Tarko complete novel - Chapter 43
Tarko complete novel Chapter 43: Tarko complete novel Chapter 43. ****** ********** ****** A gurin da na idar da Sallah don nafara dazun da rana da naga…
3,183 words
****** ********** ****** A gurin da na idar da Sallah don nafara dazun da rana da naga jini ya dauke min, Nan nake zaune bayan Salah isha,i ina tilawa a hankali, Nadauki lokaci mai tsawo ina karatun don babu abinda zanyi, a lokacin, Anty Sadiya itace da girki, a ranan bayan gama abincin tane, ta gyara guri sama sama, Aikin duk ya kai mata ko ina sai faman fada takeyi a cikin zuciyar ta, Tana cewa ita bazata iya wanan aikin wahala ba gaskiya, Yaya Abubakar ya zauna don ya ci abinci da ta girka masu, Ga ido abincin ya bashi sha awa sosai har yana jin dadin ganin ta, ta iya girki haka yanzu, Tun gurin diban abincin zuciyar shi ta fara tsinkewa, Don yana saka hannuwan shi yaji tuwon yai ruwa sosai, Bai so ba ya,kai ga bakin shi don azaton shi miya zaiyi dadi yasamu tuwon ya wuce mai, Ai da sauri ya dawo dashi ya kalli gurin da take a fusace yana cewa yo ga tsiya, Manene wanan haka Sadiya ? Sai ta tsuke fuska tace abinci mana , Abinci fa ki,kace ? Yanzu saboda Allah Sadiya shekarunki da zaman ki yar hausawa kuma tallaka ace wai baki iya tuwo ba kamar ki, ? Ya mike kawai ya sa kai ya wuce sama abin shi batare da ya juyo inda take ba, Sai cewa Sadiya tayi yanzu saboda Allah menene laifin wanan abinci dai ina dai tuwon ne bai yi karfi ba kawai, Saidai Itama da kan ta tana kai loman tuwon a bakin ta sai ta tsuke fuskan ta, Sai a lokacin ta tuna cewa bata saka maggi a miyan ba fa, Mikewa tayi tabar gurin tare da tatara kwanonin ta, Daga dakina bayan na tashi yunwa ya isheni don haka na,fito neman abinda zanci, Naga kula a rufe sai na bude tuwo na gani na shinkafa, saidai tun ga idona tuwon yai min ruwa tuwon sosai, Amma da yake ina son ci sai na yanka hakana na zubu miya mai yawa kin san mu mutanen hausa da son miyan vegetables,, Nazo saman dining na soma ci loman farko da kyat na samu na hade shi ya wuce, A take na kara kallon tulin abincin da ke gabana sai naji wani iri, Ga wani amai da ke taso min kamar zan kife, don gaba daya na ji zuciya, na ya rufe min ban da sukuni ko kadan, Da gudu na mike zuwa dakina, kafin in kai bathroom har na fara shekashi, a hanya, Na dauki lokaci duke ina zuba amai gurin sanan na mike daga tsugunen da nake ina cewa wai, wai ina maida numfashi, Sam ban san cewa Yaya Abubakar yana tsaye kaina ba sai da na juyo don komawa bedroom dina, Ya na tsaye hannayen shi harde a saman kirjin shi fuskan shi babu walwala a cikin ta, Wani kallon tuhuma naga yana min ya, ce mai yasamay ki may kikaci ne haka,? Ina kokarin goge fuskana da haban rigana sai kokarin kaiwa saman gadona nake yi a lokacin, Har inda na zube saman gadon ina cewa wai, wai Yaya ya tako yazo ya tsaya a kai,na yana cewa May ke faruwane haka wai ina tambayan ki ne fa don dai ba zazzabi bane ko, ? Da kyat na iya daga mashi kai nace ba zazzabi bane kawai dai, abinci naci shi zuciya na ya tashi, Cikin karaji ya tambayeni wani abincin badai wanda Sadiya ta girka ba ko, Na daga kai alaman shi daidai lokacin da nake kokarin gyara kaina ga filo, Sai kuma naji tankar wani aman zaizo min take na mike zaune da sauri aiko aman ne na nufi bathroom, Sai da na samu na amaye guntun wanda ya rage min a ciki sanan na samu saida, Yaya yana kaina sai faman tambayana may zanci yakeyi nace mai ban son komai na koma na kwanta, Sai sauke numfashi guda guda nakeyi a wahalce ina faman cewa wai, ina juyawa don indan ji dadi, Barcin dole ne ya dauke ba shiri ban san inda nake ba, Tausayi sosai na ba Yaya Abubakar wanda ke tsaye a kaina yana min duban tausayi, Shima abinci zai fita nema shine yazo ya tambayeni may nake son ci ? Daga stairs din da yake saukowa yagan ni na f da gudu, Bayan yasayo min abinci ya samu still ina barci sai ya aje min su a gefen gado na yajawo min kofan dakina, tare addu,a
Acan cikin dare na farka da wani irin yuwan sai nake jin kamar banda ko hanji a cikina, Kokarin tashi nakeyi in fito don neman abinda zanci, Sai idona yakai ga ledan da yaya Abubakar ya aje min a gefen gado, Na mika hannu na na jawo ledan naji dadin ganin abin dake ciki, Kaza ce gassa irin na modern dinan yaji kayan hadi sosai sai drinks masu sanyi da kuma snacks, Kamar ance in kashe tocin wayana don na duba kofana nagan shi a rufe duk da haka saida na sa key daga ciki, tare da addu,a nayo fitsari, sai na hau cin kazan ina dan korawa da drinks din,,, Idan har ba ki manta ba na taba fada maki cewa nataba jin nishin wani abu a cikin gidan mu har sai da nai zazzabi washe gari A rin daidai lokacin da naji wancan din yau ma haka naji wanan nishi maiban tsoro, Tankar ana wani irin huci ne na gajiya ko na wahala, Dama saura kiris in gama don haka nai shiru ina sauraren shi, Inajin abin tankar bayan gurin parking space din motocin yaya hucin ke fitowa, A hankali na kauda ledan na dan jawo jikina tso nahaye gado naja bargo, Bakina yana dauke da addu,oi ina ja idona na rufesu, Gabana sai wani harbawa yakeyi tankar zai tsage, don tsoro, Can kamar minti talatin lokacin har barci ya fara daukana Sai jin wani irin ihu nayi tankar kunnuwa na zasu tsage, Numfashi na naji kamar zai dauke don tsoro, ihu nakara ji a karo nabiyu abinda ya tabbatar min da acikin gidan mu ihun nan yake, Ban san lokacin da nakai zaune ba don tsoro sai naji ihun da yafi na bayan karfi mikewa nayi wuf na nufi hanyan fitowa waje, Bakina dauke da addu,a, daga dakin Anty Sadiya waban ihun ke fitowa cikin tashin hankali, Ai gaba dayan mu muka nufi dakin nata dai lokacin da shima Yaya Abubakar ya sauko daga sama, Muna shiga dakin Sadiyan na hango abin kamar maciji tana kokarin fita ta window dakin ta, Shima yaya Abubakar ya hango wanan abin da idon shi , Sadiya tana tsaye hannuwa a kwandare kamar mahaukaciya sai ihun fitan hankali takeyi, Da sauri yaya Abubakar ya bi abin baya sai dai baiga komai ba, Ga Sadiya taki barin ihun da takeyi tankar zautata, hannu a kwandare mata, Yadawo ya samay mu adakin ina ta tofa mata addu,oi Shiya kamota yashiga karanto mata ayar Allah sai kallon shi nake yi da mamaki don zakace ko wani alaramma ne, A hankali nake bin abinda yake karanto mata daga inda nake zaune gefen su Sallawatu tafado dakin a firgice tana cewa, May ne may ke faruwa ne, wai ? Hannu yaya ya daga mata batare da ya tsaida karatun shi ba yana mata alaman tayi shiru, Muna tsaye cirko cirko sai mukaji Sadiya tafara nuna karkashin ta tana cewa a cece zai shige mata a gaba, A lokacin ji nayi tankar in tsula buli don tsoro daga gurin da nake, tsaye, Da sauri yaya yace a dauko mashi waya adakin shi, Daga cikin mu ba wacce ta motsa don tsoro ganin Sallawtu ba zata ba dole na mike don in tafi, Muryan shi naji yana cewa dakata in tafi nai wani dadeba ya dawo alokacin yana kokarin kiran nomban wani, Ashe mijin Fattu ce ya kira sai yafita da suka iso ya bude marsh kofan shigowa, Tare da mama suka shigo tana tambaya cikin damuwa may ke faruwa ne, Mama ce ta karasa gurin da yake rike da hannayen Sadiya da sukq zage a lokaci guda tankar ta taba ruwan zafi, Bayani yaya ke masu suma duk hankalin su a tashe yake suka kara fita suka zagaya gidan, Dai dai gurin window abinda suka iya gani shine tankar wani abu mai mai yabi gurin da jan jiki, Dole suka dawo aka dauke ta zuwa asibiti sai kokarin bude zanin ta takeyi wai abin yana nan yana kokarin shige mata a gaba, Tsoro duk ya kara kama mu a lokacin don haka akace Baba Hamza' ya tsaya atare da mu gida su kuma sai su tafi har mama,biu Mama itace bayan motan zaune tare Sadiya wace take tankar zautata, Mama tana rike da hanayen ta duka biyu tana tofa mata addua, Sun isa asibiti ba su gane komai ba sun daiyi mata alluran barci tare da cewa lafiyan ta kalau subari idan ta tash aga reaction din ta,
Wanan abin yai mugun tayar wa kowa da hankali don abune na sihiri, Har safe muna zaunr a babban falon zaune kowa da abinda take sakawa akai Nidai a halin yanzu gaskiya gida nake son yaya Abubakar ya maidani Don kwata kwata duk garin da ya fita raina sam ban son zama Jinkiran sallah yasamu mikewa kowa ta futa zuwa sallah, Bayan na idar na shiga kitchen na hada masu breakfast don akai masu, Batare da tunanen komai ba na kira baba Hamza nace ya kai masu asibiti na bashi key din motan da mukan fita da ita anguwa, Sosai sunji mamakin ganin yadda na aiko masu da breakfast a cikin lokaci, Abin da ita kanta Sadiya amatsayin ta na babban a gare ni batai tunanen yi ba, Yaya Abubakar hankali duk a tashe, yake don abubuwa sun zo mai acikin tashin hankali, Duk abubuwa sun zo mai acikin tashin hankali gashi ba kowa akusa da mu, sai, abokan arziki, Yaji dadin yadda su Maman Biu ke gwada muna mutunci, abinda farko su da Sadiya basu san cewa zaman lafiya da makwabta yana sa azama daya, Sai yanzu da farko yaso ya hanani hurda da su amma sai yaga idan ya hanani bazan so ba sai ya kyaleni kawai, Sai gashi daga baya zama dasu yai mashi dadi sosai tunzuwan Mama Ladi jinya Dakuma kwanciyana asibiti sai gashi kuma yanzu sun mashi wanan halarcin , Don mijin Fattu shike ta zirga,zirga a cikin asibitin,, Saboda shi yaya duk jikin shi yai sanyi sai faman tunane yakeyi barkatai, Babu abinda ya ke mai yawo azuciya kaman wanan dodon sihirin da yaga fitan shi daga dakin Sadiya, Don da bai gani ba da sai yace kila dai mafarkine ko wanu abu,
Sadiya ta farka cikin yanayin damuwa sai dai yanzu complain takeyi da cewa hannun ta, hannu ta na mata zugi da radadi, Ganin haka yasa mijin Fattu wanda Yaya ke kira da, Lawal, Yace wa Yaya su zo gefe su tatauna, akan zancen, A wani kauye can kauyen Suleja suka yanke shawaran zuwa tare, har ita Sadiyan da Mama, Basu wani dade ba suka iso gurin malamin, malami ne mai aiki da alkur,ani, Don haka yai mata addu,oi tare da bada abubuwan da za, adinga shafa mata da kuma hayaki, Tun anan ya bayar aka shafa mata wani abu a hannun nata, Cikin ikon Allah sai ta dan lafa jin zafin Sosai hakan yasa malamin samun yin magana da ita, Ta soma da cewa, Nafito daga dakin maigida zuwa nawa dakin don ban san may yasa ban son kwana can har safe ba, Bayan nashigo ne sai nadan kewaya daniyar inyi fitsari, Na duka shine naji kamar abu yana lasana koda na haska toci shine naga wani irin halitta, yana kokarin shige min a gaba, Ganin yana son shige min yasa nai kokarin rikeshi da hannuwa na ina ihu, neman ceto, Takarashe zance acikin kuka da neman mafita murmushi malamin yayi tare da kada kai yana cewa, cikin irin harshen su na gwari, Allahu Akbar wanan wani sihiri ne mai karfi gaskiya, To amma yanzu atafi a shafa wanan abubuwan da ya bata zuwa gobe in Allah ya kaimu sai su dawo harda ita don yana son yin istihara akai, Godiya Yaya Abubakar yai wa malamin tare da bashi kudi sai malamin ke cewa su bari kawai idan sun dawo sai su bashi, Amma sai yaya Abubakar ke cewa yadai karba ai sadaka ne ya bashi dole mutumin ya karba, Sunkamo hanya kowa da abinda yake sakawa azuciyar shi, A lokacin wayan Lawal mijin Fattu yai kara yadauka tare da Sallama Fattu ce a layin tana fada mashi cewa babu fa abinda zasu dafa agidan, Yadda Yaya Abubakar ya fahinci zancen mijin da matan sai suka bashi tausayi don ya fahinci sai ya fita gurin buga bugan shi yake samo masu abinda zasu ci, Don haka bayan sun kai su mama gida da Anty Sadiya inda muma muka bita dakin don mata sannu da jiki, Bayan kara yiwa, Mama bayanin magani Yaya yace wa Lawal yazo su fita tare,, Basu tsaya ko ina ba sai kasuwa nan suka sayi kayan stuff duk wani abin bukata sun saya aka loda wa mai Nape ya biyo su baya dashi, A gidan Lawal Yaya Abubakar ya tsaida mai Nepep inda ya umurci da a sauke kusan rabin sayayan da sukayo a kofan gidan Lawal, Mamaki sosai ya kama Lawal inda har ya kasa yin magana yakai wani lokaci tsaye a cikin mamaki, Sai da ya ji muryan Yaya Abubakar yana ce masa lokacin sallah magrib yayi, Yakamata su karasa massalaci don kada su rasa jam,i, Sunyi sallah sun ka fito don zuwa gida duba jikin Sadiya, Sai a lokacin Lawal ke cewa maigida ban sanbirin godiya da zan maka ba gaskiya, Don rabona da, samun irin haka tun lokacin da nake aikin Banki, Sai kwatsan wata rana aka turo muna da takardan sallama daga aiki har mu biyar, Batare da mun samu wani sallama da ga chan headquarter mu ba, Wanan dalilin yasa na sai da duk wani kaddaran dake gareni na dawo nan, nai muna wanan ginan, Sai nake fita kullun kasuwa ina yawon dillanci don mu samu abinda zamu ci, Yaya Abubakar yanisa tare da cewa ai aikin banki baida tabbas, Don idan tsiyan su ya tashi daga sama kawai zasu ce sun sallami mutum Ba don komai ba sai don kada suyiwa mutane sallaman barin aiki, kamaf kowa, Don haka ni sam ban dauki aikin banki acikin aiyukan kwarai ba, Lawal yace ai maigida mun sheda hakan sosai wallahi, don alokacin abin kamar zai tabamin kwakwalwa, Godiya na ga Allah daya bani mahaifiya irin mama wace tasan yadda zata kwantarwa da mutum hankali, Don da taimakon Allah da na ta har na dawo normal person dina, Takuma aura min Fattu diyar yar uwar ta don matar da na aura da farko fafir taki wai banda komai ita bazatai zaman wahala ba, dani, Tafi abinta tabar ni batare da ta tausaya min halin da nake ciki ba, Nisawa kawai yaya Abubakar yayi don ya fahinci matar bariki ce Lawal ya aura, Don haka ya ce Allah ya kyauta a ta kaice kawai, batare da ya kara cewa komai ba, Bayan fitowan su daga Sallah suka shigo a tare don duba jikin Sadiya, Sun samu tana zaune Mama tana shafa mata magani a hannayen ta da suka kunbura sukai wani irin jajir dasu, A daidai lokacin na shigo dakin dauke da kulolin abincin su ahannu, Bansan cewa su Yaya Abubakar suna dakin ba a lokacin don haka ina ganin su sai na koma baya da sauri , Hijjab dina na sa nafito na dawo dakin inda na gabatar masu da abincin su, Amma sai Sadiya take cewa bazata iya çiba don bata jin cin komai, Nadan koma kusa da ita ina cewa ko in hado maki tea mai zafi ki sha ta gyada mun kai kawai alaman eh, Bandade ba nadawo dakin dauke da cup din tea mai zafi da bread, Amma sai tace inbar bread din don ruwan tea din kawai zata sha, Gurin daYaya Abubakar yake tsaye ya kura mata ido dagani nazarin abubuwa da dama yakeyi a lokacin, Cikin dan tausa murya nace wa Yaya Abubakar Yaya abinci fa,? Sai da ya nisa tare da lumshe ido yake ce min Meenat zanci , Amma naso sai nai wanka tukun nace to barin hada maka ruwan zafi ko? Yadan lumshe idon shi kadan yace no kibarshi kawai kin san cewa ke ma ba lafiya bane dake, Kibi jikin ki a hankali don kada jikin ya tashi maki,don stress na iya saki kwanta again, Nai dan murmushi na ce, ai naji sauki Yaya zan iya insha Allah, Ya ce No ki dai bari kawai, a lokacin Salawa ta shigo dakin tana saye da wani dogon riga baka maidan karamin hannu kamar shimi, Kanta, ya saye da fullan mai net, wanda ke nuna kitson attachment din ta daga cikin sa, Sannu da zuwa tai masu yay Abubakar tare da jira mai zaice ba Ta juya tana duban inda Sadiya take tana cewa Sadiya ya jikin naki, ? Sai da Sadiya ta dan murmusa kadan sanan tace a hankali cikin daurewa Da sauki, Sai kuma dakin yai tsit a lokaci tankar babu kowa a gurin, Jin kada Salawatu ta juya yayin da zata bar dakin tana cewa Allah ya sauwaka,, Tabar dakin abinta zuwa dakin ta ba,ai wasu mintuna ba Yaya Abubakar yabi bayan ta, Kafin ya karasa fita nake cewa mijin Fattu malam abincin kaima sai yaya yafitone zakaci,? Yace kai haba aini yau maigida ya wadatar da mu Anan yake fadawa Mama irin alherin da Yaya Abubakar ya sai masu, Har dani dake gefe dakin sai da na taya su murna tare da godewa Allah Mun kai wani lokaci zaune mu na taya Sadiya da mama hira, Sai wani lokaci Fattu da maigidan ta sukai muna sai da safe, Bandade ba nima na nai masu saida safe na koma dakina sai dai zuciyata tab da tsoron abinda dare zai yi ywu, Na rufe kofana tare da jero addu,oin da duk na iya a bakina, Nabi duk wani kafa nq dakin na toshe da adduoin, A hankali na kwanta saman gadona a takure ina mai jin tsoron dare, Da haka har barci barawo yai gaba dani batare sa na sani ba,
ZEEE MAKAWA YELWA [8/22, 08:10] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 6⃣0⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH-AL- MAJEED
YA ALLAH MUNGODE MA DA KA NUFE MU DA GANIN WANAN RANAN MAI TARIN ALBAKA, YA ALLAH KA SA MUNA CIKIN YANTATTUN BAYINKA, YA ALLAH KA SADA MU DA RAHAMAN KA YA ALLAH KA TAUSAYA MUNA DUNIYA DA LAHIRA, YA ALLAH KA GAFARTAWA IYAYYEN MU, YA ALLAH KA KARA RUFA WA IYAYYEN MU ASIRI DUNIYA DA LAHIRA, YA ALLAH KA BAMU MAZA JE MASU MUTUNCI, ADINI SANIN YA KAMATA MASU, ALBARKA YA ALLAH KA GAFARTAWA DUKKAN QULLUMIN MUSULMIN ALLAH MAZA DA MATA BABBA DA YARO, TSOHO DA TSOHUWA , YA ALLAH MUN GODE MA YA ALLAH MUN GODEMA YA ALLAH MUN GODE MA DA KAYO MU MUSULMAI YA ALLAH KA KARBI TUBAN MU, KASA MU MUTU MUNA MUSULMAI ALLAH, AMEEN YA ALLAH 👏👏👏👏👏
BARKAN MU DA SALLAH YAN UWA