Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 37

Tarko complete novel - Chapter 37

Tarko complete novel Chapter 37: Tarko complete novel Chapter 37. Tun daga nesa nake jiyo karan cibaben spoon su suna kara,, Kamshin naman ya doki hanci na…

3,309 words

Tun daga nesa nake jiyo karan cibaben spoon su suna kara,, Kamshin naman ya doki hanci na har sai da naji shi har cikin rai na, Maimakon in nufi dining table din inda suke sai kawai, na, nufi gurin kujera na zauna, Fuskana babu yabo babu fallasa, acikin sa don haka bazasu iya gane halin da nake ciki ba, Ido Yaya Abubakar yabini dashi don bai fahinci may nake nufi ba, Anty Sadiya ce tace Meenatu zo mana ga abincin ki ki ci, Yayan ki ya leka ya samu kina sallah yace don haka muka fara ci, Cikin dan murmusawa nace anty bazan iya cin abinci ba yanzu, Yaya Abubakar dake kokarin kai abinci ga baki yai saurin juyowa yana na kallo na, Cikin daure fuska yace baza kici ba may ki ka ci da zaki ce bakya ci Na girgiza kaina ga da cewa babu ko mai kawai dai ban jin cin abinci ne, Ban yarda ba in ji Yaya Abubakar, don babu abinda kikaci balle ki ce bakya cin abinci, Murmushi na dan sake na ce wallahi Yaya kawai banjin cin abinci ne, Anty Sadiya tace ko jiyafa haka ki ka ki cin komai Meenatu, Ki dauki ko naman ki ci inji, Yaya Abubakar yace a cikin dan yanayin damuwa, Gaskiya inji Salawa don dai kinga, zai yi sanyu in baki ci yanzu ba, Na mike daniyar in dauki ledan naji sallaman Hamza, Kulan da na basu abinci shi da abokan shi ya dawo min da shi yana cewa Ina wuni Sir sai kuma yake cewa su Anty sannu ku fa ya gajiyan gida, Anty yake ce min duk da ya girmayni ni sa ba kusa ba amma saboda girmamawa ya ke ce min haka na Anty munfa gode abinci ma da wasoso muka cinye kin san kuraye na awajen, Nace, Baba Hamza da gishirin kuka ci abincin hakana ? Da mamaki ya dan tsayar da tafiyan da ya,keyi yana cewa gishiri ? Ai ba hishiri a ciki wallahi don har na aika mama ta bamu gishi taimin fada wai in daina vin gishiri hakana bakyau, Wallahi ba hishiri acikin sam, Gaba dayan su ido suka sako muna suna jin yadda muke zance da Baba Hamza, akan abincin da akace yana dagishiri aciki, Nace to mukan namu gishiri ya hana muci shi wallahi, Baba Hamza wanda nakewa karan suna saboda Baba Hamza kanin mahaifan mu, yace Kai wana maganace kawai don wallahi bani kadai na ci abincin ba gaba dayan mu awaje kowa ci babu kuma wanda ya ce gishiri, Wani irin shu umin mirmushi na sauke don ko yanzu Alhamdullahi na samu sheda Kitchen ya nufa ya ije kulan da na basu abinci a ciki yafito yana cewa Sir a rufe get don zamu watse zamu kallon Ball ne, Muryan yaya Abubakar ya na cewa Hamzo zoga wani abincin ka dauka ko? Take way dina na bashi tare da diban masa naman dake gaba na mai yawa so sai, Sai godiya yake ta zab gawa ya addu,a tare da fatan alheri ga maigidan da mu,,, Babana Hamza na fita daga falon na sauke wani irin gwauron numfashi take, nafara dancin nama na a hankali, Ina korawa da ruwan holandia, milk mai sanyi dake gabana, Zuciya na tai mun tas don Allah ya wanke ni daga TARKO da aka dana min Yaya Abubakar tunda ya duka ya fara aiki a system din shi bai dago kai ba, Ko ba,a fada ba nasan ran yan mazan ya baci ke nan yau, Nice ta farko mikewa daga bin dokan da akasa muna na zaman dole falon, Zaman da kusan duk a takure muke sai dai Sallawatu wace da farko tana dan jan shi da hira, Amma da taga tai magana daya biyu ba ansa tai shiru tama fara waya, wai tana gaisawa da mutanen gidan su, Daki na koma inda na fara shirin zuwa turakan maigida, Yana daga zaune ya hango ni lokacin da na shiga kitchen don in dan sa ruwan zafin Lipton a wuta, Don yanzu shan ruwan Lipton ya zama min kaman wani kwazaba shan shi na keyi sosai, Hakan yasa shi duba time din system din tare da dan sauke hamma, Tun fitowa Anty Sadiya ta mike tana kokarin hada yan abubuwan ta a hankali ta dan dubi gurin da Yaya Abubakar yake tana ce masa sai da safe ni zan tafi in kwanta, Kofan dakina na rufa ina saye cikin wani zumbulelen hijab sai kamshi ke tashi a jikina, Hannu na yana dauke da dan flasks dina da cup dan karami, Na tsaya inda Yaya yake zaune ina cewa zan kwanta Yaya Na juya gurin Sallawatu wace keta wayan karya da dariya nace to sai da safe ko ? Kai kawai ta gyada min ba tare da tace komai ba wai ita tana waya, Ban ko kai ga karasa hawa steps din ba naji shiru banji muryan ta ba,

Ban dade da kwantawa ba naji shigowan Yaya Abubakar dakin, Bathroom yafara shiga yadan jima ciki yafito, yana saye da wani dan wandon boxer, Injin ya kashe fitilan dakin a lokacin har na dan fara barci, Ta baya naji ya rungomini yana cewa yau barci kike jine haka ? Cikin yanayin mayen barci nadan bude idanuwa na da suka fara nauyin saboda batci, Jikina gaba daya ban jin dadin shi, don haka nake kwanakin,nan idan dare yayi, sai inji zazzabi a jikina, Yaya Abubakar ya ce ga jikin naki da zafi mana Meena ? Dan murmushin karfin hali na sake nace haka nake duk kwanakin nan,ai, Cikin murya mai kama da fada yace shine baki fada min ba mu koma asibinti akara dubaki, Yaya haka yanayin zazzabina yake sai a hankali zai dai, Are you sure ? Nace wallahi ko Yaya da sannu zan daina jin shi ai, ya amsa da fadin OK Sai naji ya kara matse ni a jikin shi ya na sauke ajiyan zuciya a hankali, Cikin wata irin siririyar murya nace, Yaya ya amsa a hankali da fadin na,am , Nace dazun kaman da Anty Samira naji kana waya ko ? Ya ce itace mana, Nace haba Yaya yanzun fa kune iyayyen mu, don Allah ya hore maka shekaru ilimi da kuma abin duniya, Kamar yadda kowa ke kokarin ganin cigaban gidan su, At list ace akwai wani jigo wanda idan wani abu yw taso zai tare,, Ya ansa ciki ciki da fadin hakane , Nace to yaya ai ina tsan manin ba Anty Samira ba ko mu da bamu fito ciki guda da kai ba a yanzu zamu iya neman taimakon ka ka ba mu , Umhmmm inajinki ya ce, nace yaya don Allah ka taimakawa yar uwanka kamar yadda Allah ya taimake ka,, Shin kin manta da halin Mama ne Meena, yanzu ina bata Mama zata ce don may na bata, Sai a lokacin na juyo muna fuskantar junan mu nace, Taimakon tsakanin ka da mu yan uwa ka daban ne ba dole bane sai Mama taji In yaso ita kuma Mama sai ka tura mata da nata kace gashi ayi sha,anin haihuwan Samira dashi kaga ai baka tauye kowa ba, Nadan marairaice murya na nace, Ko ya kagani yaya ? Amsa kamar a ikin bacin rai da cewa, shike nan naji Kice ta turo da account nomban ta zuwa Wednesday nace to Yaya mun gode, Ban san lokacin da na kai hannuna a jikin shi ba nafara shafa,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 5⃣4⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH-AL-KAREEM

Yan Uwa Massoya ZAINAB MAKAWA Da Novels, Dina Ina Kara Mika, Godiyana, A Gare Ku, Kau,nan Da Kuke Gwada Min Banda Bakin Da Zan Gode Maku Akan Shi Sai Dai, Ince Allah Ya Kara Rufa Muna Asiri, Don Na Samu Alheri Sosai Daga Gare Ku Massoya Na, Ubangiji Allah Ya kara Rufa Asiri Ya Sawa Sauran Dukiya Albarka,,,,,, Nagode Nagode Abin Daga Allah ne Kawai, Alhamdullilahi Ala Kulli, Halin👏👏👏👏 Ba sai na fadi sunayen ku ba duk inda kuke kun san kan ku nagode kwarai wlh,,,,

