Abubakar yai min a lokacin zamana dashi, Allah mungode ma Anty Amarya tace tare da daga hannun ta sama ta shafa a jikin ta, Meenatu takira suna na a hankali , Nasan cewa abu mai muhinmanci zata fada don haka na ansa mata da murya kasa,kasa, Tace da farko na tsorata ainun da auren ki da mutumin nan, Ga irin yadda nai ta jin labarin shi da kuma uwar shi, Gama kuma da nagan shi a fili sai na kara tsunkewa da al,amarin sa,, Amma kin ga abin Allah sai gashi duk zaton mu ba haka bane ashe, Don haka yanzu abinda nake so dake ahine ki kara zage damtse gurin dankr mijin ki, Yadda ba wata macen da zata iya shige maki gaba da komai, Kin san dai yadda makiya sukayi wa auren ku yawa, don haka kara daurewa zakiyi kibawa marada kunya, Na amsa da cewa insha Allah Anty, zan yi duk yadda kika ce din Nan muka dan dauka n zama Abuja tare da yadda na hadu da Fattu da Uwar mijin ta, Sai Monday na fara fita school sai da ban manta da maganan da yaya Abubakar yai min ba, Akan in kula da rayuwata, bakomai yake nufi da hakan sai in tsare mutuncin kai na, Wanda dama ni Allah ya rufa min asiri ban da wanan irin rayuwan, Don ni ko kawa ban yarda da yi ba,a makaranta, Abinda yakai ni shine nasa wa gabana don haka yanzu ma ba wasa don wani katon hijab baki na zumbuda ajikina wanda ya rufe min ko ina nawa,
Sakon Uncle dina ya samu isa gurin iyayyena wanda mutane na ta mamaki daga ina wanan kayan ya fito haka ? Sai gulma akeyi ako, wani sashe, na gidan mu inda abin yadan yi sauki dan gidan Baba Shaibu da yaraka yayana Ibrahim gurin dauko kayan a tashar mota, Shike fada masu cewa,daga gurin Kanin Mama Saratu sakon ya fito, Hakan yasa zancen yadan lafa, Bayan dawowan Baba na gida yasau sakon kayan da Uncle ya turo mai dasu, Kwana biyar biyar,aka debawa ko wani sashe tare da zuba masu manjan a wani kwano, Sai shigowa sukeyi zuwa godiya mazan su da matan su, Wasu kuma na cewa, ta inda ake zaton abin ya fito sai gashi bai fito ta gurin ba,,,
Zaune matan gidan suke suna zancen abin duniyar dake gudana musanman a gidan su, Matar Baba Shaibu ce ta fara cewa, ita waccan may, bakin cikin, Ta,na nan dan tana can na wa duniya, yayafin arzikin shi, Sai matan Baba musa take cewa ai, ko bakin cikin ta ita zaici don dai a yadda malam ke fadi, Yanzu wani irin daula ne na arziki ya taso mashi amma nan gashi tare tako ina kada wani yaje ya lakato, Matar Baba Hamza tace, aiko zata sha mamaki nan gaba don muddin yarinyar nan ta kara nan gaba bazata iya tare ta,ba, Ai dai gamu gani inda rayuwar mu zamu sha kallo a gidan nan, Baki gani yadda Saratu ta canza cikin kwanakin nan sai wani sheki takeyi kamar mai sabon ciki, Wace tafara maganar tace, to ita kan ta mama Ladin, ai a wahalce take,, Ace wai danka nada hali irin na mama ladi amma daki ko gurin zama babu ballr shimfidar kwarai, To wai ku kuna mamakine baku gani gidan ga kowace mace dan uwan ta na zuwa amma ban da dangin mama ladi, Duk tabi ta kakabe su, ba mai zuwa gurin ta saboda mugun hali, Yanzu ai Hajja ce dangin nata inji matar Baba musa, Dagin sheri ba tunda mugun abin su iri guda,ne ai shiyasa nasu yazo daya,,
****** ********** ****** A kwance yake saman gadon dakin shi sanyi AC kawai ke tashi a dakin, sai faman juyi ya keyi Daga inda yake kwance ne yake kallon yadda dakin ya hargitse babu gyara, tun bayan tafiyan Meenatu wace ke gyara mashi, a kullun take da girki Gyara kwanci ya kara yi rigingine sanyin na ratsa mai jikin shi, Kewar matarshi ne kawai ke damun shi don sai yanzu ne ya san cewa sun shaku da yariyan fiye da tsan manin shi, Gyara kwanciyar shi yayi don cigaba da tunanen shi, Idon shi ya lumshe saboda tuna abubuwa da dama akan ta, Tarbiya, tsabta, girki, iya soyayya cikin dabara, take tafiyar da komai, Wayan shi dake gefen shi, ya lalabo, tare da neman laban wayan ta, Kira yake wayar kamar zata katse, sai yaji na dauka acikin siririyar muryan nan tawa, Wani irin sanyi yaya Abubakar yaji ya ratsa zuciyar shi saboda jin murya na da yayi kawai, Jin muryan kawai ya jefa shi ackin wani irin nishadi a lokaci guda, A hankali nace ina wuni yaya ? Lumshe idon shi yayi çikin wani irin ya na yin jin dadi, Ya gajiyan aiki yaya? Da kyat ya iya tataro natsuwar shi guri guda ya amsa min da cewa, Tau da sauki dai, Acikin damuwa nace da sauri lafiya kuwa yaya,? Sai da yadan nisa yace ina fa lafiya Kaunar yaya kin wuce kin bar yaya acikin tunane da kewar ki, Kunya maganar tashi taba har nadan sake murmushin jindadi ta yadda zai iya jina a inda yake, Hakan yasa yaya Abubakar lumshe idon shi a hankali saboda wani irin abu dake fisgan shi ,
ZEEE MAKAWA YELWA [8/4, 21:37] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 4⃣3⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH- AL- KHABEER
Jiki da jini yau Allah da ikon shi an wayi gari Mama Ladi ba lafiya, Tun safe Mama Ladi ta kasa koda fitowa kofan dakin ta, Ganin irin yadda jikin ya matsa mata Mama, Sa,a wace Mama ladi ke ji tankar ta shaketa kowa ya huta,, Itace taji shiru Mama Ladi bata leko ba kuma bata motsin ta ba a sashen ta, Don haka ta daure ta zagayo zuwa sashen mama Ladi din, Kwance ta samay ta acikin wani irin yanayi mai ban tausayi, Ta,yi amai duk jikin ta ya baci ko ina da aman, ga wari dakin kamar may, Da sauri ta karasa gurin Mama Lafin wace ke kwance cikin mawuyacin hali, Ganin dai abin bana wasa bane yasa ta komawa da sauri zuwa kiran maigidan su wanda ke waje gurin mahaifin shi suna karatu, Dan aike na fada mashi bai bata lokaci ba ya garzayo zuwa ciin gida, Da shi da Mama Sa,a ne suka gyara,mata jikin ta suka canza mata sutura, Da sauri Mama Sa,adatu ta, tada yaro yaje gidaje da yaran ta su ke aure ya fada masu halin da mahaifiyar su ke ciki yau, Ba bata lokaci sai gasu gabadayan su suncika gida, Hankalin kowa a tashe yake ganin irin yadda jikin ya matsawa, Mama Ladi, Samira ce ta dauki waya ta bugawa yayan su Abubakar , Nan ta ke sheda mashi irin halin da mahaifiyar su ke ciki tun safe, Waya yakira abokin shi Aliyu dake cikin Birnin Kebbi da yazo ta kai ta asibiti, Gado aka bawa Mama Ladi don ciwon yai mata tsanani, sosai, Mama Saratu itace ta farko aika masu da abinci asibitin,, Inda sauran mutanen gidan ba wanda ya kai mata komai, don sunce ko ciwo su keyi sai Mama ta ga dama take zuwa gaida kai, balle ma idan yaron kane baida lafiya,, Wanan dalilin suka rike yau su ma suka ce sai sun rama, Babana Samaila shine yazo da motar shi yace duk wace zata gaida ita tazo ta shiga su tafi, Wanan daman yasa matan gidan namu zuwa shiga mota don suje suyo gulma, A kai akai yaya Abubakar ke bugo waya ranan don jin ya karfin jikin mahaifiyar nasu, Andai tabbatar mai da cewa i yanzu ta dan samu sauki sai dai tana jin jikin har yanzu, Wanan zancen ne yasa yaya Abubakar, shiryawa zuwa kebbi dan ganin halin da mahaifiyar shi take aciki,bai tsaya wani shiri, washe gari ya kama hanya, Saboda yazo ya ganewa idon shi halin da mama take aciki idan ya kama a tafi da ita, Abuja ne gurin su sai ya wuce da ita,,,
****** ********* ****** Fitowa na daga lectures ke nan gurin da, nake yawan zama kusa da school mosque, na zauna ina jiran lokacin sallah azahar, yayi, Wayana dake acikin jakata ke ringing alamar kira ya shigo min, Ganin mai kiran nawa cikin wanan lokacin ne ya bani mamaki, Nomban yaya Abubakar ne kiran yai matukar ba ni mamaki sosai don baya kirana da rana sau dadare lokacin da yasan cewa ina free, Bayan na dauka mun gaisa yake sheda min cewa yana hanya ya kusa shigowa sokoto, zai tafi Birnin kebbi, A hankali na ke tambayan shi ko lafiya zai yi tafiya haka, shine ya ke tambayana acikin mamaki banda labarin mama tana asibiti kwana biyu kenan, Cikin wani irin murya nake cewa subbahanallahi, Banda labari gaskiya, ban san da zancen ciwon mama ba haka, gaskiya A take na nu damuwa da kullawa na ta hanya ce O ni Allah mama may yasamay ta haka, ? Allah ka dube mu da idon rahaman ka ya Allah, Sosai yaji dadin jin yadda na nuna concern di na akan mahaifiyar shi , Batare da na nuna bata kauna in nuna jin dadina akan ciwon ta ba Muryan yaya Abubakar ne naji yana cewa ban san ko kina free ba don ina son in tsaya indauke ki don mu je tare Ina school ne yaya amma zan kira Anty Amarya ta fadawa uncle dina, Ok zaki samu zuwa ko in wuce kawai ya fada cikin nuna dan bacin rai, Amsa na bashi da cewa zan tafi, Sai naji yai wani yar sanyayar ajiyan zuciya lokaci guda tare da cewa sai na shigo zan kira ki,
Bayan kashe wayan ne nai shiru sai kuma naga banda enough time na tunane don haka na kira Anty Amarya na shedawa yadda mukayi da yayana, Murmushi naji tayi tare da cewa Meenatu akwai ki da shirmay, Uncle din ki yanzu yana da iko a kanki ne dazai ce bazaki bi mijin ki ba Balle gida zaku gurin mahaifiyar shi wace ke fama da jiki, Ki yi sauri duk inda kike ki dawo gida, ki shirya kanfi ya iso, Sosai Anty Amarya ta min shirin gagawa na ban mamaki, Don ina kallon yadda tai ta min jike jike da kuma yan sauran dabarun mata,, Sai bayan biyar ya shigo garin sokoto inda nai mashi kwatancen gidan uncle din mu, suka karaso, Driver ne ke jan motar shi kadai zaune, a bayan motar, Masha Allah, kalman da su Mummy suka furta ke nan Yayin da yaya Abubakar yasamay su waje tayowa yan uwan ta rakiya, Nan take sheda masu cewa ai, tana ganin shine Mijin meenatu, A lokacin anty Amarya tafito, daga cikin gida don tai min rakiya, Kafan shi wanda yasa wasu bakaken takalma sai wani irin walkiya yakeyi, Yafar fitarwa, daga cikin motan a hankali, sanan ya fito da gangan jikin shi wanda, ke saye cikin wsu yadin silky mai laushin da sulbi, Annurin shi duk ya cika gurin ga zatin shi mai daukan idon al,umma, Cikin wani irin tafiya na kasaita wanda bawai da gangan yakeyi ba halitta,ne hakana din, kawai, ya karaso gurin su mummy din, Ya gaisa da su Anty da mummy cikin mutunci da girmamawa, Muka kama hanya, zuwa gida garin mu Birnin Kebbi, Tun shigana motar inda yake zaune a baya cikin dan gyara zaman shi, Batare da ya kalli gurin da nake zaune ba naji hannu yaya daidai saitin kunkuruna, Ya kamoni zuwa jikin shi tare da sauke wani irin ajiyan zuciya, Ya kike yace yayin da yake kokarin sunsunar wuya da hancin shi, Ganin a kwai driver a gaban motan yasa ni dan kara kama jikina kadan daga abin da yaya ke min, Zance Anty Amarya ne ya fado min a raina cewan da tayi yau sai na daure, don zan ya bawa aya zaki, gurin yayana, A hankali nacewa yayan nawa ya hanya? Ya labarin jikin Mama kuma,? Hannu na ya damke a cikin nashi tare da dan matsewa a hankali, Sai ya dan ja ajiyar zuciya a fili yace Alhamdullahi cikin kada kai, Kafin muyi wani magana kuma wayan shi ce akakira, A yadda nake tsanmani daga gurin aikin sune wanan kiran saboda irin bayanan da naji yanayi da mai shi, Dankali da su tumatari din hanya danagani anasayar wa na saba dama idan zan tafi gida in tsaya insaiwa malam tsoho,,, Wanda shi a rayuwar shi baida abinda yafi mai cin dafafen dankalin hausa, da kulikuli dakakke, Ganin Dankalin fari fet saman hanya yasha wanki yayi wani irin kyau gasu manya manya, Ban san lokacin da na cewa yaya wanda ke waya har zuwa lokacin, Nace mashi cikin murya maikama da shagwaba, yaya don Allah, zan sayawa malam dankali please? Dakatar da wayan da ya keyi, a lokacin yayi cikin bada umurni yana cewa driver stop there please, Cikin wani irin jan burki driver ya taka burkin motan a gaban wani dan yakwamamay tsoho mai farin gemu, duk rigar shi ta mutu saboda tsufa, Yaran dan tsohon naganin mu suka taso suna cewa, Dankalin mu yana da zaki da gari ga gardin ci , na,nawa zakawo maku, Kokarin bude zip din jakata nakeyi, amma sai naji, Yaya Abubakar nacewa dan saurayin mai dankali kowa wancan kwanonin dukka gaba daya, Sai da ya shake bayan buth da dankalin manya,manya masu kyau sanan muka,wuce,,