Tarko complete novel - Chapter 32
Tarko complete novel Chapter 32: Tarko complete novel Chapter 32. Ni kadai ce adakin don Yaya Abubakar yana gurin da suke zaman karshe, Yau sun,fi kullun…
3,325 words
Ni kadai ce adakin don Yaya Abubakar yana gurin da suke zaman karshe, Yau sun,fi kullun dadewa don haka har zuwa lokacin barci don haka na tashi, nashirya cikin wasu jajjayen kayan barci iyakar tsayin su gwiwana, Na daure kaina, da wani ribon baki, sai, na koma bakin mirror na fara shafa turare ta ko ina ajikina,, A gajiye Yaya Abubakar ya shigo dakin yana rataye da couth din shi ga kafadan shi, Kokarin cire takalman shi yakeyi a lokacin nakaraso gurin shi cikin wani irin tako, rigar jikina yana shaking, Hannayen shi ya ware na shige ya mayar ya rufe hannayen dani a ciki, Ajiyan zuciyan zuciya muka sauke kusan atare, tankar mundade bamu ga junan mu ba, Bayan yai wanka yai sallah shafa,i da wutir, sai nagabatar mai da abinci Zaune nake a gaban shi na tsurawa abincin ido na kasa cin komai, sai faman tunane nakeyi Hannu shi na hagu yai amfani dashi gurin kada min hannu, Abinda yadawo dani daga duniyan tunanen da na shiga ke nan, May kike tunane haka bayan ga yayan ki a gaban ki kuma ? Murmushi nayi nace a hankalo ba komai yaya ina dai tunanen cewa gamu anan muna cin abinci mai kyau da lafiya amma , Har mu rage afita dashi batare da mun iya cinyewa ba, Amma gida suna can yanzu nasan a wanan irin lokacin na damana da abu kan yiwa mutane tsaye suna nema, Murmushi kawai Yaya Abubakar yai min tare da kokarin tsiyaya ruwa a cup ya sha Da sauri na karbi goran ruwan ina tsiyaya masa a cikin cup na mika mai, Sai da ya kora ruwan sanan ya dan kalle ni yace, Kina nufin cewa yanzu gida a matse suke cikin irin wanan lokacin ? Cikin yar murya irin ta mai shagwaba nace Yaya kasan fa ba wai suna wani aiki bane, Sai fa abinda Allah ya basu zasuyi amfani dashi, Ajiyan zuviya naji yayi a lokacin tare da sauke numfashi a hankali, Har ya gama cin abinci bai kara cewa komai ba na mika mashi tissue ya goge hannu da bakin shi, A irin yanayin da naga Yaya Abubakar tun zancen mu na abinci sai na dan shiga damuwa batare da na bari yagane ba, Don inaga baiji dadin zancen da nai masa ba a take nace wa kai na sannu dai Meena uwar rigima, Daga gani saki sai in kama talala, Daga gurin da nake a kwance ina kallon Yaya Abubakar tsaye a gaban mirror ya na shafa roll on a hammatar shi tare da dan, jefa mintin a bakin shi dan na zube muna saman mirror ne, idan zamu kwanta sai kowan mu ya dauki yar kallan da yake son tsotso, yasa abaki don sanya dan kamshi baki, Ina jin lokacin da ya hawo gadon tare sa rungumoni daga baya inda ya fara sunsunar wuyana har zuwa sumar kaina, Sai naji ya kira sunana acikin wani irin murya mai rauni, A hankali na amsa mashi da na,am Yaya,saboda na fuskanci magana ce ta muhinmin zai fada min, Tambaya naji ya jefo min da cewa shekaranki nawa yanzu ? Gaba yaba da dam don nasan dama na taba yan mazan yau ,, A hankali nace ina cikin na sha tara Yaya Hmmm naji ya ce tare da matseni yaci gaba da addu,oin kwanci, Barci ya fara dauka don nasan yau ba kan,ta don ran yan maza da alamar a jagule yake, Muryan shi naji yana cewa Meenatu banda abinda zance sai dai in kara godewa Allah ubangiji subbahanahu,wata,ala da ya bani ke amatsayin abokiyar rayuwa,, Meenat wanan zancen da kikai min a gamay da gidan mu ya kamata ace hankali na yakai can da dewa, Amma sai kawai shedan yasa na shagaltu da zance saboda aiyukan da sukai min yawa mutane kuma suna shakkan fada min gaskiya