Tarko complete novel - Chapter 36
Tarko complete novel Chapter 36: Tarko complete novel Chapter 36. ****** ********* ****** Yau Anty Samira tun da safe take tashirin zuwa gida don ta wuni,…
3,212 words
****** ********* ****** Yau Anty Samira tun da safe take tashirin zuwa gida don ta wuni, Cikin ta zuwa yanzu ya fito sosai don haka, da ka ganta zaka san cewa ta kusa haihuwa,, Dan vesper tashigo daga Badariya zuwa unguwar su shiyan Sarakuna, Sai dai mai yar vespan ya kasa karasawa da ita har cikin uguwar nasu saboda yawan yashin da ke shiyan sosai, A hankali take tafiya da kafa don ta karasa gidan su, Baba Buhari saman sabuwar mashin din shi sabuwa fil, da ita, Tun daga nesa Samira ta hango Baban,azuciyar ta ke cewa kai Allah sarki Baba ho ko ina kuma ya samo sabuwan mashin haka ? Shikuma Baba ya hango diyar nashi wace ke tafiya guda guda don nauyin ciki, Cikin dan murmusawa yace a,a Samira ta? Ta amsa da fadin Ni ta Baba, Mun samay ku lafiya ko ? Wallahi Samira lafiya kalau Yau naka batun zuwa shiyan ku in gwada maki abin arzikin da Yayan ku ya sai min, Ido Samira tafitar tana iye Baba shin ka dai ince mashin dinga taka ta ? Samira Yayan ku ya sai min ita yau kwana uku ke na, A,a lailai kan Baba mun ko yi murna wallahi, to ki buga mai ki mashi godiya ke ji, Yace zan tafi inyo cefane a can yar kasuwa, Anty Samira tace Baba a dawo lafiya Allah ya tsare,, Ya ja mashin din shi Samira ta bi mahaifin su da kallon tausayi , Azuciyar ta ce Baba mutum mai saukin kai wanda ba ruwan shi da girman kai, A dan gajiye halin irin na masu ciki Samira ta karasa gidan su, Sai da ta fara gaida malam tsoho, wanda ke waje da jama,an shi, Inda yake ta mata ba,a akan cikin ta tare da tambayan lafiyan maigidan ta da jama,an gidan su, Sai da tafara zuwa sashen mama Saratu ta gaida su tare da sauran mutanen gida, Gurin Mama Sa,a tafara shiga kafin ta karasa gurin mahaifiyar su, Cikin fara,a da jin dadi Mama Sa,a ke cewa a,a lalai marhabin da mutanen Badarriya, Samira ke ta kikai nauyi haka ? Gaskiya tubarllaka ciki na miki kyau, Dariya Samira tayi tana cewa kai Mama ho, takau da zancen da cewa ashe Baba yai sabuwar amarya na ? Dariya suka gaba da yan su atare Samira tace Allah yasa a more, Ameen inji Mama Sa,a tace ai,dada fa huntuwa tayi zani, Dariya Samira tayi tana cewa ai yanzu sabuwan bazawara zata lake mai, sai tashigo, Mama Sa,a tana dariya tace tazo aiga gidan nan gwalmaddiya,i, Allah dai yakara daukaka Abubakar yasa amorewa saura Ameen inji Samira ta saikai tafita zuwa sashen Mama Ladi,, Sanan ta karasa sashen Mama Ladi a gajiye ta jawo kujera yar tsuguno na mata da ke gefen dakin Mama ta zauna, Tana cewa wasshi Allah walle duk nagaji sai kace da kafa nai tafiya, Mama Ladi wace ke zaune saman tabarma a kofan dakin ta tamike kafan ta don taji dadin zama, Ta ce wa yar nata yau kuna kun ka tuna da mu, Samira tace Mama yanzu banjin dadi komai wallahi ko dazan tashi kafin a ce haka komai ban yiba sai dai dare yayi, Mama Ladi tace me munafukanga ka fada maki ? Naji ta tun daga can tana ta tsiyaya adole taji dadi sun samu mashin din banza sai atai zuwa hawa yanzu ai kiga zuwa anguwa ya tashi, Dariya Samira tayi tare da kada kai tace mama in kina so aikema goyaki zaiyi, Allah dai ya sauwaka min, min zanyi saman mashin da malam Nan suka fara gaisawa Samira tana tambayar lafiyan jikin Mama, Sai kuma Mama Ladi ke