Tarko complete novel - Chapter 47
Tarko complete novel Chapter 47: Tarko complete novel Chapter 47. ****** ********** ****** Washe gari ina cikin wani material lace yellow da purple din…
3,030 words
****** ********** ****** Washe gari ina cikin wani material lace yellow da purple din flower a jikin shi sai stones a kasan shi, Dinkin dogon rigane akai min dashi, sai na dan zauna a gaban mirror nayi simple make up, a fuska na, Na dauko takalmana na saka akafana, sai kamshi turaren shekkah ke tashi a jikina, Dakin Anty Sadiya na nufa don in gaida ita, da jiki, don tun safe ina ta aikin gyaran falon mu da yai dauda, Sai kuma girkin da na hada don karyawan jama,an gidan, Karfin hali kawai nima na keyi don jiki na sam bana jin karfin sa, Abin karin ta nadauko daga kitchen zuwa dakin ta daga kofan dakin na tsaya ina sallama inda Yaya Abubakar dake acikin dakin yai min iso, A zaune take da alaman wanka tayi, don magani na ga yana shafa mata ajikin ta, Gefen da take zaune na nufa da tire din na aje mata ina fuskan tar ta nace ina kwana Anty Ya karfin jikin ya kuma dare ,? Ta amsa a hankali idon nakai ga hannayen ta sai na ga duk sun faffashe suna dan fidda ruwa,, Magani Yaya Abubakar ke kokarin kadawa ga cup na karba na kada na nufeta dashi, Da kaina na kafa mata a baki har saida ta shanye shi gaba dayan shi sannan cire cup din ina mata sannu da jiki, Shiru mu kayi dakin gaba dayan mu ba mai cewa komai daga cikin mu, idon mu ga hannayen Anty Sadiya dake fitar ruwa, Muryan Yaya Abubakar naji yana cewa wanan matar zuwa yaushe zata turo matar da take magana a kan ta, A hankali na dan dago kaina da fuskana mai nuna damuwa na ce ban san lokaci ba gaskiya . Najuya acikin rashin walwala na bar dakin don zuwa inci gaba da abinda na keyi,, Yaya Abubakar wanda ke daga tsaye gefen gadon ya bini da idanu har na fita daga dakin, Ina fitowa Salawace na gani tana fitowa daga kitchen ta hada tea da wani leda mai katon bread a cikin sa, Kala bata ce min ba sai kokatin gittawa take a gabana, Sanin cewa gaba baida kyau yasani daurewa cikin dakiyan zuciya nace, Ina kwana ya jikin ki ? Kamar bazata ansa min ba sainaji bayan ta dan gwautani kadan tana cewa lafiya, Ta wuce tana wani irin karairaya tare da dan matse fuskan ta, gare ni, Ni dariya ma tabani sai na tuna da zaginta da Antyn Saloon tayi jiya, Ban wani dade da shiga dakina ba naji muryan a kofan dakina a na kwada min sallama, Nafito don ganin ko waye kawar Antyn Saloon ce da wata mata baka, A cikin dan sakin fuska nake cewa a, Anty kece tafe yanzu,? Sannu ku da zuwa daga nan muka shiga gaisawa da su tare da tambayan yadda suka koma jiya, Nan take ce min jiya bayan ta koma gida taje gurin matar da take magana akai , Ba,a samu wani jayayya ba ta yarda da cewa zata zo tagwada ta gani, Kawar Anty saloon tace to ki saurara da,kyau tallo, Wanan din itace muka sani kamar yadda na fada maki da farko kishiyar ta ce ba lafiya muke son ki dinga taimaka mata dan Allah, Tambaya tayi da cewa ina mara lafiyan nace tana dakin ta , Nace amma fa kin san cewa jiya sai andaure don haka don Allah kiyi hakkuri please, Tace babu komai insha Allah zata yi kokarin tun madam ce ta