Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 31

Tarko complete novel - Chapter 31

Tarko complete novel Chapter 31: Tarko complete novel Chapter 31. ****** ********** ****** Sam yanzu bata ganewa dodon ta don ya dai yi mata kaman da, da…

3,319 words

****** ********** ****** Sam yanzu bata ganewa dodon ta don ya dai yi mata kaman da, da farko, Irin abinda dafarko yake kawo mata yanzu sam bai kawo wa gashi kuma sai yawan shan ruwa fiye da da, Gurin bokan ta, ta koma tana sheda mashi irin abin da take ciki da dodon ta yanzu, Bayan yan dube duben da yayi yadan yi gyaran murya, yace, Abinda yake samu ga alkawarin da kikai may yanzu ya daina samu shi, Don kin ga da farko a koda yaushe, yana samu abubuwa irin yadda ya kamata, Amma kuma yanzu sai yai kwana ki da dama bai samu abin da kikai masa alkawari ba dashi, Shiru tayi don ba abinda yazo mata arai sai mugun tsohon nan da ya hanata shakat Watau malam, tsoho, wanda take ganin cewa shine wanda yai mata karan tsaye ga al,amurorin ta, Dole ne fa tasan abin yi kafin ya kai ta ga makara don idan har tabari ya kai ta bango to asirin ta zai tonu ne , Malam boka yace banda wani abinda zan iya maki a halin yanzu sai dai kawai ki yi kokarin aiwatar mashi da bukatan shi, Sosai zuciyar hajja ya sosu don hankali tashe tabar gidan boka zuwa gida don gudun kar dodo ya bukaci wani abu bata a gida,

Bayan ta dawo gidane ta yanke shawaran zuwa gidan Mama Ladi, don tun,da ta dawo bata samu zuwa, gaishe ta ba, Sai yau da take da bukatan zuwa don jin halin da gidan na dan ta ke ciki watau gidan yaya Abubakar Tafe take,cikin shigan zani da riga inda tai mayafi da irin zanin da ke ajikin ta daure, Malam tsoho wanda tun shigowan hajja uguwar nasu, jikin shi yabashi cewa akwai mugun abinda zai faru, Bala babban almajirin shine yakira yace ya samo mashi rushin wuta da sauri, Acan cikin gida hajja na shiga kafin ta kara,sa sashen mama ladi Sukayi kicibis da matan gidan zaune a karkashin iccen darbejiyan da ya sake masu innuwa a gidan, suna zaman hira a gurin

Atake Rakiya matar Baba Hamza taji kanta yai wani sarawa alokaci guda, Take tafara ganin guri yana juya mata a hankali hankalin ta ya fara gushewa daga jikin ta, Wani irin ihu, ta sake a lokaci guda tare da mikewa tsaye, Duk wanda ke acikin gidan malam tsoho alokacin da kewaye sai da yaji wanan ihun na Rakiya,,, Gurin hajja Rakiya ta nufa tana cewa ku yi ta kanku wallahi ga diyan macizai nan da kan kare suna lasan jikin ku, Ai take mata suka sa ihun gida ya rude, wayyo Allah Innalillahi, A,uzubillahi, Hajja dole ta ja tai tsaye jikin ta sai rawa yakeyi, don kaduwa, Wuyan ta, Rakiya matar Baba ta, riko dukk idon Rakiya fito waje sai wani yare takeyi, wanda ba wanda ya taba, jin tana wanan yaren, a duniya, Da guda aka kira mazan da ke kofan gida don su kawo a,gaji,,, Mama Ladi tafito daga sashen ta tana ta masifa wai an wa kawar kazafi don ana bakin, da ita Ba wanda ya kulata sai kokarin ganin an banbari Rakiya daga jikin Hajja, Saidai jama,a duk sun kassa banbaranta daga hannun Rakiya, Daga bayan Mama Ladi akaji kuwan anty Mariya cikin wani irin ihun tashin hankali wanda duk ya kara ruda gidan, Sai ihu takeyi tana çewa wayyo Allah ga sunan suna shiga jikin ku suna lassa, Take guri ya kara rudewa da tashin hankali,saboda, yadda Anty mariya take ihun baida dadin saurare sam,

Malam ne yau ya tako da kan shi har zuwa cikin gidan sashen sarakunan shi, Wani abu ya yarfawa tarun jama,an dake gurin gaba dayan su,, Wani tsawa malam ya dakawa mariya da Rakiya, Bala daga bayan shi ya zuba wani hayaki a rushin wuta gaba daya wanda ke gurin ya fara atishawa,, Sai a lokacin Rakiya ta dan sassauta rikon da taiwa Hajja, Malam ya tako har zuwa garesu bakin shi dauke da addu,oin tsari, Cikin tsawa fuska a daure yace Rakiya ku sake mata wuya nace Ba mussau aka sake Hajja wacce idon ta duk yafito, waje saboda wuya,, Tana batun gudu malam tsoho ya daka, mata tsawa yace dakata kiji Cikin daure wan fuska malam ya kalleta abinda yasa hajjin cikin Hajja kadawa, Don sai tana ganin cewa malam zai tona mata asiri ne sosai, Ciki kadu malam yq ce ke, saurara ki ji may zan fada maki, Kinyi babban kuskure da har kika shigo gidana da nufin sheri, Kai Hajja ta kada alamar a,a Malam tsoho yace bari kiji ni Abubakar Sambo Manya, Mugu ko muguwa bazai taba shigowa gida na har gurin iyalai na ya wanye lafiya ba, Ko ina a raye ko a mace mugu bazai taba samun nasara a gida nan, ba, Kai ko a makwabtana balle har cikin gida, na ke ki sani cewa, ba yau ba nasan cewa ke muguwa ce ta sosai, amma da baki tabani ba sai ban taba ki ba,, Yakara kallon ta rai bace yace, daga yau kada ki sake ki kara shigo min gida cikin iyalina, Fice ki bamu guri muguwa kinji kunya kirasa inda zakiyi sheri wai sai wanan gidan, Simi, simi Hajja tabar gidan batare da ta waiga ba saboda tsoron malam din, Kafin wani lokaci har labari ya karade unguwa da gari baki daya cewa hajja mayya ce wai, Mamaladi duk jikin ta yai sanyi saboda abinda ya faru da aminiyar ta, Sosai yau tai nadaman zama da Hajja duk da ziciyar ta, na ce mata kazafi akai wa Hajja, Abu guda ke sa ta gaskan ta zancen saboda tunda ta haifi Mariya bata taba sanin cewa tana da iska ajikin ta ba ,sai yau, Wanan dalilin yasa Mama ladi ta dan yar da da sherin Hajja, Baba Buhari ya,shigo gida yana ta masifa da Mama cewa duk gurin kwashe, kwashen ta ta hadu da Hajja da ta zama masu matsala,, Gashi har kin yi sanadin hada zuri,a da ita yanzun haka kike son diyar ta ta haifa muna jikoki a gidan nan, ?