Abin duniya duk ya taru yai mata yawa a rayuwa don babu dama tashiga taron mutane yanzu, Sai a fara gudu a na cewa ga manya, ga manya nan, Saboda banda gidan malam tsoho ta kara shiga wani gidan buki kusa da gidan ta, Iskan kusan mata biyar ya tashi a gidan ranan da kyat tasha don sun mata mugun shaka, a wuya, Hakan ya ba mutane tabbacin cewa ita muguwa ce ta sosai, Yanzu diyan ta da yan uwanta da ya zama ma dole sai sun shiga gurin ta ne kawai ke shiga gidan ta, Ta zama mujiya a cikin al,umma, sai dai maza su wa yanda take sana,a da su basu tsoron ta don sun ce ai in ma maya ce bata cin mutane akwai dai irin sihirin da take yi, Don haka su kan je neman hayan mashi ko yar vesper gurin ta don tana dasu tana bada hayansu, Abin da tafara hankalta (kula) da shi yanzu shi bata samu kamar farko, Yadda Dodon ta kan mata aman kudi da farko yanzu sam baya yi, Bai wuce a sati yai mata sau guda ba ko sau biyu kuma basu yawa irin farko, Kai ta gyada tare da kuftawa, tana cewa a ranta ba kowa ya fara jawo mata matsala ba sai wanan mugun tsohon malam Manya, Yanzu bata da aiki sai na wahalan jan ruwa daga rijiyan gidan ta ko famfo zuwa cikin randan da ta boye dodon ta a ciki, Matsala guda shine yanzu boka yai nisa dasu wai ya koma can dajin Bargu da zama,, Saboda yanzu baya samun wani alheri a nan addini ya ratsa zukatan mutane, ba kamar farko ba, Don yai wa wata mata aiki, bayan Mama Ladi itama matar ha gida ta mayar mai da kayan shi tai ta mai tujara da tonon asiri, Yadda akayi shine, matan tazo gurin shi da kukan tana son sana,a don duk abinda ta rika baya zama kudi, sai ya lalace, Shine yace ta kawo sabon kwarya wanda ba,a taba aiki dashi ba, Jiki na rawa takai masahi sabon kwaryan yace ta tafi bayan kwana uku, ta dawo, Da ta dawo ya bata kwarya da wasu duwatsu guda uku, acikin sa, yace ta boye inda babu mai gani, Dukiya sai dai agani a wajen ta ta bashi dubu uku kamar yadda ya bukata, Ta tafi gida tana murna da jindadi takai kwaryan ta can ta boye karkashin gadon karfen ta, Kaman kwana biyu cikin dare sai ji tayi wasu irin manyan tsuntsaye har guda uku sun tashi daga dakin ta zuwa, Saman rufin dakin basu bukatan wai saman ya bude duk da rufin kwano da dakin ke dashi, Bata kara barci ba tana zaune har zuwa asuba sai ganin tsuntayen nan sun dawo suna ta amai a tsakiyan dakin ta zaban tausayi, Hakalin matar ya tashi matuka saboda yadda taga wanan halittan suna amai, Kafin wani lokaci sai taga kamar hayaki sun koma cikin kwaryan da ta aje a bayan gadon ta sun zama kamar duwatsu, Juyowan da zatayi sai ganin wanan aman da sukayi tayi ya koma mata kudi gudan mai yawa, Innalillahi ta fara fadi ga bakin ta tana cewa wanan mugun maita ya bani ashe,? Badani ba sam bazan karbi wanan fitinar ba gaskiya sam da sake, Tun da safe da kudin da kwaryan ta kwasa ta mayar mai da abin shi tana kokarin tara mashi mutane a gida,

****** ********* ****** Anty Samira bata bata lokaci ta turo da account din wata kawar ta, Ya Abubakar ya tura mata da dubu dari a ciki, ina barci da rana musalin sha biyun rana, Saboda girkin Salawatu ce gaba dayan mu ni da Anty Sadiya muna daki kwance abin mu, Ta manta cewa mu mutanen hausa ne kishi dashi aka haife mu na tsabata bawai na sheri ba, don tun muna yara muke taya uwayen mu kishi, mun san kan zama da mutane iri, iri, Zaka fan mu kamar kauyawa amma zama da mu wahala gare shi don kar muke kallon ka,

Karan wayan Anty Samira ya tayar dani barcin da na keyi badon naso ba, Cikin muryan barci nace Anty Samira ya kuke ya gajiya, Tace Meenatu an bansan ko me zancewa ba, don na rasa kalman da zan maki godiya, Na ce, a,a wallah na mi anaty ? Shin Meenatu ke ko ga kudin da yaya ya turo min? Har fa dubu, darin ya turomin dasuwa,, Nace cikin sakin fuska kai Anty Samira am nai maki murna, Sai atai zuwa shagali ko ? Cikin wani murya tace wani shagali zanyi da su duka, 'Dariya na sa mata don jin abin da tace, "Tace ke san dama ina son jari in fara yar sana,an gida irin na mata, Na, ansa da fadin gaskiya na Anty ke ga sai dai ki saro kayan su, turaren wuta, takalma da su manshafi masu dan dama, Tace Allah dai ya barki Meenatu, kaman kin san shawaran da ni ke nema ke nan, Cikin zolaya nace amma dai sai kin tai kin gwada ma Mama kudin ko kafin ki fara taba su,? Cikin wani irin murya da karfi tace, Wata,? Niya ? Ai in kin gani lahira maza su ka kaini,, ta dai jiya ga baki amma koshi sai angama sha,ani zan fada mata, Nace a,a ke ko Anty kaman yadda tace ki kai mata ko dubu goma kice ga su nan suna kin ka samu kawai, Shiru naji tayi can ta numfasa tace to shike nan ance ba,a kin shawara zan gwada yin haka mugani, Takara min godiya tare da kashe wayan ta, A hankali na juya ina mai lumshe idona wanda zuwa yanzu barcin da nake yi ya fita min ga ido ko, Don haka namike na bude drawer mirror na dauka comb da masillan kitso, Nafara sance kaina da ya fara yi min kaikayi don yana neman agaji, Tsab na sance na daure shi da ribon ta baya, sai dai ina a gaban mirror na ga ya dace inje wankin kai, haka nan, Waya na jawo na kira Fattu muka gaisa na dan tambaye ta mutanen gidan ta Sai take ce min Mama tana nan ta na biski wai zata kawo maki,, A take na tuna da zancen Yaya Abubakar gashi kuma ina sha,awancin wanan biskin da akai min tayi, a gidan Fattu, Don haka na kira Yaya Abubakar ina sheda mashi cewa ina son in dan mika kafa gidan su Fattu, Bai ha,na ni ba sai ce min da yayi a dawo lafiya na amsa da fadin Allah ya nufa na gode, A gidan su Fattu can na dan sake jikina muka ci abinci tare, da ita muna fira jafi, jefi,, Maman Bi,u sai dadi take ji na shigo gidan su duk ta rasa inda zata sani saboda murna, Munyi da Fattu zata rakani gurin wanke kai kamar yadda mu ka taba zuwa tare da , Sosai,naji dadin zama da su saboda sai nake ji tankar a gida Birnin Kebbi nake , Tunda na tunkari hanyar shigowa, gida sai naji duk jikina yai min sanyi , Zuciya na ya cunkushe min na dinga jin babu dadi, sam a rayuwata, Mutum yai ta zama batare da yai magana da kowa ba saboda kishi, da mugun hali, A falo na samu Salawatu, zaune tare da wata farar mace wace mai ya kodar da ita har zaka iya ganin kwancin jijiyoyin ta, Sallama nai ma su ban tsan mani sun karba min ba don haka ban tsaya ta kansu ba, Don ina kallon yadda gaba dayan su da zan shigo suke wurga min harara tare da jan dan guntu tsoki,, Nashige part dina ina kokarin bude dakina da key, Kunnena ya jiyo min lokacin da bakuwar Salawatu ke cewa wana ai batafi sha takwas ba ma, Murmushi nayi kawai na shige abina ba tare da na tsaya jin su ba don duk basu gaba na, Matar tace wa Sallawatu yanzu ma akan wanan kika tayar da hankalin ki haka, Shiru Sallawatu tayi tana sauraren abinda matar ke, fadi, can ta nisa tana cewa, Wata Adah baza ki gane bane aikin san dai koni wacece ko ? Matsalan na daga gurin maigidan nan don duk wasu dokoki da ya aza muna sai kiga komai a dole ya zama equal a gidan sa,, Matar tace ba matsalan komai na san yadda zamu fito mata, Sallawatu, ta gyara zama tace kin gane ne Adah nafi son ace, babu wata mace a tare da shi ko a gidan nan sai ni kadai, Matar da take kira da Adah tace kar ki samu damuwa, yanzu kifara kawo wanda zan fara zuwa dashi mu gani,,

Yau manyan matane ke girki, a gidan don haka ta kasa ta tsare, taki gusa daga falon tana zaune don zan iya cewa a nan ta wuni ranan, A gajiye ya dawo gidan daga office don haka yau sai a hankali, Salawatu sai rawan kafa ta keyi da don ta na haka kada wata daga cikin mu ta samu kafan shige mashi, Ya shiga yai wanka ya fito duk muna daki babu wace ta fito, daga cikin mu, Hakan yadan sashi fara dube duben kofan shiga dakunan mu a lokacin, Anty Sadiya akai sa,a tafito daki a lokacin don tai mashi sannu da zuwa, Fuskan Sallawatu yana kicin,kicin, don may Anty Sadiya zata fito gaida maigidan, Ita ko Anty Sadiya kar take kallon ta don ta fahinci may take nufi da daure fuskan da tayi haka nan , Cikin irin sakin fuska shi da ba wani fara,a yace Sadiya ya gidan dai,? Yana saye da doguwar jallabiya a jikin shi kafanshi plat shoe's din mazane, Direct part dina ya dosa a lokacin don ganin halin da nake ciki, Wani kunci Salawa taji ya rufe ta tabi bayan shi da harara, Komawa tayi saman kujera ta zube don takaici, da bacin rai

Ina zaune Tv na yana aiki na kai Africa TV 3, suna program na addu,oin marance, Daga gurin da nake a zaune ina dan bin su a hankali, kamar yadda suke yi idona a lumshi, Kamshin turaren Yaya Abubakar ne ya daki hanci abinda ya haddasa min bude idon nawa a hankali, Cak muka hada ido dashi yana tsaye kallo guda nai mashi na gane cewa tun dazu ya shigo kena, don har yai shirin fita sallah magrib can kasan mu Kokarin gyara zamana nayi ina cewa sannu da dawowa Yaya, Ya an,sa da cewa,, lafiya kike daki bangan kin fito gaidani da dawowa ba ? Lafiya lau Yaya na ba shi ansa da hakan ina cewa, wani program ne ya dauke min hankali ban san time yayi ba, Ya maida kallon shi ga tv don yaga kowani tasha nake kallo, Kan shi ya juya, yana cewa ai ina ce ko har yanzu jikin ne ? In ce mu tafi asibiti hakana dai, Na girgiza kaina da sauri ina cewa, ai naji sauki yaya don ko alaman fever na daina jin sa yanzu, Ya ce ni zan fita zuwa massalaci saina dawo, Allah ya tsare hanya nace tare da fatan adawo lafiya, Har ya kai kofan daki na na manta Yaya mun fa gode Allah ya saka da alheri Allah ya umfana dukiya, Murmushi yayi daga gurin da yake tsaye yace har ta sanar da ke, ke nan ko ? Nace Yaya kasan abin dan uwa ai yadda yake ko ? Daga haka ya sai kai ya fita dakin fuskan shi dauke da murmushi,

Sallawatu wace ke zaune ta hau tayi fan a motar kishi, Sai faman jijiga kafa takeyi tana leken han fitowa daga part dina, Hango shi da tayi tafe, yana dan murmusawa, yasa ta mikewa tsaye, Kafin ya karaso gurin ta, ya kara daure fuskan shi tam, do ya gane nufin ta tun daga nesa, Dan dabur cewa tayi tana ce har kafito ga time ma yana son ya kure maka, Batare da yai magana ba ya sa kai yabar gida tare da turo kofan shiga falo,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull