Tarko complete novel - Chapter 48
Tarko complete novel Chapter 48: Tarko complete novel Chapter 48. ****** ********** ****** Tafiya ya keyi zuwa gida malam saboda karbo wa Sadiya magani shi…
3,050 words
****** ********** ****** Tafiya ya keyi zuwa gida malam saboda karbo wa Sadiya magani shi da Baba Wadda, Wayan ce tai kara yaga ashe Mama Ladi ce ke kiran layin nashi, Sai da ya bari kiran ya tsaya kamar yadda yake mata kulun sai ya kara kiran ta, Mama bata bari sun gaisa ba tafara cewa Kai mai sunan malam shin batun ga da najiya da gaskiya na ? Yace cikin tambaya mama wane batu ke nan kika jiya ? Tace wai Aminati tasamu tagon kaya ? Kwanan nan shin ? Yace cikin dakewa hakane Mama gaskiya na yayi barin kwanan nan, Salati ya Abubakar yaji Mama ta sake a lokaci guda, Tana ewa da ka tona min asiri maisunan malam ace duk cikin zuka zukan matan ka ka rasa wace zakaiwa ciki sai waga yar ficikan yarinya, Me kagani gare ta shin ? Me zaka ganewa gurin wagga dagin bararo, Nace maza ka dawo da yarinyar nan gida kafin wani sati ya zagayo, Kajiya ko ? Shiru yayi Mama takara cewa shin kaji abinda na fada maka ko ? Najiya Mama ya bata ansa da fadar hakana, a takaice, To kadai jita nan zuwa wani sati ka turo masu ita gida su san wadda zasuyi da ita, Ya kara ansawa da fadin to Mama zanturo ta kafin lokacin, Su na kashe waya ya furzar da iska daga bakin shi yana mai dafe gefen kan shi da hannun shi guda da bai tuki dashi,, Ya ce kai, Mama ho, ba dai fitina ba Mama, don kawai ata da sabon fitina a gida, ta dawo da wanan zancen,, Baba Wadda wanda ke zaune daga gefe yace to wai ita, Maman Mariya dake cewa haka shin, may ye hujjan ta, Babu inji yaya Abubakar ya bashi ansa da cewa, kawai dai akidace ta su irin na mata, Wayan shi dake a gefe ya laluba ya na neman nomba Uncle, dina, Ya ce hello Uncle su ka gaisa a cikin mutunci da girmamawa,, Yace Uncle dama ina son don Allah a taimaka min a school din su Meenat don a bata excuse saboda tace zasu fara exam gashi kuma tana nan on medication, Uncle ya ke ce mai zai tafi school din na mu ya bin cika ya gani, inda yadda za,ayi,, Sukayi sallama acikin mutunci tare da yiwa juna fatan alheri, Baba Wadda wanda ke daga gefe ya dan murmusa ya ce kai o,o yanzu, ita maijiran dawowan Meenatu fa can gida, murmshi kawai yayi, Sun karbo maganin kamar yadda kullun ake zuwa karba , Ya tafi Baba Wadda ne don yaga wuri saboda ya dinga zuwa karba don shi baida enough time, Baba Wadda ne ke tunasar dashi zancen sadakan da malam tsoho ya cd su yi, Baba Wadda yace ina fa yin sa a wanan kauyen zaifi don ka ga acan cikin gari babu yaran da zaka bawa, Yays Abubakar yace gaskiyane Baba barin wa malam magana sai a sayo min, Shawaran Baba Wadda yai amfani sosai gurin, don yara har sunfito fiye da tsanmani saboda sun saba karban sadaka a gurin malam sun san da yana sada shiyasa da anfara cewa Ana Sadaka,,, zasu fito dayawa karba,
****** ********** ****** Sallaman Fattu naji a daidai lokacin da nike daga baya ina shanya kayan dana wanke muna, Dan saukin da na samu ita Sadiya bata amfani da kaya sosai, Sai godiya take min a lokacin da nashiga kwasan kayan wankin nata a dakin ta, Nawa na fara wankewa