cewa shin wane shiri kin kayi zuwa yanzu akan haihuwan ki ? Mama shirin mizanyi haihuwan farina fa zanyi, ? To, nan kin ka labe ko ? Kina jiran aimaki? To Mama mi zanyi, nawa nake dashi nida ba ni aikin komai, Har za,a sa ran, a samu wani abu gurina Mama ? Cikin daure fuska Mama Ladi tace ke tsaya kijiya keji, Inkina kawa abinda aggareki ki kawo aba yan uwan ki su kara suyi maki soye,soye da shi, Take Samira fuskan ta ya matse a lokaci guda don tasan cewa maganar gaskiya Mama Ladi tafadi abinda tace shi din za,ayi, Samira rayuwan ta yabaci matuka inda tafara fushi tana cewa yanzu ya akeson inyi banda kudi kuma shi ba aiki ya keyi ba, mama kin sani, Rayuwan Samira abace yake, har akai sallah zahar sai fushi take faman yi taki sake jiki ta, Daga inda take kwance tunanen Yayan ta fado mata, arai sai dai kuma zuciyan ta na tuna mata lokacin da yayanta ta Safiya ta haihu, Alokacin ya,na aiki a Lagos da ta buga mashi waya tana tambayan shi, akan ya taimaka mata da abinda zasu yi dawai niyar buki, Amma sai yace sai mama ta kirashi ta fada mai saboda ya na shakar ya bata mama tai masa fada, Don haka Mama ya turo wa, da kudin da ta nemi taimakon, Ita kuma Mama ta kuma karbi, na hannu Safiya ta hada batai mata koma ba,, Shiyasa take tunanen cewa ita irin na Anty Safiya ake son yi mata ke nan, Taso sai da yamma ta koma gida amma saboda zancen da mama ta tare ta dashi yasa ta komawa gida da karfe uku, na rana, Tanan har dare bata iya yin wani abin kwarai ba tana ta faman tunanen irin mahaifiyar da Allah ya basu, Yanzu ita yaya zatayi da wanan zancen gashi yan uwan ta kowa tana fama da laluran rayuwan ta, A take wani tunane yazo mata a zuciyar ta wanda taje ganin gara ta gwada taga sa,an ta,,,,,,,
****** ********* ****** Zaune nake a bakin Mirro na fitowa na ke nan daga wanka, ina son in shirya in, fita falo kafin mai gidan ya shigo,, Kasancewa yau nice da girki duk abin ya bani mamaki kwarai don kusan tare da Anty Sadiya mukai aikin, Don ita ce ta gyara min falo acewan ta banda lafiya bari ta taimaka min da aikin, Waya na dake caji saman mirro gefe guda dan nisa kadan da gurin da nake zaune, Da sauri na mika hannu na dauki wayan Anty Samira nagani baro, baro a saman screen din wayan, Da sauri nadauki wayan cikin murna da jin dadi ina cewa sai Anty na, Ta,ce a,a wallah wace Anty bayan an manta damu, Nadan tausa murya tare da langabe kai tankar tana gani na, Nace a,a fa anty Samira aiko dai kin san ina da kokarin bugo maki waya, Anty Samira tace yaushe rabon da ki bugo min waya Meena ? Anty keep n san munyi tafiya da yayane wallahi bamu kasan mun tafi makwabta, Kuma koda muka dawo wallahi ban da lafiya ne anty da fever na dawo , To na dai jiya yanzu ya kuke lafiya Anty, Takara tambaya keji sauki dai ko ? Nace insha Allahu Anty, Sai kuma tai shiru can na ce Anty ya Yaya Munbashir ? Tace yana lafiya, Nace to yaya tsufa Anty ? Sai naji ta nisa tai shiru kuma can tace cikin wani irin murya mai sa mutum yanayi, tace, Meena ke dai san halin Mama ba sai na fada maki komai ba, Wai zancen kayan haihuwa ne yau mun ka kwasa da Mama tace wai sai na kawa kudi sanan za ai min GARA,,, Uumm,Ummm nace itakodai mama ina zaki samo kudi hakana ? Nace, yanzu anty yaya za,ayi ga yan gidan mijin nan naki basu da mutunci, Kin san na aure ma har ankai wani lokaci suna gori akai, Ta nisa tare da cewa bari kedai Meenat shiru