****** ********* ****** Sai dare muka shiga kasan Niger din,wani babban, hotel din da a kasan aka kama mu na, Direct, can muka nufa saboda duk sauran abokan tafiyan nashi suna a hotel din, Ko ina haske ne ya haska farfajiyar hotel din gwanin ban sha,awa, Tafe muke muna takawa guda guda, saboda steps din da akayi gurin shiga cikin hotel din, Duk wanda muka wuce sai yadan kara waiga mu saboda yadda mukayi kyau gashi kuma abu ga jini kamar mu guda da yaya Abubakar din, Muna shiga dakin wayan yaya Abubakar a na kiran shi a lokacin, Don haka yadan tsaya daga shigowa dakin, abinda na fahinta shine daya daga cikin matan shine yake waya da ita,a lokacin, Don haka na kara,sa shigewa cikin dakin, inda a hankali na ciren gyalen abaya na da na yafawa kaina, Saman gadon dakin na aje gyalen, a hankali nake kwabe abayan da na a,za saman kayana, Ya Abubakar wanda ke waya ina ganin how happy he's, Is ,, a lokacin, Tufin dana saka daga ciki wanda yadan matsen min jiki yai min kya surar jikina suka fito filli, Daga gurin da Yaya ya,ke tsaye ya lumshe idon shi don ganin irin yadda na koma a idon shi Mikewa nayi na jawo yar jakar da nazo da ita na fidda zanin daurin da nazo dashi da hijab, Yaya yaci gaba da kallona yana mai mamakin yadda a lokaci guda na juya na caza zuwa wata classic lady, Nai mashi wani irin kyau ga fuska,ko ina nawa ya ciciko a murje na yi wani fresh fatana sai sheki yakeyi, Lumshe idon shi ya karayi daidai lokacin da na fada bathroom din dakin, Wanka na yi don inji dadin jikina tare da dauro alwala don in gabatar da sallolin dake tare dani, A kwance na samu Yaya saman gadon dakin yadan kishingida kafan shiguda na tokare, fuskan shi na kallon kofan bathroom, Daurin zanin gaba nayi hannuna yana dauke dakayan da na cire a jikina, Yaya ga ruwan zafi can na hada maka, a bathroom, Bai amsa min ba sai wani irin kallo da yake min cikin mamaki, yana wani lumshe idon shi a hankali, Don gani yayi na yi mai wani irin girma a idon shi harda kiba, Duk wani abinda yake bukata ga irin macen da ya dade yana son ya mallaka a gidan sa ya baiyyana a jikina, Ganin da nayi cewa bazai bani ansa ba, kawai sai nafara war,ware hijab dina don in ta da Sallah, Alokacin ne naji muryan Yaya Abubakar yana cewa may yasa baki jirani mun shiga tare ba,? Murmushi mai sauti kawai nai masa batare da nai magana ba na tayar da Sallana kawai, Har zuwa lokacin da na kusa sallamay wa na,ga ya mike zuwa wanka, Bayan ya gama muna Odan abincin da zamuci daren da muka iso,,, Bayan na idar da sallah ne na mike tare da dan, gyara muna kayan mu, inda na zuba su cikin, Wardrobe din da nagani a dakin na nufa na sa kayan mu a ciki, Sai na fitarwa yaya Abubakar, wasu simply kaya don ya saka ajikin shi idan ya fito, Rigace mai yar guntun hannu da wando tree quarter, na samu acikin kayan na shi Suna fitar mai don ya saka idan ya fito daga wanka,na kuma feshe mashi su da turare, Dago kan da zanyi ashe Yaya ya fito, yana zaune a bakin gado daure da towel, sai wani dan karami, da yake ta gugan sumar kan shi da shi, Idon shi na akaina duk lokacin,, Kayan da na fitar mai su ya saka ajikin shi bai wani bata lokaci ba ya ta da sallah, Nagama gyara jikina tsaba yadda ya kama ta batare da na bari ya gane may nakeyi ba, ba, Daga gurin da yake zaune yana addu,a yadan waigo yana ce min, ki saka hijjab dinki don ga wani nan zai shigo ya kawo muna abinci, Bamusu da sauri na saka hijab dina akaina, na koma can bayan gefen gado nadan zauna, Wani buzu ne ya shigo bakin shi dauke da sallama, A binci ya kawo muna wanda ke dauke da abinsha mai sanyi, Abincin ba laifi don tankarka kalan namu na Nigeria,

ZEEE MAKAWA YELWA,,,, [8/11, 05:43] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 5⃣0⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL-HAFEEZ,,,

Jumma,at Mubarak,,,

Shafin yau na kine ke ka dai kuma bada kowa ba SADIYA SIDI MARUBCIYAR, SIDIYA, Nagode da irin kaunar da kike gwada min,,,,,