na shanya sai na fara nata na shaya a daidai wanan lokacin ne Fattu suka shigo gidan ita da Antyn Saloon, Da murna na tare su muka shiga ta falo don zuwa part dina, Salawatu tana zaune a falo tana kallon wani tashan wakoki ata faman raye raye a cikin sa, Da mamaki take kallon Anty mai Saloon don batai tsan manin cewa nasan irin ta ba, Natura kofan dakina da na sakaya lokacin da zan fita zuwa backyard gurin wanki, Sai kamshin dadi ke tashi tare da sanyin Ac daya gauraye dakin ,gwanin ban sha,awa, Ga dakin ta ko ina yasha gyara da daukan idi sai kyali yake yi, Bayan sun zauna na nufi kitchen don in hado masu drinks din sha, Cikin wani tiren silver mai ruwan golden na zuba hade da ruwa da cup,,, Ina direwa naji Antyn Saloon tana cewa yanzu ita wanan ce kishiyar kaunata, Fattu na fadin wallahi itace Anty wanan ai zata ma iya haihuwan ki Sai suka sa dariya irin na wayayyon mata nidai na aje masu ina murmushi, Na samu gefe guda na zauna ina masu sannu da zuwa a cikin murmushi, Àntyn Saloon ta dubeni tana cewa, kaunata duk kin ramay wallahi, Nidai ina daga zaune sai murmushi nake sake masu, Kawar Anty ce tace to ke ko ai dole ta ramay bakin ji abinda ya faru da ita ba, Anty tace wallahi fa a kasuwa muka hadu da Fattu shine nake tambayan ki sai take sheda min , Sorry ko Allah ya kawo sabon rabo nace Ameen Anty, ya kuke ? Ya kuke ya shago da yara tai murmushi tace komai Alhamdullahi kaunata, Sannu ko Nai murmushi kawai tare da cewa Anty kusha ruwan don Allah dai Munkai wani lokaci tare da su muna fira sai nake cewa Fattu ai na kusa komawa sokoto insha Allah, Fattu tace wallahi Meenat ni ban kan so tafiyan nan naki don idan kin tafi sai gidan nan naku ya koma tankar babu kowa a cikin sa, Nai murmushi nace hai Fattu wanan ai sheri ne gida da mata biyu zaki ce ya koma tankar ba kowa acikin sa, Kedai kawai don dani kika saba shiyasa kike cewa hakan, Fattu tace Allah yasa kada Yaya ya barki ki tafi muga tsiya, Da sauri nace ba amin ba Fattu aima dole ne ya barni tunda, karatu nakeyi, Tambayana kawar Anty tayi da cewa ina dayan kishiyar tawa take, Nake ce masu aitana daki bata da lafiya, suka tausaya mata sosai sai sukace idan zasu tafi sai su gaida ita, Daga cikin sabulan da yaya yake sigo muna ban komai da su na zuba masu a leda da drinks din su da basu sha ba, Dakin Anty Sadiya muka shiga tana daga zaune tana son ta tashi tundazun ta kewaya Fattu ce ta taimaka mata shiga bayin tare da tsayawa har ta karasa, Sai na fara gyara gadon da ta tashi sudai bakin suna kallon mu daga gefe zaune, Godiya Sadiya ke muna tana kokarin zama da kyat don irin yadda take jin jiki, Dayar matar da Antyn Saloon tashigo da ita ce ke cewa may ke damun Sadiya ne, Fattu ce ta fara basu labarin abinda ya faru da ita sai inda naga zata zure in gyara mata, Sun matukar tausaya mata har suke zancen mai kishiya bata mutuwar Allah, Suna cewa ai kila sherin kishiya ce yanzun haka kila aike akayo muna ni cikina ya zube ita kuma ai mata wani sherin, Nace a,a ni cikina fada mu kayi da Salawa, lokaci guda suka hada baki suna cewa fada har ciki ya zube, Fattu aka shiga labarta masu zancen da yadda na sha wahala sosai a daren har nai zuban jini, Nace to aike Fattu jiya mun tashi yin wani nabasu labarin abinda ya faru a tsakanina da Salawa, Gaba dayan su har Sadiya suke ce min daga yau in daina bin mutun har daki don yin hakan ba daidai bane, Hakan zai iya sa komai gaskiyan mutum ya dishe saboda kamar ai takaka na kai mata, a lokacin, Ni mutun ce mai daukan shawaran naga da ni in dai har shawaran mai amfani ne, Don haka nai masu godiya nan suke bani shawaran cewa, idan na girka har ina bukatan abina to in kwashe in boye kada inbarshi a fili, Sai matar guda ke cewa amma gaskiya kamata yayi a samu wace ke kula dake sai a dinga biyan ta ina ga zaifi, Fattu yar rigima kecewa maigidan kuwa zai yarda sai matar ke cewa ai ita wallahi da zata ganshi zata bashi shawara, Tace saboda kinga wahala takeyi fa sosai a haka dubi fa tundazun take son kewayawa amma babu wanda zai taimaka mata dole tana zaune, Anty Saloon tace dagama dai sun samu Meenatu yariyan ce mai kirki da tarbiya in ba hakaba aida tuni an bare wallahi, Sukai mata sallama mukafito daga dakin Anty Sadiya don in masu rakiya, Motar Yaya Abubakar ce ta Parker sun shigo shida Baba Wadda, Fattu ke cewa su Yaya sannun ku da zuwa Yaya kamar yadda nake ce mai ita ma haka take fada mai, Su Anty Sallon suka gaidashi a cikin girmamawa, tare da mutuntawa, Daya matar da ke tare da Antyn Saloon wace ban san sunan ta ba, Take cewa maigida ashe kuma madam ba lafiya haka cikin daure fuska Yaya ya amsa mata da cewa Eh, Sai take cewa a cikin rashin damuwa, gaskiya yakamata a samo mata supporter wace zata dan dinga taimaka mata, Saboda inda ka kula abin nason wanda zai zauna a kusa da ita akoda yaushe, Ok idan har ka yarda ni zan iya samo maku mace mutumiyar kirki don ta taimaka maku, Yana tafiya batare da ya tsaya ba ya ke cewa sai najiki, yashige abinshi yabar a tsaye muna bin bayan shi da kallo,, Murmushi nayi daga gefena nake cewa hmm anty kin dai matsa saida kikai wanan zancen Tace wallahi matar tabani tausayi ne sosai shiyasa na damu, Amma ai, zai yarda idan yaga matar don tanada mutunci sosai, saboda maigidan ta ya rasa dadaewa yaran ta biyu maza amma duk suna wai Lagos a zaune suna sana,a a can, Haka mu kayi sallama dasu har Fattu wace zata shige nata gidan daga can, Ina shiga falo na samu Yaya Abubaka shi da Baba Wadda a zaune Tambaya yaya ya jefo min da cewa, a ina kika san wa yan nan matan Meenat ? Naja na tsaya fuska a dan daure nace matar da take min gyaran kaine da kafa, ansar da na bashi ke nan a takaice, Zan wuce naji yana ce bana son yawan kwashe kwashe na fada maki, Nace bani na kirasu ba yaya sun dai zo gaida ni da jiki ne, Daga haka na shige ba tare da na tsaya jin may zaice ba, Ina shiga daki na kara gyara inda su Antyn Saloon suka zauna tare da sharo dakin nawa, Yaya Abubakar ne ya shigo dakin nawa yana mai cewa baki girkawa Baba abinci bane, Na aje filon dake hannu na saman gado nace Yaya gani nayi cewa banice da girki ba don haka yasa ban yi, Ya ce look Meenat ko da baki a matsayin mata ta nai bako ashe bazaki iya bashi abinci ba , Balle kanin mahaifin mu, da yazo idan wata bata bashi abinci bake ba mai bashi bane,? Kaina yana kasa ban daga ba nace Yaya amma kasan halin Salawatu zata iya cewa, ai don may na girka abincin tunda ni ba girki nakeyi ba, Ya ce ba tace bazata iya girki ba don bata son warin girki kuma tana fama da zazzabi , Nace ban san wanan zancen ba don haka shiyasa nake taka tsantsan kada tace don may, Ok kifito ki bashi abinda zaici, ya juya yabar dakin batare da yakara cewa komai ba kuma, Dama na girka abinci na aje inda babu mai sanin cewa nayi, Don haka na gabatar masu dashi a dining table , Har yaya Abubakar sai da ya ci abincin don baici komai ba shi ma,
****** ********** ****** Washe gari ina cikin wani material lace yellow da purple din flower a jikin shi sai stones a kasan shi, Dinkin dogon rigane akai min dashi, sai na dan zauna a gaban mirror nayi simple make up, a fuska na, Na dauko takalmana na saka akafana, sai kamshi turaren shekkah ke tashi a jikina, Dakin Anty Sadiya na nufa don in gaida ita, da jiki, don tun safe ina ta aikin gyaran falon mu da yai dauda, Sai kuma girkin da na hada don karyawan jama,an gidan, Karfin hali kawai nima na keyi don jiki na sam bana jin karfin sa, Abin karin ta nadauko daga kitchen zuwa dakin ta daga kofan dakin na tsaya ina sallama inda Yaya Abubakar dake acikin dakin yai min iso, A zaune take da alaman wanka tayi, don magani na ga yana shafa mata ajikin ta, Gefen da take zaune na nufa da tire din na aje mata ina fuskan tar ta nace ina kwana Anty Ya karfin jikin ya kuma dare ,? Ta amsa a hankali idon nakai ga hannayen ta sai na ga duk sun faffashe suna dan fidda ruwa,, Magani Yaya Abubakar ke kokarin kadawa ga cup na karba na kada na nufeta dashi, Da kaina na kafa mata a baki har saida ta shanye shi gaba dayan shi sannan cire cup din ina mata sannu da jiki, Shiru mu kayi dakin gaba dayan mu ba mai cewa komai daga cikin mu, idon mu ga hannayen Anty Sadiya dake fitar ruwa, Muryan Yaya Abubakar naji yana cewa wanan matar zuwa yaushe zata turo matar da take magana a kan ta, A hankali na dan dago kaina da fuskana mai nuna damuwa na ce ban san lokaci ba gaskiya . Najuya acikin rashin walwala na bar dakin don zuwa inci gaba da abinda na keyi,, Yaya Abubakar wanda ke daga tsaye gefen gadon ya bini da idanu har na fita daga dakin, Ina fitowa Salawace na gani tana fitowa daga kitchen ta hada tea da wani leda mai katon bread a cikin sa, Kala bata ce min ba sai kokatin gittawa take a gabana, Sanin cewa gaba baida kyau yasani daurewa cikin dakiyan zuciya nace, Ina kwana ya jikin ki ? Kamar bazata ansa min ba sainaji bayan ta dan gwautani kadan tana cewa lafiya, Ta wuce tana wani irin karairaya tare da dan matse fuskan ta, gare ni, Ni dariya ma tabani sai na tuna da zaginta da Antyn Saloon tayi jiya, Ban wani dade da shiga dakina ba naji muryan a kofan dakina a na kwada min sallama, Nafito don ganin ko waye kawar Antyn Saloon ce da wata mata baka, A cikin dan sakin fuska nake cewa a, Anty kece tafe yanzu,? Sannu ku da zuwa daga nan muka shiga gaisawa da su tare da tambayan yadda suka koma jiya, Nan take ce min jiya bayan ta koma gida taje gurin matar da take magana akai , Ba,a samu wani jayayya ba ta yarda da cewa zata zo tagwada ta gani, Kawar Anty saloon tace to ki saurara da,kyau tallo, Wanan din itace muka sani kamar yadda na fada maki da farko kishiyar ta ce ba lafiya muke son ki dinga taimaka mata dan Allah, Tambaya tayi da cewa ina mara lafiyan nace tana dakin ta , Nace amma fa kin san cewa jiya sai andaure don haka don Allah kiyi hakkuri please, Tace babu komai insha Allah zata yi kokarin tun madam ce ta kawo ni, Nace to mungode barin je inga maigidan in fada mashi cewa kin iso ko,
Da sallama na tura kofan dakin yana tsaye yana daurawa hannuwan shi agogo a,hannu guda, Jin sallama na yasa shi dago kan shi ya na duba na daga inda yake tsaye, Ban karasa shiga daga dakin ba nace yaya matar ce tazo da mai aikin , Wani irin kallon ya watso min yace da karfi, ke, Zonan waye zaki tsaya daga can kina fadawa magana haka kai tsaye, Baki naturo gaba cikin nuna alaman fushi azuciya na, Dan nesa dashi kadan na tsaya ina dan kallon shi ganin irin yadda ya tsure ni da ido yasani dukar da kaina kasa, Banyi aune ba sai jin shi nayi ya rungumoni zuwa jikin shi , Kokarin kwacewa daga rikon da yai min na keyi, na ce, nika sake ni please ? Banyi aune ba sai ji nayi yana kokarin kai bakin shi a cikin nawa yana son yi min kiss, Duk kokarin da nakeyi in kwace kaina bai ma san inayi ba, shi, A tare muka fada saman mamakeken gadon dakin shi, Inda ya shiga jagwagwala ta yadda rashi yaso, Kamar wanda akaiwa tsawa naga ya sakeni ya juya da sauri gefe guda yai rub da ciki,, Yana maida numfashi guda guda, daga inda yake akwance, Da kyat na samu na tatara hankalina guri guda tare da saurin gyara gaban rigana da ya kware, Muryan Yaya Abubakar naji yana cewa ki fada mata cewa gani tafe Hannu na nasa na goge dan hawayen da ya zubo min, Nasamu su kawar Antyn saloon zaune suna kallo a dakina, Nace don Allah kuyi hakkuri na samu yana bayi ne shi yasa, Tai murmushi tace, haba ai ba komai tunda har munriga da munzo ko, ai, Ba ai wani daukan lokaci ba ya shigo dakin da sallaman shi , Suka gaisai faram faram tare da kara mashi ya mai jiki ? Fuska a daure yake cewa Alhamdullahi da sauki sosai, Tace ga matar da nake magana zata iya aikin tazo, Sai lokacin ya dubi matar ba wata tsohuwa ce ba sosai haka, Kara gaishe shi Ramatu tayi tana çewa barka da rana yallabai, Yace ina fatan zaki tsaya kiyi abinda ya kawo ki kamar yadda kikai alkawari, Don kinga aiki nan sai an,daure, ansa hakkuri a cikin sa sosai, Agina, kawar Antyn Saloon tace duk nai mata bayani sir, Yaya Abubakar yace, OK nawa ne kuka shirya da ita, ? Aginatu, tace gaskiya bamuyi wanan zancen ba tun farko iyaka dai makwabciya tace ita maigidan ta ya dade da rasuwa , Naga wahala yai mata yawa shine nace barin mata hanya tunda naga kamar yar shiyan state din kuce ita,, Yace, yanzu ke nawa ki ke ganin cewa zan baki ya fadi a kage don duk ya matsu yabar mu, kamar mai tsoron mata, Ramatu tace Alhaji duk abinda ka bani nagode Allah yasa masu albarka, Yace OK zan ganta sai muyi magana akai yana nufin wai zai gan ni sai muyi magana dashi, Daga haka yasa kai daniyar barin dakin har ya kai kofan fita sai ya dakata, Batare da ya juyo ba yace kisan cewa a tsakiyan mata uku zaki zauna sai ki kiyayye please ? Tace insha Allah zan kiyayye Alhaji nan inda aka daukeni zan tsaya da kafana,