Tarko complete novel - Chapter 26
Tarko complete novel Chapter 26: Tarko complete novel Chapter 26. Mun shiga garin lokacin dare, ya soma don haka muka wuce direct asibitin Sir yahaya, inda…
3,655 words
Mun shiga garin lokacin dare, ya soma don haka muka wuce direct asibitin Sir yahaya, inda mamatake kwance, cikin jin jiki, A mota muka dan tsaya yaya yakira abokin shi Aliyu, yana sheda mashi cewa mun shigo garin, Wani Ward mama take kwance, ne wai ? Females Ward take zakuga su Wadda ai a haraba asibitin idan zaku shiga, A,nan nake jin yaya na ba Aliyu umurnin ya kama mashi hotel mai kyau kafin ya karaso,, A cikin girmamawa naji Aliyu, na karbawa yaya Abubakar umurnin shi, Females Wards muka nufa, atafe muke tare da yaya Abubakar sai, Baba Wadda wanda ke gaba yana muna ja gora zuwa dakin,, Dakin su kadai ne aciki dakin kudi, aciki ba na taro bane, Duk ilahirin diyan Mama suna dakin a lokacin gaba dayan su, Tare da wasu sauran yan uwan mu yan mata da su ka zo gaida mama din a,lokacin, Jikin nata ba laifi don da dan dama amma akwance take rijib, Sallaman da yaya yai masu yasa gaba dayan su juyowa suna fuskantar kofan, dakin, A cikin mamaki su ke kallon mu suna muna sannu da zuwa,, Duk da dare ne amma gaba daya idon su na a kai na, Kowan su na kokarin ya ga yadda na koma, kamar yadda suka,ji labari Duk da a fuskan su akwai murnan ganin mu amma akwai kyashi ga zukatan wasun su,, Saboda irin kallon kurullah da suke min a lokacin, da na shigo, Ni dai ina bayan yaya Abubakar sim, sim dani kamar zan shige cikin sa, A bakin gadon da mama take a kwance muka, tsatsaya muna kallon yadda take barci numfashi sama sama take fitarwa, Ido na kafe mama da shi sai ruwan da ake kara mata wanda ke shiganta kamar digo, Jikina duk ya dauki rawa saboda tsoro da tausayin yadda mama ta koma acikin lokaci guda, Da baya baya na koma ta kofa, ina mai zubar da hawaye, hankali na a tashe,don bazan jure ganin wanan abin ba mama ce haka a,kwance kamar ba ita bace hakan duk ta ramay ta canza halitta, Daga gurin da yaya Abubakar yake tsaye idon shi kyar a kan mahaifiyar shi, Ganin ina kuka ya,dan sa shi, dago kai tare da juyawa yana kallon gurin da nake tsaye, Fuskan shi da gani babu dadi acikin ta ko kadan don shima hankalin shi a tashe yake, Irin halin da ya riski mahaifiayar shi a ciki, kwance, Anty Samira ce da dan karamin, cikin ta, da ya fara turo rigar ta, sai faman zubar da miyau,takeyi, Ita ce ta biyoni inda nake ta dan ja min hannu mu ka fito wajen dakin, tare da ita,, A hankali take ce min Meenatu ai kun samu Mama taji sauki, sosai inda ga kwana biyu da ya wuce ne ai baza ki iya ganin taba ashe, ? Subbahanallahi na furta a hankali ina mai yiwa Mama addu,an samun sauki , Sai kuma Anty Samira ta dan kara kallo na wanan karon fuskan ta da guntun murmushi makale, tace, Meenatu wai da ke da mijin naki may kuka ci ne haka wai? Kun wani sake kun canza a lokaci guda gaku kamar wasu larabawa, can, Sai lokacin na dan yi guntun murmushi na ce kai Anty Samira ho, May ko mu kaci idon ki dai ne ya nuna maki mun canza,kawai, Hararan, wasa ta jefo ni da shi, tana cewa tunda makauniya nake ba, koko in ce muke ba,, Meenatu kin yi wani irin girma ga haske, ga kuma waye,wa atare da