Tarko complete novel - Chapter 44
Tarko complete novel Chapter 44: Tarko complete novel Chapter 44. Bayan tafiyan Lawal da iyalen shi Yaya Abubakar ya koma dakin shi don ya huta, Sai kuma…
3,278 words
Bayan tafiyan Lawal da iyalen shi Yaya Abubakar ya koma dakin shi don ya huta, Sai kuma zuciyar shi ta kasa barin shi ya huta din,don tunanen abin mamakin da ya auku yau a gidan nashi, Lalai badon da idon shi ya ga abin ba da bazai taba yarda ba , To may ye wanan abin ya tambaya da kan shi, daga ina yake haka, May ya kawo shi gidan shi mau yake so a cikkin iyalin shi Iska mai zafi ne ya furzar da ga bakin shi tare da kai ma hannayen shi naushi a,lokaci guda, Malam tsoho ne ya fado mashi a rai don dole ne ya fadawa tsohon wanan abin saddabarun da ke faruwa a gidan shi, Sai ya kai duban shi ga agogon wayan shi take yana sa a ran shi cewa dare yayi sosai a lokacin, Don haka dole ne ya bari har zuwa gobe da safe ya kira malam din, Da wanan shara ya shirin kwanciya barci inda ya bi lafiyan gadon shi, Sai bayan ya kwanta yake tunanen cewa Meenat bai ganta a waje ba tun bayan dawo wan shi gidan, Hakan yasa shi mikewa da nufin zuwa dakin nawa don ya duba ya ga halin da nake ciki, Salawatu ce ta shigo dakin, ta na saye cikin, wani rigan barci mai kama da babu komai a jikin ta a lokaci, Sau guda ya daga kai bai kara kallon ta ba, Zagayowa tayi ta bayan shi ta rungumo shi tana cewa, Sweet Oga har yanzu fushi kakeyi danine please ? Tana son su hada baki yai saurin ture ta yana cewa Salawa are you out of your sense ? Baki san halin da nake a ciki bane halan ? Har zaki shigo kina son in making love da ke a haka Cikin wani irin juya ido takara kwanti mashi a jiki tana cewa to amma ai sai naga taji sauki ko ? Wani mugun harara ya watsa mata yana cewa ok don ciwon ba a jikin ki yake ba ne har kike ganin cewa, zaki samu kai na a yau din, A gaskiya ni ban gane ba dear duk kwanakin nan baka da time dina sam, Kai ya kada yana cewa look Salawa, ban son yawan magana don ina a cikin yanayi yanzu haka , Sai dai duk da irin yadda Yaya Abubakar yake neman ta kyale shi Salawatu bata yarda ba don saida tai irin halin su na matan bariki ta hilance shi, Abinda yasa Yaya Abubakar ya manta da zancen zuwa duba ni a lokacin da yai niya yi ke nan,
****** ********* ****** Malam tsoho wanda tun a tsakar dare bayan ya idar da sallah nafilan shi kamar kulun daga gurin da yake a zaune barci ya dan fisgeshi, Mafarki yayi da wai gashi a gidan Yaya Abubakar, Inda yaga matan shi a cikin damuwa, sai kuma shi Abubakar din wanda, yafi kowa shiga hall n damuwa, Sai kuma aka dan nuna mashi fuskan mace tare da wata, tana, ta azabantar da ita ta hanyan sihiri, Firgigit ya farka sai yaga har tasbahan da ya ke rike a hannun shi yana ja ya fadi kasa,, Hankalin malam ne ya tashi inda ya kai indon shi ga mamakeken agogon bangon dake dakin don ya duba time, Karfe uku da wani abu na dare lokaci ya nuna mai hakan yana nufin cewa tsakiyan dare ake, Abinda ya keyi ne yaci gaba dayi tare yi wa family din jikan shi addu,an, neman tsari daga sherin shedan,
Kamar yadda wa yan da ke kwana raye gurin kokarin kai kukan su ga Allah Ubangiji Subbahanahu wata, ala, mai jinkan bayin shi, Barci da shedan kan dan so rinjayen mutun a waau lokuta irin haka, Malam tsoho still, barcin ne kuma yaso yakara rinjayen shi har ya dan fara mafarki Kamar farko wanan katon da mamaki ya tashi don wace ya gani acimin mafarkin nashi a lokacin, Hakane ya tabbatar mai da cewa lalai akwai matsala sosai a gidan Jikan nashi duk yadda aka yi, Hakan ya kara sa malam qaimin gurin ganin yai wa jikokin nashi addu,oi,,