saboda su na ganin cewa wai ina dashi nafi karfin su yanzu, Wani irin ajiyan zuciya na sauke tare da dan kokarin juyowa na dan fuskance shi, Ai tuni idona ya ciko da kwalla, hankalin Yaya, Abubakar yadan kara tashi jindayayi ina hawaye, Janyoni yayi zuwa, jikin shi ya kara matse gam yana cewa, Kada kiyi hawaye Meenat, nasan cewa kece kwanciyar hankalina iyanzu, Saboda nadade ina neman mutumin da zai dunga sani a hanyoyin alheri arayuwana, Nasa gefen hannuna na share hàwaye da ke zubo min a hankali , Nace Yaya nadade ina shawaran yadda zan sanar da kai irin bukatar da mahaifan mu ke çiki a gida, Musanman ma Baba Buhari wanda mutane ke maka kallon baka kula dashi don tun ina karama nake ji a na fadar haka, Subbahanallah naji yace haka mutane ke kallo na Meenat nagyada kaina nace kwarai ma yaya don gashi ko dan abin hawa Kakasa saiya mashi don komai nisan guri akassa zakaga Baba yanatafiya zuwa, Innalillahi naji yaya yana ta maimaitawa don da alamar maganar ta daki zuciyar shi sosai har cikin rashi, Abin mamaki sai gani kawai nayi mutum kamar Yaya Abubakar yana hawaye, Yace Meenat, wallahi ban fara hawa abin hawa ba sai da na sayawa Baba mashin amma mama tace yace baison abin hawa indai bashi kudin shi, Kinji dalilin da yasa ban sha,awan saya masu abu sai in bashi kudin Innalillahi nace a raina don nasan sherin Mama Ladi haka, Gashikuma mahaifiyar shi ce ba dama in fada ma gaskiya akai, Don haka nace a fili yanzu ai kamata yayi kasai mashi kabashi hannu da hannu kaji mai zaice, Sai da yai ajiyan zuciya da karfi yace haka za,ayi meenat don mutane su sheda cewa shine bai so Na ansa da cewa kwarai kuwa yaya, hakan zaifi sauki sosai, Ban san lokacin danace nagode kwarai yaya Allah ya saka da alheri, Meeanat ni ya kamata in,gode maki ai saboda kin bani shawaran da kowa ya kasa bani arayuwa na,, Murmushi nayi tare da lumshe idona saboda jin dadin daya Banyi aune ba sai jinayi Yaya na kokarin nemo bakina ban bashi matsalaba hakan , Don haka muka manne guri daya inda muka tsinci kan,mu awani yanayi, Nagane Yaya Abubakar kan shi yadau zafi don haka bazan iya cewa ga irin yadda ya sarrafa ni a ranan ba,
Washe gari mun shirya tsab don shirin tafiya komawa gida Nigeria, Yadda aka lodda kaya ga buth din motan yaya saida ko ina ya shake dam da kayan da na sayo muna tsaraba a Niger, Ina daga gefen Yaya Abubakar ina mai lfahari da mijina wanda duk inda mazaje suka kai zai iya shiga ya ratsa asan cewa ya shiga, Yana saye acikin wani yadi fari mai laushi da santsi dinkin rigar iya gwiwa,hannun shima dan gajeren hannu ne ya kafa wata farar hula mai gashigashi, sai kamshin turare kawai ke tashi a gurin,, Inda nake tsaye Yaya ya kalla ina saye cikin shigan dogon riga baki jallabiya na yafa dan kwallin shi nai rolling din kaina, duwatsun riga na walkiyan blue da fari, Yaya Abubakar ya ce yau na sheda cewa nai tafiya da mace wanan irin tsaraba haka ? Wayan shi ce tai kara a lokacin Aliyu ne anokin shi bayan sun gaisa ne yake sheda mai cewa, mijin Sister din shi da ake jinya a kano ya rasu, Salatin da naji Yaya yayi irin ta mutuwa yasa na maida hankalina gare shi don son jin may ke faruwa, Naji yaya yana cewa yaushe ke nan abin ya faru sai Aliyu ke bashi ansa dacewa, jiya ne a cikin dare, Yanzu haka ankawo gawan shi sokoto, inda za,aimai jana izza, Allahu Akbar naji, yaya fada tare da cewa Allah yai mai rahama, Nima daga gefe na ansa da fadin Ameen Allah yasa ya huta,, Tun lokacin sai naga jikin yaya Abubakar yai sanyi yana fadar Allahu Akbar, duniya bata da tabbas, Haka muka kamo hanyan Sahara desert, babu komai sai yashi da yan itatuwan sabara jefi, jefi, Bamuyi wani nisa da tafiya ba sai na fara jin kamar ban jin dadin jikina , Don haka na dunkule gefen jikin yaya saboda yadda nake ji, a haka barci ya dauke ni, Ganin da Yaya Abubakar yayi barci nake yi yasa shi dan sake murmushi don yasan cewa daren jiya nayi kokari sosai, Don haka yakara gyara min kwanci a jikin shi, don inji dadin yin barci da kyau, Wani gari muka tsaya don Yaya nason ya sai Kilishi da wani abunan da suke sayarwa, Sai a lokacin na,dan farka daga barcin a hankali sai naga aiduk a jikin Yaya na keyin shi,, Cikin yar murmushi yadan dagoni yana cewa Sarkin barci kin farka ko don ba AC, Daga wanan garin bamu kara tsayawa ba sai cikin garin sokoto lokaci yamma ya fara sosai Don haka , muka fara zuwa Yaya yai bucking, din daki shida driver shi, Duk ban jin dadi jikin wani iri nake ji sai daurewa na keyi kawai don ban son, Yaya ya gane hakan, Yaya yadan taboni jin nayi shiru yana cewa yarinya a garin Uncle din ta da Anty, amma bazata kwana gurin su ba, Da sauri yadago kai yana cewa Meenat lafiya kike kuwa, Cikin dakewa tare da langabe kaina nace ina ganin wahalan tafiya ne, Girgiza kansa yayi tare da cewa, dole kiga likita, don ya dubaki, A hankali na dan kara zuke jikina na, nade,sosai guri guda, nace, Gajiyane kawai don ban tafiya mai tsawo haka, shiyasa kawai, badon ya yarda yasa mufita zuwa dakin da ya kama muna, Kamar kada mu shiga dakin sai wani sanyi ya kara taso min a lokaci guda dole na dunkule guri guda, cikin bargo, Aliyu ya nema yazo nan masaukin namu shine yai kokarin samo wanda zai dubani, Likitan kamar abokin sune inda yai dan aune aunen shi ya shedawa yaya cewa gajiyane ya haifar min wanan zazzabin haka, Inajin lokacin da yaya yakira Uncle yana sheda mai cewa muna acimin garin sokoto saidai banda lafiya shiyasa banzo gida ba, Anty taso mu gaisa amma ina barci saboda maganin da nasha,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA [8/12, 05:33] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 5⃣1⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH - AL- MUQEET,,,
Allah da ikon shi, washegari sai na samu sauki kamar bani bace, jiya ba lafiya, Ina zaune inda nai sallah Asubahi, Yaya Abubakar ya shigo hannun shi rike da tasbaha yana ja a hankali, Kafin in masa ina kwana shi yafara yi min da cewa Meeanat ya kika kwana ya kika kara ji ? Na,ansa da fadar Alhamdullahi Yaya naji sauki, ai Ya ce, ashe kaunar tawa bata,son wahala daga yanzu idan zamuyi tafiya sai dai mu shiga jirgi ke nan ko,? Murmushi nayi ina mikewa tsaye tare d nade Sallaya nace, ciwo daine yazo Yaya aikumaya bari, Gado na koma nadan kwanta na dunkule guri guda kamar yadda yaro ke kwanciya cikin ciki, Daga bathroom Yaya ya fito ya samu wayan shi da yasa caji tana kira, Uncle naji ya ce bayan ya dauki wayan Inajin haka nasan cewa Anty Amarya ce zata sa Uncle kira don jin ya jikin nawa, saboda nasan jiya batai barci ba da dadi, Yaya ya cewa Uncle na samu sauki ai don har na tashi nayi sallah, ko, Nan Uncle ke cewa wai kada mu ci abincin hotel an girka muna agidan shi, Godiya naji Yaya Abubakar ya zabgawa uncle a wayan, Nan naji yana fadin cewa bada safe zai wuce ba don yana son tsayawa yayi ta,aziya a nan sokoto don anwa abokin shi rasuwa,, Bayan sun kashe wayan ne ya dan juyo gurina yana taba wuya na don jin zafin jikin nawa, Alhamdullahi naji yace aijikin bazafi, zaki iya tafiya ke nan ko? Gabana ya fadi don jin may yace, don nasan cewa da zaran mun shiga Abuja shi ke nan duk wanan tarairayan bazan samay shi full ba, Mijin mai mata kenan komai na auren mai mata ragagge ne sosai wallahi, Nace su Anty Samira sunji dadin su su kadai a gurin maza jen su, Anty Aisha,ce ma naji ana cewa wai zata auri may mata inda nice ke da zabi ai bazan auri mai mata ba nace a rai na, Karfe tara, da rabi mukabar hotel zuwa gidan Uncle don mu karya, Dakin Anty na,shige na haye gado don sam zazzabin ya takura min sai dai banjin shi sosai sai alamomin shi kawai, nake ji, Antu shigo dakin dauke da nawa kayan a hannun ta tana cewa,a,a kwanciyar kuma kika karayi Meenatu, Wallahi Anty banjin kwarin jikin nawa sam ido ta kura min har dan wani lokaci sai take ce min tashi ki karya ko ? Daidai lokacin da take zuba min ruwan zafi a cup ni kuma ina son mikewa zaune take ce min, May likitan da ya duba ki yace ? Nace cewa yayi,wai,wahalan hanya ce tai min yawa tare da sanyin Ac sai yaja min zazzabi, Allah ya sauwaka tace tare da turo min cup din tea da plate din Irish da kwai soyayye, a gabana, Tea din na dauka ina kokarin kaiwa a bakina, amma sai naji tankar zanyi amai dole na cire cup din da sauri na, aje, Ido anty takara tsura min tace min lafiya cikin dan mararaice fuska nake ce mata, Wallahi sai kawai naji bana son warin milk din da naji, Anya kuwa Meenatu ? Ba ciki kin ka samu ba ? Wani iri naji datace hakan nace cikin shagwaba haba dai Anty don Allah daina zancen nan please, Tace cikin dariya,to na daina na koma na dan kwanta ina cewa Wallahi likita yace wahala ce tai min yawa tunda ban saba ba, Tace hakane fa kuma to amma aida kinci koda kwai ne da dan dankali ko ? Ba don naso ba na kara mikewa zaune a hankali ina yar tsuki gefe, don sam ban san may ke min dadi ba, Ba laifi don na dan ci Irish din da kwai, nacewa Anty barin sha ruwan Lipton zalla ingani ko zan iya sha, Anty tamike da kanta tana hada min Lipton din zallah, Tace min ance wai anwa mijin ku rasuwa a nan gari ko, ? Nace eh haka naji suna magana da Aliyu, mijin kaunan Aliyu ne abokin shi, Wace da ya tashi aure amma Mama ta hana wai yar boko ce, Dama anan sokoto take aure, shine mijin ta ya samu accident, ankai shi kano jinya Allah yai mai rasuwa jiya, Allah ya jikan shi na ce Ameen tamiko min cup din Lipton din na gyara don insha, Lipton din, Tsab Anty Amarya ta gada min kayana ga trolls dina guda biyu, da mamaki na kalli Anty Amarya nace bafa zandade sosai bane anty wanan kayan sun yi yawa ai da arage su kawai, Saida ta gama jan zip tai tsuki tace akai zaki dauka halan ? Sanan ke san ko may zaki iske a can din, yanzu fa ba daga ke sai Sadiya bace, Murmushi na yi tare da kokarin mikewa zaune nace, ai shiyasa surukin ki ya tambaya cewa halan kece ki ka gyara mai ni haka,? Ke Meenat don Allah dai bari namike zaune da kyau na dauki, Irish' guda na jefa bakina nace tun ranan da muka shiga kasan Niger waahegari yake tambayana hakan? Kunya ne ya kama Anty do komawa tayi saman gado tazauna tare da dafe fuskan ta, Nan na dan fada mata yadda muka kwasa da shi har zuwa dawowan mu, sai dain in brief ba gaba daya na fada mata ba, Uncle ne ya bude labulen dakin ta re da sallama yana cewa, maigidan ki yana falo yana magana da ke, Gyalen na dan aza akaina na nufi falon Yaya yana zaune saman kujera one, seater, da waya a hannun shi yana dakila, a hankali, Jin motsin fitowa na yasa shi dago kai ya tsura min ido kamar may son gano wani abu gare ni, Da dan murmushin karfin hali ga idona na karasa gurin shi, zan zauna a kasa yace min come,up, dawo nan kizauna tare da danbubuga min gefen kujerar shi, Kafada na dan make lokacin nakai zaune a kasan carpet ina cewa, nan gidan mune kada wani ya fito yagan mu hakana, Hmmm kawai naji yace tare da cewa to yaya jikin naki ne yanzu, Naji sauki nace tare da dan dago kai na kalli fuskan shi, Uncle ne ya shigo falon da sallama abakin shi yana cewa, nayi magana driver yace gashinan cikin gari zai zo, Sai lokacin Uncle ya, dan mai da kallon shi gurin da nake zaune yake cewa , Uhumm ki rubutawa kowa sunan shi a kayan shi yanzu driver zai zo ya kai masu sakon don kin ga baza mu wuce dashi har Abuja ba kuma, Set set mu kai ta rubuta sunan nida Anty sai da mu kafidda na kowa, Nafitar da wanda na sayowa Uncle da su anty sai hajiya Mama wace itin katon gyalen nan da manyan mata ke ya fawa na sayo mata, Nono Rakumin da cukkui din da na sayo nace ma anty ta aje su anan amma sai tabani gora biyu wai in tafi dasu can, Anty ta nosa tace Meenatu wanan irin tsaraba haka kamar wace ta tafi saudiya, Murmushi nayi nace to anty ai shine daidai tace gaskiya ne kuma, Kasamu kaci da wani shine samu inji Allah da mazon shi, Uncle ya zo tare da driver yaya da wani suka kwashi kayan zuwa motan da zata,kai Birnin Kebbi, Sai bayan tafiyan su ne Uncle ke sheda muna cewa, ai har da kayan masarufi ya tura masu da shi, Sai dai abinda ya bashi mamaki shine su tufafin yace ace wai inji ki, Murmushi nayi shine nake dan ba su uncle labarin yadda akayi sayen kayan, Uncle yace shi yasa yake samun cigaba sosai agurin aiki don kinga shi mutum ne mai gaskiya ga al,amarin shi, Don haka Meenatu, kisan yadda zaki zauna da wanan mutumin, kiji ko nace naji kawu,
****** ********* ****** Ba mu samu wuce Abuja ba a ranan don yan zirga zirgan da Yaya yayi shida Aliyu da Uncle dina, Sai zuwa yamma yazo ya dauke ni wai muje yiwa Fatima kaunar Aliyu da mijin ta ya rasu gaisuwa, Gidan jama,a ne ciki cimjin tako ina, yan uwanta da na maigidan, Aliyu ne yai muna jagora har dakin ta dakin yana da falo amma ita tana can daga kuryan dakin ta, Tafito cikin wani katon hijab har kasa hannu rike da tasba, Ta zauna gefen wata tsohuwa, tana muna sannun ku da zuwa, Mun mata gaisuwa inda Yaya ya jajanta mata tare da mata addu,an Allah yasawa yaranta Albarka, Idon ta sun kode sunyi ja saboda kuka, ta ansa a hankali da fadin Ameen, Aliyu ne kewa wa tsofin ga matar shi nan ai wace malam.tsoho ya hadasu auren gidan, Wani iri naji da yafadi hakan take idon kowa yayo kaina suna cewa Allah sarki tubarkallah Wata daga cikin su tace ai daga nin su jini guda ke aiki don kamar su yayi yawa, Sannu keji ai,ta hakkuri kin ji, zaman aure sai da hakkuri, Fatima wace ta dago ido a hankali ta kalle ni sai kuma ta dan kalli Yaya Abubakar ta maida fuskanta kasa da sauri don, ganin yadda yai mata wani kwarjini,, Wata tsohuwa ke tambayan cewa, daga Abuja yanzo ko ? Aliyu yace Niger suka fito shine ya tsaya suyi gaisuwa, Sai suka kama fadin aiko, angode angode, sannun ku da hanya, Yaya Abubakar yasa hannu ga aljihu yadebo kudi zasu kai dubu hamsi ya aje mata a gaban ta inda ya waiga gurin da nake ya yace muje ko, Na mike na bi bayan su shida Aliyu wanda ke muna jagoran fita daga gidan, Gidan Uncle na koma don wai zasu fita shida Aliyu, Acan gidan Uncle bayan nagama cin abinci mu kadan yi hira da Anty akan irin tausayin da Fatima kaunan Aliyu taba ni, Don muna hanya dawowa Aliyu ke ma Yaya Abubakar hira cewa wai yan uwan mijin dama basu son Fatima, a gidan saboda haka suka sashi ya kara wani aure, Baifi wata uku da auren matar ba ya samu accident din da yai sanadiyar shi,,,