Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 42

Tarko complete novel - Chapter 42

Tarko complete novel Chapter 42: Tarko complete novel Chapter 42. Tare suka fita da, mijin Fattu wanda yau ne haduwan su na farko Mijin Fattu bayan sun dan…

2,980 words

Tare suka fita da, mijin Fattu wanda yau ne haduwan su na farko Mijin Fattu bayan sun dan fita can kasan wani bishiyan mangoro da ke cikin asibitin, Yake cewa Yaya Abubakar gaskiya abin ma yazo da sauki don ba karamin tashin hankali bane zuban ciki, Saboda halin damuwa da Yaya Abubakar ke ciki yau shi da kan shi ke cewa mijin Fattu a cikin yar damuwa, Kunsan ance idan magana taima yawa kasamu wani yardadde ka fada mashi don samun shawara, ko dan warware damu saboda kunci, Abinda ya faru tsakanin mu da Sallawatu ya fada wa mijin Fattu din, inda ya kare da cewa shi yanzu ya rasa hukuncin da zai dauka akan mu, Mijin Fattu cikin kwantar da murya yace mashi, Hakkuri zakayi maigida don ka ga ita wanan dai itace aka zalunta, Saboda kaida bakin kace tasamay ta tana aiyukan gida ita kuma bata gidan ma tun safe, Kadai a takaice ita aka zalunta sosai don wanan barin çikin da tayi ba karamin rashi bane ai, Amma ita wacen matar, ya kama ka dan hukun tata don tasan batayi daidai ba, Yaya Abubakar ya kada kai, alaman ya gamsu da zancen mijin Fattu, Don haka ya mike yana cewa, yagode kwarai da wanan shawaran don shi da farko, so yayi ya sake ta gaba daya, ya huta da tashin hankali, Mijin Fattu yace a,a ba,a hakana ya dinga hakkuri da mata don su haka su ke, kamar tunkiyoyi, Daga haka ya ci gaba da bashi shawara akan abinda ya dace da kowacen, mu, A take Yaya Abubakar yaji dadin zama da mijin Fattu wanda a kullun sukan hadu massalaci amma ba wani, alaka a tsakanin su, Sai yau da dalili ya hada su har suka danfahinci junan su, Har zuwa dare suna tare don a tare su ka tafi gida ranan, Daga gurin da nake a kwance wayana ya fado min a rai sai na tunacewa Fattu ta bani, wayan da safe da ta zo, Don haka sai na lalaba wayan na a karkashin filon da nake kwance , Wayan baida wani enough caji sosai, amma dai zan iya kira dashi hakanan, Anty Amarya ce nakira ta dauki wayan tana magana acikin fada tana cewa , Meenatu wai yau ina kin ka shiga haka tun safe na ke kiran wayan ki amma bai zuwa,,? Nace cikin murya irin ta yanayin mara lafiya, Anty Walleh banda lafiya na yau, Cikin nuna damuwa tace missamay ki halan ? Sai da na dan cije bakina na dan hade wani abin bakin ciki na furta a hankali na ce, miscarriage na nassamu Anty, What ? Tafada cikin wani irin daga murya mai, kara tare da kara maimaita tambayan ta, Sai kuma tashiga cewa Innalillahi ,waina alaihim raj,un, Yan wagga bakar diya sai da tajawo muna wagga, irin hasara, Walle sai ta gani ga rabon ta, Sai kuma tace shin yanzu kina ina na ? Nace a hankali walleh ina asibiti anty tun daren jiya, Subbahanallahi takara fada sai kuma tace, To su asibiti shi mi sunka ce ? Saida na dan gyara kwanciya na sanan na ce ban san ko min sunka fada mai ba, Sai naji tana nanata ,a,a a miscarriage shi wagga diya anyi mugguyan shegiya, Dama du wadda ankayi tasan cewa kina da ciki kila shina tattaho maki da jidali don dai kuyi fada ta goga maki tsiya, To in Allah yayi duniya don Annabi kan ya za ya karewa, Don ke kin godema Allah ke gwada itako wassa sherin da taka kunsawa, Sannu Anty Amarya takara yi min tare da jamin kunne in samu mu rabu lafiya da ita, Nacewa Anty amarya to tace hutun mu ai ya kare in shirya in naji sauki indawo sokoto kawai abina nace mata insha Allahu danaji sauki zandawo sokoto da zamane, Ina jin kafin in kashe waya anty amarya tana ta surfawa Salawatu zagi na fitan arziki,

****** ********** ****** Ba laifi don zuwa yanzu Alhamdullahi na ji karfin jikina sosai, Don waye wangari sai na tashi jikin nawa Alhamdullahi, Wanan dalilin yasa likita da yazo dubani yabani Sallama Tare da yan magungunan da zan sha don su kara min karfin jiki na, Malam Abdullahi ne suka zo da driver suka maidani gida don Yaya Abubakar yana da Meeting a ranan, Nasamu Fattu a dakina ta gyara min shi fes sai kamshi ya keyi, tankar ina dakin a lokacin, Sai da na dawo gida Anty Sadiya tashigo har dakina na ta gashe ni, Abin bai wani bani mamaki ba don la,akari da irin yanayin, mutanen mu gurin kishi, Na mayi arziki da har tazo ta gaida ni ina matsayin kishiyar ta nayi barin ciki tazo gaisheni, Don inda agida mu ke bazan samu wanan daman ba, Sallawatu wace ban ma sa rai cewa zata zo gaida ni din ba don haka rashin ganin ta bai damay ni ba,, Itama dai din a daidai wanan lokacin suna ta kwasan rikicine da maigidan , Don yace sai tabar masa gidan shi don bazai iya zama da fitinanan mace ba shi, Sallawatu kan ta shiga tashin hankali sosai, don gaba daya ta rasa yadda zata shawo kan al,amarin, Duk yadda taso ya tsaya su fahinci junan su dashi yaya Abubakar yaki bat lokacin sa, Ta buga waya yafi a kirga yaki koda kallon wayan nata balle ya daga, Ta yi tunane barkatai ta yadda zata bullowa al,amarin amma ta rasa mafita akan zancen, Ta rasa tsaye ta kasa zaune a gidan don bata san abin yi ba, Gashi bata son fita ta koma gidan yan uwanta da take zaune, Don ko gida Lubbuna bata kaunar ta tafi don hakam tonon asirine agare ta, Sai faman sintiri kawai takeyi, don hankalin ta baya tare da ita,, Can daga inda take a zaune gefen mirror ta, taji karan shigowan motar shi gidan, Zubur ta mike, ta leka ta tagar dakinta, ta hangoshi yana kokarin zuwa parking space din gidan, Sosai tayi kokarin gurin tataro hankalinta, don samu ta fuskance shi, Daga labulen dakin ta take hango shi lokacin da ya shigo gidan dauke yar case din shi kamar kullun, Direct part dina ya nufa daga shigowan shi gidan abinda yasa Salawatu sake dan guntun tsuki ke nan a lokacin, A take numfashinta ya shiga kai da komo wani azabbaben kishi ya ziyarci zuciyar ta, sai ji take tankar numfashinta zai dauke,, Sai kuma ta tuna cewa yanzu fq ba lokacin kishi bane tukun dole ta aje komai a gefen, Ta fuskanci yadda zasu sasanta da maigidan nata wanda izuwa yanzu duk ya jagula mata lissafi,

****** ********** ****** Kwance nake cikin dakin nawa saman gado na sai kuma Maman Biu wace ke zaune daga kofa tana dan lazimi irin ta manya idan an fara girma, Da sallama a bakin shi ya shigo dakin inda yake kokarin gaida Maman Biu tare da mata ya gajiya, Ta ansa da fadin lafiya kalau ya kokari da aiki ? Dan murmushi Yaya yai mata yana cewa Alhamdullah, Ya maijikin ta ji sauki ko ? Ta bashi amsa da cewa ai jiki yai kyau, don yau kan Alhamdullahi gaskiya don babu matsalar komai, Kokarin tashi Maman Biu ke yi don ta fita, daga dakin, saboda ta bamu guri, Daga gurin da na ke kwance nace wa Yaya sanni da dawowa , Ya dan ya mutsa fuska yana kara matsowa gurina yace ya jikin naki ne ? Nai murmushi nace naji sauli sosai yaya, Alhamdullah, ban jin komai yanzu ai, Ya dan ya mutsa fuskan shi yana cewa naso nazo nadauke ku da kaina amma sai kuma ga meeting yazo muna, Nace yaya aiba komai tunda ga driver da malam Abdullahi sun zo ai, Yaya ya saki murmushi, ya ce ok barin tafi indan watsa ruwa in fito, Zandan fita in samo maki fruit don likita ya ce a dinga baki fruits da vegetables kina ci,, Nace cikin dan murmusawa ai nasamu lafiya Yaya ba sai naci ba, Har yakai kofa sai ya juyo ya kalleni tare da cewa hmmm kawai, Yasa kai ya fita daga dakin yayin da na sauke yar ajiyan zuciya Saboda nasan cewa yanzu yaya ya daina fushin da yakeyi dani,

Yana shiga daki kamar yadda yace din bathroom ya shiga ya watso ruwa ajikin shi don yaji dadin kara fita,. Jin fitowan shi yasa Salkawatu da ke zaune tana jiran fitowar shi yin, Firgigit ta mike tsaye daga zaunen da take tana nufar sa, Duban ta yakeyi a cikin mamaki da ganin karfin halinta na zuwa dakin shi, Duk da irin kashedin da yayi mata na cewa kada ta yarda ya dawo ya samay ta a gidan shi Cikin daure fuska ya ke kokarin zuwa gurin wardrobe din shi don daukan kaya, Kasa takai da gwiwowin ta har biyu tana ce masa don Allah yayi hakkuri ya yafe mata, Haushi da takaicin ta ne suka rufe masa zuciyar shi,, Tayaya take nufin zai iya manta wanan abinda Salawa tai mashi a ratuwan shi, Takara cewa dullah dun Annabi Mohammed (S,A,W) kayi hakuri Oga sherin shedan ne Ta hada hannayen ta biyu guri guda tana cewa iam so sorry Oga Banyi haka da wani manufa wallahi just dai akasi aka samu kawai, Ya girgiza kan shi lokacin da tace hakan tare da mata wani irin mugun kallo, Yace look Salwa zan iya maki sauki saboda Allah da Annabi Mohammed, Don haka sai kinbar gidan nan na two days I am telling you,, Wani irin mugun shock taji don jin abind yace mata,na zancen barin gida, Yace cikin bacin rai I don't know who you are before , , Wani irin kallon mamaki tai mashi don jin abinda yace mata, tasan cewa rayuwan shi ya kai karshe ga baci, Ya ci gaba da cew kin bani mamaki Salwa do min banzaci haka ba daga gari don nazaci samun peace of mind daga gurin ki saboda you are mutual enough, Kokarin riko mashi hannu tayi yai sauri ya ja baya daga gurin ta, ke yana mai ture ta, Wasu irin hawayen takaici ne suka zubo mata alokacin don takaici, A take ta soma rera masa kuka adakin cikin wani irin murya mai ban tausayi, Yace ke ce kika boye min true colour dinki don ban san cewa haka kike ba, Yarinya karama acikin ku ma tafiku kwantar min da hankali a gida idan anyi magana sai kuce wai nafi son ta ne Abinda Meenat ke mun na kulawa duk cikin ku babu mai mun shi, For god sake Salwa live me alone please ? I want to be alone for now Yama kasa karasa zancen shi ya yasa kai yana mai barin dakin har ya kai kofa ya juyo yana ce mata kada ki bari indawo in samay ki a nan, Ganin zata nufo shi yai saurin fita yabar mata daki inda yabar gidan gaba daya, Wani sabon kuka Salawatu tasa a gurin inda ta durkusa ita kadai tana ta rusa kuka har sai da tagaji ta sauko daga sama zuwa part din ta,

****** ********** ****** Ina daga kwance naji motsin mutum anshigo dakina, A zato na ko Maman Biu ce tashigo batare da na juyo ba nake cewa Mama don Allah ki dan kashe min Ac din nan sayi nake ji, Naji an kashe AC din amma ba,ai magana ba don haka na juyo don ganin kowaye, Salawa ce tsaye da rinanun ifon ta da tasha kuka su kayi ja, Ganane ya fadi lokacin da na gan ta amma sai Allah ya bani ikon fadar kalman nan da akace yana tarwatsa muguwar kishiya, Watau La,illah,ha,illah Mohammed rasululah,,, A hankali naga ta tako zuwa inda nake kwance ta zauna Idon ta na mai zubar da hawayen nadama cikin wani irin ban tausayin yanayi, Kaina nakawar gefe saboda nasan cewa bata kaunana har cikin ran ta kawai dai muna funci ne ya kawo ta, Amma yadda naga babba da ita tana kuka agabana sai ta bani matukar tausayi, Takira sunana cikin muryan kuka tace Meenat nazo ne in baki hakkuri bisa ga abinda ya faru, Wallahi banayi shi bane intentionally, kawai dai haka Allah ya kawo, Ta dan dafani a hankali tace don Allah don Annabi Meenat kiyi hakkuri, sherin shedan ne, Nadago idanuna na kalle ta sai naji tausayin ta ya kamani Nace Salawa ina iya kokarina inga cewa inawa ko wacen ku biyayya don babu sa,a ta acikin ku, Ta dago idanunta sharkaf da hawaye tana dubana dasu, A idon nata sai naga babu alamar yaudara cikin su, Nace a hankali komai ya wuce insha Allah Allah ya yafe muna baki daya, Ta ansa da fadin nagode, Sai naga taci gaba da rusa kukanta hankali a tashe tace, Meenat Yayan ki ya dauki zafi dani sosai don yaki saurare na kamar yadda ke kika saurare ni, Nace kiyi hakkuri zai sauko shima insha Allahu, Ta kara cewa ta gode alokacin datake mikewa tsaye don barin dakin nawa, Daidai lokacin da Maman Bi,u ta shigo dakin tana ma Salawa kallon mamaki, Sallawa na fita Maman Bi u ta karaso gareni cikin damuwa tana cewa may wanan yazo yi gurin ka, ? Tanayi tana dan duduba min jikina tana yi kamar tana neman ganin wani abu, Mama tace Meena Meena kayi hankali fada wanan matan mugune sosai wallahi, Wanda yai ma dukan har ciki yafita may zaizo yi gurinka kuma don dadin baki,,,, Nadan murmusa nace Mama na sani nima dai don har dakina tana bani hakkuri,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 5⃣9⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL- WADUDU,,,

YAN UWA MUSULUMAI BARKAN MU DA WANAN RANAN MAI TARIN ALBARKA, YA ALLAH KA SADAMU DA RAHAMARKA YA ALLAH KA SADA MU DA NI,IMAN KA YA ALLAH KA SADA MU DA DARAJOJIN KA YA ALLAH KA SADA MU DA ALHERORIN KA, YA ALLAH KA SADA MU DA GAFARAN KA, YA ALLAH DARAJAN WANAN RANA KA SAUKE MASU CIKKAKAN MU LAFIYA, YA ALLAH WA YANDA BASU SAMU HAIHUWA BA ALLAH KA BASU, YA ALLAH MASU MAZA ALLAH KA KARA MASU ZAMAN LAFIYA DA KWANCIYAN HANKALI, YA ALLAH KA TAUSAYA MUNA KA BAMU MAZAJE MASU ALBAKA GA DUK WACE MA BATA DA,,, YA ALLAH KAI MAI,JIN KAN BAYINKA NE,ALLAH KA ANSA MUNA WANAN ADDU,OIN, KA SA MUNA JIN TSORON KA AZUKATAN MU KA BAMU IKON BAUTA MAKA BAUTA MAISTARKI YA ALLAH YA ALLAH MUN GODE MAKA MUN GODE MAKA DA KA YO MU MUSULMAI, ALLAH MUNGODE MA ALLAH MUN GODE MA, ALLAH KABA MU IKON CIKAWA DA KYAU DA IMANI, ALLAHUMA AMEEN👏👏👏👏👏👏👏👏👏👏

Kayan fruit's masu yawa Yaya Abubakar ya sayo min kuma na sha su so sai, ba kadan ba Naji dadin shan wanan fruit din da nayi don bakina yai min dadin test,, yanzu, Ganin na samu lafiya Maman Bi,u tace zata koma gida su kwana guda kawai tayi a gidan mu din, Gadiya sosai mu kai mata inda ita kuma kafin ta tafi sai da ta kara jamin kunne akan Sallawa, din, A lokacin da Mama zata tafi sai naji kamar a ce kada ta tafi gidan su anan zamuyi ta zama tare da ita, Tafiyan ta yasa na dan kara mikewa don kauda kadaici, na Ina zama ina kallon tv ina dan fita ina gyaran daki na, Da neman abinda zanci wa raina don ban girkawa gaba daya, gidan Ba,don komai ba sai ganin irin yadda har Anty Sadiya wace na ke gani kamar ta saduda, ashe har yanzu tana dani rike a zuciyar ta, Ta na min daukan kishiya a cikin rayuwan ta boyewa kawai take min, Sai da nai wanan ciwon na,kara sanin halin kishiya da kyau, Tsakanin Salawatu da Yaya Abubakar, wasan yar boya akeyi a gidan, Don haka bayan tazo dakina tai min magana akan inyi hakkuri aikin shedan ne, Sai ta bani tausayi sosai shigowan Yaya Abubakar dakina nake ce mashi don Allah yayi hakkuri abarwa Allah komai haka Allah ya kaddara, abin zai zo, Cikin wani kallo mai kama da hararan shiga hankalin ki tare da wani irin tsawa Yaya Abubakar ya daga min hannu yana ce min in masa shiru, Ni na aje masa ita ko shi ya aje ta da zan gwada mai yadda zan yi, da gidan shi, Kamar ruwa ya ci ni ban kara ko daga kaina ba tunda ya fara fadan shi kaina ya na a duke har ya fita, daga dakin nawa, Inda nima ya kara daukan zafi dani sosai don sai ban kara ganin sa ya shigo ba,

****** ********* ****** Iyanzu gidan mu komai lafiya ba wanda ke da lokacin wani, Idan gari ya waye maza sai su fita gurin neman kudi Don duk yawancin Iyayyen mu dan kudin da Yaya yake turo masu dubu hamsin hamsin sai suka dan fara sana,ar dogaro da kai da shi,,, Daga haka yanzu gaskiya abubuwan suyi dama sosai a gidan, Mama Ladi izuwa yanzu abin Yaya Abubakar ya fara daure mata kai sosai, Gashi tayi tayi dashi da ya saki Meenatu amma yaki sai ce mata ya keyi akwai abinda yake jirane, Idan lokaci yayi ai zai sakeni din, Ita kuma tasha alwashin cewa bazata yarda ta hada da irin zurian mu a cikin iyalin ta ba, Babana yanzu yan buga bugan shi sun kara yawa don yakan tafi kauye ya sayo abin da zai yi saurin shiga idan ya kawo Birni, Hakan yasa zaka fahinci samun walwala saosai a tare da shi yanzu sama ga farko,

Hajja wace tun bayan dawo wanta kasan bargu wurin bokan ta batai wasa ba gurin ganin ta yi duk abinda ya umurce ta dayi don ganin dodo ya dawo daidai kamar farko, Yanzu din ko abin yana da dan dama dama don dodon nata iyanzu ya rage yawan langabewan nan sai aukin shan ruwa don yazu duk yadaina yawan shan ruwan nan sosai, Ta tara daki a kayan masarufi masu yawan gaske amma bata kaunan ta sai abin koda ashirin ne, tafitar da kudi, Bata kwantuwa ko kadan sai in ya kai mata dole dole zaka ga tafitar da kudin,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull