Tarko complete novel - Chapter 38
Tarko complete novel Chapter 38: Tarko complete novel Chapter 38. ****** ********** ****** A bangaren Mama Ladi Yaya Abubakar yakira ta sun gaisa yake…
3,344 words
****** ********** ****** A bangaren Mama Ladi Yaya Abubakar yakira ta sun gaisa yake tambayan ta akan zancen haihuwan Samira, Sai cewa tayi dama tana son fada mashi cewa ya turo da abinda za,ai mata, hidima dashi, Don dai yasan cewa yanzu ita bawai wani karfi ne da ita ba, Kuma gashi haihuwan Samira na farko ke nan a gidan, Don haka kaga ba karamin sha,ani za,a yi ba ke nan don haka katuro da abin kwarai,, Yace to Mama zan turo ma Baba Wadda sai ya kawo maki, Sai naga sakon ke nan ta fada kai tsaye kamar mai fada a lokacin, Suna kashe wayan ya numfasa tare da lumshe idon shi, don lamarin Mama yana bashi, mamaki sosai, Don ita ko diyan da ta haifa bata barsu ba sai tai mashi nasu kalan, Sam ko yan uwan haihuwan shi,mama bata kauna yai masu wani alheri a tsakanin su, Don sai dai sakon yafito ta hannun ta dole saboda tadan samu ta tsankwara,, daga ciki,, Amma yanzu wanan shawaran da Meenatu ta bashi haka zai dinga yi a tsakanin su,,
Bayan ya dawo daga sallah ne, Salawatu wace ke zaune daga bakin gado, Ogana ina son zamuyi magana da kaine please idan har ba damuwa, Ba tare da ya kalle taba ya natsaye daga bakin wardrobe yana ciro kayan da zai saka a jikin shi, Gaskiya Ogana ina son inyi request a wurin ka irin yadda kaduty kana shiga wani daki please, Da sauri ya juyo yana mata wani irin kallon mamaki, Yace are you out of your mind,, Ta dan fadi a hassale, da cewa gaskiya mind dina is not styling idan kana haka,? Ya ce so da wanan kika shigo min gida ? To dakata kiji bazan yarda ki kawo min matsala acikin family na ba, Ke da su wa ya fara shigowa gidan nan first ? A hankali, tace sun rigani zuwa gidan, gaskiya, Yace may yasa su basuyi bakin ciki dake ba sai ke ce zaki nuna bakin cikin ki a kan su,, Shiru tayi tana cewa, gaskiya ni bana jin dadin hakan ? Amma kin san cewa suna gidan ki shigo ko don haka sai kiyi hakkuri amma idan bazaki iya ba hanya a bude yake gaskiya,
Ni dai a ranan kaman nasan yadda sukayi da Yaya Abubakar, Haka kawai naji ban son fita falon kamar yadda ya ya umurce mu dayin haka kullun, Sai ma da na tabbatar da suna falon a lokacin na mike don in gabatar da Sallah da na idar kuma zan kwanta ne kawai abina, Saboda irin yadda naga take taken ta tun da rana yasa nace barin kama kaina, Ina kokarin shimfida sallaya Salawatun da kan ta tashigo dakin daga kofa tadan tsaya tana ce min Oga yana magana da ke a falo wai, Nace mata cikin alaman nuna ina sallah da cewa uhum, uhum, Ta juya batare da tace komai ba ta nufi fallon don ta sheda mashi cewa ina sallah, Bayan na idar na kawo nafilfili na dora akai, dafa bisani kuma nazauna naci gaba da yin addu,oi na,,, A takaice dai sai da na ga time ya kusa na barin falon yasani tashi don in tafi falon, Idona ya fara kawai ga kayan dake saman table din a cikin ledoji guda uku duk da alama iri dayane, Kamar kullun na nufi kasan carpet na zauna irin yadda na saba yi, Sai da ya gama tura sakon nan shi a,system yadago kai ya dubi time yana cewa, May kika tsaya yine haka baki fito ba yau da wuri haka ? Nace, Sallah na gabatar Yaya sai kuma, na tsaya nadan watsa ma jikina ruwa, Ok kawai ya furta, tare da kokarin jawo ledejon dake gaban shi, Inda Anty Sadiya take yace kizo ki zabi guda daga ciki, Anty Sadiya tamike tazo gaban table din ta mika hannu ta dauko wanda tagani can daga karshe, Sai ya juyo gurin da nake zaune saman carpet ya ce oya zaki zaba ko ? A lokacin ne naga Sallawa tana wani kada kafa, kamar yadda idan ran mutum ya baci yake yi, A hankali na dan karasa bakin table din na dauki ledan dake gabana, Tare da cewa cikin wata irin murya mun gode Yaya, Allah ya kara dukaka, Naji lokacin da Yaya yai wani irin ajiyan zuciya tare da cewa hmmmmm, Sai ya juyo gurin Sallawa wace ke ta wani irin taunan baki tagefe tana karkada kafa, Ta mike, jiki ba kwari zuwa gaban table ta dauki ledan karshe din , Nikan ina zaune na jingina bayana ga kujeran da nake zaune a kusa da shi, Kafana yana daga mike ina karkadawa a hankali batare da ma na kalli ledan ba, Hankalina yana gurin TV da,nda suke wasan tseren ruwa, Karan bude ledojin da ke gefen su nake jiin suna tayi, Nidai ban bude ba sai ma mikewan da nayi a hankali ina cewa zan kwanta sai da safen ku, Na mike tare da daukan leda na wanda Sallawatu ta kura,wa ido kamar tana son ta kwankwance abinda ke cikin Ledan nawa, Nikan ina shiga daki, na aje Ledan saman mirror dina na rufo kofana na kwanta kawai, Sai da na jero addu,oina na shafe ko ina na jiki na sanan na jabargo na kwanta,
Barci na soma yi amma sai nake jin kamar hayaniya daga cikin gida, Tun ina daurewa har yakai na bude idona inajin muryan su su uku ana ta masifa a tsakani, Saida yaya ya daka masu wani irin tsawa su kayi tsit gaba dayan su,,, Magan ganun da nake ji jefi,jefi a kan ledan kayan da yaya ya siyo muna ne sukeyi,fada, Don naji anty Sadiya wace bata magana ma ko banza tana cewa daga kawai, Nshiga kitchen dauko ruwa zaki canza min leda an fada maki cewa ban gane kallah roban man dake ciki bane, Tsuki nayi kawai tare da gyara kwanciya na ina mai jin haushin su a zuciya na,
Afuwan yau ba yawa sosai please,,,,,,,,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA,, 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 5⃣5⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH- AL-RAQEEB,,,,
Alheri, Rahama Ni,ima, Gafara, Daukaka, Daraja, Baiwa Dake a cikin wanan Watan mai albarka ya Allah muna rokon ka , ka sada mu da shi gaba dayan shi,,,,👏👏👏👏👏👏👏👏
Yau Anty Sadiya ce da girki, don, haka na tashi tun da safe na fara gyara gida, Kagin kowa ya tashi ko ina na gidan mu sai kamshi ya keyi,, Ko da Sallawatu tafito don ta sa girkin breakfast ta samu kitchen din mu na wani irin kyali saboda yasha gyara don har store din kitchen sai da na sharo, Gaba dayan su duk wanda ya fito sai ya ja ya tsaya don mamaki, saboda gyara shine gida, Dining table din mu har kafafuwan shi sai da nagoge su tas, don tun daga nesa zaka gane hakan, Wai duk wanan aikin da sha babu ko mutum daya da ya fito daga cikin gidan a lokacin, Na kare na koma dakina don in yi wanka indan sarara, Na dade zaune a gaban mirro ina gyara jikkina tare da yan shafe ,shafe, Sai a lokacin na hango ledan kayan da Yaya Abubakar ya bamu adaren jiya,, A hankali da gurin da nake na mika hannu na bude ledan don inga abinda ke ciki, Sabulai ne na wanka da man shafi,masu kamshi maclean, su tissue, cotton bund, da sauran su, Sai wani material mai kyau da dauka ido kalan nawa, light pink, Kalan yai min kyau sosai a idona don nakai wani lokaci ina ta shafan material din,, Namayar da kayan a leda na dauka na sa cikin wardrobe, dina,,
Dogon riga na yan kasan Niger da na sayo ya ji aiki a gaban shi nasa,,, Nayi wanan kwalliyan ne don kin san idan kina da kishiya, bawai sai ranan da zaki karbi girki bane zakiyi kwalliya a,a Next day to kiyi girki zaki gyara jikin ki ta yadda mijin zai rude yaji kamar ace ke ce zakiyi, girki a ranan, Jin banji motsin kowa a waje ba yasa na koma saman gado na na haye,,, Gadon da yasha gyara cikin wani zani gado ja mai zanen flowers farare,,, Dakin yaji room fresh tunga labulen dakin zanin gado da bathroom don sune ake sawa room fresh, sai daki ya dade yana kamshi, Dan kwantawan da nayi ashe barci ya fara kwasa na saboda gajiya, Sai muryan Anty Sadiya naji kaman a mafarki, tana cewa Au, Meenatu kin kwanta ne,? A hankali na bude idona ina kokarin tashi daga zaune, ina kuma, cewa, yanzu fa na kwanta ashe barci ya dauke ni, ko Idon Ànty na saman rigan da nasa alokacin, yana daukan ido, , Anty ina kwana ? Tace Alhamdullahi Meenatu, Ya gajiyan aiki,? Na tashi naga ko ina gidan yau sai kyalli ya keyi murmushi nayi nace naga idan anyi tun da safe yafi sauki ne shi yasa nayi, Ta ce to nagode, murmushi nayi yayin da naga ta juya zata bar dakin don fita, Ni kuma sai na koma saman pillow da nake kwance da farko, Amma sai kuma Anty ta tsaya tare da juyo wa tana fuskan ta ta, Tace Meenatu dama yau, tuwon alkama naso in muna kuma sai dai nasan idan nayi zai sake ne, nace to babu matsala Allah ya kaimu anjima lafiya , Sai dai ina son idan anbarni zan tafi gurin wanke kai anytime na dawo sai muyi, Na karashe zancen cikin murmushi , Tace ai badamuwa ko sai kin dawo, ke nan don ni zan shige ciki, Komawa nayi na kwanta sai dai kuma barcin baizo ba again, don haka sai na lumshe ido,na,,, Tausayin irin rayuwan, Anty Sadiya nake,yi mutum ba ruwan shi da komai shi, Idan ba ka zauna da ita sosai ba sai ka dauka bata son mutane ne ita, Kamar tana kyaman zama da mutane don yawan, daure fuskan ta, Amma daga yau tunda har na fahince ta insha Allah a tare zamu dinga aiyukan mu na gida, Na nisa nace, aiko banza ita matar yayana ce kuma kaman yan uwa muke don zama gari guda, da muke, Idona yana daga lumshen da yake ina ta tunanen duniya, Alaman mutum ya na tsaye a kaina naji sai kuma kanshin turaren da hanci na ya shako, min, na dan baiwa, watau Yaya Abubakar, ke nan, Hakan yasa ni bude yan daradaran idona sai cikin na Yaya Abubakar wanda ke tsaye, a gaba na, fuska ba yabo ba fallasa, ya kura min idanun nan nashi masu firgita mata,, Kokarin mikewa nayi zaune ina mashi wani irin murmushin jan ra,ayi, Kafin in ka daga zaune sai naji muryan shi
Tambaya ya jefo min Barci kike ne ko kuwa hutu ? Nace, kawai dai ina dan hutawa ne kawai, kafin in fita, Ina kwana Yaya ? Lafiya kalau ya kika tashi ,? Ko da yake naga ai lafiya kike tunda har kin yi wanan irin aikin haka ? Murmushi nayi nace gidan ne yai min ba dadin gani shi yasa na kamawa Anty gyaran shi, Kin kyauta yace tare da dan murmusawa, ya ce zai tafi shi sai ya dawo, Ban san lokacin da na jefo mashi tambaya ba da cewa kayi break fast ne ko Yaya ? Sai naga ya dan bata rai yana dan jiji ga kai yace yau bazan tsaya break ba agida kifita ku karya, Na ansa mashi da fadin to Yaya, Zai fara tafiya nace Don Allah Yaya ina son yau in tafi saloon gurin gyaran kai ? Cak ya tsaya yadan yi shiru zuwa can ya nisa yace, Ok ki dauki ki nan a saman drawer a dakina Hamza ya kai,ku, amma dan Allah ku kula kada yai tukin ganganci da ke , Nace tare da Fattu zamu tafi insha Allah zamu kulla,, Ya ciro kudi daga cikin ajihun wandon shi ya miko min,, yana cewa, Ba matsala yace yasa kai ya fita abin shi, Godiya nai masa, tare da fatan a dawo lafiya,,, Na nisa bayan fitan shi tare da komawa na kwanta,
****** ********** ****** Mun samu mata da yawa a cikin saloon din, don haka muma muka bi layin zama,, Matar mai shago tafito a take ta shedani, don bata manta da ni ba, Da murna tare da sakin fuska, ta, tare mu ta na jin dadi, Ta umurta da a kawo muna ruwan, sha duk yadda naso, kada ta wahal da kan ta gare mu amma sai taki, Bamu kadai ba ranan harda sauran mutanen da ke shagon ta saya muna ruwa masu sanyi,, Mata sai hiran duniya akeyi ana ta yan dararaku kowa da abinda ake mata, Wata daga cikin matan ta dan dubeni take cewa da za a wanke maki kafa, ai maki ado zai yi kyau, Murmushi nayi ina cewa ai naga kamar da layi da yawa yau, akwai jama,a agurin, Anty mai shagon tace barin maki da kaina kaunata, Ba bata lokaci a ka kawo roba a gaba aka fara gyara min kafa, Matar da tabani shawara a fara gyara min kafa wayan ta yai kara ta dauka suna magana, sai dai a cikin zafin rai take zancen ta, Bayan taga tafara fada ita kadai tana cewa ita za,a kawo iskan ci ? Sai Anty mai shago tace to ai shi wanda kike fadan dashi yanzu baya kusa, Matar tadan ja tsuki gefe tana mai kauda kan ta ,tace,,, Bari kawai Anty wata shegirya matace ke son shiga gona ta, Wata mace ce gurin aikin su guda da maigidana shine take ta kokarin shige masa, Yanzu wai kirana yayi yana ce min wai an kawo lace masu kyau a shagon su amma, Aliya ta zaba muna, Ina ruwan ta da ni da har zata zaba min a binda zan sa tasan colour din da nake so ne,? Anty mai Shago ta nisa tace aiko naki ya samay ki wallahi, Don kin san irin matan nan idan sun lakewa mijin ka sai Allah, Fattu daga gefena tace, irin amaryan gidan ku ke nan Meenatu, Nai murmushi kawai batare da nace komai ba don dariya abin ya bani, Anty mai shago tace, ke kardai ki ce min an ma kauna ta kishiya kuma, Da ba kun ce su biyu bane,? Fattu tace wallahi Anty, wata irin garmakekiyar mata na nan a cikin su wai itace amaryan su, Duk ta girmay masu har maigidan nasu, sai kishin bala,i,, Anty mai shago tace hmmm,ummm, amma gaskiya abin da mamaki sosai a ciki, Fattu tace ai ina ga dama kamar zancen auren ta yana gaban na Meenat don da alaman sun dade a tare,, Sai matar da tafara zancen tace itama wanan din wani brother din maigidana yace min wata mai kama da yar Togo ce, ba yarinya bace irin tsofin barikin nan ne, Fattu tace shima dai maigidan su Meenatu bazaka ce zai iya auren wanan mace ba wallahi, Sai Anty mai shago tace o kin mutu wallahi an fada maki cewa baki sake suke rike mazan, ? Ai sai sun dade suna masu shiri sosai kafin su tun kari na miji tukun, Wata taso taimin haka ga maigidana na bita har gida na ci ubanta na nuna mata nafita zaman bariki, Wai har abinci take kawo wa maigidana a office da kuma ziyar a gida idan ban gidan, Fattu tace ai ina ga ita Meenatu tasu ta samu shigane saboda yadda rayuwan uwargidan su yake na ko in kula, Abinci fa sai maigidan ya sayo masu take away, don bata iya dafa wa ita bata da time, Sai matar wace kekira da , Humaira, tace kinga kowa nima halina ke nan don ban da time da safe idan nafita gida ban dawo wa sai, after six kinga a lokacin duk nagaji, Anty mai shago tace yo kin mutu wallahi Humaira idan zaki gyara maza ki gyara kafin ai maki sakiyar da ba ruwa,
Sai wanan lokacin nasa masu baki a hiran su daidai lokacin da nake kokarin gyara kafana, nace, Amma gaskiya don kina zuwa makaranta bashine zai baki excuses din kin dafawa maigidan ki abinci ba, Anji cewa da rana baku a gida gaba dayan ku, to da safe da kuma dare fa, ? Baki da right da zakice bazaki kula da mijin ki ba idan har kikayi sakaci yanzu ne wata sai ta dafe maki shi, Duk da dai mun san cewa mata hudu shari,a ta yarda masu dasuyi, To amma ai mutum sai yayi kokari ya gyara ta ban garen shi kafin yazama ma mitum to latet, Cikin dan marairai ce murya matar tace, to yaya zanyi ni don Allah wallahi har kunsa duk naji jikina ya mutu, Fattu tace wallahi wani lokaci mu matan sakacin mu ke kai mu ga halaka ai, Matar a take duk tashiga damuwa tace wallahi kamar kun sani cewa Yanzu duk hankalin shi na kula da yana gurin ta don ko da dare na zaki ga yana waya muku muku, da ya gan nin sai ya kashe yana cewa I will call you back,,, Cab,di,jam inji Anty, maishago, tace gaskiya a kwai aiki sosai Hummaira, Na ce ba wani aiki kawai, dai sai dai ta gyara mu,amulanta da mijin ta, Bakin su na haduwa gurin ce min kamar, yaya fa,? Nace,kamar ta kyautata tsakanin su mana ta yaya za,a ce mace sam bata da time din mijin ta kwata,kwata, Anty mai shago tace gaskiya Humaira baki da gaskiya anan, Don ma sai ince kece kika ba da kafa ai maki hakan ma, Humaira ta ce to, ya zan yi ne ni dan Allah duk na rasa ko may zanyi wallahi, Na dan ce masu hummm, gaskiya abubuwa da dama,, Kin ga da farko dai abinda zakiyi, shi ne ki fara sake jiki dashi, Kamar kuci abinci a tare, ko kuma idan kin rigashi ci idan ya zo zaici, sai, ki zauna gab dashi, Kece mai service din din shi, kamar suzuba abinci a plate, Kara miya idan da bukata hakan, kara gishiri ko maggi, Da farko ki tabbatar da tsabtar gidan ki a kullun kafin ki fita, Sai kuma ki tabatar da cewa, kin tanadi komai wanda zakiyi abincin dare, da idan, kin dawo daga makaranta, Sai kuma abinda zakiyi maku breakfast kada ki fara kibar, mijin ki yafita gidan ki bai karya ba, Don kada keep mantq cewa wanan bokon da kike zuwa yi iya karshi a duniya zaki bar shi,, Sai ke kuma kikai sakaci da gobe kiyaman ki kika kama duniya kawai, Shin bakya tunanen, cewa, Allah zai tambaye ki yadda kikai zama da Amanan mijin ki da ke kanki, Humaira ta wani nisa,wa tace, gaskiya ban san may ma zance ba, Nace to kinga wanan ke nan Humaira gaskiya akwai matsala gare mu matan yanzu, Gaba dayan su su kace gaskiya kan, Sainaci gaba da cewa sanan ki tabbatar da cewa idan kin gama girkin duk saurin da ki keyi ki ba mijin ki time tukun kafin fitar ki, Zuba ruwa a cup ko drinkis, Ki dan rika jan shi da fira jefi,jefi, idan ya gama sai ki, zuba ruwan wanke hannu, ko mika tissue, da toothpick, kwashe kayan abincin zuwa kitchen ki gyara gurin cin abincin, Ki tabbatar da kin tsabtace makwancin ku kin gyaro ko ina a dakin, Kada ki nuna gazawanki gare shi wurin mu,amulan aurataiyya, A jiyan zuciya Humaira ta sauke a lokaci guda tare da kallon mu gaba daya,, Kin ga dai in har zakici gaba dayin haka na insha Allah ba yar Okene ba ko yar Eteku ce dole ta barki, Tace Meenatu bani noban ki please zamuyi magana Tafara yi muna, godiya kaman zata fadi kasa, Nace sai mun kara haduwa zan fada maki yadda zakiyi mu,amullah da yan uwan maigidan ki, Tace ai kaji wani matsala Babba don sun sani gaba yanzu haka da muna funtata, Daga haka muka cigaba da kara tattaunawa a tsakanin mu akan yadda irin wayan nan matan masu zaman kansu ke kama mazan mutane su mayar nasu, Ta hanyar sakaci irin na mu matan hausawa musan,man matasan mu na yanzu,, Irin yadda mukafi karfi da neman duniya sama ga lahiran mu, Mun manta da maganan Allah da Annabin sa akan biyayyan aure, muna yawan shagala da rayuwan mu,