ke duk a lokaci guda, Kai haba dai Anty Samira duk a lokaci guda haka gaba daya abinda kika lissafo min,, Baba Wadda ne ya leko daga kofan dakin yace in zo Mama ta farka daga barcin, Mum samu ita da yaya Abubakar suna magana haka na kutsa kai zuciya na tare da fargaba, zuwa har bakin gadon da take kwance, Mama sannu da jiki ya karfin jikin, ? Shiru Mama tayi tankar bata jini ba sai kuma dan annurin fuskan ta da ya gushe, a lokacin da ta ganni, Dakin yayi tsit ana sauraren mu gaba daya an sako muna ido a dakin, a ga yadda zamu yi, da ita, Yaya Abubakar ne yake cewa mama Meenatu na gaishe ki, Mama tai wani irin lumshe idon bakin ciki tace, lahiya, a takaice, Na ce Allah ya sauwaka ya bida lafiya daga haka na juya da zuman komawa gurin da nake tare da Antyna Samira,, Kujeran da Anty Mariya ta dauko mashi ya zauna ya nuna min yace zauna nan, Wani irin nauyi da kunya ne ya kamani don ganin yadda yayyene yan uwan haihuwan yaya su ka sako muna ido gaba dayan su dakin,, Kai na dago daniyar in,cewa wa yaya Abubakar ya bari in fita waje amma sai annurin shi da kwarjinin shi ya hanani iya bude bakina alokacin,, Still dai kujeran ya dan kara, matso min da ita gabana inda nake a tsaye gab da shi don in zauna da kyau, Ba mussu na zauna kamar yadda ya umurce ni da yi, Daidai zan zauna naji daga bayan mu daya daga cikin su Antyn nawa wata ta sauke wani irin ajiyan zuciya, Dakin gaba daya yai wani tsit a lokaci guda inda kowa mu yake kallo, Mamaki ne karara a tare da yan uwan mu wai yau ni Meenatu mutum kamar yaya Abubakar kebawa gurin zama, Hmmm,umm wani abu sai mace, kaina duk yai wani nauyi don nasan cewa akwai magana ke nan, agidan mu,, Shigowan Aminin yaya watau yaya Aliyu makwabcin mu ne shima, uguwar mu guda dashi Acikin shiyan Sarakuna tare sukayi tundaga primary har secondary da yaya Abubakar, Zuwa gaban secondary ne suka rabu, don shi yaya a lokacin gwaunatin jahar sokoto na lokacin ta dauki nauyin karatun yaya Abubakar din, Yasa hankalin kowa komawa gurin shi, don agaisa da shi, Sun gaisa da yaya ta hanya bawa juna hannu tare da tambayan gajiyan hanya, Sai lokacin yaya Aliyu yan da kula dani a zaune, cikin mamaki yace, A kace min tare kuke da Madam ashe,? Mama Ladi wace ke kwance tana bautan Allah ta ji wani irin haushi a ran ta hakama sauran yaran ta masu mara mata baya, haushin abinda yacd ya kama su, A cikin mutunci fuskana dauke da yar murmushi na gaida yaya Aliyu da cewa ina wuni yaya Aliyu, Ya ansa min cikin fara,a da jindadi ta hanyar cewa lafia kalau Meenatu,, Kun taho lafiya yaya hanya ya, karatu shin ko kina Abuja ,har yanzu ? Ban bashi ansaba sai murmushin dana dan yi kawai, Yaya Abubakar ne ke cewa yaya Aliyu da motan ka kazone, Ya amsa mai da cewa eh tana waje, yace ok bari Baba Wadda ya tafi da driver mu can gida, ya sauke ma Meenatu tsaraban ta, Ka kai mata sashen Baba Samaila, don kar ya lalace, Saboda na gaji baza mu iya shigowa gida yan,zuba dare yayi daga nan masauki zamu tafi, Yakara fuskan tar gurin da Baba Wadda yake yana cewa, idan an sauke kayan sai ka,kai driver inda Aliyu yai mashi masauki don ya huta, ko,,, A yake yan uwan mu dake a zaine sai suka fara kallon,kallo a tsakanin su don jin may yaya Abubakar yafadi a gaban su,,
Ina zaune saman kujera idona kur akan Mama wace ke kwance shamay shamay saman gadon asibiti cikin ban tausayi, Sai dai har yanzu da alamar bata saduda ba ga al,amarin Ubangiji, don irin halin da alaman yanayin ta ya,nuna,,, Yaya Abubakar sun fita waje da yaya Aliyu, don haka ni da yan uwa na matane,a zaune dakin, Daga inda Anty Safiya take zaune tace min Meenatu mutanen Abuja dada kin tahiyar ki ke kyale kowa, ko? Murmushi nayi ina cewa Anty Safiya ba hakana bane,, Nomban wayar ki ta ban dashi ai da keji kira na,, Daga can bayan ta Anty Mariya tace a,a wallah ina taka kiran mutane ta samu maisunan malam ta kalalamay,shi Baki ga wadda shika rawan kafa akanta ba na? Daga baya kuma Anty hafsat tace to ko ke ce, aka rike ma kan maciji mika hanaki wasa da bindi nai,? Yanzu fa da kunnuwan ki kin kaji yace, tsaraba da yattaho da ita wai ta Meenatu ta, Lungun Baba Sama, za a aje mata suwa,, Samira ce tace kai jama,a asibitina fa muke ba gurin dadi rai ba,,, Shin mikkawo wagga magana wai,? Babane tare da Mama Sa,a su kazo akan babur din makwatan mu da ya aro, Cikin murna da jin dadin ganin mu gaba dayan su sai murmushi su keyi,, Amenatu ashe kuna hanya bamu da labari, na dan mike tsaye ina Kokarin ba Baba Buhari kujera, I zaman ki Aminatu ke ji, da kun ka kwaso gajiyan hanya, Na kai kujeran har gaban gadon da mama take dai inda Baba yake tsaye, Durkusawa, nayi har kasa na gaishe su shida matar shi na mike zan fita waje, Anty Safiyace ke tambayana ina zan tafi,? nace mata sallah zanyi don ba muyi sallah ba, daman,,,, Ita ce da kan ta ta taso tabani buta da sallaya sai kuma ta rakani tana nuna min inda zanyi tsarki,
Gurin da na idar da Sallah muke zaune da Anty, Safiya da Samira, muna kara zance akan ciwon Mama, Samira ce ta kara jefo min tambaya cewa har yanzu ina Abuja ne ko na dawo sokoto, Nace mata ina Sokoto ai tun sati kusan uku, da suka shude, Sai naji ta nisa tana kallon yar uwar ta can dai tace, Gaskiya Anty Safiya idan har Meenatu bata Abuja za,a samu matsala sosai idan ance Mama zata can jinya,,, Anty Safita tana kallon yar uwar ta tace, matsalar may, Ai baza a samu matsalar komai ba kin manta cewa Sadiya diyar Mama ce, Ni Samira ta kalla amma sai nai kamar ban fahinci may take nufi ba don haka sai mukabar zancen kowa yai shiru a cikin mu, duk kan mu uku kowa da abinda yake kiyastawa a zuciyar shi, Daga inda muke zaune muka hango yaya Abubakar shi da Aliyu tare da wani doctor, sun nufi dakin da mama take kwance a ciki,, Ba,a dauki lokaci ba sauran yan uwan mu dake cikin dakin har mama Sa,a su ka fito waje daga dakin, Gurin da muke zaune, su ka dawo suna cewa likita zai duba Mama, ne, Nan kuma gurin aka sake hada wani sabon daban hira sai kace ba jinya a,kazoyi asibiti ba,,, Sun dauki lokaci adakin tare da likita ciki zuwa can likitan yafito yabar su yaya da Baba acikin dakin,, Sun dauki lokaci a ciki saiga su sun fito har Baba Buhari,, Gurin da muke a zaune,da yan uwa nan suka nufo mu gaba dayan su, Yan bayanai yaya ya kewa su Anty Mariya da cewa zasu bari zuwa gobe sugani idan mama ta dan kara samun sauki,sai su wuce Abuja da ita,, Ina daga can zaune tsakiyan anty,Safiya da Anty Samira, Yaya Abubakar ke cewa kizo muje ko zan samu indan huta, hakanan, Wani irin nauyi ne da kunya suka rufeni a lokacin don duk wanda ke gurin ya girmay ni don nice karaman su, Anty Safiya ce da Mama Sa,a suke cewa alokaci guda, Meenatu tashi kuje kinji yace duk ya gaji don Abuja ba kusa bane, A hankali na mike tsaye daga inda nike zaune saman sallaya, Barin raka matar yayana inji anty Safiya, anty Samira kuma cewa tayi barin bisu su sauke ni gida nikan ,, Bayan shigar mu motane, naga zamu tafi yqyq bai bar masu komai, ba, Daga can bayan motan nake cewa yaya ya kamata fa kabar masu dan wani abun kashewa, Bai yi musu ba ya ciro kudi daga aljihun shi yace wa Anty Safiya da batai nisa da motar mu ba tazo takarban masu, Anty Samira wace ke tare dani a bayan mota tace wa dan uwanta, Yaya shima Baba fa da mashin suka zo shi da mama Sa,a,,, O,o Allah na nace, daga gefen da nake zaune, nace Allah ya yaye muna wanan halin da muke ciki Anty Samirace takarba da fadin Ameen ke dai Meena,
ZEEE MAKAWA YELWA,,, [8/4, 21:38] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 4⃣4⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH- AL-HALEEM,,,,
Wanka na fito ina daure da tawul, fari na hotel din a jikina, Yaya Abubakar yana daga bakin gado zaune cikin wani dan wandon boxes na maza, Kokari nakeyi in daure kaina da ribon fin da na dauko daga cikin jakata, Muryan shi da abin da yake fadi yana kawowa daga gurin da nake a tsaye bakin mirror, Hakan ne yasani gane cewa da mace yake magana kuma ba Anty Sadiya bace, Saboda irin yadda naji yana bada amsa cikin shauki da so,, Wani irin abune naji yai min tsaye a zuciya ta,har naji kamar idona yana rufewa, Amma abinda yafado min arai shine zancen Anty, Amarya, alokacin da nai mata hira lokacin da Salawatu tazo gidan mu a Abuja, Anty Amarya tace min,Meenatu koda mata biyu yayan ki zai auro yanzu a lokaci guda babu ruwan ki don ba yadda zakiyi,, Don auren ki dashi aure ne na mutu ka raba ban ga dalilin da zai sa ki tayar da hankalinki ba,. Abu gudane yanzu agaban kishine kisan yadda zaki tafiyar da rayuwar ki dana Mijin ki ta yadda duk wace ma zai auro bazata iya dake ba sai dai ta barki, da shi,,, Ajiyan zuciya na sauke tare da dan kirkiro farin cikina a fili, Ban san zuwan yaya Abubakar kusa da ni ba sai dai jin hannun shi nayi a baya na, Daga haka muka dan yi tafiyan hazo a tare ba tare da na kara, tunazancen wata Salawatu can ba,
****** ********* ****** Karfe takwas na safe muna a haraban gidan mu kofan gidan malam tsoho dake uguwar shiyan Sarakuna cikin garin, Birnin Kebbi,, Idan na tsaya baiyyana irin farin cikin dake dauke a fuskan kakan mu malam tsoho da wasu daga cikin iyayyen mu dake gurin, Babu wanda yakai mahaifina farin cikin ganin mu a lokacin don dagani har yaya Abubakar ban san wanda yafi jin daddin gani ba a tsakanin mu, Nafito daga bayan mota tare da ni da yaya Abubakar cikin murna yau gani a gida, bayan dan dadewan da nayi batare da na shigo ba, Yaya Abubakar yana gaba ina biye dashi kamar yadda yake a gidan mu, Don kusan doka ne hakan don duk wani dan gidan idan har yai tafiya yadawo dole ne sai ya fara zuwa rufar malam tsoho ya kai gaisuwa da neman albarka, Sosai malam ya kasa boye irin farin cikin da yake ciki yau don ganin yadda TARKO shi yai kamu, Mun gaisa da shi cikin wasan jika da kaka inda yake cewa watau Abubakar wayau da kai min ke nan, ? Ka karbe min mata katafi da ita birni, kuka barni nan a cikin rumfa ko, Dariya sukayi atare inda yaya Abubakar yana zama yace mai, ai, kai ba jarumi bane sunan kawai muka ara maka, Don haka kaga da ni jarumin maza tadace shiya sa ka,sadaukar kabar min kawai, Atare suka kara sa dariya malam na cewa to haka zaka ce min yanzu ko, Tun da nai maka wanan, halarcin kake ganin kamar ban kai jarumi ba ko, A hankali yaya Abubakar ya dan sasauta muryan shi kasa kasa yace bance ba tuba nake, malam tsoho mai ran karfe, Nan nabarsu zaune a tare da malam din suna kara tataunawa a tsakanin su, Direct sashen mahaifana na wuce kai tsaye,, Na samu Mamana tana kokarin hada muna breakfast,, Da dan gudu na nakarasa gurin ta na rugumay ta, ta baya, nadade rungumay da mama ina jin dumin jikin mahaifiyata, Sai kuma ga hawaye sun zubo min shar ga ido na subbanallahi Yar Baba may ye haka kuma farin kisa wata tashigo taganki kina kuka ace ai, wani abin ne ya faru, dake kuma, Cikin muryan kuka nace mama naji marmarinku ne wallahi, Tace to yanzu ba gaki ga muba sai ki cinye mu tunda kinji marmarin mu, Kaina nakara nutsarwa a jikin ta nace, mama idan na cinye ku ingawa kuma, Muryan mahaifina ne mukaji daga bayan mu yana shigowa gidan, yana cewa, To ke Saratu tunda sun zo ai sai abarshi su karya anan ko? Anan kuma malam mama ta tambaya cikin mamaki, da fargaba, Nan muka zauna gaba dayan mu a yar barandar tsakar gidan mu ana hiran yaushe rabo,, Babana yakalleni yai murmushin jindadi yace, to ya wajen kawun naki, ina fatan duk suna lafiya ko,? Na ba Baba ansa da cewa duk lafiya suke suna gaisheku, Baba yace , Nafi,u dan rigima,saiga shimkafa da su mai, ya turo min dasu wai, muyi anfani da su, Shigowan yaya Abubakar a sashen mu yasa ma sauri dauko hijabin ta tasa, Wai kada suriki ya ga jikinta,surukin da tun ba mu zo duniya ba yake ganin ta a hakana, Shima afaninyaya Abubakar din yau sai yake jin wani irin nauyin Mama da Baba, Don haka sai ya kasa sake jikin shi kamar yadda ya saba, Baba ne yai mai umurni da ya zauna su karya a tare dashi, Bai fi minti biyar da zaunawa zai yi breakfast ba sai ga Baba Wadda yana sheda mashi cewa, wai ana sallama dashi a waje, Har zai mike sai baba yace dakata ka tsaya kaci abincin ka kafin ka fita, Don yanzu haka da ka tashi bazaka kara dawowa ka zauna ci ba, Masa ne da miya, sai, kunu koko, da kosai, da sugar, Sosai yaya yaci masa da miyan da aka siyo muna gudan mai yawa, sosai, Kafin ya kai karshe,sai ga yaya Aliyu ya shigo yana ce mai wasu daga cikin abokan su ne su kazo mashi murnan samun girman da yayi,,, Daga wanan fitan ban kara ganin yaya Abubakar ba har zuwa, wani lokaci, Nikuma ganin haka yasa nasamu sakewa da mahaifiyana da yan uwana munata hirar mu gwanin ban sha,awa,, A dakin mamana in kwance saman gadon ta mana tana zaune saman kujera, Mamana tace yar Baba naji dadin ganin kuna zaman lafiya da maigidan ki fiye da yadda muke tsanmani, Da farko zancen auren ku hankalina ya tashi sosai wallahi sai nake gani kamar zai wullakanta min ke, Amma tunda mahaifin ku ya ce min mubar wa Allah al,amarin sai kawai naji hankalina ya kwanta sosai Don haka nashiga rokan Allah da ya kara sanya alheri fa wanan al,amarin, Yakawar da duk wani sheri ko kulli dake tattare da wanan auren naku, Tambaya najefo mata da cewa amma Mama Ladi ta daina wanan irin zagin da take muna ko, Murmushi Mama tayi wanda ya nuna min cewa bata daina ba, har yanzu tana yi, Sai Mama tace inma har bata daina ba ai sai tayi da wanda ya kulata, Yanzu ai wanan ciwon kawai ya isheta ishara in tana da hankali, Haka mukai ta hira da mahaifiyata mu na yi muna girkin abincin rana, tare, Sai bayan Sallah azahar yaya Abubakar yabugo min waya yana cewa daga gida suka wuce, gaida mama sai kuma wani abokin su da gidan shi ya kone suka tafi mai jaje, Akarshe yake tambayana da cewa ba dai matsala ko ? Murmushi nasake ina cewa saidai na rashin ganin yayana a kusa dani, ba, Yaji dadin may na,ce haka yasa shi dan murmushi jindadi, Yace ai, gani zuwa don nasan mama tai min abinci rana, yanzu haka ko , Nace kaman kasani yaya amma dai tuwon shimkafa nace tai maka shine ta hada ma harda dan wake wai tasan kana son cin danwake da, Murna sosai naji yanayi yace wa kifara min godiya kafin in zo, don ban san yaushe, rabona da cin dan wake ba, Kafin yazo na dan tashi na shiga wasu sassan gidan mu ina gaida su,, Sai zuwa dare na samu shiga asibiti,gurin gaida mama, Gaskiya yau jikin ya dan yi dama sau don da alamar taji sauki, Tun shiga na mama wace ke zaune tana shan kunu acikin cup, Mu kayi arba da ita, sai naga ta kauda kai gefe guda, kaman bata kaunan gani na, Har gaban ta na karasa ina gaishe ta da jiki, Kamar bata son ansawa ta nsa min tare da kauda kanta gefe guda,, Nagane may take nufi amma sai naki gushewa daga gaban ta naja na tsaya, mata, Da ta gaji da aje kanta a gefe guda sai takai kwance , Anty, Safiya ce ke min magana daga bayana, tana cewa, Matar yayana jiyafa munga sako, daga yayan mun gode,, Da mamaki na juyo ina kallon Anty Safiya ina murmushi nace nikan anty ai wanan zancen kune ba nawa bane,, Sai da dare yaya zo dakin inda yake tambayan yan uwan haihuwan shi, koda wace cikin su za,ai tafiyan, Inajin yadda suke muhawara a tsakanin su, don anty ,Samira ce tafara magana tana cewa nidai kar ku sani don kun ga halin da nake ciki, Haka dai sukai ta cecekuce, inda anty mariya tadage akan cewa itace zata, Dole kowa ya kyale ta, ta tafi din su zasu zo daga baya suga jikin mama din insha Allah,, Motar asibiti ce yaya yai haya zata kai, Mama Ladi har Abuja, tare da baba Wadda da Anty mariya, Washe gari badon naso ba mukayi sallama da iyayyena da yan uwa da abokan arziki, Mun kusa shiga sokoto,ne na dan matsa kusa da yaya Abubakar,nadan kwantar da kaina ga kafadar shi, A hankali naji yana sauke ajiyan zuciya mai yar nauyi, A hankali nace mashi yaya Allah yaba wa mama, lafiya Ya ansa min da amin a hankali,, Inda naji ya dankara matse ni zuwa jikin shi yana cewa, kici gabada kula da kanki pls, Kudi ya mikomin don zasu kai kamar dubu hamsin, zanyi magana ya kada min kai dole nayi shiru bance komai ba sai dai ina rike a jikin shi,,, A sokoto yaya Abubakar suka saukeni a gida tare da tsarabar da nazo ma su da shi, Mun rabuzukatan mu babu dadi acikin ta don ga zancen ciwon mama ga kuma kewan rabuwa da junar mu da zamu kara yi,