****** ********** ****** Ya Abubakar bai farka ba sai gabanin asuba inda ya sauke idon shi akan Sallawatu wace ke kwance rub da ciki tana barci a gefen shi, Dan tsuki yayi yana kokarin mikewa don ya duba time, I zuwa yan karfe biyar saura na asuba hakan yasa shi sauri mikewa da sauri don, bai zaci cewa lokaci ya kai haka ba, Don yaso ace cikin dare ya ziyarci su Maman Bi u da Sadiya don ya ga irin halin da su ke ciki Amma sai wanan shu,uman matar tashi ta ja hankalin shi har ta shagalar dashi, Bathroom ya fada inda yai wanka tare da dauro awala kafin ya fita massalaci sai da ya tafi dakin Sadiya, don ga kwanan su, Yasamu mama tanawa Sadiya fitara duk da sanyin Ac dake a dakin Amma sai korafi Sadiya keyi na cewa ita zafi takeji sosai, Cikin mamaki Yaya Abubakar wanda ke saye da jallabiya a jikin shi, Yake tambayan Maman Bi,u abinda ke faruwa take fada mashi irin halin da suke ciki, tun gabanin asuba,,, Gab da Sadiya ya nufa yana mata sannu da jiki tare da tambayan ta yadda take ji, Bayan yasamu tai dan mashi bayani sama,sama ya yi mata addu,, a Tare da tofa mata aruwa yabata tasha yadauko mata wani standarding fan yasa masu a dakin, Take tasamu barci daga haka ya wuce yin sallah asuba, Sai da gari yai haske sosai, sosai sanan Yaya Abubakar ya shigo gida Ya samu ina dakin gurin su Anty Sadiya ina masu yaya dare,? Ganin da yai min zaune a gefen carpet din da Mama take akai, na wani takure guri guda kamar mai jin sanyi, Ina kwana nai masa da,ga inda nake zaune a cikin ladabi tare da girmamawa, Gurim da nake yake duba na yana cewa to yaya jikin naki ? Na ansa mashi da cewa a cikin wani irin murya da Naji Sauki, Yace yanzu bakya dai jin komai ko ? Eh nace mashi kaina yana a duke, Sannu Mama ya maijikin bata farka ba har yanzu ko ? Eh mama tace mai ai Alhamdullahi tun dazun barcin takeyi, Kafin ya ce wani abu wayan shi ce tai kara alaman kira, ya shigo mai, Saida yai tsuki don yana mamakin wanda ke kiran shi da wanan safiyan haka ? Malam tsoho yagani a rubuce saman screen din nasa, Yai matukar mamakin ganin kiran malam din a wanan lokacin, Cikin mamaki yace malam tsoho Abinda yasani saurin dago kai ina duban shi ke nan, A take kuma naji gabana ya bada dam a lokaci guda, don jin sunan wanda ya ambata, Gaisawa naji sun fara yi tare da tambayan lafiyan mutanen gidan Sai da naji suna ci gaba da zance yasa hankali na yadan kwanta kadan, Don nasan cewa, lafiya babu wani abinda ya faru ke nan a gida, Saidai kuma ina tunanen dalilin wanan kiran da wanan safiya haka,, Mikewa Yaya Abubakar yayi zuwa waje inda suka fara zance da malam din,
Malam ke tambayan Yaya Abubakar da cewa lafiya dai ko kake da iyalin ka? Yaya Abubakar yarasa abinda zaicewa malam din sai yai dan shiru Malam yakara tambaya yana cewa domin jiya cikin darai nai mumunqn mafarki a kan ku, Innalillahi Yaya Abubakar ya ce da yaji may malam din ya ce mashi, Cikin murya irin ta damuwa yake cewa wallahi malam abin sai a hankali domin gaskiya, Meenatu ce ta fara samun matsalan barin ciki satin da ya gabata, Bayan tadawo gida da kwana biyu sai kuma ita Sadiya tasamu wani matsala, Subbahanallahi malam ya furta a cikin damuwa, tare da nuna kulawan shi, Ya jikin ita Meenatun yanzu da sauki ko Yaya Abubakar ya amsa mashi da cewa taji sauki sosai don kwana guda tayi aka sallamay ta daga asibitin don jinin da yake zuba ya tsaya da wuri, Allah ya kawo rabo na moriya inji malam tsoho saidai yaya Abubakar yakasa ansa mai Ameen a fili sai dai a cikin zuciyar shi, Malam tsoho yace ita kuma dayar may ke damun tane fa,? Ya Abubakar yace malam al,amarin ne kamar na jinnu wallahi don abin ma ban san yaya zan fada maka ba, Amna dai gaskiya zan iya ce wa aikin jinnune kawai don yadda abinke mata, A take Yaya Abubakar ya kwashe duk yadda abin yafaru ya gayawa kakan nashi, Sai da malam ya gama sauraren sai ya nisa yana cewa lalai duniya tai nisa, sosai Abubakar, Da a kusa kake dani da akwai maganan da zamuyi na musan man akan wanan zancen Shiru yaya Abubakar yayi yana sauran malam din acikin tashin hankali Shiru su kayi na dan wani lokaci bayan malam din ya kare zancen shi, Ya Abubakar ne ya dan kau da shirun da cewa, yanzu malam may nene mafita,? Malam ya nisa yace Allah ya kare ya tsare amma gaskiya dole mu san abinyi, Malam tsoho yacs amma duk da haka Wadda zai taso yau din nan in sha Allah, Sai dai duk wani bayani sai bayan ya iso insha Allah zata samu lafiya, sai daga baya musan abin yi akan zancen, Yanzu lafiyan ta yafi muna komai don haka sai mu tashi muci gaba da mata addu,a, Ya Abubakar yace gaskiya ne malam nan ma akwai wani wanda mu ka fara zuwa gurin shi kuma da alaman aikin sa na da kyau. Malam tsoho ya ce hakan na da kyau, amma don Allah idan Allah ya kawo Wadda lafiya ka tabatar da cewa kasha magani, Insha Allah inji Yaya Abubakar yana mai cewa kakan nashi, Malam tsoho yakara tambayan jikin Meenatu da fatan babu wani matsala atare da ita, yanzu, Nan yaya ya tabbatar mashi da cewa na samu lafiya sosai,,, Sukayi Sallama inda yaya Abubakar ke ta godiya sai dai zuciyar shi fam da mamakin yadda akayi kakan na shi ya san zancen Sadiya,
****** ********** ****** Har zuwa wani lokaci babu abin kari a gidan don Salawatu tana can tana barci abin ta, Ga mara lafiya tana neman abinda zataci don yunwa, Sai bayan dawowansu Ya Abubakar daga kauyen da suka tafi karbo magani, suka, dawo, Yake tambayan abin karyawan shi Sadiya ce tafara mashi korafin rashin cin abinci tunda safe har yanzu sha dayan rana da wani abu, A fusace ya shiga dakin Sadiya wace ke kwance share,share saman gado, Tana kwasan barcin ta hankali a kwance da gani ko wanka batayi ba alokacin, Wani wawan duka ya kai mata abaya, ta mike a firgice tana cewa my dear, kadawo ne, Tambaya ya jefo mata da cewa ina breakfast din su Sai cewa tayi ban samu yi ba don nagaji sosai wallahi hakan ya sa ban tashi ba takarashe tana bata fuska, Ido Ya Abubakar ya kura mata cikin takaici yana cewa, Yanzu har da yar uwar ki da bata da lafiya baki masu breakfast ba ki ka bar su hakana, Mika tayi tare da daga hannayen ta sama ta hada su guri guda,, Tai wani mika wanda ya bayanar mata da duk wani sassan jikin ta, a fili, Wani irin tsukin takaici yayi yabar dakin cikin takaici, da bacin rai, Yana fitowa adaidai lokacin da nafito daga dakina zan shiga kitchen saboda wani irin yuwan da nake ji tankar banda komai a cikina don sai nike ji ko hanji babu,, Batare da nace mai komai ba na wuce gigice zuwa kitchen din, don neman abinda naci, Tun bayan dawowa na daga asibiti nake yawan jin wanan yuwan haka, Indomie na dafa nacika mai ruwa da yaji tun yana asaman wuta nafara diba ina ci, Ban juye a plate ba tun a cikin tukunya na cinye abina sai da na kusa gamawa na tuna da ruwa, Gurin fridge na nufa da sauri na balle goran ruwa na kafa kai,, Sai da na kusa rabin goran ruwan san na kula da Ya Abubakar wanda ke tsaye a kofan kitchen din hannayen shi a harde saman kirjin shi, Cikin dan kaduwa da firgita nace cikin dan in,in iniya Sannu yaya, Lafiya kike kuwa ina kokarin tatara natsuwa na nake cewa, Lafiya kalau nake yaya Kina lafiya kike cin abinvi haka kamar mayunwaciya, Nai murmushi kadan nace yuwan dai naji kawai shiyasa, Don tun da naji sauki sai na fara wanan yawan cin, Inaga kamar maganin da suka bani na karin jini ke sani wanan yawan cin da yawa, Ok kawai yace tare da tamvayana may Sadiya zataci ne mai sauki, Nace ko adafa mata noodles din itama ? Idan zataci a dafa mata shi din ko ? Na dafa mata nakai mata sai dai na samu kamar tana barci ne, Don haka na aje tare da juyawa, a lokacin naji fitowan Mama wace ashe tana bayi tana wankewa, Nan nake fada mata cewa idan ta tashi ga abinci nan, Maman Biu ta tabe baki tana cewa gidan ku babu tsari sam wallahi , Gida da mara lafiya za,a ce ba,a girka abincin safe ba har yanzun nan ? Murmushi nayi nace mama yanzu ne dai abin ya juta haka amma da farko ba haka zancen yake ba, Sadiyace ta bude idon ta daga gurin da take tana cewa tana son cin abinci, Ba bata lokaci aka bata abincin da na kawo mata tafara ci, Zan fita waje alokacin ne Sallawatu ta shigo dakin daniyar gaida Sadiya da jiki, Tun safe bata shigo gaida Sadiya da jikin ba wai sai yanzu, Ban tsan manin cewa Anty Sadiya ta karba mata gaisuwan nata ba, Don banji muryan ta ba agaskiya, Bata wani tsaya basai faman wani ya tsune fuska takeyi wai ita dakin ba ventilation, a cikin sa sam, Ni dai nai tankar ban fahinci abinda ke wakana a tdakanin su ba, Sai muryan Salawa mukaji tana cewa Ok Allah ya sauwaka ko, Ta sa kai ta fita tana wani irin karairaya ga tafiyan nata, Ina daga inda nake tsaye wani murmushine ya subbuce, min Sai naji Sadiya na cewa muguwa kawai sai ta cuci mutun tazo tana nuna ita bata san komai ba, Nan Sadiya ta fara cewa nasan babu inda wanan abin yake sai daga gurin Salawa, Don na fahinci muguwa ce ta karshe sosai, saboda, Ance idan mutun yai maka mugun asiri bazai zo gaisheka ba, Ban san ya akayi bakina yace to ai gata tazo gaishe ki ita, ko ? Inda nake tsaye Sadiya ta kalla tace cikin takaici, Meenatu baki san komai ba, Wanan matar da kike gani muguwa ce don ni sam ban yarda da ita ba tun farko, Baki ganin ko mutum yana ciwo bata damu da ta gaida mutum ba, Nace niko sai na dauka kishine yake sata yin hakana, Don idan kin kula ita ra,ayinta duk a watse abar mata Ya Abubakar ita kadai, Sadiya tace ai tasan yana da mata ta aure shi dn may bata tafi ta auri wanda baida mata ba, Murmushi nayi ina cewa kowa dai da halinsa wallahi mna ai zaman lafiya yafi zaman irin wanan, Kishiya fa idan ka hadu da ta kwarai abokiyar zamace, Sadiya tace kikace ko Meenatu ni ba zan taba yarda da kishiya ba, Don duk yadda kuke tana son jin sherin ka sabanin hairan, Wani irin mamaki naji a lokacin da ta fadi hakan don tana nufin har ni bata yarda dani ba don zan iya mata sheri, Muryan Maman Biu naji tana cewa ni dai wanan matar batai min ba gaskiya bata dace da maigidan ku ba, Ai duk matar da bata son kwanciyan hankalin mijin ta bata san may ta keyi ba ke nan, Sadiya tace ba kowa ke harin rayuwa na ba sai wanan makiran don nasan cewa kowa rantsuwa nayi ban kaffara, Mamakin ta daine ya kara kamani don jin ko may tace akan Sallawatu,,
****** ********** ****** Da yamman ranan suka koma gurin maimagani harda Sadiya, sai dai mama bata samu zuwa ba tace kan ta na ciwo, Sun samu malamin a gida sabanin dazun da safe da suka zo,, Amma yace ace da safe yamna su dawo su samay shi, Bayan yadan dade yana wasu yan abubuwa irin nasu na malamai, ya dago kai yana kallon su, Yace gaskiya Alhaji a kwai matsala sosai a gidan ka, Saboda idan har ba a fitar da wanan fitinar ba a gidan to irin haka zaku dinga gani, Wani irin nisawa Yaya Abubakar ya sauke don jin may malam yace, Don haka ya tambaya da cewa malam ai sai in sake gida ko, Don ina ganin cewa hakan zaifi man sauki don ba musan ina wana mugun abin yake aje ba, Malam wanda yai shiru yana kallon wani tasbaha dake hannun shi, Can ya nisa ya na cewa ai ba a ainifin gidan akasa wanan kullin ba, Asalima ba a wanan gatin da kuke yake ba, don haka kaga ba zanven gida bane, Yace tun can garin ku kazo da abinka, don haka sai katashi tsaye sosai don neman mafita, Saboda ai ba wanan ne karo na farko da hakan yafaru ba, Sai dai ku baku iya gane hakan kuma du inda kuka tafi wanan abin yana bibiyan ku, Yanzu duk yadda akayi akwai akasin da akasamu da har kuka gan shi da idon ku, Malamin yace barin fada maka gaskiya Alhaji idan har a gidan ka za ai ciki to ba zai taba samuwa ba ga matan ka, Sai dai idan har babu wanan kullin akusa za,a iya samun ciki bance maka a,a ba, Wani irin firgicin rayuwa suka shiga gabadayan su sai Lawal ne ya ke kara tambayan malamin da cewa, Yanzu malam baka fada muna yadda al,amarin yake ba sai magana kake muna adunkule Murmushi malam yayi yana cewa bazan ce komai ba amma bada dadewa ba komai zai walwale insha Allah,,, Kuje kuci gabada yin abinda na baku mu gani har Allah ya bata lafiya,
Baba Wadda ya iso garin alokacin su yaya basu gida sun tafi gurin katban magani, Don haka ni kadaice agida saboda Salawa tafita ita ma alokacin, Nan Baba Wadda ya fitar da sakon da malam ya bayar akawo min harda zuma mai yawa acikin sakon nakarba tarr da godiya nakai dakina na boye, inda babu maigani, Abincin da na girka na debowa Baba Wadda, tare da bashi abin sanyi don jika makoshin sa,
A hanya su Yaya Abubakar suna dawo wa daga suleja sai zufa yake faman sharewa, Don maganganun malamin yana mashi yawo a rai, Kenan ita Meenatu da ta samu ciki ba,a nan ta samay shi ba ke nan ko? Sai ya tuna cewa ai, duk yadda akayi kenan tafiyan mu kasar Niger Republic nasamu cikin da ya zube kenan, Bai san lokacin da ya furta Innalilahi, Wa,inna,Alaihim Raj,un Yanzu yaya zaiyi ke nan ana nufin crwa idan har zaiyi ciki da wata mace sai bai kusa dawa ke nan, Bayani dai ya nuna cewa, Meenatu dai bata aciki ke nan tunda har ta samu ciki, Innalillahi ya kara furtawa a filli, tare da goge gumin da ya karyo mai agoshi, Watau rashin haihuwa agidan shi yana da wani nasaba kenan da wanan abin sihirin da ya gani, Ashe zama bai gan shi ba ke nan don dole ne ya mike, on neman mafita akan al,amarin kafin yai yawa don gaskiya iyanzu yafara son haihuwa, a rayuwan shi,,,
ZEEE MAKAWA YELWA,, [8/24, 05:58] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 6⃣1⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH-AL-BAAITH
SAKON GAISUWA DA BARKA DA SALLAH GARE KU MASOYA ZAINAB MAKAWA, FATAN ALHERI ZUWA GARE KU KAMAR YADDA KU KE MIN, IDAN NACE ZAN TSAYA ZANA SUNAYEN KU BAZAMU SAMU ZANA LABARIN BA YAU, AMMA DUK MAI KAUNATA DAKU MA YAN UWA MUSULMAI NA DUNIYA ZAINAB NA MAKU BARKA DA SALLAH ALLAH YA MAIMAITA MUNA,,,,,,