Bayan mun karasa, cin abinci ni da kaina na gyara gurin na kawar da kayan abincin a can gefe, Hand bag dina na bude na ciro daya daga cikin Sweet's din da Anty ta sayo min masu kamshi, nasaka ga baki na, Wayan Yaya Abubakar yai kar da alamar daga cikin abokan tafiyan shine suke waya, Nikan sai da na kara kakabe gadon sanan nazauna ina gabatar da addu,oina kamar yadda na saba yi, A hankali na kai kafada na saman katifa saboda gajiya, na dan lumshe idona tankar mai barci, Tunanen matan Yaya Abubakar ne yazo min a rai yadda akayi baizo da dayan su ba mussanman ma amaryan sa, Nai zurfi ga tunane ban san cewa Yaya ya gama wayan shiba, Yana zaune a gefena ya kura min kyawawan idanun shi, Duk duniya ya fahinci ba macen da zai gani yaji sha,awan ta ya motsa mashi, kamar wanan yarinyar, Sai yanzu ya gane cewa komai na Meenatu daban yake da na sauran matan shi, kai dan das da shi gwanin sha,awa, Muryan shi kawai naji gab da kune na yana ce min, Meenat, nayi rashinki da yawa atare da ni, Firgigit na bude idona adan tsorace, Ashe gab yake dani kwance, idon shi sun canza kala zuwa wata irin muguwar sha,awa, A hankali na dan motsa dan in gyara kwanciya na alokacin, A hankali, naji hannun shi kuma a jikina yana wasu maganganu da zan iya cewa bai san may yake cewa ba ma, Wani irin mahaukacin soyayya ya gwada min ranan, Don duk yadda nake tsan manin cewa, yai amarya bazan samu wani doki ba sai gashi ya ma fi kullun, nuna min, duki, Don irin yadda Yaya ya gwada min ban san da cewa ana iya yiwa mace shi ba, balle ma shi da nake ganin bai dauki mace a wani matsayi ba, Sai kusan asuba nasamu Yaya ya sarara min nai barci, Daga ni har shi sai da muka makara ga sallah asuba ranan, Sai dai shi ya rigani tashi don haka sai da ya tabbatar da cewa na tashi sanan ya kyale ni, Sai da na idar da sallah na mike zuwa gaban mirror dake dakin ina gyara jikina, Zuciya ta fam da tunanen iri, irin, yadda Yaya ya canza min sallon soyayya, Shin kodai harda shawaran da Anty Amarya taba ni da cewa ni ma in gwada mai nawa, sallon, Murmushi nayi tare da dan rintse ido na ahankali ina anyana cewa mutum mai mata biyu, zaiyi wanan irin abu haka, Muryan Yaya Abubakar ne naji daidai satin kunnuwa na yana cewa my queen, Ya gajiyan hanya da na Yayan ki ? Murmushi kawai na sake mai tare da cewa sai hamdala, duk ka biyun, A can cikin kunni na ya rada min a hankali, Anty ce ta kara gyara,min ke ko Meenat ? Dif na dakatar da murza turaren da na keyi a jikina tare da dan sake murmushi, kadan, Mikewa yayi tsaye daga dan rankwafo min dayayi a kafada na, Jin ya mike a bayana yasani sauke dan ajiyan zuciya tare da dan lumshe ido na, Azuciya na nace No Wander, nasha wuya jiya hannun Yaya, Ashe yaji abin da yaji ne ajikin nawa, Idona na lumshe a hankali ina cewa a raina watau wanan gyaran da su, anty ke tamin da gaske yana da amfani ke nan, Mikewa nayi na shirya tsab cikin wasu, tsaddadun material dinkin riga, da skirt, a kai masu ya dan matse ni das don mazauna na sun fito tsab daga cikin shi, Dan kwalin su na daura a kaina sai dan kitson kaina da yadan fito da ribon din kai na, waje kadan daga baya, Wasu plat shoe's Anty ta sayo min don in hada su da kayan, Dan karamin gyale na, yafa a kaina , tare da kara shafa kamshi a jikina Saboda naji har malaman addini na cewa kamshi yana kara kauna tsakanin mata da mijin ta sai dai ban shafawa, a gurin da nasan cewa zai min illa kama saman nono, karkanshin nono da saman gashin kaina, saboda gudun cancer, Zaune Yaya Abubakar yake a bakin gado ya gama waya da masu kula da abincin mu, A hankali nake takowa har zuwa inda yake zaune ya tsura min ido, har na karaso gare shi, Gefen shi dan tsuguna har kara tare da dan dafa gadon da yake zaune akai, nace, Ina kwana Yaya ? Murshi yayi tare da dan kamo hannu na namike tsaye zuwa jikin shi ya zaunar dani a saman cinyar shi, A hankali yace Meenat ki karya ki kwanta ki huta kinji nasan cewa daren jiya ban kyauta maki ba don kina tare da gajiya kuma ban sarara maki ba,, Murmushi nadan sake ina mai dan dukar da kaina nace, Yaya nifa matar kace dole ne inyi hidimar ka duk sanda ka bukaci hakan daga gare ni, Murmushi yayi tare da dan rausaya kan shi azuciyar sa yace lalai meenat ta,sake ga yadda ya san ta, A hankali ya kai min kiss a goshina yana mai cewa Meenat ina mai alfahari dake, Meenatu, Nasan cewa iyayyen mu sun, muna hadin mafi, alheri a rayuwar mu, Fatana mu zauna lafiya, a tare dan, su kara alfahari da mu arayuwan su, A, hankali na ansa da Ameen ya Allah, Ranan kafin su fara fita abinda yakawo su haka na zama mai shagwaba, da wani irn langabewa, Take yaya duk ya wani bi ya susuce ya koma tankar karamin yaro,,,,

****** ********* ****** Rayuwa ke nan a yayin da muke kasar Niger Republic da Yaya Abubakar muna jin dadin rayuwan mu, Sai dai kuma iyayyen mu suna can a cikin halin, haula,i Don abin duniya ya kai ko ina Saboda rashin wadda ta da talkawan kasa ke a ciki, Don a bangaren mahaifina yar akwalar motar da mahaifina ke neman kudi dashi ya ja ya tsaya saboda tsufa, Sai malam tsoho ya taimakawa iyayyena da dan abin sayen abinci, Wani lokaci kuma sai Yaya Ibrahim ya dan je ya samu yunwar haya ta yar vespa, ya dan yo cefane, Shikuma Baba yakan tafi ya samo aikin karfi ya samu kudi, A cikin haka kuma yake tallafawa Baba Buhari don sai yake ganin ya fishi dan hanyar samu,wadata, Sam.iyayyen saboda irin tarbiyan da suka samu daga mahaifin su malam tsoho basu taba damuwa da cewa Dan su yana acikin waddata yaki ya taimaka masu, Sam basu sa rai ga dukiyan dan su ba balke ni mace wace auren shi kawai nake yi, Mutane ne kawai yan gani da dauka kan,ce Mama Ladi ta hana dan ta ya taimakawa mahaifin shi dan uwan shi, Wasu kuma sai suce daga dai Yaya Abubakar din ne baida halin kyauta don rayuwan turawa gare shi, Ance gidan shi ma wai idan ba notice ka tafi baza, a baka abinci ba, Kuma ba,a bari ma ka shiga cikin gidan sai dai wai mutum ya koma, Wasu kuma su ce wai baidai da halin yin alheri ne , ko kuma su ce bai samu matan kwarai wace zata dinga bashi hawara ba, shi yasa bai damu da gida da dangin shi ba, sam,

****** ********** ****** Izuwa yanzun mun kusa kai sati biyu a Niger, don aiki sosai su Yaya ke yi acan din aiki na tsakanin kasa da kasa, Yau ma kamar kullun ya,dawo da wuri daga gurin aikin saboda yana son mudan shiga garin muyi tsaraba kamar yadda na ce mai, Don ni yanzu na fara fahintar shi Yaya Abubakar mutum ne mai I don't care attitudes, ko a kansa balle wanin shi, Don haka nakan yawan jin yana waya da amaryan shi wace ina zaton bata san cewa tare muke da yaya ba kasan Niger din Takan yawan ce masa ya sayo masu tsaraban Niger, Ganin bai damu ba yasani cewa, idan zamu wuce zan shiga garin mu sayi tsaraba, Shaddodi masu kyau da tsada muka saye na mata da nashi sai kuma dinkankun kaya wanda suke har kasa sun sha design masu kyau wasu kuma zani da rigane hade, Wasi shago naga kayan suna da sauki don haka dan tsaya ina son inji saukin price din su, Daidai bayana Yaya Abubakar yadan dawo yana cewa har yanzu shadda basu isheni bane, Kai na langabe ina cewa wanan dinkin yaimin kyau a fuska ina son a sai wa malam tsoho ne yasamu na zuwa jumma,a, Murmushi Yaya yai min tare da cewa ai sai ki zaba mai ko? Kai na kara langabewa nace to Yaya idan da hali ai da ka sayawa su Baba don da wuya asamu irinsu acan da saukin kudi haka, Ba musu Yaya, yace idan zan iya daukan kaya ai Bissimillah ko ? Kaloli masu kyau na zabawa duk iyayyen mu maza gar Baba wadda, Azato Yaya zaice min kayan sunyi mashi kudi da yawa sai kawai naga ya biyya batare da wani gardama ba, Mamaki ne fal a zuciyana ina tunanen nafara sanin wasu daga cikin bahagon halaiyar shi da mutane basu gane, ba, Don tun ina karama nakan ji malam tsoho yana cewa Abubakar ai bahagon mutum ne, mai murdaden hali ,,,, A kasuwan na ga nonon rakumi na sayo su da yawa na kuma sayo chikwi da dabino da sauran kalar abinda bamu dashi a kasar mu, Ranan a gajiye muka dawo daga kasuwan sai korafi yayake min wai duk nice nasa shi yin wahala, Murmushi kawai nayi nace yaya aikin lada ne fa mukatsaya yi sai yakan ce min sai kuma akace a,wahala ko ?

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull