Tarko complete novel - Chapter 33
Tarko complete novel Chapter 33: Tarko complete novel Chapter 33. Yaya ya bugo waya lokacin ina barci wana kuma yana gurin caji dakin Anty, Don haka, dole…
2,368 words
Yaya ya bugo waya lokacin ina barci wana kuma yana gurin caji dakin Anty, Don haka, dole ya kyaleni gidan Uncle na kwana ranan, Cikin dare zafin jiki ya tadani daga barci, amma zuwa asuba saina samu barci don sai naji zazzabin ya bari, Tun da safe bayan mun karya muka kama hanyar Abuja, inda driver yai ta sharan gudu damu don ya samu hanya, Duk yadda naso in boyewa Yaya Abubakar rashin jin dadin jikina hakan bai yi ba don zazzabin ya kara rufe ni a mota again,, Nan Yaya Abubakar yahau min fada cewa may yasa ban fada mashi tun can banji sauki ba likita ya kara dubani, na biyo hanya da ciwo, haka,
A kofan gidan kamar kulun Samarin dake zama a kofan gidan suna nan, Tsayawar motan mu ya sa hankali su duk yayo kan mu baki dayan su, Nice ta karshen fitowa daga motar abinda yasa hamza saurin mikewa da sauri ke nan, Ya ce a Amarya tazo ke nan fa, ? Wani daga gefen shi cikin suke tambayan shi wata amarya yace mai wanan da ta ke bamu abinci mana, Sai suka mike gaba daya zuwa taron mu suna faman yi muna sannu da zuwa, Makullin dakina na,ciro daga cikin jakkana na mikawa Hamza wanda sai a lokacin ya kula da cewa banda lafiya ne, Cikin tausayawa yake mun sannu yayin da sauran abokan shi suka fara yi min sannu suma tare da cewa anzo lafiya,
Tana zaune, a falo, cikin shigar wani dogon wandon jeans da wani bakin riga mai dogon hannu,, Hamzs ya shigo gidan da sallaman shi, da sauri ya nufi part dina yana budewa, Salawatu ta mike tsaye tana masa wani irin kallon rainin hankali, za tai magana ke nan na shigo gidan da Sallama na , Baki na ya sauke da addu,oin tsari kamar yadda kakana ya sanar dani, Kallon mamaki take min don da farko bata gane ni ba sai da taga shigowan Yaya Abubakar yana cewa akai kaya a part dina, Hamza ke daga kofa yana shiga da kayan cikin dakina, A hankali na ina bude bakina ina ce mata ina wuni acikin muryana da yasa ta kara sandarewa, tsaye, Ban san ko ta karba don ni wucewa nayi don in samu guri indan kwanta, Hamza ke cewa barin fadawa Fattu cewa kin zo ba lafiya daidai lokacin da na shiga dakin, Bai bata lokaci ba ya fita kiran Fattu a lokacin ne Yaya Abubaka ya shigo dakin nawa, Gadon ba zani gado saman shi, sai dai katifa hakana kwanta sama ina jin wani irin amai na taso min, Inna Allah Allah Yaya ya fita dakin in samu in shiga bayin dakin, Ganin yana kokarin taba ni yasa ni mikewa da sauri har ina ture shi na fada bandakin Amai nayi sosai sanan na samu sa,ida na wanke baki na da fuska na nafito dan kwalina a hannu, Yaya yana tsaye daga kofan bayin ya tsura min ido cikin tsarguwa, Yace Meenat har baki da lafiya haka kika bari mukabi wanan hanyan mai tsawo da ke, Sallaman Fattu a kofan dakin shi ya dakatar dashi, Yace mata bissimillah ko ? Tashigo tana cewa Amarya ba lafiya kuma kukai wanan tafiya haka, Dan dariyan yake nai mata nace a hanyane ciwon ya kamani ai, Fita Yaya yayi zuwa gurin sauran matan shi yabar mu da Fattu, Ita ce ta taimaka min da gyaran dakin take dakin ya koma neat, kamar bashi ba, takawo room Fresh ta fesa ko ina har bayi take guri ya dauki kamshi, Anty Sadiya ce ta shigo da Sallamanta fuskanta ba yabo ba fallasa a cikin sa, Ina zaune ina shan ruwan Lipton da Fattu tasa Hamza ya kawo min daga gidan su, Acikin muryan nan nata kamar bata son magana tace, , Meenatu ba lafiya kuma ga tafiya, a hankali nace sannu Anty, Tace yawa, kun zo lafiya ya mutanen gida ya karatu? Na ansa da Alhamdullahi, daga inda Fattu take tana kokarin sa min trolls dina guri guda tacewa Anty Ina wuni Anty,? A dasashe ta ansa wa Fattu ba a cikin dadin raiba, Daga haka anty ta juya tana cewa Allah ya sauwa ka, muka karba mata fadin ameen, Lafewa nayi saman gadon kamar may barci yayin da Fattu take zaunw daga gefe guda ta zura min ido, Yaya Abubakar ya shigo dakin yana cewa in tashi mu tafi asibiti, Badon naso ba muka tafi asibiti da shi, akai min alluran malaria da kuma kwayoyin sa akaba bani, Da na dawo na samu Mama Bi,u tazo tana zaune a dakina don haka ranan tsohuwar mai mutunci itace ta kula dani, Washe gari na tashi jikin nawa da sauki don muyi waya da Anty ina mata bayanin yadda jikin ya kasance min, Ta tambayeni ko ya muka kwashe da Salawatu, sai da na ja tsaki nace ni tun shigowa na ban ganta ba ma har yau, Kina nufin ba tazo dubaki ba ke nan na cewa Anty gaskiya hakane, Share muna fuka kawai ki kama harkokin ki bakin ciki takeyi dake don may ki kazo,, Kada ki yarda ki biyewa jikin ki ki mike kifara harkokin ki a cikin gida kamar kowa,, Na amsa mata da to Ànty na gode takara ce min kadafa kiji tsoron kowa ki dake kawai ki kama harkokinki na kara cewa to Anty nagode, Muna gama wayan da Anty sai naji tankar tabani wani magani ne a jikina don sai kawai na mike tsaye, na shiga yan gyare gyare a dakina har zuwa dan corridor din sashe na, Daga nan na fada kitchen don indan sa ruwan zafi wanda zan sha ruwan Lipton shayi, Salawatu tana cikin kitchen din tana aiki wanda hakan ne yasani gane cewa, ita ce da girki a gidan, Sallamu Alaikum na ce tare, cewa ina kwana lafiya kawai tabani ansa, Direct gurin Gas din da ba bu komai a sama na nufa don in kunna wuta,, Muryan Salawa naji daga baya na tana cewa, wanan dayan Gas din zan yi amfani dashi yanzu, Amsa na bata a takaice da cewa ruwa kawai zan dafa sama, Naci gaba da abinda nakeyi, sai dai bakina ya dauke da addu,an haduwa da muguwar kishiyya, Komai na hada daga Lipton har kayan yaji a cikin ruwan har ya fara batun tafasa, Muryan Yaya Abubakar naji daga baya na yana cewa,Sallawa har kin samu lafiyan fitowa hada girki, Dan murmushin irin ta ma,ana na sake nace ba girki bane Yaya dan ruwan Lipton zan dan dafa da kayan yaji inzuba a flasks dina, Ashe Salawa tana a bayan shi sai naji yana cewa bakin ce ta,tare maki gurin girki da nata girkin ba, ? Batare da na kula suba tankar basu gurin najawo flasks dina a gaban shi na fara daurayewa tare da daukan dan soyoyon tace ruwan zafi, nafara tace ruwan a cikin flasks, Ina jin lokacin da yaya ya juya yana cewa cikin murya kamar a zafi zuciya yace, bazan yarda da zaman fitina a gidana ba fa, Idan ke baki sani ba su sun sani ai don na riga na fada masu, tun farko So, Mind your self,,, Sororo Salawatu tayi tabi bayan mijin su da kallo don ita ba haka tazo ba, Daga in da nake tsaye na sake wani irin ajiyan zuciya,tare da numfasa, Na kashe Gas din tare da dauraye tukunyar na zubar da kayan yajin a dustbin, din kitchen,, Fitana daga kitchen din tabi bayan nawa nima da kallo har na bace mata ga gani, Dakina na fada na aje flasks din a gefen mirror na, Bakin gadona na zauna nafara tuna nen cewa ashe zancen Anty Amarya gaskiyane, na cewa sai nayi fama da kishin Salawatu, Na mike tsaye ina cewa ashe akwai aiki kenan a gaba na bari kawai in murjewa wanan macen ido, Abincin da yasa dokar cewa a tare za,a dinga ci sai naga ba,a kirani ci ba Tunda nadan sha ruwan Lipton dina tare da magani na sai na samu guri na kwan ta don dama ina bukatan hutu,,
Sau kusan biyu Yaya Abubakar ya yana lekowa ya ga ko na farka daga barci, don yaji ko nasha magani na, Wanan abin ya matukar bakan tawa Salawatu rai don tun zuwan ta gidan ta, tare komai tana nuna kamar ita ka dai ce matar gidan,, Ita Anty Sadiya ko a jikinta, don ita har kan su baya gaban ta Duk wani duniyan cin da Salawatu zatayi bai a gaban ta, Hakan ke sa bata damu da fita waje ba don bata da lokacin su, Ita ko Salawatu sai take gani kamar duk a cikin samun gurine hakan agareta, Amma yau sai gashi kan yar karamar matar sa har yake ta zuwa da dawowa,
****** ********* ****** Driver yana shiga garin Birnin Kebbi bai tsaya ko ina ba sai kofan gidan malam , Abinda ya jawo hankalin al,umman uguwar ke nan zuwa kallon motan da ta tsaya kofar gidan tsohon, Driver wanda ya fito ya nufi wurin da malam yake cikin rufan kofar gidan shi, Babu abinda zaka hango sai farin gemun shi tun daga nesa, Shima kansa malam din kallon mamaki ya kewa driver motan, Sun gaisa da malam a cikin mutunci tare da taron hababa daga malam din har sauran mutanen dake gurin, Mutumin ya dubi malam yace sako ne da Alh Abubakar na gidan nan, Yace ina zo in,baka wanan sakon hannu da hannu ya mika masa envelope, Kudi ne acikin envelope din da yar takarda, mutumin yace, yace wa yancan kayan aba Wadda ya rabawa kowa ga takarda wai a bashi, Cikin mamaki malam yace a ina ka gan shi bawan Allah, Yace Sokoto sun fito Niger da shi da matar sa, saboda bai samun zuwa shi da matar sa yaba da sakon akawo, Take guri ya dauki zance cewa Abubakar ta turo wa iyayyen shi da abinci mota guda taf da kaya, Baba Wadda aka nemo a cikin gari yazo da sauri inda ya fara fitar ma da kowa da nasa rabon, Har zuwa makwabtan su da ya sa sunan su a cikin don sun zama tankar yan uwa, Sai kuma kudin sabon mashi wanda za a saiwa Baba Buhari,, Baba Wadda yaba kowa shadda da kudin dinkin da yaya Abubakar yace masu nice na sayo masu tsaraba a kasar Niger, Haba gari ya dauki ciri cewa, Abubakar ya aiko wa iyayyen shi da sako, Wasu ce ai yanzu ya daina daukan shawaran Mama Ladi ne, Wasu suce ai saboda yanzu yana auren yar gida yasa yafara kula da gida, tau kowa dai yasan halin dan Adam,,, Ranan Mama Ladi kamar zata kama da wuta don may zai yo sako bai fada mata ba sunyi shawara, Ita Meenatu aiki takeyi da zata samu kudin sayen irin wanan kayan haka? Sam baza ta yarda a mallake mata da ba kamar yadda uwata ta mallake ubana ya kasa kara aure ,sai abinda tace kuma take so akeyi a cikin gidan mu, Zagi dai kala kala mun sha shi gurin mama Ladi ni mahaifiyata a ranan, Malam tsoho yasa arabawa mutanen shiya mabukata kason shi tare da cewa Abubakar ne ya aiko masu dashi,,
****** ********* ****** Ina zaune a dakina ina dan shan faten wanken da Fattu ta,shigo min dashi don faten yai min dadin sha dosai, Ya Abubakar yabude labule ya shigo da sallamar shi, Na amsa tare da dan dago kaina plate din dake gaba yake kallo, Tambaya ya jefo min da cewa mayye wanan haka a gaban ki, Nai dan murmushi nace fate ne nake sha, Yakara kallon plate din yace, fate kuma,? Nace Fattu ce ta dafa min wai ko zanji dadin bakina sai naga fuskan shi ya matse da ga yar fara,ar da ya shigo da ita, da farko, Meenatu bana son mutanen nan suna shigo min da abinci dafafe a gida, Idan basu, dauka agidana ba ashe kuma baza,a kawo saga gidan su ba don dai ba alfahari ba nasan cewa nafi karfi, Jiki na yai sanyi sosai da jin zance Yaya Abubakar Don haka a hankali na dago kai nace masa nice nace ta da famin Don bazan iya dafa abinci yadda nake ji, jikina ba, Na fadi hakane don yasan cewa ba a, bani abinci ba agidan, Na karashe zance da kwantar da muryana na ce amma kayi hakkuri baza,a sake ba insha Allah, Ya juya batare da yace min komai ba ya nufi waje, cikin fushi, Nima murmushi nayi daga inda nake zaune don ko banza na rama abinda Salawatu tai min da safe, Dakin Salawa ya nufa ya samay ta zaune tana waya tana fadawa Salawtu ce nazo garin Abuja, Kallon da yai mata kawai yasa ta gane cewa da magana yazo, Don haka ta kashe wayan ba shiri tana mai kako murmushi a fuskan ta, Oga lafiya dai ko? Ko kana son wani abune ? Lafiya kalau yace, tare da fuskan tar ta da kyau ya ce ina abincin Meenat, Meenat ta tambaya cikin maimaita sunan, Yace eh Meenat my second wife, Kai tsaye tace ban sama mata ba saboda naga gaba daya ake zubawa agidan, aiko, Yace amma kin san aibata da lafiya ? May yahana ki kai mata a daki ? Ta katse shi da sauri cikin murya mai baiyana mama tace, Sir nice zan kaiwa wanan yarinyar abinci har daki ? Don kin kai mata abini laifine, ? Ba kishiyar ki bace ita,? Idan akwai abinda yafi muni Salawatu taji shine wanan kalman da ya fadi Gaba daya duk jikin ta sai yai sanyi rayuwar ta ya baci, Amma sai ta dake tace ma shi ban yi wanan tunanen ba gaskiya amma kayi hakuri please , Tashin hankali Salawatu duban Yaya Abubakar takeyi yadda ya sake mata a lokaci guda, Kamar ba Ogan ta ba da suke ta zuba soyayya da amarci tare, Juyawa yayi ya haye sama dakin shi rai bace don duk mun taba shi, Salawa ta dafa bakin gadon ta takai zaune da kyat, Idon ta sunjuye sunyi jajir akan wanan little baby din yau Oga ke batun ci mata mutunci haka ? Lai ko wani abu sai aure wanan yar karamar yarinya za,ace takaiwa abinci har daki nerve gaskiya da sake,,,,,
ZEEE MAKAWA. YELWA🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 5⃣1⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH - AL- MUQEET,,,