muka yi zuwa can nace Ke fadawa yaya ne ? Cikin wani irin dan ihu ta ce, wacce ? Niya, ? Barni in mutu ina Samira na, Baki san yadda akayi dashi ba lokacin haihuwan, Anty Safiya, Na katse ta da cewa kinsan yadda za,a yi zuwa karfe takwas daidai ki bugo waya kada ki bari a wuce takwasa din kinji Anty, Tace cikin jin dadi to Meenat nagode nagode kinji, Haba dai Anty may na godiya Allah dai ya sa mu dace, Mun kashe wayan zuciyana duk ba dadi saboda, irin abinda Anty Samira ke fada min Abinda nafara yi shine jin haushin wanan irin al,ada na mutanen mu na kashe zarahi, Abu tun iyaye da kakan ni har zuwa yanzu yaki mutuwa, Sai ma kara yiwa abin kwas kwarima da aketayi yanzu, Sai kuma Mama Ladi wace ban san wani irin rayuwa gareta ba da har da diyan cikin ta take ma mugun hali, Mikewa nayi naci gaba da abinda na keyi don gyara, ko ina ,
****** ********* ****** Tsab na gyara jikina acikin wani material purple mai dan design din flower light, chuculate, Dinkin, riga da skirt akai mun, dan kwalinshi yana da sulbi sosai don haka daurin danayi mai sai yai kamar style nayi, Dan hill shoes kamar kullun na saka ma kafana, Don ance sa takalma mai dan hill yana kawo wa mace hip's, Mai mai kamshi na dan murza na daga rigana na shafa kasan nono na da sama har zuwa hamatana, Dama na feshe kaya na da turare masu kamshi da dadin shaka, Daga dakina naji tsayawan motan yaya Abubakar hakan yasa nasan yadawi daga sallah ke nan,
Fitowa na yai daidai da shigowan shi falo Salawtu, tana zaune a falo ta kurawa kofan shigowa ido, Wani irin muguwan harara ta sake min tare da nuna kishin ta gareni filin Allah, Murmushi dauke a fuskana na nufi hanyan shigowa ina cewa, Sannu da dawowa Yaya,? Ina kokarin karban brief case din dake hannun shi, Murmushi ya sakar min har a cikn zuciyar shi yaji dadin ganina haka ? Daga inda take zaune take cewa you are welcome oga, How are you my dear ya amsa mata, Batare da ya tsaya, falon ba ya bi bayana alokacin na fara hawa steps din hawa saman shi, Wani uwar harara Salawatu tawatsa min tare da sake tsuki tana cewa yeye girl, You will know my true clour soon, Murmushi nakeyi daga infa nake ina cewa sai kace ba renon anty Amarya ba,,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA [8/14, 09:06] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 5⃣3⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH - AL-JALEEL,,,,,
Already na riga na gyara mashi dakin sai kamshi ke tashi ta ko ina, Na,wuce gurin side drower, na aje yar briefcase din a hankali, Yana tsaye da ga kofan daki ya harde hannayen shi, kafafuwan shi ma a harde suke guri guda, Wani irin kallo yake min cikin nuna so da kauna acikin wani irin yanayi, Shidai har kull bai gajiya da mamakin irin yadda halittuna suke, Duk da wai wasu mutane kecewa muna da kama dashi sai dai tsayi ne da ya,ke shi namiji ne ,, A hankali na nake takawa har zuwa gurin shi,, Kafin in karaso ya ware hannayen shi biyu na shige ciki, Wani irin ajiyan zuciya naji yana saukewa ya fadi a hankali miss you sweet sister, Kara shigewa nayi cikin farfadan kirjin shi da yai min masauki dashi, Kamshin jikina naji yafara shaka yana wani lumshe ido kamar wanda ke cikin maye, Bakina ya nemo ya manna nashi a ciki abinda ya dan jawo min rawan jiki, Don ni har kullun jin Yaya Abubakar nakeyi kamar sabo a gareni, Yaya Abubakar din shi dayake tsohon hannu ne yana sane da irin re,action dina kullun, Hakan ne ma yasa yake kokarin ganin cewa ya kawar min da kunyan shi gaba daya, A cikin yanayin da muke ban aune ba sai jina nayi a saman gadon dakin Yaya Abubakar Bayan komai ya lafa a tsakanin mu a hankali na mike zaune ina kokarin saita kaina, Shiko ya Abubakar din mirginawa yayi gefe guda yana sauke numfashi a hankali, Zuciyar shi fam da tunane, Murmushi yayi irin mai ma,anan nan yana cewa hmmm,Meenat,,,, Wayan shi yai kara a daidai lokacin da nake kokarin mikewa don shiga bathroom in hada mai ruwa, Ji nayi ya jawone da hannun shi guda abin da yai sanadiyan nadan fado mashi a jiki, Ganin kiran wayan zai katse yasani mika hannu na dauko mashi wayan, Samira nagani an rubuta, don haka na mika mashi tare da cewa Anty Samiran gidan mu ce ke kira, Yaya Yar tsuki yayi tare da magana acikin yanayi yana cewa, May kuma ya faru take kirana, Da sauri ina kokarin tashi zaune, bakin shi na fidda tsuki ya dauki wayan nata acikin wani irin murya, Samira Yaya dai ? Ita kuma bayan sallama tana cewa Yaya ina wuni, A hankali natsuwan shi ke dawowa ajikin shi don haka na zauna bakin gado inji yaya zasu kwashe da yar uwan shi, Jina yi ya ce, look Samira, ni maye nawa a,ciki, ba Mama ce ke gudanar maku da wanan harkan ba, Da,sauri na kalleshi, muka hada ido sai na canza annurin fuska na gaba daya na hade rai, Anty Samira dai bata gane komai ba sai yar fadan da ta samu, sukayi sallama, Ban taka masa ba sai mikewa nayi zuwa bathroom na hada mashi ruwan wanka, Nafito ban tsaya,ba fuska a dan daure nace ga ruwan wanka can Yaya, Gurin Wardrobe din shi na nufa ina son in dauko mai kayan da zai sa, idan ya fito, Daga inda yake,tsaye, yake ce min, bazan samu cudawa ba ke nan, Gurin gado na nufa na,fara gyara,gadon don duk mun chukwikuye shi kamar bashine na gyara dazun tsab ba, Ya,shige bathroom ni kuma na fito zuwa, daki na don in kara kintsa jikina saboda Yaya ya bata min shiri,
Salawatu bayan shigan mu, takai yan mintuna zaune a falon taga ai ban sauko ba, Don haka sai taji tankar ta kama da wuta don haushi, kishi nata azalzallar ta, Kusan sau uku taje ta dawo, taje ta dawo don taga ko na sauko sama, Abincin dake jere a saman dining table tariga da tun shigan mu tai masa ta,asa, ko, Wanka na shiga na gyara jikina tsab, kamar bani bace, dogon riga na sa wanan karon, Misscalle din Anty Samira na samu har uku, ta kirani don haka na,dauka ina ce mata, ta ai ina gurin naji yadda su kayi amma ta bari zan kirata insha Allah,, A gurguje na fito falon fuska hade don yau kan gaskiya mun makara sosai ba mu ci abinci ba, Anty Sadiya bata wasa da cikin ta tana falo zaune, tana jiran fitowan mu tare muka fito da maigidan don zan shiga kitchen naga saukowar shi, Jug na,dauko wanda na hada muna zobo,drinks a cikin sa, Salawatu ce karshen fitowa fuskan ta tamau, ba bu walwala a cikin sa, Ni dake da girki nice zaune a kusa da Yaya Abubakar, ina zuba mai abinci a plate, Sadiya itace tafara cin abincin tana kai cibi a baki sai tai saurin furzarwa, Cikin wani irin murya na mamaki tace Meena, ? Tana mai min wani irin kallo, Abincin na kalla sai kuma na,dago ido na kalleta, Kafin in sauke idona sai naji Yaya Abubakar daga gefe na ya furzar da nashi wanda ya fara kaiwa baki, Yaya akayi haka ne wai ? Ya tambaya cikin bacin rai da kuma mamaki fuskan shi a daure, Diba nayi daniyar inji may suka ji, gishiri ne kamar zai daye bakin mutun don kaifi, A hankali nace gishiri a girki na ? Sai kuma nai murmushi ce, to nima ban sani ba don ban girki da gishiri ni, Sai dai ban san ya akayi kuma gishiri ya shiga ba, haka don ban ko ga roban salt din ba ma ni, Salawatu tace bama zan ko ci ba don ban shiri da gishiri ni, Amma dai ai ya kamata ki kula da yadda zakiyi girki kada adinga barnan abinci, Sai da na rausaya kai kadan ina mai kokarin maida abinci a cikin kula nace, Sai dai kuma ba yaune farkon girkina a gidan miji ba ban taba samun akasi akan girki ba, Yau din ma dai kalau nai girki na don min ina da shedan hakan, Enough please na fada maku cewa ba zan lamunci, cacan baki ko wani abu irin haka a gida na ba, Gaba dayan mu shiru mukayi yayin da shi ya mike ya suri keys din motar shi yafita batare da ya ce wa kowa komai ba,, Na kwashe kayan rai bace na mayar kitchen, ga abinci lafiyayye amma na rasa yadda zanyi da shi, don bai ciyuwa, Daki na shiga na kira fatu ina tambayan ta ko hamza yana gida, tace yafita tun,da yagama cin abincin da na basu, Nace don Allah Fattu ko kinji yana cewa da gishiri a ciki tace a,a don cewa ma yayi zai kara gishi don baiji mai ba, Saida mama tai masa fadan cin gishiri shi ne ya fasa zubawa, Ajiyan zuciya nayi don nagane cewa sheri akai min a gidan don a hadani fada da Yaya Abubakar,
****** ********* ****** Cikin, murna ta daga wayan ta tana kiran noban Lubuna , A a matar Oga ya akayi ne wai, ? Hmmm bari ke dai Lubuna ai kwanan nan ina cikin yar damuwa wallahi kin san wanan shigiyar yarin matan Abubakar tazo, Wai kin samay irin yarinyar tana son ta raina min wayyo sai don wallahi ban taba tsanmanin zan samu matsala daga gare ta ba wai sai gashi akan ta Oga yana ta wani rawan kafa, Dariya mai sosa rai Lubuna taiwa Salawatu ta dan dakatar da dariyan tana cewa, Kema ai kinsan dole ne sai, kin samu irin wanan challenges din daga wurin shi, Nafarko fa yar uwar shi ce yarinyar and so what inji Salawatu,, Murmushi Lubbuna tayi tare da cewa becareful my friend, don komai zai iya faruwa fa, Daga haka Salawatu taci gaba da bata rabarin su irin yadda zaman su yake a yanzu da kuma sherin da fara kulla min a gidan, Da kyau nawa inji Lubbuna kawai dai ke ma don kina son sa ne in bashi ba may zai sa ki tsaya wahal da rayuwan Akan mutum guda har nawa zai iya baki da zaki wani tsaya har ana wullakanta ki haka ? Ni mamaki kike ba may yafi mazan da kike hurda dasu a baya, ? Look Lubbuna ban son yawan sa ido fa ni dai nace maki ina son abina haka na, Sai kin ji ni again bye ba zan iya sauren kina tofa bakin ki akan abin da nake kauna ba, Daga haka ta kashe wayan tare da jin haushin aminiyar ta wace ke kokarin zagin rabin ran ta,, Komawa tayi saman godon,ta ta zauna tare da bushewa da wani irin dariya tana cewa, Yarinya dani kike zance an fada maki cewa, ni din ta wasa ce, Don dole ki bar min a binda nake kauna ko kuma ki zama yar kallo a gidan nan,
****** ********** ****** Take away ne ya shigo dasu daga waje kowa guda guda da naman rago mai zafi irin na gargajiya mai yawa a leda kowancen mu da na ta kumshi,, Tun bayan abinda ya faru zuciya na yaki yi min dadi saboda irin yadda nake ji a raina, Saidai ma ko waye nabar mai shi da Allah abinda kawai na ce ke nan, don idan nace zan yi bincike ta ina zan fara, Amma dai muje zuwa da mai shi don nasan idan halin mai shine gobe ma karawa za,ayi,