kawo ni, Nace to mungode barin je inga maigidan in fada mashi cewa kin iso ko,
Da sallama na tura kofan dakin yana tsaye yana daurawa hannuwan shi agogo a,hannu guda, Jin sallama na yasa shi dago kan shi ya na duba na daga inda yake tsaye, Ban karasa shiga daga dakin ba nace yaya matar ce tazo da mai aikin , Wani irin kallon ya watso min yace da karfi, ke, Zonan waye zaki tsaya daga can kina fadawa magana haka kai tsaye, Baki naturo gaba cikin nuna alaman fushi azuciya na, Dan nesa dashi kadan na tsaya ina dan kallon shi ganin irin yadda ya tsure ni da ido yasani dukar da kaina kasa, Banyi aune ba sai jin shi nayi ya rungumoni zuwa jikin shi , Kokarin kwacewa daga rikon da yai min na keyi, na ce, nika sake ni please ? Banyi aune ba sai ji nayi yana kokarin kai bakin shi a cikin nawa yana son yi min kiss, Duk kokarin da nakeyi in kwace kaina bai ma san inayi ba, shi, A tare muka fada saman mamakeken gadon dakin shi, Inda ya shiga jagwagwala ta yadda rashi yaso, Kamar wanda akaiwa tsawa naga ya sakeni ya juya da sauri gefe guda yai rub da ciki,, Yana maida numfashi guda guda, daga inda yake akwance, Da kyat na samu na tatara hankalina guri guda tare da saurin gyara gaban rigana da ya kware, Muryan Yaya Abubakar naji yana cewa ki fada mata cewa gani tafe Hannu na nasa na goge dan hawayen da ya zubo min, Nasamu su kawar Antyn saloon zaune suna kallo a dakina, Nace don Allah kuyi hakkuri na samu yana bayi ne shi yasa, Tai murmushi tace, haba ai ba komai tunda har munriga da munzo ko, ai, Ba ai wani daukan lokaci ba ya shigo dakin da sallaman shi , Suka gaisai faram faram tare da kara mashi ya mai jiki ? Fuska a daure yake cewa Alhamdullahi da sauki sosai, Tace ga matar da nake magana zata iya aikin tazo, Sai lokacin ya dubi matar ba wata tsohuwa ce ba sosai haka, Kara gaishe shi Ramatu tayi tana çewa barka da rana yallabai, Yace ina fatan zaki tsaya kiyi abinda ya kawo ki kamar yadda kikai alkawari, Don kinga aiki nan sai an,daure, ansa hakkuri a cikin sa sosai, Agina, kawar Antyn Saloon tace duk nai mata bayani sir, Yaya Abubakar yace, OK nawa ne kuka shirya da ita, ? Aginatu, tace gaskiya bamuyi wanan zancen ba tun farko iyaka dai makwabciya tace ita maigidan ta ya dade da rasuwa , Naga wahala yai mata yawa shine nace barin mata hanya tunda naga kamar yar shiyan state din kuce ita,, Yace, yanzu ke nawa ki ke ganin cewa zan baki ya fadi a kage don duk ya matsu yabar mu, kamar mai tsoron mata, Ramatu tace Alhaji duk abinda ka bani nagode Allah yasa masu albarka, Yace OK zan ganta sai muyi magana akai yana nufin wai zai gan ni sai muyi magana dashi, Daga haka yasa kai daniyar barin dakin har ya kai kofan fita sai ya dakata, Batare da ya juyo ba yace kisan cewa a tsakiyan mata uku zaki zauna sai ki kiyayye please ? Tace insha Allah zan kiyayye Alhaji nan inda aka daukeni zan tsaya da kafana,
Bayan fitan yaya Abubakar ne muka kwasa zuwa dakin sadiya gaba dayan mu mu uku, Barci takeyi tun dazu nan nafara yiwa bakuwar mu Ramatu bayani abinda zata dinga yi, Muryan mu da Sadiya taji yasa ta bude idon ta, a hankali tana kallon mu, A kusan tare mu kai mata yaya jiki tace da sauki a hankali, Tana kokarin mikewa ne nasa filo nadan gyara mata a bayan ta, Kara gaisawa sukayi nan nake ce mata ai an kawo wace zata zauna da itane saboda Maman biu bazata iya ba, Sun gaisa da Ramatu tana cewa, ok zaki ko iya yi yar uwa don kinga da wahala abin, Ramatu cikin sakin fuska tace babu damuwa yar uwa zan iya insha Allahu Allah dai ya baki lafiya, Muka karba gaba dayan mu da Ameen Ameen, Munyi Sallama da Aginatu mata mai mutunci da tausayi, Inda na karbi nomban ta da cewa duk abinda ake ciki zan kirata in sheda mata, Duk abinda mukeyi madam din gidan mu tana kallon mu sai dai bata sa baki Kamar yadda ta nuna ciwon Sadiya bai damay ta ba kuma baya gaban ta ma sam, Sai wani nan nan yanzu naga Yaya Abubakar yana yi da ita wanda hankalina baigano ko may ye dalilin hakan ba, Gashi duk dare sai naga ya shigo mata da ledan kayan fruit masu kyau, Ina so amma dayake ita yake kawai ko a kitchen nagan su cikin fridge duk son da na ke masu ban sha, Sam iyanzu babu wani shiri a tsakanina da Salawatu don duk ta dauki tsanar duniya ta samin, Idan da farko tana boyewa yanzu sam bata iya boye don ko a hanya muka hadu cikin biyu sai na samu daya, Harara ko tsuki daga gare ta, abin dariya yake bani don nasan babu yadda zatayi dani dai, Kuma ganin irin rawan kafan da yaya keyi yasani kawo ido in sa masu, Dole aiyukan gida duk da bawai naji saukin jikina bane nice dai maiyin su, Sallah na idar ina zaune gurin ban kai ga dagawa ba naji waya ta tana kara, Yaya Abubakar ne yakirani daga office murya kasa kasa yake cewa, Meenat ina fatan yau zaki karbi girkin ki tunda kinji sauki ko ? A cikin marairai cewa nace don Allah yaya kayi hakkuri bazan iya ba , Don har yanzu nakanji marana yana min ciwo time to time, Yadan tausa muryan shi yace please Meenat for Allah sake ya kuke son inyi ne please ? Nace cikin murya kamar zanyi kuka wallahi yaya bawai naji sauki bane kawai dai karfin hali nakeyi don kada a zauna da yunwa a gidan, Yace look Meena bawai shawaran ki nake nema ba command ne na baki Naji fit ya kashe wayan inda nabi wayan da kallo tankar shi nake kallo, Wahalan da nasha aranan nan ne ya fado min a rai lokaci guda, Inda na rutse idona, cikin wani irin jin zafi azuciya nasan cewa tunda har yaya ya ce hakana to ya zama wajibi in kai masa kaina daren yau in har ina son kaina da lafiya,
A haka naci gabada aiyukana batare da hankalina ya kwantaba saboda ina tunane yadda zanyi da Yaya Abubakar a daren yau, Don nasan cewa maganar gaskiya ke nan ya furta har cikin rashi, Dole nadan fara yin an abuwan shirin kwana dakin maigida kamar yadda mata keyi inda kanada kishiya ko kishiyoyi, agida, Kamar daga fara gyara dakin maigida yin yan gyare gyaren gida, sai kuma girki tare da tsala kwalliyan daren don taron maigida, Saidai duk ni yau acikin fargaba nakeyin nawa saboda yadda yanayin jikina yake, Duk abinda nakeyi yar sa idon gidan mu tana biye dani don ganin shirina, Na,gane may takeyi amma sai nai tankar ban fahince ta ba, Daga inda nake ina gyara kaya a dining table na hangota tafito a lokacin yayi daidai da time din dawowan Yaya Abubakar gida yayi, Har gaban table din da nake tafito tana wani taunan chewing gun irin na yan duniya ,
ZEEE MAKAWA YELWA🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 6⃣2⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH- ASH -SHAHEED
Daga kwance nake rigingine fuskana yana kallon Ac din dakin da ke sako min ni ima wanda ke sani cikin wani yanayi mai dadi, ga kamshi dake tashi na turaren humra, daki, Duk da Motsin da naji na shigowa dakina a lokacin, bai,sani juyawa don ganin kowaye ba, Ya iso gab da gurin da na ke, zaune a bakin gado,,, yana min wani kallo acikin mamaki, Muryan shi naji yana cewa lafiya kike kuwa yau, ? Batare da na kalle shi ba nake cewa, lafiy kalau nake, Hmmm naji yace, Kamar zai juya amma sai naji muryan shi yana cewa, Breakfast din Baba Wadda fa,? Banyi ba na bashi ansa a takaice, Saboda may ? ya tambaya cikin mamaki Nace don banice da alhakin badawa ba nagani , yau din, May kike nufi da hakan ne,? Ai bani kadai bace da alhakin wanan laluran ko Wani irin tsawa ya daka min tare da cewa Ke ni zaki gaya wa magana haka kai tsaye kina rainawa hankali ina fadi ki na fadi ke ma, Ban yi magana ba sai hawayen da idona ke fitar wa shar a lokaci guda, Ki tashi ki fita ki girka mai abinda zai karya idan ya dawo, Daga haka yasakai ya fita dakin a fusace cikin bacin rai, Ban ce komai ba sai kokarin mikewa da na keyi don zuwa kitchen din, Na jawo dan karamin gyale na na rufawa kaina tare da gyara daura zani na, Abinci lafiyayye na hada mashi tare da ni da su Anty sadiya, Nasa saura a kula don nasan cewa zuwa anjima kadan yunwa zai iya zo min, Nakai abina daki na gyara gurin da nai aikin a lokacin na juya daki na shiga wanka, Bayan na fito ina zaune a bakin mirror ina shafa mai don yanzu ba zama yin kwaliya na keyi ba, Ina kokarin zura wani dogon rigan pepper lace da akaiwa combination,da shi, Yaya Abubakar ne ya shigo dakin yana min wani kallo amma fuskan shi acikin daurewa yake, Tambaya na abincin sa saboda yana son fita, ban kai ga bashi ansa ba idon shi ya kai, ga abincin da na zuba a plate saman mirror don yasha min isaka kafin in zauna ci,, A tsatsaye yafara kai spoon abakin sa,yakai kusan sau biyar da yaci a tsatsaye don da alama sauri yakeyi a lokacin, Bayan ya aje spoon din,Ya dan juyo gurin da nake tsaye ina gyara dankwalina yana cewa, Shi zai fita amma da Baba Wadda zasu fita don akwai inda zasu tare, Murya ciki, ciki nace Yaya lokacin komawa na sokoto fa yayi, Wani kallo naga yai min na yarinyarga fa kin rainani naci gaba da cewa, Don da mun koma zamu tafi final teaching practices din mu, inha Allah, Tankar baiji may nace ba don bai ma nuna yaji din ba sai sa kai yayi yabar dakin,, abin shi Ganin uana fita baice min komai ba nabi bayan shi da kallo, Yana fita daga dakin gaba daya nasa wani irin kuka mai tsuma zuciyan mai sauraro ta, Ina cikin kukan da babu mai rarashi na sai Allah naji anshigo dakin, Yaya Abubakar ne ya dawo dakin yana cewa inzo mu gaisa da Baba wadda kafin su fita, Ganin da yai min na kifa ciki ina kuka cikin filo ya sashi tsayawa yana kallo na acikin mamaki yana cewa, May ke faruwa ne wai Meenatu ? Banyi magana ba ya kara jefo min tambaya da cewa, An maki wani abune wai don tun jiya nake ganin damuwa a fuskan ki, Nadan tsakaita kukana ina cewa ni gida kawai nake son komawa yanzu, Murmushin takaici yayi tare da cewa bazaki ba idan kuma kika matsa min karatun ma gaba daya sai ince a fasa yin sa, Don dama banga amfanin shi ba don ba dai aiki zakiyi ba balle, jin haka yasa na, Kara gumzan kukana nayi yadda zai tayar mai da hankali, Da sauri ya juya ya bar dakin hankalin shi a tashe bai iya cewa Baba Wadda komai ba sai kawai ya nufi hanyar fita waje, Shima Baba Wadda yana ganin haka ya tashi ya mara mai baya suka fita tare,,,
****** ********** ****** Labarin ciwon Anty Sadiya ya iso Birnin Kebbi ko A, take zance ya fara yawo cikin gari kala,kala, don kowa da abinda yake fadi, Wasu suce ai kishiyoyine sukai mata su suce ai sherin uwar ta ce, Ranan da mama Ladi ta samu labari hankalin ta ya tashi sosai, don kada iyayyen Sadiya suji suce ba,a dauki mataki akan ta ba, Don haka bata tsaya bata lokaci ko ina ba sai gidan Aminiyar ta Hajja, Don kada taji labarin ga mutane tace ai ba,a fada mata ba, Amma bayan zuwan ta sai tai mamaki da taji Hajja na cewa ai mai sunan malam ya bugo mata waya Amma ta fada, ma shi cewa, ai basai ta tura,kowa daga nan ba, Don a can ai,basu rasa mutane ko amma haka dai zai sa in tura mashi mutun daga nan, Wama yasan ko may ke damun ta balle adawo nan ana yadda zance kan karya, Abinda mutum baiji ba bai gani ba ya taho yace shi ya gano acan, Don haka ni banga abinda za,a ce sai an tura wata ko wani daga nan ba, Hakane inji Mama Ladi tace amma dai duk da haka da daga cikin yan uwan ta a samu wata a turata, mata can ina ga haka zai fi, Don fa ranan wuya sai naka , Hajja ta tabe baki tana cewa, haka ne amma gaskiya ni babu wanda zan tura daga nan don Ai fanin, ku, da kuma mijin ta baku rage ta da komai don haka abar zancen tura wani, saboda tana samun kula daga mijin ta ai, Tun da Mama Ladi ta gane cewa Hajja bata kaunar zancen kwata kwata yasa ta kyale wa,, Sai suka fara hiran wani abu can daba don sam bata kaunar wanan zancen, Don zancen yana tayar mata da hankali saboda bata san may zatayi ba i yanzu akai,, Haka mama ladi tai sallama da ita batare da ta gane komai ba gare ta, Ga warin hamman Dodo da ya isheta tun zaman ta,
Amma anan cikin gidan mu gidan malam tsoho sai zance ya canza da cewa, Ai sherin Hajja ce duk yadda akayi ke bibiyan don tunda har malam ya saka bakin shi ciki, zance, Zance yazowa Mama Ladi cewa ai nayi barin ciki, a kwanakin nan,, Anan Mama ta fara fitina tana zage,zage tana masifa, Ita Allah ya tsare ta, da ta hada zuri,a da zuri,an irin Baba samaila, Da kuma mahaifiyana ita dole Maisunan malam ya sako Meenatu, tun bata kara yin wani ciki ba, Yanzu shi mai suban malam har may yagani ajikin Meenatu da ya,rude shi har ya afka mata wai harda samun ciki, Aiko amanan ta ya ishi cikin ya zube don dai Allah yagani ita bazata hada da irin mu ba, Kuma wanan sherin na malan tsohone shi da yai uwa yai makarbiya harda hada aure tsakanin jikokin shi, Yakuma rasa wanda zai hada wai sai yar Samaila da na ta, Dan dama, dama dama ace a cikin diyan wa yanda suka fito ciki guda da Baba Buhari ne zata dan yarda, Dole sai Yaya Abubakar ya turoni gida kwanan nan inba haka ba zai hadu da fushin ta,